TARIHIN SAHABBAI 001

TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI,

(manzon Allah S. A. W) “yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al’umma ta”

Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu ” usman” usman dan Amir dan Amir dan ka”abu dan sa”adu da taimu dan murratu dan ka”abu dan lu”aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka”abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya “Abdul ka” aba” daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi “Abdullahi” An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi”antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da “Atiku” shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Muhammad (S. A. W) shine yafara haduba a addinin musulunci. Shine abokin zaman kogo tare da manzon Allah na farko kuma shine nafarko cikin sahabbai goma da aka musu albishir da gidan Aljannah tun a duniya shine farkon Amirul hajji kuma yana cikin marubuta wahayin da akema Annabi Muhammad (S. A. W) An haifi Sayyidina abubakar (R. A) a makka bayan Shekara giwaye da shekaru uku (573 A. D) manzon Allah. Ya girma shi da shekaru uku. Yana cikin manyan shuwagabannin kuraishawa a lokacin jahiliya kuma a bakin manzon allah ne na kasa tun kafin aiko shi. Sau dayawa ma. Yakanje gidan shi su tattauna shine mafi sani duk larabawa game da tarihin nasabar kuraishawa. 
Kuma yakira mutane da yawa zuwa ga addinin musulunci. Biyar daga cikin su suna cikin sahabbai goma. Da aka yiwa bishara da Aljannah sune kamar haka :  
Ya sha a zaba iri – iri daga kafiran makka saboda shigar shi musulunci 
Har takai babu wani musulmai da azabtu kamar shi. Duk da irin matsananciyar azabar da suka sha suda sauran musulman farko daga kafiran makka. Bai yi kauraba zuwa kasar habasha ba. Ya tare ga manzon allah (S. A. W) lokacin kaura zuwa madina yana tare da Annabi Muhammad (S. A. W), tare suka shiga kogo kafin suwuce zuwa madina shine cukon mutane biyu da Allah ya ambata a alkur”ani in da yace : ” Idan baku taimakeshiba. ( Annabi), to ai Allah ya taimake shi yayin da kafurai suka fitar da shi ( daga makka) na biyu (mutane) biyu yayi dasuka shiga cikin kogo yake cewa da abokin shi (Abubakar)” kada kaji tsoro, Mu Hakika Allah ya na tare damu “( da taimako shi)” cikin suratul tauba:40, yayin da suka isa madina. Sayyida Abubakar, A wurin kharijatu dan zaidu. Da shi kuma manzon allah yahada su ‘yan uwantaka yayi da ya rinka hada yan’ uwantaka (ta musulunci) tsakanin mutane makka ( muhajiruna), da na madina (Ansaru) Sayyida Abubakar shine tamkar Waziri ga Annabi Muhammad (S. A. W), wajan gudanar da al’amuran daular musulunci. Mai babbar hedikwata a madina: birnin manzo,,,

Abubakar saddik ( R. A) ya dukkan yake _ yaken daukaka musulunci da yada shi da Annabi Muhammad (S. A. W) a yakin badar shine kan gaba wajan kula da wurin da manzon allah yake. Yana shir yanda yake zai gudana tare da rokon allah. har dai allah ya amsa addu’ar Annabi, ya aiko da rundunar mala”iku. Musulmai suka samu nasara. A yakin uhudu kuwa, Sayyida Abubakar. Shine jagora tsirarun Manyan sahabbai, suka gabata a filin yakin. Tare da manzon allah (S. A. W) yayin da kafurai suka tarwatsa rundunar musulmai.

Bissalam

Continue reading

ANNABI MUHAMMAD ﷺ

  • Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers
    Nasarorin Da Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Samu Cikin Shekaru Biyu, July 2020, Zuwa July 2022 Ga wasu daga cikin nasarorin… Read more: Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers
  • TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI
    ══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════ ══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════                       GABATARWA══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════                           … Read more: TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI
  • ZATIN UBANGIJI
    SHAUQI CIKIN AL AMARIN GAIBIYYA Kasantuwar Ubangiji A Buya Bai zama tawaya Ga Imanin Mai imani Sai dai Yana kara imanine… Read more: ZATIN UBANGIJI
  • GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI
    Ban Shan Sigari Ban Shan MoringaBan Shan 200 Kayan zamani Ban Leqa tagaKayan Wani bai idona Ni nai ga KatangaShiga Sha`anin… Read more: GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI
  • KUJI TAUSAYIN MARAYAN ALLAH
    Bansan me Nayi mussu baNufata da Sharri suke basu barniba Nayi kukan ZuciyaHar na Ido Hawayena Basu fad’i ba Ganinan na… Read more: KUJI TAUSAYIN MARAYAN ALLAH
  • FASAHAR ZAMANI
    Menene capacitor?  Dauki masu gudanar da wutarlantarki guda biyu (abubuwan da suka bari Wutarlantarki ta ratsa su) sai ka raba su da insulator(kayan da ba su barin wuta ya ratsa sosai) sai kayi capacitor: wani abu da zai iya adanamakamashin wutar lantarki. Kara makamashinlantarki ga mai iya aiki shi ake kira caji ; fitar dakarfin daga mai iya aiki shi aka sani dadischarging. Capacitor yana dan kama da baturiya, amma yanada wani aiki daban. Baturiya na amfani dasinadarai don adana makamashin lantarki da sake shi a hankalita hanyar zagaye; wani lokaci (a yanayin agogonkwata) zai iya daukar shekaru da dama. Mai iyaaiki yana sakin karfinsa da sauri-sau da yawa acikin sakanni ko kasa da haka. Idan kana daukanhoton flash, misali, kana bukatar kyamararka don samar da babban burst na haskea cikin fraction na sakan daya. Wani mai iko daaka hađe da bindigogin flash na ‘yan sakanni taamfani da makamashi daga batirin kyamararka.(Yana daukar lokaci kafin caji capacitor shi yasayawanoci dole ka jira kadan.) Da zarar an caji maikarfin, zai iya sakin duk karfin nan take ta hanyarxenon flash bulb. Zap! What is a capacitor?Take two electrical conductors (things that letelectricity flow through them) and separate… Read more: FASAHAR ZAMANI

Kanun bayannai

  • Nasabar Sa
  • Iyayen Sa
  • Haihuwar Sa
  •  Aiko Shi
  •  Hijirar Sa zuwa Madina
  •  Yaƙoƙinsa
  • Matan Sa
  • Yayayen Sa
  •  Masu yi masa hidima na musamman

 Muhammad  Annabi ne kuma Manzo ne wato ma’aikin Allah Madaukakin Sarki. Allah Ya aiko shi domin ya tabbatar da addinin da Annabawan da suka gabace shi suka koyar, Kamar Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Annabi Isah da dukkannin sauran Annabawan Allah (tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gare su) Annabi Muhammad (s.a.w) shine cikamakon Annabawa, wato Annabin karshe wanda daga kansa babu wani annabin Allah. Dukkan wanda yayi ikirarin annabta bayan zuwan Annabi Muhammad (s.a.w) to karya yake. Shine kuma ya hada kan dukkan larabawa suka dunkule waje daya, tare da daidaita yan adam ta hanyar koyarwar sa da Alkue’anin da yazo da shi.   

Nasabar Sa

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗɗalibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam. Manzon Allah ne. Khataman-Nabiyyin da addinin Musulunci. 

Iyayen Sa

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) ‘yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abu-Qasim, Abu Ibrahim. 

Laƙabinsa:

Al-Musɗafa (zababben Allah) yana da sunaye da suka zo a cikin Ƙur’ani Mai Girma kamar, Khataman-Nabiyyin, da Al-Ummi da Al-Muzzammil da Al-Muddassir da An-Nazir da Al-Mubin da Al-Karim da An-Nur da An-Niˁima da Ar-Rahma da Al-ˁAbdu da Ar-Ra’uf da Ar-Rahim da Ash-Shahid da Al-Mubasshir da An-Nazir da Ad-Da’i da sauransu. 

Haihuwar Sa

An haifi Annabi Muhammad (s.a.w) a wajen shekara ta 570Miladiyya. Mahaifinsa shine Abdullahi ya rasu kafin haihuwar Sa. Mahaifiyar sa Amina itama ta rasu lokacin da yake dan shekara shida a [[duniya]. Haka yasa kakan sa Abdul-Mudallib ya rike shi har zuwa lokacin daya rasu, lokacin Annabi Muhammad (s.a.w) yana dan shekara takwas a duniya. Daga nan sai kawun sa Abu-Talib yaci gaba da rikon sa. Abu-Talib ya taimaka ma Manzon Allah (s.a.w) sosai a rayuwar sa. 

Aiko Shi 

Kogon Hira, wajen da aka fara wa Annabi WahayiAikoshi: An aiko shi a Makkah 27 Rajab yana ɗan shekara arba’in. Koyarwarsa Ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan-uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.

 Mu’ujizozinsa

 Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Ƙur’ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa. Kiransa Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makkah a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. 

Hijirar Sa zuwa Madina

Bayan Tsanani da takurawar Kafuran Makkah akan Annabi Muhammad (s.a.w) da wadanda sukayi inami da shi yayi yawa, sai Allah Yayi ma Manzon Sa da sauran Wadan da sukayi imani da shi izinin akan suyi kaura daga garinsu na haihuwa wato birnin Makka zuwa wani garin daban na wati Madina. Mutanen birnin Madina kuwa sunyi matukar murna da zuwan sa garin su kuma sun bashi kyakkyawan masauki. Sanna kuma sukayi imani dashi suka shiga AddiMusulunci. A farkon Hijira dai Shi Annabi da kansa dakuma babban aminin sa kuma na farko wajen imani dashi wato Sayyadina Abubakar Sukayi tasu hijirar tare. Sannan sauran musulmai sukayi ta bin bayansu daya bayan daya. Kaurar Annabi (s.a.w) daga Makka zuwa Madina shine ake kira Hijira kuma shine farkon kalandar Musulunci. 

Yaƙoƙinsa

Inaso Mai Karatu Yayi haquri, Wannan Babi Zamu daukeshi amatsayin Darasinmu na Gaba

إن شاء الله 

Matan Sa

Annabin Musulunci Muhammad Ya auri mata goma sha daya, ga Jerin sunayen su. 

  • Khadijah(Kubura ‘yar kuwailadu)
  • Saudat
  • A’ishah(‘yar Abubakar )
  • Hafsah(‘yar Umar)
  • Zainab(‘yar Kuzaimata)
  • hindatu(ummu salama)
  • Zainab(‘yar jahshin)
  • juwairiyya
  • ramlat
  • safiyya
  • maimunah

Yayayen Sa

Ammominsa: Tara ne, su ‘ya’yan ˁAbdul-Muɗɗalib ne: Al-Haris da Zubair da Abu Ɗalib da Hamza da Al-Ghaidaq da Dirar Al-Muqawwam da Abu Lahab da ˁAbbass. Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Aminah da Ummu Hakima da Barra da Atiqa da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirul-Mu’minina Ali ɗan Abi Ɗalib (a.s) da Hasan ɗan ˁAli da Hussain ɗan ˁAli da ˁAliyyu ɗan Husaini da Muhammad ɗan ˁAli da Jaˁfar ɗan Muhammad da Musa ɗan Jaˁfar da ˁAli ɗan Musa da Muhammad ɗan ˁAli da ˁAli ɗan Muhammad da Alhassan ɗan ˁAli da Muhammad ɗan Hassan Mahadi (a.s). 

Masu yi masa hidima na musamman

Mai tsaron ƙofarsa: Anas ɗan Malik. Mawaƙinsa: Hassan ɗan Sabit, da ˁAbdullahi ɗan Rawahata, da Ka’abu ɗan Malik. Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da ˁAbdullahi ɗan Ummu Maktum da Saˁad Al-Kirdi. Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah! Tsawon rayuwarsa: shekaru 63. Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23. Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H. 

Wajan da ya yi wafati: Madinah.

 Inda aka binne shi: Madinah a Masallaci Maɗaukaki Mai Alfarma. Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne ƙarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari’arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kaɗai ce shari’ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa ƙarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaɗai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ɗaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W): Shi ne Muhammad ɗan ˁAbdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu ‘yar Wahab. An haife shi a Makkah ranar juma’a goma sha bakwai ga watan Rabi’ul awwal bayan ɓollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa). 

Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)

 An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana ɗan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makkah ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaƙi . Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makkah a lokcin akwai jama’a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saƙon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: “Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta” . A lokacin tunda mutanen Makkah mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riƙa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa’adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: “Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni” . Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane ƙalilan, na farkonsu Imam ˁAli sannan sai matarsa Khadijah (A.S) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S). Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madinah wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya daɗu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari’arsa Mai Sauƙi Mai Hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madinah har suka fi dukkan duniya da addini na sama da waɗanda ba na sama ba. Kuma an samu yaƙoƙi masu yawa a Madinah kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga maƙiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zaɓar ɓangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waɗanda ake kashewa daga ɓangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaƙoƙinsa tamanin da wani abu, wato; waɗanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu ba. Mutuwa Mai Zafin Gaske Tun lokacin da aka aiko Annabi da saƙo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Ƙur’ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a haɗa shi kamar yadda yake a yau ɗin nan. Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu’amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.

Continue reading

NASIHOHIN RAYUWAR

IDAN KAJI TSORON ALLAH ZAI BAKA MAFITA.

Hausawa suka ce bin Allah maganin wayyo Allah, tabbas hakane, lallai idan mutum yabi Allah kuma yaji tsoron sa, ya bauta masa, ya kuma kaucewa saɓa masa, to haƙiƙa bazai koka ba, kuma lallai Allah zai sanya masa hanya madaidaiciya wacce zai bita ɗoɗar ba tareda ya karkace ba”

“A rayuwar ka idan ka kasance mai yawan jin tsoron Allah abisa dukkanin ilahirin lamuranka, to lallai Allah ɗin zai baka mafita daga dukkanin wani ƙunci, bala’i da masifu, kuma zai azurta ka ta hanyoyi mabanbanta waɗanda baka san su bama, amma sharaɗin ɗaya ne, shine sai kaji tsoron Allah kuma ka guji dukkanin nau’ukan saɓon Allah”

Allah ta’ala yace: Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (yaji tsoron Allah) Allah zai sanya masa mafita. () Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma’ishinsa. Lallai Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama’auni ga dukan kõme.
aT-Talaaq 2-3

HAKIKA AN TAUYE HAKKIN AL’UMMAR AREWA

Ma’aikatar cikin gida (Ministry of Interio) karkashin jagorancin Minista Ra’uf Aregbesola ta fitar da sakamo na jahohin Nigeria matasa wadanda suka samu nasaran daukar su aiki domin cike gurbi a hukumomin tsaro na Civil Defence, Correctional, Fire Service da Immigration
Amma a cikin wannan sakamon an cuci yankin jihohin Arewa, an danne musu hakkinsu, kashi 99 cikin 100 na wadanda aka daukesu aikin daga Inyamurai ne sai Yarbawa, tsakani da Allah me ya kawo Sunan Ikechukwu jihar Jigawa?
Kuma a haka wakilan Arewa zasu zuba ido ba zasuyi magana ba?
Wato an mayar da ‘yan Arewa saniyar ware, an mayar damu marassa amfani kawai, amfanin ‘yan Arewa sai lokacin zabe yayi azo neman kuri’ah ana watsa mana hatsi daga cikin mota kamar kaji muna caccaka
Mu dai Arewa an barmu da yiwa juna hassada da kyashi da munafurci, mutanen kudu sun mayar da hankali wajen kokarin gina ‘yan uwan su, sun mamaye dukkan ma’aikatu dake babban birnin tarayya Abuja, har a cikin jihohin Arewa inda ya kamata a ga sunan Hausawa sai dai aga sunan Inyamuri, saboda sun fimu hadin kai da son juna ba tare da nuna banbanci ba
Wannan babban kalubale ne wa Ministocin Nigeria ‘yan Arewa, ya kamata ku dauki darasi da abinda Ma’aikatar cikin gida tayi, ku dena nuna tsoro ko shakkar masu zagi da suka, tabbas kuma zaku iya yin abinda Minista Ra’uf Aregbesola yayi a ma’aikatunku idan an tashi diban aiki, shugaba Muhammadu Buhari yayi iya bakin kokarinsa da ya baku mukami, saura kuyi abinda ya dace
Allah Ka taimaki Arewa da ‘yan Arewa Amin

HADIN KANMU HANYAR TSIRARMU

💾📱📚

Ismail Hussaini Alpholtawy

  Rayuwa ta ishemu Wa’azi
Malamai kuji tsoron Allah wajen Karantarwa kada kusa Son Zuciya. Domin tsira da mutuncinku aduniya da tsira da imani aran Qiyama

Dalibai muji tsoron Allah, Mufahimci junananmu Yayin Sa’bani, Kada Muce komai Malam  wane yafada Gaskiya ce, Binciken Yafi Sauraron Mu yawa.

Muyi riko da Tsarin Allah Mugirmama junan mu kada Murarraba, Rabuwa A Al’uma fitinace, Yawan jayayya yanasanya Masu Son zuciya yad’a ‘Barna kuma yakan sa Wasu gaba da juna Bisa Rashin Dalili.

Mukula Da amanar junan mu gun jaddada Sa’bani, Muyawaita zantawa da juna domin warware Sa’bani mukula da Wadanda ke son tada fitina a Addini Sud’in wawayene kuma jahilai, danganeda Harkokin Addini Basusan komai ba Sai musu da Cinzarafin Malamai.

Akowace aqeeda akan iya Samun masu mummunar manufa da Kuma Son zuciya. Babbar matsalar rayuwa Shine aiki da Jahilci, dakuma Son Zuciya.

Mu Janye Gaba da juna danganeda bambamcin aqeedah. Meyin hakan Bai fahimci addini ba Son duniya da Son zuciya Shiyake sa Mutum yakasa Barin Mummunar Aqeeda da Mummunar halaye a rayuwa da Addini.

Addinin mu yatanadar mana komai, Bamu Bukatar wata hujja idan Nassi ya inganta. Maluman mu nada da Yanzu Sun mana gata.

daga Matsala ta Kunno kai Sai mubude littafi. Idan muka Zauna Kushe littafan mu da muzantashi. Zamu wayi gari Muna Qauracewa gareshi. Har yazamto mun Halaka kamar Yahudu da Nasara.

Idan Munji gyara Muntabbata gyara ce to yazama wajibi mugyara, Kada Mutsaya Sauraron Ra’ayin Wane ko Matsayar wani Malami, Kowani ‘Dan adam ajizine, Malam Wane Ba Annabi bane Yakan iyayin Kuskure Ko Qarancin Tunani.

Addini dayace Sa’bani Sharri ce kuma fitinace, Hanyar gujemata Shine bincike da Neman Ilimi. Da Gujewa Rudin Duniya dakuma Komawa ga Allah ﷻ.

Idan kai ba malami bane kadaina katsalandan aharkar Fatawa ko Matsayar malamai, Yin hakan Shike janyo d’alibi yaraina Hatta malamin dake karantar dashi.

Malamai Su hada kansu Domin kaucewa yawan Sa’bani, Rashin Zantawa da juna shikesa malamai Sa’bani wani abinma labari kakeji daga ‘Dalibanka wani kuma Baka gama jin Kammalallen saba. Yazama dole Dole muyi Bincike.

Idan kasabawa Maluman dakake tare dasu kadauka kaine akan Kuskure, Ko baka fahimcesuba Kuma kana kyutatamasu zato amma ayimaka gamsasshiyar bayani. Amma idan Kaki kuwait Shaid`an Zai Rinjayeka Ko da akan Gaskiya kake. Domin Kurama takan Cinye Dabbar da ta Ke´bene.

Laifin Wani baya shafan wani agun mu mu ‘Yan adam, Kada Wani wanda ba aqeedarku daya ba yayi magana kayanke hukuncin Dukka aqeedar haka suke. A`a Shidai haka yake amma akwai Wasu nakirki acikinsu.

‘Dalibai Mudunga Girmama maluman mu, Munemi ilimi ba Son shaharaba. Babu amfanin ilimi idan bai zamo hanyar Tsirarmu ranar Lahiraba.

Idan wani yahalaka Sanadinka kana da Kaso cikin Sakamakon da za’a Qaddamar masa.

Idan Hasashen Mutane gaskiyace! Tabbas akwai wadanda ke kar’bo kwangila domin ‘Bata Addini. Amma kuskurene muyi Jam’i, Dole akwai wadanda da gaske suke Kuma Sunada yaqinin Tabbatuwar su akan Gaskiya Suke.

Dole ne Mu martaba Magabatan mu, Idan Munga kuskurensu mu nema masu gafara. Mudaina Tonan Silili ga ‘Yan uwanmu, Idan za’ayi tonon silili wa kowa Babu mai tsira Gaban Allah.

Munbar koyarwar addini, Mundauki Al’adar yahudawa, Amaganganun Mu komai yazo furtawa Muke babu Tantancewa. Muna da Laifi amma hangen na wasu yahanamu neman Afuwar Namu.

Muyo ‘Da’ah Cikin umarnin Annabi nadaga abinda yazo cikin Alqur’ani da Hadisi, Muhanu daga abinda ya tsawatar, Mubautawa Allah cikin Koyarwarsa ﷺ.

Kada mu yarda da Munanan kalaman da ake furtawa ga Sahabbansa رضی الله عنهم ورضو عنه, Hakan zai iya taba darajarsa ﷺ, Mud’auka Cewa Ma’kiya addinine Suke Kokarin raba kawunan mu.

Inmunga Matsala a Alaqarmu ta Aqeeda Muzauna Muwarware mukoma ga Allah musamu mafita. Na tabbata rayuwar mu zata Sauya.

Bissalam Nine naku Ismail Hussaini Alpholtawy

***SA’KON FA’DAKARWA GA AL’UMAR MUSULMI ****

      **lokaci yaquremana** 

     Idan Har a kullum zamu dinga Nisantar Wa’azine dan ana fad’an abinda Yasha Bamban da Ra’ayinmu to Tabbas Zamu Rinqa Nesantar Haske muna Tutsa kanmu cikin Duhun Jahilci, da kafirci,

     Idan Har Sai abinda yayi daidai da Da Ra’ayoyin Mutane Za a Ayyadar aduniya, Tabbas da Wuta ba ayitaba Sai Aljannah inkuwa anyisuma Ko da anzo Duniya babu mai bin Allah.

    Yawancin Mutane Tunatarwa takan Zakke Musu, yayinda Suka tuno da Me zasu tarar a Filin hisabi, Sai imaninsu ga Allah yaqaru, Inkuwa ankoma Shagalin Duniya Kuwa, Allah ma Wasu mantawa suke da Wujudinsa.

   Idan har Zamuce Wai dan Malami yafadi Sabanin Ra’ayin mu, yazamo mutumin banza to Tabbas imani a azuciyar mu zatai wahalar dasuwa. Domin ayyukanmu munana sunfi Yawa, Sukuma Malamai burinsa mu rage.

    Bai zamo dole ace wai Dukkan abinda Zuciya ta natsu dashi yazama Alkhairiba Iyakar Allah shine abinda yahana, koman Jahilcin Dan Adam, daga yashigo Da’irar Allah ta Haramci, na abinda yaqetare iyaka, Yasanta Saidai ya zakkemata domin Son zuciyarsa.

    Kamar Kid’a ma aiya haramta amma muna Saurara kuma yanayi mana dadin ji. Ammafa haramunne. Kuma ma na sanyamu Shagala da Barin Aikin Alkhairi.
   
    Kowani dadi inhar zai hanamu, ko ya nesantamu da jin dadin Lahira Allah kamusanya mana Shi da Mafi alkhairi, Kaine masanin Sirrin asirin Sansanin Sararin Sababin Alkhairan Duniya da Qiyama.

    Mun manta da Yunqurin Shaid’anu akanmu, Muyi nazarin hakan cikin Rayuwa: Sau dadama abinda Allah yahanemu
Zuciyar mu tafison Mu’aikata, Bisa Rud’i da Rinjayar Shed’anun duniya.

      Bai zamo Lallai ba ace; ko Wani abinda Yayi mana dadi Yazama shine halal ba, Tabbas Halal shine abinda yazamo akwai yardar ubangiji acikinsa Babu Shakku bare kokonto.

      Yawan Fad’a da gaskiya yanasa Qeqashewar zuciya, Tabbas idan kaji Gaskiya koda abakin Abokin gabankane, yi kokari ka Kar’beta amatsayinta na Gaskiya, Inkuwa kaqita kuma kana so ka mayar da ita abin ‘kyama, to Tabbas  Zaka Sha Mamakin duniya, Domin Sunan Allah kake yaqa wato Al_Haqqu.

     Ai kuwa dama zaka Qaryata Gaskiyar MA ayarjemaka bisa yadda kake da iko cikin mutane, daga baya Idan gaskiya tabayyana zakasha Kunya, Idan ma Allah yasoka da Shiryuwa ne Saika gyara, inkuwa bakada da rabon haka, Kamutu Ayimaka Hisabi na ‘Batar da Mutane dakuma Aikata Mummunar aiki.

   Dama habaicinnan damuke yawanyi wa juna, da Zagin Juna A Social Media, Amatsayin Sa’banin Ra’ayi ko aqeeda, Da ayoyin Qur’ani muke yad’awa haka da babu ayar da zaka Duba baka Sametaba a Internet. Ko Hadisan Annabi.

     Muyi Tarayya daku wajen yada ilimi na Addinin Musulunci musamu lada sa’bani bazai ta’ba qarewaba A Addini matukar zamu dawwama cikin yiwa juna Raddi da Jahilci. Muyawaita yiwa junar mu NASIHA.

   Wai ko Munmanta da Cewar mu Musulmai ne, Akwai Ranar fa dazata zo Zamuyi Kewar inama adawo damu Duniya Muyi koda Tasbihi guda dayane Mumutu, Dakuwa Munso hakan. Amma babu dama ankulle kofar Nadama da Aiki, Sakamako kawai ake ba Qaqqautawa.

  Kamar Misalin Jarabawar Duniya ce; Sai Ranar raba Result Saikace Ka manta Maths da English baka Baka karasa Amsaba abaka dama kaje ka gyara aikuwa lokaci kam yakure.

    Allah ka Albarkanci Rayuwar mu da ayyukan Nagarta Dakuma zuciya mai imani da dawwama a imani Har mu samu Rabo Aranar Sakamako. Allah kajikan iyayenmu matattu.

    Naraye Allah ka qara Masu Lafiya da imani da Tabbatuwa Akan imanin Har Mu samu rabo na Lahira Mu dasu Muyi Tarayya cikin Samun  kyakkyawan Sakamako anan duniya da Gobe Qiyama.

** KYAWUN FATANA GA AL’UMAR MUSULMI**

    Nayi nazari cikin tsarin Rayuwar Malumanmu na Musulunci, acikin Kyautata zatona danayi Garesu da kyakkyawan Fata sai na hango Maluman mu na Najeriya acikin Da’irar Son Ma’ki da kishin Sahabbansa da Iyalan gidansa

   Inada Lissafin yatiqe dai Munrabene Cikin aqidu Domin Nuna Kishi ahalarar Soyayya
Tayadda ‘Dariqu Suke jaddada So da Girmama waliyyai da Shehunai da Sharifai da Sufaye Domin kasancewarsu Masoya kuma dangi Jinin Fadima Yar Ma’aiki

Sukuwa Ahlussunnah kishinasu ya Ta’allaqane Akan Hidimtawa wa Da’irar Ibada bisa Tafarkin Sunnah da gyara Ibadoji da kiyaye hakkin Annabi da Alqur’ani da Kore Shubuha a Addini

Haka masu jaddada kishin Ahlulbaiti (Ahlul Kusa’i) Suma dai Soyayyace Ragamar su cikin Nuna Hidimtawa wa Sayyada Fadima ‘Yar Ma’ki da Zuri’ar Gidanta Abangaren Sayyadina Ali Allah yakaramasa Yarda

Tabbas gida d’aya Muke karkashin inuwa guda Muke, Matsalar da faruwa acikinmu itace wasunmu na aiki da Jahilci da kuma Son zuciya bisa Siyasar Masu Neman Duniya da gurbata Addini. Masha Allah, Malamai na ya’kar tsarin da salon tsarin Tabbatar da Sunnah gami da kore  Shubuha da qarfafa Shari’ar Musulunci, Muma muzamto wakilan Musulunci kada musanya ido haka kurum muna kallonsu Kamar Telabijin, Ayi muji dadi dan anyi Nasara Akan Ma’kiya Muyi dariya,
    Idan an kore Kazantar wasu To mu abinda yakamata Muyi shine ina datti yake ajikinmu muma Muyi kokari mu wanke, Dan kuwa Malumanmu Tabbas zasu Shud’e kuma Duniya na kara Gur’bata ga kuma Mummunar nufin Yahudawa da Nasara. Muyi Kokarin gyarawa kuma mu ankarar da juna danganeda Zamantakewa da Ibadoji.
  Tabbas Malamai gatarin sarane agaremu kuma tsanin hawane mai qarfi bisa haryar tsira da Digar tono asiran ma’bb’bugar Alkhairai. Inhar mukayi sakaci suka Shud’e bamuda Masu maye Guraben su Tabbas Munyi Kuskure Mafi girma, Ina mukeda yaqinin Tabbatuwa, Yaushe Za’amaimaita Kamarsu Sheikh Ismail Idris da Kuma Ja’afar da Albani.
   Ya za’ayi Duniya tamance da ginshiqannanan namu watau Khulafa’Urrashidun, Ina za’ayi jagorori Kamarsu wadanda burinsu Kullum cigaban Addini. Akwai ire_irensu Wadanda ban ambata ba Ammafa Sun Shud’e Wadanda sukayi hidima ajanibin Ma’aiki da Halarar Tsaftace Al’uma daga Jahilci da Duhun kafirci.
    Saidai kuwa Jimamin mu Kullum Shine; Gamu karkashin inuwar Rumfa guda amma Wasu na Kokarin Jijjige rumfar ga barazanar Abokan Gaban dake tunkaran mu, hakan na faruwane ta silar Wasu wawayen cikin mu da bisa Siyasar Masu Son zuciya da marasa hankalinmu.
  
  ** Mecece mafita?**
   Mafita agaremu Shine komawa ga Allah dakuma hadin kai wajen aikin Alkhairi da ya’da Addini da bawa Addinin kariya takowace ‘Bangare tareda aiki da ilimi wajen da Yad’a ilimin, Malami kuwa Yatsaya amatsayin na Fannin dayasani. Allah ne Masanin komai, Bai aikin Musulmi bane Yanke hukunci da Jahilci ko Son zuciya.
    Wani Tunani dake Zuwa cikin zuciyata Mai cikeda mamaki gamida Amsarta, Itace;

     Anya Kiristoci? Yaya Sukeji ko kallon Al’amuran mu na yawan Sa’bani?
   Kwatsam Saina amsa da cewa, Ai mu Munada yaqinin munakan Gaskiya Saidai binta yayi mana wahala bisa Rinjayar Shed’anu da kuma kasawa ta Dan Adam. Su kuwa kullum wa Duniya kadai Sukewa hidima, Sunbar Addininsu ba tsari Matansu Na fita yawo tsirara ba Mutunci Kamar rayuwar dabbobi, Mukuma Kullum burinmu Ya’kar Irin Wadannan tsarikan mukeyi, Mamakin danake garesu Kullum Shine Rashin Kulawa dasukewa ‘Ya’yansu dasukeyi Shigar banza Kamar Basu da Addini Na Tabbata Addinin Kiristanci bai karantar da hakan ba.

**Godiyar mu ga Allah Musulmi **
Addinin mu yagamamana komai kuma mun riski ilimi da Dukkan wata falalar rayuwa da Tsarin Zamantakewa da ingantacciyar Rayuwa da tarbiyya dukkan mai akasin Kyawun hali da dabi’u tabbas yakauce ne wa koyarwar addini.

**Kira ga Dalibai matasa**

          Yan uwana Matasa Dalibai!!! Murabu da malamai Abangaren wa’azantarwarsu Muzauna amajalisi akoyar damu Ibadoji da Tsaftace Rayuwa gamida tarihohin Shiryarwa Mugujewa Shagalar Rayuwa da rudin Duniya Munemi halali kurum akasuwancinmu.
    Mukuma tayasu wajen Yad’a karatuttuka a Social Media tahanyar Recording and Sharing Audio da Video da Pictures quotes gamida Rubuce Nasihohi da Wallafa manhajoji da Websites  da Rubuta Text wa ‘Yan uwa da abokan Arziqi. Domin sanya ilimin Addini cikin duniyar Network da yaqar Shubuhar mutane da wautarsu na Zagin Malamai da Hauka.
    Sannan hakan zaisanya Mu tanadar babban Guziri wa Yan baya, Domin kada Su iske bamu bar musu kyakkyawan koyiba Sai tarin Shubuha gamida Sa’bani, hakan zaisa Masu raunin imani acikinsu Kokonta cikin imani dama Shakku a Addini matukar Basu tarar da abinda zai Qarfafesu na matsaya gudaba Abin koyi. Ya Allah Kaqaramana imani da Ikhlasi da Tabbatuwa Akan imanin Harmu sameka muna Sallamawa gareka Allah karabamu Da Riya da Son zuciya.
  Allah kajikan Magabatan mu Mukuwa Allah kabamu Shahada.