Ban Shan Sigari Ban Shan Moringa Ban Shan 200 Kayan zamani Ban Leqa taga Kayan Wani bai idona Ni nai ga Katanga Shiga Sha`anin Wani banayi Cikin Garinga Bana da Abokin Hamayya koda A Singa Ni Ba Alfaharifa Nake Ba Sunce Banda Siga Kawai Dan Bana Kula Mai haukar Marashin Balaga Burina tarayya Damai Son Mutane ko a Daga Komai Wuya Bai mantawa da Allah Garinga
Buwayi Jallah ne Yatsareni ga Dukkan Wauta Shi ya Nufa Bana Daukan kayan wani Sata Kuma Ya Horemin Baiwar Neman Azurta Cikin Tsafta da Ilimi Babu Son Zuciyata Meyakai Hakan Rabone ga Tambayata
Ga baiwa Basira nasam rabauta Shin Wazai Samu Ilimi Kamata Yakuma Tsarkaka ba Tozarta DaSanin Falsafar duniyata Cikin Nema Ba Qazanta Kuma Yasan Hanyoyin Rabauta Amma Dan Gudun Duniyata Naki Duba Nai Nazarta Da kyawun hali Ba Mugunta Mutan Gari Na nufata da Cuta Na Bisu da Kyawun Hali Mai tsafta Kullum Cikin dare Har Safiyata Bana Nufin Sharri dan Gabata
Matukar Jallah Yarubuta Zan Azurta Ina Ruwana damai Duban Duniyata Yai ta Qunci Cikin rai karya Huta Yaitayi Dan Shine Zai Qaranta Bamai Hanawa Koda da Cuta
Zasu barni In wala har na Huta Duk Rintsi nafada Zan Azurta Indai Buwayine ya Qadarta Dan Shike Ayyada Qaddarata
Cikin Mafarki Wallahi Cikin Mafarki Naganta tana ta Raki Tana fadin wai Nayi karatu Najita Nabada Maki Ahakan fa Nabata Maki na Sota Taminni Kirki Asalinta Naduba nayi Nazarta So ne da Ba Raki Asalin Furuci yasaka Nai Zumunta
Muryarta da Dad`i Dana jishi Yasanya Na ´Dimauta Nayi Matta Gargad`i Abokina Nura Yagoyan Baya Gareta Abin yasakani Zumud`i Wallahi Da Murmushi fa Afuskarta Dahakan naji Dad`i Furucinta da Sanyi Nayi Nazarta
Zanen Zabo Da Shi Aka ganta Kukan Kura Jawabi Najigata Ra`ayin wani Babu Ni acikinta Burina In Tabbatar da Halinta Intana da Kirki Ni Zan Sota Dama Na Ganta azahiri na Ganinta Sannan Nafurta Abinnan na Huta Na Kalmar Soyayya Zan Kirata Sanna Nabita Da Furicin Qaunata
Na Yarda tana da Halin Kwarai Domin na jita Garai Garai Sannan Siffanta Sarai Sarai Ba Mai Kinta Idan da Rai Girma Zan Bata Cikin Tirai Zafin Qaunarta idan da Rai Zai Bi Jikina ya Yata´b´ba Rai
Ban Shan Sigari Ban Shan MoringaBan Shan 200 Kayan zamani Ban Leqa tagaKayan Wani bai idona Ni nai ga KatangaShiga Sha`anin… Read more: GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI
Menene capacitor? Dauki masu gudanar da wutarlantarki guda biyu (abubuwan da suka bari Wutarlantarki ta ratsa su) sai ka raba su da insulator(kayan da ba su barin wuta ya ratsa sosai) sai kayi capacitor: wani abu da zai iya adanamakamashin wutar lantarki. Kara makamashinlantarki ga mai iya aiki shi ake kira caji ; fitar dakarfin daga mai iya aiki shi aka sani dadischarging. Capacitor yana dan kama da baturiya, amma yanada wani aiki daban. Baturiya na amfani dasinadarai don adana makamashin lantarki da sake shi a hankalita hanyar zagaye; wani lokaci (a yanayin agogonkwata) zai iya daukar shekaru da dama. Mai iyaaiki yana sakin karfinsa da sauri-sau da yawa acikin sakanni ko kasa da haka. Idan kana daukanhoton flash, misali, kana bukatar kyamararka don samar da babban burst na haskea cikin fraction na sakan daya. Wani mai iko daaka hađe da bindigogin flash na ‘yan sakanni taamfani da makamashi daga batirin kyamararka.(Yana daukar lokaci kafin caji capacitor shi yasayawanoci dole ka jira kadan.) Da zarar an caji maikarfin, zai iya sakin duk karfin nan take ta hanyarxenon flash bulb. Zap! What is a capacitor?Take two electrical conductors (things that letelectricity flow through them) and separate… Read more: FASAHAR ZAMANI
Kanun bayannai
Nasabar Sa
Iyayen Sa
Haihuwar Sa
Aiko Shi
Hijirar Sa zuwa Madina
Yaƙoƙinsa
Matan Sa
Yayayen Sa
Masu yi masa hidima na musamman
Muhammad Annabi ne kuma Manzo ne wato ma’aikin Allah Madaukakin Sarki. Allah Ya aiko shi domin ya tabbatar da addinin da Annabawan da suka gabace shi suka koyar, Kamar Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Annabi Isah da dukkannin sauran Annabawan Allah (tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gare su) Annabi Muhammad (s.a.w) shine cikamakon Annabawa, wato Annabin karshe wanda daga kansa babu wani annabin Allah. Dukkan wanda yayi ikirarin annabta bayan zuwan Annabi Muhammad (s.a.w) to karya yake. Shine kuma ya hada kan dukkan larabawa suka dunkule waje daya, tare da daidaita yan adam ta hanyar koyarwar sa da Alkue’anin da yazo da shi.
Nasabar Sa
Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗɗalibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam. Manzon Allah ne. Khataman-Nabiyyin da addinin Musulunci.
Iyayen Sa
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) ‘yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abu-Qasim, Abu Ibrahim.
Laƙabinsa:
Al-Musɗafa (zababben Allah) yana da sunaye da suka zo a cikin Ƙur’ani Mai Girma kamar, Khataman-Nabiyyin, da Al-Ummi da Al-Muzzammil da Al-Muddassir da An-Nazir da Al-Mubin da Al-Karim da An-Nur da An-Niˁima da Ar-Rahma da Al-ˁAbdu da Ar-Ra’uf da Ar-Rahim da Ash-Shahid da Al-Mubasshir da An-Nazir da Ad-Da’i da sauransu.
Haihuwar Sa
An haifi Annabi Muhammad (s.a.w) a wajen shekara ta 570Miladiyya. Mahaifinsa shine Abdullahi ya rasu kafin haihuwar Sa. Mahaifiyar sa Amina itama ta rasu lokacin da yake dan shekara shida a [[duniya]. Haka yasa kakan sa Abdul-Mudallib ya rike shi har zuwa lokacin daya rasu, lokacin Annabi Muhammad (s.a.w) yana dan shekara takwas a duniya. Daga nan sai kawun sa Abu-Talib yaci gaba da rikon sa. Abu-Talib ya taimaka ma Manzon Allah (s.a.w) sosai a rayuwar sa.
Aiko Shi
Kogon Hira, wajen da aka fara wa Annabi WahayiAikoshi: An aiko shi a Makkah 27 Rajab yana ɗan shekara arba’in. Koyarwarsa Ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan-uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.
Mu’ujizozinsa
Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Ƙur’ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa. Kiransa Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makkah a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.
Hijirar Sa zuwa Madina
Bayan Tsanani da takurawar Kafuran Makkah akan Annabi Muhammad (s.a.w) da wadanda sukayi inami da shi yayi yawa, sai Allah Yayi ma Manzon Sa da sauran Wadan da sukayi imani da shi izinin akan suyi kaura daga garinsu na haihuwa wato birnin Makka zuwa wani garin daban na wati Madina. Mutanen birnin Madina kuwa sunyi matukar murna da zuwan sa garin su kuma sun bashi kyakkyawan masauki. Sanna kuma sukayi imani dashi suka shiga AddiMusulunci. A farkon Hijira dai Shi Annabi da kansa dakuma babban aminin sa kuma na farko wajen imani dashi wato Sayyadina Abubakar Sukayi tasu hijirar tare. Sannan sauran musulmai sukayi ta bin bayansu daya bayan daya. Kaurar Annabi (s.a.w) daga Makka zuwa Madina shine ake kira Hijira kuma shine farkon kalandar Musulunci.
Yaƙoƙinsa
Inaso Mai Karatu Yayi haquri, Wannan Babi Zamu daukeshi amatsayin Darasinmu na Gaba
إن شاء الله
Matan Sa
Annabin Musulunci Muhammad Ya auri mata goma sha daya, ga Jerin sunayen su.
Khadijah(Kubura ‘yar kuwailadu)
Saudat
A’ishah(‘yar Abubakar )
Hafsah(‘yar Umar)
Zainab(‘yar Kuzaimata)
hindatu(ummu salama)
Zainab(‘yar jahshin)
juwairiyya
ramlat
safiyya
maimunah
Yayayen Sa
Ammominsa: Tara ne, su ‘ya’yan ˁAbdul-Muɗɗalib ne: Al-Haris da Zubair da Abu Ɗalib da Hamza da Al-Ghaidaq da Dirar Al-Muqawwam da Abu Lahab da ˁAbbass. Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Aminah da Ummu Hakima da Barra da Atiqa da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirul-Mu’minina Ali ɗan Abi Ɗalib (a.s) da Hasan ɗan ˁAli da Hussain ɗan ˁAli da ˁAliyyu ɗan Husaini da Muhammad ɗan ˁAli da Jaˁfar ɗan Muhammad da Musa ɗan Jaˁfar da ˁAli ɗan Musa da Muhammad ɗan ˁAli da ˁAli ɗan Muhammad da Alhassan ɗan ˁAli da Muhammad ɗan Hassan Mahadi (a.s).
Masu yi masa hidima na musamman
Mai tsaron ƙofarsa: Anas ɗan Malik. Mawaƙinsa: Hassan ɗan Sabit, da ˁAbdullahi ɗan Rawahata, da Ka’abu ɗan Malik. Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da ˁAbdullahi ɗan Ummu Maktum da Saˁad Al-Kirdi. Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah! Tsawon rayuwarsa: shekaru 63. Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23. Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.
Wajan da ya yi wafati: Madinah.
Inda aka binne shi: Madinah a Masallaci Maɗaukaki Mai Alfarma. Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne ƙarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari’arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kaɗai ce shari’ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa ƙarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaɗai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ɗaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W): Shi ne Muhammad ɗan ˁAbdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu ‘yar Wahab. An haife shi a Makkah ranar juma’a goma sha bakwai ga watan Rabi’ul awwal bayan ɓollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).
An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana ɗan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makkah ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaƙi . Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makkah a lokcin akwai jama’a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saƙon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: “Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta” . A lokacin tunda mutanen Makkah mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riƙa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa’adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: “Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni” . Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane ƙalilan, na farkonsu Imam ˁAli sannan sai matarsa Khadijah (A.S) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S). Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madinah wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya daɗu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari’arsa Mai Sauƙi Mai Hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madinah har suka fi dukkan duniya da addini na sama da waɗanda ba na sama ba. Kuma an samu yaƙoƙi masu yawa a Madinah kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga maƙiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zaɓar ɓangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waɗanda ake kashewa daga ɓangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaƙoƙinsa tamanin da wani abu, wato; waɗanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu ba. Mutuwa Mai Zafin Gaske Tun lokacin da aka aiko Annabi da saƙo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Ƙur’ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a haɗa shi kamar yadda yake a yau ɗin nan. Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu’amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.
Idan Mutum Ya Hadawa Matarsa (SABAYA) Yana Da Matuqar Ta’asiri a Jikin Ya”Mace Kuma Yana Haifar Mata Da Ababe Uku a Jikinta Akwai Matar Da Idan Tana Shayarwa Zakaga Kamar Ta Fito Daga Gidan Yari Wata Jikinta Yana Zubewa Ruwan Nononta Yana Lalacewa
*Nafarko Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Zai Taimaka Wajen Dawo da Halittan Da Allah Yai Mata Jikinta Nonon Bazai Zube Ba *Na Biyu Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Jikinta Zaiyi Laushi Kamar Kwalabiya *Na Uku Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Da zarar ta Haihu Irin Ramar Da Mata Keyi Baza Tayi Ba
Kuma Ruwan Nononta Zai Qara Yawa Sannan Bazai Lalace Ba Kuma Yaron Data Haifa Allah Zai Kareshi Daga Dangin Cututtuka
Kuma Hatta Magidanci Idan Yasha Yana Qara Masa Lafiya Da Kuma Kuzari a Jikinsa
MEYA KAMATA ASAMO WAJEN HADA SABAYA TASU KAMAR HAKA: *Al Kama 1Mudu *Danyen Shinkafa 1Mudu *Waken Suya 1Mudu *Ridi ½Mudu *Hulba ½Mudu *Gyada Mai Bargo/Kamfala *Madara *Zuma
YA ZA’A HADASU SHINE: Ridi Da Gyada Ana Hadasu Wuri Guda Ridi a Soyashi Yadda Ake Kantu, Gyadar A Soyata Yadda Ake Quli Quli, Shinkafa Da Alkama Ana Jiqasu Tsawon 5hour Sai a Shanya Da Laima a Jikin Sai a Hadasu Wuri Guda
Da Ridin Da Gyadar Da Al Kama Da Hulba Da Shinkafar Sai a Niqa Matarka Tin Tana Da Ciki Ya Kamata Ka Fara Bata Har Zuwa Haihuwa Kaga Yadda Zatai Da Yaronta Kuma Nononta Dana Shayarwa Ko Bata Shayarwa Bazai Canza Ba Da Ikon Allah
TO YA AKE SHANSA Yadda Ake Dama Kunu Haka Ake Damashi Sai Dai Idan aka Zuba Ruwan Zafi Ana Iya Maidashi Kan Wuta, Sukace Karta Wuce Cokali Uku a Rana Musamman Cikin Babban Cokali Idan Kuma Harda Magidancin Sai a Sanya Cokali Shida
Su Kace Amma Idan Mace Bata Da Aure Kada Tasha Domin Yana Qara Sha’awa Kuma Yana Qara Yawan Nono Ma’ana Yafi Dacewa Da Matar Datake Shayarwa Domin Samun Ingancin Lafiyar Jikinta Don Kada Ya Zube
Kuyi Amfani Da Wannan Link Din Domin Samun Magunguna a Sauqaqe
You must be logged in to post a comment.