INGANCIN ZUQATAN BAYI

INGANCIN ZUCIYA!!! ***************************************** Hakika gyaran zuciya itace maqasudin kar´bar aiki. Da Akwai Ayoyi da hadisai ingantttu dake nuna jinjina ga ayyukan bayi amma dukkansu suna yabawane akan tsarkin zuciya domin shine (sababin karbar aikin). Hakazalika. ibadar da Allah yafisoma, ~Maqasudinsa zuciyace watau (Azumi).

Shi Azumi ALLAHﷻ (s.w.a) Shine kadai keda hakikanin gasgata maiyinsa, Saikuma Zuciyar maiyinsa, Sa`annan kuma ma ALLAHﷻ shi da kansa yake cewa yana son masu tuba damasu tsarki Ma´ana masu tsarkake zuciyoyinsu daga bari munanan ayyuka. Da ayyukan da aka kyamata. Gashinan in arabic text إن الله یحب التوابین ویحب المتطهری Manzon ALLAH ﷺyana cewa إن فی الجسد مضغة إذا صلحت صلح الجسد کله وإذا فسدة فسد الجسد کله علی وهی القلب Arufai kuyimin afuwa nai muku Shisshigi inda kuskere atusaddani. Dan Adam ajizine ALLAHﷻShine masani. dafatan anyi Juma`ah lafiya

MATAKAN TARBIYYA GUDA UKU


MATAKAN TARBIYYA
Daga. Alqalamin Ismail Smart
Dasunan ALLAH Mai RAHAMA Mai JINKAI.
Haqiqa tarbiyya dolece a addinin mu na musulunci musan man ma na iyalanka/ki
Domin ALLAH MADAUKAKI yana cewa:

یا أیهاالذین آمنو قو أنفسکم وأهلیکم نارا وقودها الناس والحجارة
        Awannan aya ALLAH yayi umarni ga Muminai dasu Kare kansu da iyalansu daga wata wutta Wanda yakasance makamashinta mutane ne dakuma duwatsu.
ALLAH UBANGIJI katsaremu amin  ya RABBI. Awannan ‘Bangaren Nakeson nayi rubutu  domin yan uwa musulmai su anfana.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI ya dafamin
MATAKIN FARKO
(Neman Aure zuwa da yakai 5yrs)
Dole Akan kowa Idan yazo neman aure
Yanemi Mai addini Da hali nagari Da kakkyawar zuciya. Ba kawai kyawun fuskaba ko wani martaba ko nasabar Abokin zama ba. Kuma yazamto anyi auren tanasonsa yana sonta.
Domin hakanne Zaisa suji dadin zamantakewarsu ta Aure Kuma hakan Zaisa yayansu sutaso dason junansu Da Bin doka ko umarnin Da akayi masu. Domin kada yazamto uwa tace fari uba yace Bahakaneba Baki yake. Bayan haka
Yazama dole asakawa yaro kakkyawar suna alokacin dayake jinjiri. Yazama dole ka karantar Da matanka tsarin tarbiyyar addinin musulunci ko kasa akarantar da ita Awannan sahar kokuma MA kafin wannnan lokacin. Ma’ana kafin ta sami d’a (yara).
Domin kaso saba’in Cikin Dari (70%) Na Tarbiyyar cikin Gida maqasudinsa na uwace. Yazama dole takasance Mai Lura da Meke gudana me sukeso me yakamata suyi ko so Bari duk wadannan uwace takeda hakkin koyar da yaranta.
Dakuma koyardasu Ibaadaat Kamar Sallah Azumi Dakuma koyamusu karatun Alqur’ani da tilawarsa dama haddarsa. Har sukai 10yrs  Kafin daga bisani Sai Aturasu  Islamiya. Sucigaba da karatu daneman ilimin addini. Hakan zaisa sutaso da ganin girman iyayansu. Dama duk wanda yagirmesu tayadda basai ance ga malam waneba kafin sudaina abinda sukeyi.
MATAKI NA BIYU
(Daga 5yrs zuwa 15 to 18yrs)
Dolene akan iyaye su San abokanan yayansu, Susan Kuma menene alaqarsu dasu Domin duk kyawun tarbiyyar dakasamu agida abokai sukan wargazashi, matsawar dakayi abota da marasa tarbiyya koda baka zama tamkarsu ba. Zaka rudu da wani hali acikin munanan halayyarsu.
Yazama dole iyaye su bawa yayansu tarbiyyar addini da wayewar rayuwa tahanyar sanaddasu yadda zasuyi addini da hikimomin tsara rayuwa bisa kykkyawar tsari. Kamar koyamusu dabarun kare kai da addu’o’in neman tsari da kariya. Da sanardasu tarihohi Wanda zasu sami hikima da, wa’azozi acikinsa. Domin abinciken masana kwakwalwar dan adam sun yarda akan cewa kwakwalwar dan adam takan bude da adana bayanai alokacin da mutum yake dan shekaru takwas (8) zuwa Sha biyar (15) koda haddane mutum yafi nutsuwa dashi awannan lokacin Inhar kaga yaro ya natsu awannan lokacin to tabbas ana kyautata zaton shiryayye ne. Inkuma ya kangare kuwa yanada wuyar shiryuwa Yakamata iyaye sudunga zama da yaransu suna zantawa dasu domin suji damuwoyi da bukatunsu, Harsu san tahanyar da zasu bullo musu gurin bada shawara ko kore musu matsalarsu tarayuwa.
MATAKI NA UKU NAKARSHE
(Daga 15/18yrs. zuwa auraddasu)
Yakamata iyaye su lura da yayansu su san menene wane/wacce tafi/yafi kwarewa akai saisu dage gurin nema masu mafita ta hanyar basu tallafi ko jari domin samun damar gudanar da harkokin rayuwarsa cikin sauki batare da yana zauneba saidai kullum abashi.
      Domin hakan yana kashe zuciyar mutum yazanto baya iya kafuwa da kansa balle ma har yagina wasu. Saidai kullum a bani_bani sai kuma bin abokai da yawace yawacen banza da hofi, da bin bangar siyasa, wadda daga karshe ke jawo mutum yakoma ta’asa da ‘barna acikin al’uma kokuma ma yakama shaye_shaye da bin mugaye mutane. Duk adalilin rashin aikin yi. ALLAH ya tsaremu da zuri’armu baki daya.
       Rashin aikinyi na daya daga cikin abubuwa mafi girma wanda suke lalata  tarbiyya arayuwar mutane.
Allah ka bawa iyayen mu hakurin zama damu kasauke musu hanyar dazasu tarbiyyantar damu tarbiyya ta Addinin musulunci, ALLAH kajikan maifina kahaskaka qabrinsa.

AHLUSSUNAH AYAU Posst No 1

MAFAKAR SUNNAH AYAU!!!

        Haqiqah Babu batun Sonkai, Salafawa da ‘yan izala sune ke da’awar sunnah Haqiqanin ta zallar madarar sunnah babu gauraye.

Dalilin wannan rubutu nawa:
Shine nuna mecece koyarwar aqeedar sunnah. Da manufar Izala da Salafawa akan sunna dakuma mecece asalin haqiqanin aqidar sunnah

  ********MECECE AQIDAH********

Aqidah:  amahangar Arufai (Malamai)_ wata hanyace wacce mutane suka kebance yadda zasu yi addini karkashin wata mazhaba bisa fahimtar magabata na farko, Bugu da kariaqidah takasance abace wacce take a aikace da furincin baka banda qudirin zuci. Ma’ana Azuci ni musulmine kuma nayarda da dukkan shika_shikan musulunci ina aikatasu amma bisa mazhabar malikiyya. To idan hakane madogarata bani da Ikon tilasta maibin mazhabar shafi’iyyah ko  ko hanafiyya. Bani damar cewa sai sunbi Hambaliyya
Idan mukayi duba danganeda yanayi nayanzu yadda rayuwa tashige rudani yadda Ake kawo abubuwa daban daban acikin addini. Dasunan addini.
Maluma na gaskiya suna iyakacin iyawarsu wajen wayar wa mutani kai dan ganeda hanyar tsira na addini, Amma saidai kuma akasi.
  Anasamun wasu miyagu da suke juya hankulan jama’ah suna b’ata Da’awar tasu.

Danganeda hakane Aka rarraba addini gida_gida aka kuma kirmiro aqidoji iri daban_daban hakika koda yahudu da nasarah suma abinda yararraba kawunansu kenan rabuwar kan maluma.

******Mafakar sunnah dai sune****
Marubuta da wa’azi da walima Wadannan sune hanyoyin da. Sunnah suke yada da’awarsu. Sabanin sufaye Shi’awa da ‘Yan dariqu. Su suna yada aqidun sune da sha’irai (mawaqa) da Majalisi dakuma Mawalid, idan akace mawaali shine jam’in maulidi.
   To A inda gizon ke saqa kuma, shine:   Akan samu sa’bani dan ganeda wasu al’amuran na Hanyoyin yada da’awoyin nasu.
Misali
  ‘Yan izala Da Salafawa sukan soki mauludi da zaman da’ira da Majalisi, dama kuma wake waken da yan dariqu sukeyi. Su kuma yan dariqu Basuda hanyar dasuke yada manufofi da da’awoyinsu sama da wadannan hanyoyi, Dan hakane suma suka sha AlwasAnfagdaura kambun yaqi da dukkannin wanda zai munantawa hanyar da’awarsu.

******Tasirin tarbiyyar aqidu******

***IZALAH SALAFAWA***

Yan izala da salafawa mafiya yawancin makarantunsu haddane da hadisai sai Tauhidi saikuma wasu littattafan addini a matakin farko kuma suna Anfanine da mashabobin makka da madina. Yawancin littattafansu wallafar can ne da sharhohin magabatansu.

***SHI’AH DA DARIQU**
Su kuma yawancinsu suna anfanine da mazhabobin iran da iraqi kuma afannin ilimin farko yawancinsu karatun tsangaya sukeyi. Sai agaba sunfi bada karfi wajen ilimin tarihi da baitoji yabo dana dafawa wannan dalilin ne ma yasa ake samun mawaka dayawa acikinsu.
*****“Nuni sananne dan gane da da’awar sunnah**””””””””
Maganar Gaskiya izala da salaf munada kyakkyawar manufa akan addinin musulunci kama daga maluman  mu dama marubutan mu dama Mu dalibai bakidaya . Burinmu  Azauna da juna lafiya da lumana.
Yan uwana masu  karatu kusani cewa manufar wannan rubutun nawa shine in bayyana mecece haqiqanin Sunnah
Kuma suwaye Ahlussunnah na gaskiya
Danhaka na rarraba rubutun kaso uku
Wannan shine nafarko agaba zakujini da wasu kamar haka:
        
           ******Haske Akansu******

### Suwaye Ahlussunnah?…………..)

Dukkan wanda yariqi sunnah ta annabi kuma yake kokarin dabbaqata kuma yake nesanta daga barna da rarraba kan al”umar musulmi.
      
                 ***Dakuma**

### *Sunnah ba Aqida bace!………….)

Ahlussunnah yana suffantuwane da kyawawan dabi’u baya neman ilimi domin muqabala ko dan.yakare aqidah ba.

BAYAN RAYUWAN DUNIYA AKWAI RAYUWA BAYAN MUTUWA

GASKIYA AKWAI MATTSALA!!!!


Sau nawa kake zama domin Bincike ko sauraron Yadda zaka gyara Ibadarka?????
         Sau dadama idan na kadaita sai nayita tunani dan ganeda lammarin gudanar addini agun wasun mu. Zakaji mutum nakiran kansa musulmi amma farillan alwala ma bai sani balle in ta ‘baci ya gyara farillan sallah ma bai saniba balle inyayi Rafkanuwa yagyara. Ko na wanka ballema ilimin gyaransu.
    Wayyoooni duniya ina zaki damune kowa kagani abinci kawai yake nema kokuma yadda zai huta ko yadda zaiji dadin duniya gaba. Saidai kash itakuma tafiyarnan da take gaban mu batta da rana. Kawai zuwa take kwatsam kara zube ba zato ba tsammani.
    To taya zamu tara guzirin komawa ga mahaliccin mu domin samun hujja garemu aranar sakamako?
    Ansa
    Mukoma munemi ilimin addini mugyara ibadu da mu’amalarmu kafinnan musami hanyar tsira. Wani abin ban takaici shine yawanci mukan jahilci lammarin addini bawai don rashinsaba sai don aqidanci. Mutum baida karatun komai jahilin kauye afagen addini amma saikaji na karyata abubuwan da malamai ke fada dan ganeda hukuncin halasci ko haramcin wani al Amarin addini. Dalili kuwa shine don aqidarsu ta banbanta, Alhali baida hujja ta aya ko hadisi data karyata al’amarin dalili kawai don malumansu basayi yan abiyari (inbasu wane bazamuyiba).
    Wannan shi ake kira da shi’anci ashari’ar musulunci ma’ana raba kan al’umar musulmi. Tahanyar sabawar fahimta ko mazhaba. Abubuwan da kejawo haka sune:
    _Jahilci
    _Son zuciya
    _Son shahara
    _Munafinci
          ***JAHILCI***
    Idan jahilci yayi naso (katutu) azuciyar mutun saikaga na karyata koma mene ne addini ni kuma in yayi shugabanci zai dinga shirme yayita kawo jahilci alammuran dasunan gyara daga karshe zaiyita kokarin fada da malamai idan suna fada masa gaskiya. Jahilci nasa girman kai da hassada matukar maishi na tare da masu ilimi kuma akayi rashin sa’ah yawuce su wata daukakaka tarayuwa.
       ***SON ZUCIYA***
Idan mutum nada son zuciya komai aka fada bazaibiba sidai yakowo tasa abi. Koda tasa hanyar me raunice zai toge yadage akan sai anbi tasa daga karshe in anki zai fara neman mabiya daga baya saikaji ya Fidda tasa sabon kungiyar daban ko juma yafandare yayi reshe akungiyarsa daban.
    ****SON SHAHARA****
    Mafiya yawanci anfi samu daga wanda suka ‘Danyi karatu amma bamai nisaba sunason taka hawa mai nisa amma kafarsu baikaiba. Burinsu dai komai zai wakana yazam anyishi harda furucinsu. Amma basuda cikakken ilimi abangaren irin wadannan ywanci akansamu masu kyakkyawar manufa amma rashin ilimi mai nisa yana wargaza manufar nasu.
    Yakai dan uwa shawarata gareka katsaya iya matsayin ka kabar abinda Bakasaniba.
    Masu hikima nacewa Bansaniba shima wani yankin ilimine.
   
      *****MUNAFINCI****
    Akwai wasu burinsu kawai azagi musulunci da musulmai. Zasu tsaya kai da fata su tabo wannan aqidan da wata ta daban, Harsu haddasa wata rigima tsakanin musulmai wadannan basuda wata kyakkyawar manufa akan musulmai wasunma bamusulmai bane burinsu su wargaza wata shiri ko wata tanadi wacce musulmai sukeyi, ko don su raba kawunan al’umar musulmi.
    Allah katsaremu daga sharrin makirai da fajiran munakan addini.
    Allah yamayar da makircin garesu dasu da wanda suke sasu.
    Allah kabudemana kwakwalenmu don gujewa afkawa rudanin addini.
    Allah  kabawa maluman mu damar isar mana da gaskiyar koyi na Addini.
   

AQEEDAH TA ITACE MUSULUNCI

AQEEDATA

Dasunan ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

      Wasallahu Alaa man Laa Nabiyya ba’adahu Muhammadun bn Abdullah .(ﷺ) Salawatullahi Alaihi, wa Alaa Aalihi wasahbihi wasallama tasliiman khasira.

Waba’ad;
Assalamu alaikum warahmatullahi warahmatullahi wabarkatuhu, Mai karatu idan baka manta ba ada nayi Alqawwarin fadawa mai karatu mecece aqedata, dakuma matsayata dangane da halascin wakokin yabo da kirari da Haramcin kida Amusulunci.

Ⓜ Mashaa ALLAH Alkawwari yacika;
     Ni Ismail Hussaini Basalafene (Assalafy) Ne. Sala ba Kungiyace ta Aikin addini bawai Shi`anci bane. Wata al umace dake aiki akan Hani ga barna dakuma umarni da aikin Alkhairi. wacce take kuma koyi da magabata. Ainihin Kalmar Salaf tana nufin Magabata.

Salagiyya kuma tana nufin Bin tafarkin magabata. Wannan itace Al umar damuke koyi dasu na kwarai din cikinsu. Amma mu musulmaine kamar Sauran musulmi. Kuma munyi imani da Alqur`ani da hadisai kuma manzon mu shine مُحَمَّد ﷺ

Shi muke kwaikwayo a hali dakuma ayyukan.
Basai nayi bayani akan ko mene aqidah ba. Domin abaya nayi bayani akai karin bayani dan ganeda aqidar salafawa shine { (Aqeedadussalafussalih bi muwafaqati Sunnatin_nabawiyya wa Ashabuhum) (Ma ana aqidar bin tafarkin annabawa da sahabbansu) }.
   Aqidar itama Ahlussunnah ce akarkashinta akwai izala kamar yadda akasani, wadda suke da manufa iri daya dan ganeda da`awa da tsarukan karantarwa iiri daya saidai ita salafiyya kuma tafi yada da awarta ta social media fiye dana izala. ma`ana tafi dukufa wajan rubuce rubucen tarihi ta hanyar wayar da kai ga addinin musulunci da musulmai bisa yadda Zamani yakasance.  Dawayar da kan mutane Dan ganeda rayuwarsu dazamantakewarsu da Ladaftar dasu da koya masu dabarun rayuwa dawayar dasu Ga addini suyishi sukuma dabbakashi dayadashi a duniya.  Dukka sune Aikin salafawa.
Kar nazurfafa atakaice wannan itace aqidata. saikuma magana akan maulidi da kasidu masu kida da da marasa kida.

WAKOKIN YABON ANNABI
Haqiqa wakokin yabon annabi babu Kida ya halasta kaidai dolene yazama duk yaren dazakayi wakan yabon annabi dashi. yazamana kana da ilimi akan yaran sosai domin kiyaye kalmomin da zakayi amfani dosu, donyin yabon kuma dolene ka koyi ilimomi aka yaran kamar haka: ilimin balaga, Qaamusu, Ka`idojin rubutu, Ilimin Grammar, Dakuma tarihim annabin dama mawakansa  nada, domin azamanin annabi  ﷺ Anyi masa waqoqi dayawa harma ayari yake dasu na mawaka Ammafa su basuyi da kida bakuma yi sukeba Dan holewarsu ba ssunayine domin maida martani wa kafirai sai kuma domin dafawa Ga fiyayyen halittaﷺ kutambayi malamai zasu baku karin bayani akai.
    To awannan zamani namu akwai mawakan dake waqoqi nayabo amma da kida ko nace kayan sauti mabanbanta. wallahi! Tallahi!! Billahillazi La ilaha illahuwa wuce gona a kayan kida sautin shaidanune!!!

Me karatu kayi shari ah ta adalci٠
Masu wakokin yabo ayanzu musan man agun maulidi shin kaso hamsin cikin dari suna tantance me suke fada kafin su fada awakokinsu? babu shakka Amsar itace a`a.
   Muyi wa kanmu adalci waqa na ilimi wanda ba kida nayabon Annabi yahalasta amusulunci, ko muma a Tafiyarmu ta salafawa munada mawaqan yabon annabi amma basuyi da kida kuma sai an karantaddasu kuma littafai suke bugawa akuma tantancesu agaban malamai kafin suje subayar ga masu hazakar furuci su rera wakokinsu ba cinzarafi da zagi ko aibata wani ko wata aqida da ace ´yan d`ariqun sufaye da ´yan Shi`ah suma zasuyi adalci wa kawunansu dasai suma su rage msu hankalin cikinsu yakamata su daina waka da kida suyi waqa tsarkakakkiya da yabo wanda yadace da tunani mai kyau da koyarwar Addinin musulunci.
 

 BIKIN MAULIDI 

Bashakka bikin Maulidi Bai ingantaba koda ahadisine mai raunine babu, ba  ko wata yarjeniya ta wata ayari namaluman sunnah danayanzu dana da duk sun daidaita akan bai ingantaba. Hasalima suna kirantane da bidi´ah muhadatha ma`ana bidi`ah kirkirarriya. Batada tushe ko asali daga magabata, akwai hadisai dayawa wadanda suke tsawatarwa danganeda kirkira a addini. Arufai na tsawatarwa danganeda kirkira a addini. Ayanzu acikin maulidi allah ﷻ Shine kawai yasan bidi`o`in da aka kirkiro.
  Banso Raba rubutun  ba amma dolene ta saka `yan uwa kuyi hakuri muhadu arubutu nagaba mai Taken Aqeedata