BAI JUYA MAKU BAYA BA!!! MU HUKUMTA JUNA BISA ADALCI

Sau dadama Wasu Zakaji Suna Korfin Cewa Wane Tun Sadda Yasami Wata Daukaka Ko Wani Cigaba ko Shugabanci, Shikenan Yamanta Damu Cikin Huldarsa Na rayuwa Da Tarayya!

Dafarko dai Shi Al amarin Cigaba Nufin Allah neﷻ,  Haka Kuma Aka Halicci Dan Adam da Rauni Na Mantuwa da Kuma Shagaltuwa da Al`amuran Duniya Da Mance Baya, Kuma Cikin Hikimar Ubangijiﷻ Wannan Al`amari Shima Nada Amfani Arayuwar Dan Adam Bisa Yadda Harkokin Rayuwa Ke Wakana Inbabu Mantuwa! Tabbas Dan Adam Bazai Samu Sukuni ba.

Kada Kazargi Wani Dan Yasamu Daukaka Da cewar Ya Gujeka Kazargi Kanka da Hassada dakuma Yanke Zumunci, Domin da zarar Mutum Yasamu Daukaka Al`uma Sun kara Yimasa Yawa Kuma Bazai Samu Damar Ji Da Kowaba dole Sai anayimasa Uziri, Kuma Kai me Raki Dolene Ka ziyarceshi Matukar Ba Hassadar Daukakarsa Kake ba, Inhar Kana Buqatar Zumuncinku Yacigaba.

Mudinga Yiwa Juna Uziri Muna Tuntubar Lafiyar Juna Mudaina basar da Junanmu Cikin Lamarin Rayuwa, Mu Sulhunta Junanmu Cikin Sabanin tunanani Ko Rashin fahimta, Muyawaita Yiwa Junanmu Fatan Alkhairi Da Nasiha.

TARIHIN SHEIKH ISMA’ILA IDRIS BN ZAKARIYYA

TARIHIN SHEIKH ISMA’ILA IDRIS BN ZAKARIYYA !!!
     **Gwagwar mayarsa wajen Kafa Izala da Sunnah***

Sheikh Isma’ila Idris

yatasone cikin al’umar nan tamu ta Nigeria, ayankin Arewa inda awannan lokacin babu wata aqida a Qasarnan bayan Dariqar Tijjaniyya, Qarqashin jagorancin sheikh Ibrahim Inyas Alkaulahy.
     To dake zamani ya Nausa tafiya tayi nisa, Al’uma tasamu kanta cikin yanayi na Cakuda addini da Son zuciya. Ana samun Malamai masu Sanya Son ransu acikin addini suna anfani dasunan Addini Suna isarda Munanan manufofinsu ga Al’uma kalar Bokanci da Sihirin Duba dama wasu Tsubbace_tsubbace su na Son Zuciya da Neman duniya.
    Wanda yaci karo da koyarwar Addinin Musulunci. Dukkan mai irin wad’annan aiki Bai tabayinsu Saiya fita a addinin Musulunci, Yazamo dukkan wanda yayi Sunansa kafiri da Nassin Aya acikin Suratu baqarah. Haqiqah bayan Wannan Akwai wasu littattafai dadama wadanda Maluma suka shigo dashi ake karantasu na Labaran mafarki da Tatsuniyoyi dasunan Adddini, Irin wadannan abubuwa dakuma makamantansu Sune maqasudin Da’awar ta Sheikh Isma’il Idris, abisa fahimtar masu kyautata masa zato.
    Da’akwai wadanda suke ganin cewa kawai yafara da’awar izala ne kawai Don Neman Suna dakuma Zagin Wasu malamai (Shehunnan ‘Dariqu) dakuma Sufaye. Wanda kuma hakan kuskurene domin  Aikin Musulmi shine kyautatawa juna zato. Da Kuma nemawa juna gafara agunda akayi Kuskure danganeda Sa’banin Ra’ayi ko Fahimta.
    Zamu cigaba ta Tarihi.
    Bayan Malam Yabar aikin Soja wanda acikin Aikin nasa na Soja ya fara da’awa akan barin Tsubbu da Daura layu da makamantansu, Malam yasha tsangwama daga makiya dakuma wadanda basu da ilimi wanda basu fahimceshi ba. Ba awannan Lokaci malam yaga cewar Wannan Da’awa tasa bazata cigaba ba Har saida wata Qungiya Wacce zata Tallafa masa Danganeda samun cikar Qudirinsa na Farkadda mutane game da Sunnah Asali.
    Awannan lokacine malam ya Assasa wata Kungiya mai Suna; ”Jama’atu izalatul Bid’ah ” Ma’ana ( Gungiyar dake kawar da Bidi’ah ) Wannan Kungiya Tasa tasamu karbuwa hatta aciki ‘Yan uwa Sojoji na wannan lokaci, Saidai kuma tasamu naqasu Sosai daga Malaman wannan zamanin Musamman wadanda keda Wannan aqidar ta Tsubbace_tsubbace da Duba. Tayadda sukayita yimasa Tuggu da zagon kasa gurin Sun ga sun dakushe wannan aikin Nasa, Tare da Wargaza aikin Nasa tahanyar kirkiran karya akansa hadda cutar dashi domin Su samu Galaba akansa, Amma ahakan Allah ya Tserataddashi daga dukkan tarakunan nasu Allah ya kuma karfafa Wannan Da’awa tasa har ilayau Qugiyar izala tana nan kuma tana cigaba da aikinta wajen karantar da Al’uma bisa koyarwar magabata dakuma Tabbatar da Qur’ani da Hadisi sune tafarkin Tsira ga Bayi.
    Ahakan aka cigaba da kasancewa har takai yaje izuwa ga Malamin sa na Tauhidi Assheikh Abubakar Mahmud Gumi, Domin neman izini da Karin lamani dangane da Da’awar tasa. Awannan lokacine Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya nuna Bashi Cikakkiyar goyon baya gamida Cikatamasa Sunan Gungoyarsa da ” Wa’iqamatissunnah ”  ma’ana ( Dakuma Tsayar da Sunnah ) Wcce tazamo ” Jama’atu izalatul Bid’ah Wa’iqatissunnah ”
    Ma’an ( Qungiyar dake kawar da Bidi’a kuma take Tsayar da Sunnah )
    Domin acewarsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi; Babu Yadda za’ayi akawar da bidi’a abarta haka ba acike Gurbinta da wani abu ba, Shine Yace to sai Acike Gurbinta Da Sunnah.
    Kunga Ashe kenan ita Izala ba Fitina bace Sabanin Yadda wasu daga cikin maluman ma da basu fahimta ba, Kuma bawai Reshen addini bace kamar yadda wasu suke yimata Mummunar fahimta Har ma wasu ke ganin Cewa in baka ciki to baka cika musulmiba, wasu kuma ke Mata ganin Cewa inkan cikinta Musuluncinka da Gyara Haqiqa Dukkan Mai yiwa Wata Aqidah ta Musulunci ganin Wannan Al’amari, Alal hakika ya Jahilci Hakikanin Musulunci,
    Wannan kadan kenan daga Tarihin Sheikh Isma’ila Idris da Gwagwarmayarsa gurin kafa Izala, insha Allah Anan gaba Zan kawo muku Cigaban da iza ta Kawo Wa Musulunci da Kasarmu baki daya. In Allah mai Komai ya kaimu bayan Sallah.
    Nine naku Isma’il Hussaini Adam Alpholtawy
    Kuma Wannan Shine karshen Rubutuna danganeda Shafukan Tarihin na Bana A Hijira sheka ta 1442 Saikuma Allah ya Kaimu Almuharram Shekara ta 1443 Zan cigaba da Wannan Tarihi.
    Mai karatu ga Addu’a ta Katayani da Ameen.
    Ya ALLAH Kajiqan Mahaifina Hussaini Adam Jumba wanda Ya Rasu a irin Wannan wata Mai Alfarma kuma Aranar Idin Adhhaa, Idin Babban Sallah Allah Kajikansa Ka gafarta masa ka kai Harke Qabarinsa, Kabashi Aljannah Madaukakiya.
    Ya ALLAH Mu Zuri’arsa Da muka Rage a bayan Kasa Allah ka azurtamu da Dogora abisa Addininka, Kabamu Shahada irin tasa, kasanyamu Cikin Wadanda kake Yantawa Zuwa Aljannah.
    Ya ALLAH Ka Sitirtamu da Sutura ta Musulunci, Ka azurtamu da Arzikin imani, da Ikhlasi da Tabbatuwa akan imani, Har Mu Mutu muna masu imani Da Miqa wuya gareka Allah.
    Ya ALLAH ka daukaka musulunci da musulmai, ka Qaskantar da Kafirci da Kafirai kadirkake makiyanka makiyan addini Allah kataimaki bayinka Nagari.

SUWAYE KHAWARIJ ???

SUWAYE KHAWARIJ???

 

khawarij

Sune Mutanen da Banbancin Aqida Ko Maslahar Rayuwa Tasanya Suke Kafirta Shashin Wasu Bangare daga Cikin Musulmi Bisa Ko Da Ilimi Ko Babu Kuma Suna Kisa, Wacce takai Har Suka ‘Dauki Makami Suna Ya’kar Musulmi Suna Kashesu Kuma Suna Halartar da Jinanansu, Wanda hakan Yasamo Asaline: Daga Tsatson Wani Mutum Mai Suna Zul Khuwaisirah Attamimi.

سبحان الله

Wanda Bayan Anyi Yakin Hunain
Bayan anyi Sulhul Hudaibiyya
Ansamu Ganima ayakin Hunain, Manzan Allah ﷺ Yazo Rabo, Sai Munafukai Suka Fara Gutsiri Tsoma Cikin Zancensu Suna zargin cewa Annabi ﷺ Bazaiyi Adalci ba, Suna Wannan Tattaunawar Tasu Cikin Ayarinsu na Munafukai Sai Wannan Mutum Mai Rashin kunya ( Zulkhuwaisirah Attamimi)
Yace: Shifa Saiyaje Yasameshi Danme Baza afadamasa Gaskiya ba Cewar Su Annabi ﷺBazaiyi Adalci ba.

Bayan Hakane Wannan mutumin Mara Mutunci Yazo Kan Annabi Cikin Yanayi na Rashin Kunya Yana Cewa: Da Annabin ”Kaji Tsoron Allah Kayi Adalci” Wa’iyazu Billah ALLAH Ka La’anci Khawarij Makasa Dangi da Sahabban Manzan ALLAH ﷺ. 

        Cikin Sanyin Murya Annabi Yace Dashi ”Yanzu Inbanyi Adalci ba Waye Zaiyi Adalci ” ﷺ.
Nan da Nan Sayyadina Umar Yazare Takobi Yace: Ya Rasulalllah  Barni Insare Wuyarsa Sai Annabi Yace Dashi: ”Barshi Koka Kasheshi Yana da Tsatso, kuma Wasu Zasu Bayyana a Karshen Zamani Makamantansa, Wadanda Idan kaga Sallahr Su Saika Raina Taka, Komai Sukan yi Na Addini fiye da yadda kuke Zato, Amma kuma Suna Fita Daga Addinin Kamar Yadda kibiya Ke Fita daga cikin Baka, Annabi ﷺ Yayi ta Bada Misalinsu kafin Karshen rayuwar sa, Yadda Yakara da cewa Zakagansu Suna Da kananan Shekaru, Kuma Suna Karanta Alqur’ani Amma Bai Wuce Makoshinsu (Ma’ana Babu Alamun Sanyashi Cikin Ayyukansu).
Kuma Suna da Tsantsan Rashin kunya da Nuna Tsantsaini Akan Duniya, Sunada Wofantattun ‘kwa’kwale (Abu Kad’an Yakan iya Canza Tunaninsu).

Sannan Suna Kafirta Kowa Wanda Baibin Bayansu, Idan Fitinarsu Ta tashi Za Su rin’ka Kashe Musulmi Suna Barin Kafirai, Suna da Jayayya dakuma Rashin Amintaka da Yan uwansu Musulmi, Amma Ba Ruwansu da Kafirai, Burinsu Kullum inane Musulmi Yayi Ba Daidai ba (Bin Diddigin Musulmi).

      Kuma Burinsu Akullum Nasu Itace Turba Inzaka zamo Mafi Tsoron Allah agun Kowa Inbaka Cikinsu Kai Ba Musulmi Bane agunsu Dan Haka Idan Sun Bayyana Ku Kashesu Ku kashesu Ku kashesu.

Bayan Zamani yayi Nisa Kuwa Sai Wadannan Mutane Suka Bayyana  Danhaka Suka Fara Sa’insa da Gofnatin Musulunci Tun Azamanin Sayyadina Umar (R. A) Alamun Hakan Tafara Bayyana, Amma Basu Ware Kansuba, Sun Fara Bayyana kansune cikin Munanan Halayyar su Wanda Annabi ﷺ Ya Ambata, Ananne Suka Fara Nuna Adawarsu Da Tawayensu ga Gofnatin Musulunci Haryakai ga Sun Fara Gutsiri Tsoma Ga Shugabancin Gofnatin Na Sayyadina Umar.

Aganinsu Umar Yana Tsanantawa Gurin Hukunci Tayadda Akasamu Wani acikinsu Mai Suna: Abu Lu’uLu’il Majusi Ya Sokeshi Sayyadina Umar (R. A) Da Wu’ka Acikinsa, Wanda Wannan Itace tazamo Jinyar da Tayi Sanadin Shahadarsa.Bayan Shahadar Sayyina Umar (R. A).
  Sai Sayyadina Usman Yacigaba Da Khalifanci, Wadda dama Annabi ﷺ yafada Wa Sayyadina Usman Cewa: Zaiyi Shahadane Tahanyar hakurin da Zaiyi Yayin Wata Musiba Da Zata Shafeshi, Hakurinsa Itace Maslahar Al’uma Sannan kuma itace Zata Kaishi Aljannah, Zaiga Musiba Akarshen rayuwarsa Dan haka Saiyayi hakuri, Inji Annabi Muhammad ﷺ Saboda haka: Bayan Ya Sami Nasarar Zamowa Khalifa, Sai ya Umarce Mutanen Sa cewa Kada Wani Ya Tunkari Mutanen da Duk Sukazo Domin Niman Ransa.    Domin Tunawa Da Wasiyyar Manzan Allah ﷺ Domin Yasan Cewa Shahadace Karshen Rayuwar sa, Kuma Hakan Zai Farune Tahanyar Wasu Daga cikin Musulmi.
Dan Hakane Har Suka Samu Suka Hauro Katangar gidansa, Suka Sameshi na Karanta Alqur’ani Sukayita Saransa Harsai da Jininsa Ya Zuba Akan Alqur’ani Alhali Yana Azumi, Amma Ko Daga Kansa Baiyi ba Haryakai ga Yayi Shahada Sukuwa Suka Fice daga ciki Gidan Sukayi Tafiyarsu, Sunyi Masa Wannan Ta’addancine: Domin Aganinsu Suna Ganin Cewa Yana ‘Daura Danginsane Kad’ai Amuqaman Gofnatin, Kuma ‘Yan Qabilarsane Danhaka Dangoginsane da Gofnatin, Sukuma Sunfison Dangin Manzan ALLAH ﷺ.
  Amma hakikanin Gaskiya itace Zalunci Ne kawai Da Tayarda Rikici wa Addinin Musulunci.

   Sannan kuma Sai Wadannan Mutanen dake Inkarin Mulkin Na Sayyadina Usman (R. A): Suka Nemi Sayyadina Aliyyu (R. A) Daya Maye Gurbinsa, Acewarsu Yacigaba da Khalifanci Da Jagorancin Musulmi,
Sukayita Kurarashi Da Wasu Dadin Baki Amma Sayyadina Aliyu Yaki Amincewa, Domin Acewarsa Yanajin Kunyan ALLAH Akan Wannan Al’amari, Ankashe Wanda ALLAH da Mala’ikunsa sukejin Kunyarsa, Dan haka Shi Da’awa Yasaba Abarshi Yayi Da’awarsa Azabi Wani Yayi Shugabanci. Sai da Wasu  Daga Cikin Manyan Masu Fad’a aji na Sahabbai Suka Sa Baki Sannan Sayyadina Aliyu Ya Amince.
  Dalilin Daya’ki Amince wa Kuwa: Shine Yana Ganin Cewa Bayadda Za’ayi Ayi Wa Sayyadina Usman Wannan ‘Danyan Aikin Bai Dauki mataki ba, Sannan Kuma Ace Ya Zamto Anbashi Ragamar Shugabanci Kunsan Aliyyu Kadanga Ne: Kasar Yaki Dan Baffan Manzan ALLAHﷺ Aganinsa Ankatse Masa Dukkan Wata Damarsa ta Ganin Ya ‘Dauki Mataki Danganeda Al’amarin Matukar Aka Bashi Ragamar Mulki.

   Bayan Ya amince da Yarjejeniyar Zama Khalifane: Domin magance dakuma daidaita Tsakanin Matsalar Musulmi Domin Khawarij Suna Sonsa Sannan kuma Sauran Sahabbaima Shine Za’binsu, Domin Su Wadannan Mutane Sunce Babu Wanda Zaiyi Jagoranci Awannan Lokacin Sai Shi Sayyidina Aliyyu. Kuma Wasu daga cikin Mutanen kirki acikin SAHABBAI Suma Sungoyi Bayansa. Awannan Lokaci Yaga Maslahar Al’umar kawai Itace Ya Rungumi ‘Kaddara Ya Cigaba da Khalifanci.

Bayan Ya Amince da Hakan Ya Kuma Samu Mubaya’ah daga Dukkan SAHABBAI, Sai Kuma Suka ‘Kara Kunna Wata Sabuwar Rigima, Ta Cewar Sai Ankamo Wadanda Suka Kashe Sayyadina Usman, Domin A Aiwatarwa Musu Da Hukuncin Alhali Kuwa Babu Wanda Yasan Su waye Suka Kasheshi.

Daganan Sai Suka Fara Rura Wutar Rigima Tsakanin Musulumi Na Yankin Madina, Har Rikicin Yafara Shafan Wasu Daga Cikin Sassan Sauran ‘kasashen Musulmi, Wanda Har Wasu Daga cikin SAHABBAI Masu Kyakkyawan Manufa Sanda Wannan Rikici Yaritsa dasu, Wasu Kuma Suka ‘Ki Sanya Baki cikin Rikicin, Wanda Harda da Matan Annabi ﷺ Wadda Dama Suna Madina aka Kashe Sayyadina Usman, Lokacin Sunzo Hajji ‘Kar’kashin Jagorancin Aishatu (R. A). Dasauran Matan Manzan Allah ﷺ Duk Sun Daidaita Akan Cewa Sayyadina Aliyu Yafara Bincike Ya Hukunta Wadanda Sukayi Wannan ‘Danyan Aikin. Shikuwa Sayyadina Aliyyu Burinsa Daidaita Al’amarin Shugabanci Kafin Tsara Yadda Gofnati Zata Gudana, Kafinnan Sai Ya Fara Bincike.

  Daganan Bayan Haka Aka Kai Koken Zuwaga Mu’awuya Tahanyar Wadannan Munafukan, Wadda Shikuma Sayyadina Usman Yakasance ‘Dan Uwan Mu’awuya Ne najini, Sai Shima Mu’awuya Yace Bazai Yi Mubaya’a ga Aliyyu ba Harsai Ya Zartar Da Hukuncin ga Wadanda Suka Kashe Usman. Kasancewar Mu’awuya Shima Gofnane Agarin Basra A’kasar Sham Siriya Watau Iraqi Ayanzu.

ALLAHU Akbar Yau ga Ranar Manzan ALLAH ﷺ Ina Ma Ace yana Cikin Duniyar!!! Wallahi Nasan Wannan Ba Komai Bane Agunsa ﷺ Cikin Sakanni Zaiyi Maganin Matsalar ﷺ.

Daganan fa Sai Labari Ya Riski ‘Dalha Bn Ubaidullah, Cewa Akwai Matsala A Can Basra Inda Mu’awuya (R. A) Yake Mulki, Domin Mu’awuya (R. A) Shi da Mutanen sa Sunce Bazasuyi Mubaya’ah ba ga Aliyu.

   Sannan Madina Tayi Zafi, Rikici Yayi Yawa, Aliyyu Kuma Yakoma (Kufa) Can Ta Yankin Da Mu’awuya Yake Mulki, Domin Mutanen Kufa Sunce Da Aliyyu Yazo Yankinsu Su Sun Aminta dashi, Kuma Sunada Babbar Daula Danhaka Yabar Madina Domin MadinaRikici Yayi Yawa, Yazo Gurinsu, Zasu Bashi Cikakken Goyon Baya Yakafa Daular Musulunci Awannan Yankin, Ya zamo Itace Cibiyar Musulunci Wanda Shugaban Musulmi Yake Cikinta Amaimakon Madina ta Asali Afarko.
Sannan Yacigaba Da Dukkan Wata Qudiri dakuma Aikin Shugabancinsa Zasu Dafa Masa Har abinciko Wadanda Suke Kokarin Rushe Daular.

‘Dalha Bn Ubaidullah da Zubairu Bn Awwam Manyane Daga Cikin Manyan Zaratan Sojojin Manzan ALLAH ﷺ Suma Suka Koma Makka Sai Suka Hadu Da Nana Aisha.
Domin Suma kansu Yayi Zafi Tunaninsu Ya Bambanta dana Sayyadina Aliyu (R. A) Cewar Suna Ganin Yakamata Sayyadina Aliyu yafara Kama Wadanda Sukayi Wannan Mummunar Aiki, Domin Yaji Dadin Mulkinsa Dakuma Magance Matsalar Munafukai dasuke i’kirarin Cewa Harda Hadin Bakinsa Aka Kashe Sayyadina Usman (R. A)

Bayan Sayyadina Aliyu Yakoma Kufa Kuma Ita Kufa Wata Babban Jihace Akasar Iraqi Wanda Har ayanzu Tana Cikin Manyan Daulolin Kasar, Ananma Sai Sayyadina Mu’awuya Yace Bazai Ta’ba Yarda da Khalifancin Sayyadina Aliyu (R. A) Ba Harsai ya Binciko Wadanda Suka Kashshi.

Akan hakan Kuwa Yasa Shi Mu’awuya Yakiyimasa Mubaya’a Domin Sa’banin Ra’ayin dake Tsakanin Su, Sannan Haryakai ga ‘Dalha Bn Ubaidullah Da Azzubair Bn Awwam Suka Taso Daga Makka da Nufin Cewa, Dole Ne Sai Sun Shiga Cikin Matsalarnan Tahanyar: Yin Sulhu Tsakanin Mu’awuya da Sayyadina Aliyu (R. A) Kafin Asamu Maslaha.
  Bayan Sun sami Matsaya Danganeda Shawarwarinsu Saikuwa Suka Shirya Domin Zuwa Sulhu Kasar Iraqi Aisha Ma Tace Hankalinta Bazai Kwanta ba Ga Ahalin Gidan Annabi Muhammad ﷺ Cikin Wani Hali Danhaka Sai Yabisu, Sai Kuwa Suka Sauka A Basra Inda Mu’awuya Yake Mulki, Domin Neman Sa daya Janye Akan Yayi Mubaya’a Wa Sayyadina Aliyu, Awannan Lokaci Ne Munafukai Suka So Rura Wutar Gaba Tsakanin ‘Dalha, Aisha, da Zubair (R. A) Da Gulman Cewa Su AISHATU DA ‘DALHA DA ZUBAIR sunje Gun Mu’awuya Ne Domin Suna Goyon Bayan Mu’awuya.

    Shikuwa Sayyadina Aliyu Ai Ba Wawa bane Rainon Manzan ALLAH ﷺ Ba Wasa Bane, Yafi Karfin Zugon Munafukai Kuma Ashe Yagane Akwai Munafukai Masu Rura Wutar Rigima, Saiya Aiki wani Daga Cikin Manyan Zaratan Kwamanadan Sojojin Manzan ALLAH ﷺ Qa’aqa’a Bn Attamimi.
Domin Ya Binciko Masa Menene ake ciki Domin Kada Ya Yanke Hukuncin ABisa Rashin Sanin Hakikanin Abinda yake Gaskiya, Sai Kuwa Yazomasa Da Labarin Cewar Ai Sunzo Yin Sulhu Ne.
Sai Sayyadina Aliyu Yace Aikuwa Baici tazama ba Dolene Yajema Kawai Caan Ayi Sulhun (Yaje Basra) Ayi Acan Domin Ga Manyan Mutanen dayake Jin Nauyin su Acan Basra. Agefe Guda Kuwa Wadannan Mutane Masu Mummunar Manufar Sunanan Suna ta Kullace_Kullacensu.
   Lokacin da Suka Sami Labarin Cewa Sayyadina Aliyu Yatafi Zaije Sulhu Da Mu’awuya Kuwa: Sai Suka Fara Tunanin Yadda Zasu Wargaza Wannan Sulhun Yazamo Ba’ayi Shiba. Domin Sun Tabbatar  dacewar Anayin Sulhu Kan Al’umar Musulmi Zai Hadu Kuma Za’akamosu Ahukuntasu. Shine Suka Rabu Gida Biyu, D’aya Sukaje Basra.

Bayan Sayyadina Aliyyu Yakama Hanya Tareda Rundunarsa Wadanda Sukace Bazasu Bari Yatafi Shidayaba Dole Sai sunbishi Domin kare Ransa da Lafiyarsa. Hakan Kuwa sukayi Suna tafiyane Sai Dare Yayi Musu Ahanya Sai Kuwa Ya Yada Zango Da Rudunar Mutane Dubu Ashirin A wani Guri domin Dare Yayi Dan Su Huta Sai Safiya Acigaba da Tafiya.  Cikin Dare Sai Wadannan Munafukai Wadanda suka Kasu Gida Biyu: Domin Cimma Mummunar Manufarsu ta Wargaza Sulhu, Wani Bangaren Suka Zo wa Rundunar Sayyadina Aliyyu Suna Kashesu Suna Saransu Wasu Bangare kuwa Suka Je Ga Sayyadina Mu’awuya AKasarsa Suna Kashe Sojojin said Suna Cewa Ba Maganar Sulhu.  Nanma Gun Rindinar Sayyadina Aliyu Suka Kama Saran Sojojin Sa Suna Cewa Babu Sulhu, Daganan Kuma Suka Hade Guri Guda Aka Kama Yaki Musulmi da Musulmi, Ana Kisan Juna ba tareda Ansan Dalilin Yin hakan ba Kowa Na Saran Dan Uwansa Amma Baisan Daliliba Sudai Sunsan Cewa Hari Aka Kawowa Kowanne daga cikin su.
Nagartattun Cikinsu Wasuma Basusaniba Wasu kuwa Sunki shiga Yakin Haka kuma Wadanda Suka shiga ma Sunayine Domin Kare Kansu Domin Su aganinsu Kamar Ankawo Musu Harine.
    Awannan Rikicinne aka Kashe Zubair da Dalha Sannan Wasu daga Cikin Sojojin Aliyyu Sune Suka Kashesu Domin Rashin Sanin Hakikanin Me Yakawosu, Yankin Mu’awuya Aganinsu Sune Suka Ruruta Wutar Rigimar, Wani Daga Cikin Sojojin Aliyu Yasamu Azzubair Ibnl Awwam Yana bacci Yadauki Takobinshi Yakasheshi da Ita, Sannan Kuma Ya dauki Takobin Yakaiwa Sayyadina Aliyyu Domin Nuna Bajintarsa Ga Sayyadina Aliyyu,
Da Sayyadina Aliyyu Yaga Wannan Takobi Sannan Wannan Mutumi Yace Dashi Wannan Takobin Dan Awwam ne Da ita Na Kasheshi Dan Sune Suka ruruta Wutar Rigimarnan, Sai Sayyadina Aliyyu Ya Fashe da Kuka Yana Cewa Shin Kasan Hidimar da Wannan Takobi Tayi wa musulunci kuwa?
     Da Wannan Takobine Akayi Gadin Manzan Allah ﷺLokacin da akayi Yakin Khandaq, Annabi ﷺ Baya Samun Bacci Azzubair Shike Gadin Annabi ﷺ Haryasamu Yin Bacci. Manzan ALLAH ﷺ Yakira Azzubair da Hawariyyinsa, Domin Yace dukkan Annabi Yanada hawariyawa Nikuwa hawariyina Shine azzubair.

Sannan Shima Dalha Ibn Ubauidullah Shima Awannan Yakinne aka kasheshi tahanyar Harbin Kibiya Da akayi masa, Sayyadina Aliyyu (R. A) Yafada wa Sayyadina Hassan (R. A) Yace dashi ”Lokacin da ‘Dalha Yazo Cikawa Yace Dani, Abin Baiyi Masa Dad’iba Domin Sunzo Sulhu  Maimakon Sulhu Kuma Sai Ankama Kashe Juna.
Sayyadina Aliyyu Yana yaki yana kuka Yana Fadin wai Meyafarune!!!.

Bayan Anyi Wannan Yaqinne Sai Sayyadina Aliyyu yace: ”Zamu koma Kufa Domin Abin Baimana Dadin Ji da Ganiba” Aisha Kuwa Da taji Abinda Yafaru hankalinta yatashi Sai Tace Zata Koma Gida, sai Aka Sanya Wasu Rudina Karkashin Jagorancin Mu’awuya (R. A) Sukayi Rakiyarta Gamida Wasu Guziri.
Munafukai kuwa dasukaji haka Har Wani Yafara cewa Aidama Ance Kaza_kaza akanta, Da Sayyadina Aliyyu yaji Haka Saiyasa aka kama wannan Mutumin aka tubeshi akayimasa bulalan ‘Kazafi Na Haddi, Sannan Yace Dashi Wannan itace matar Annabi ﷺ Aduniya kuma Qiyama.

    Dagananne Aka Samu Bangarorinnan Na ‘Yan Tawaye Ahlul Bagyi ‘Bangaren Su (Mu’awuya), Dakuma ‘Bangaren Masu Gofnati Su (Sayyadina Aliyyu), Da Munafukai Masu Fad’a Da Dukkan Tsarin Sune (Khawarij), wadanda Dama Annabi Yafadesu Cewa Akwai Wasu Bangarori Biyu Masu Gaskiya Zasu Yaki Juna, Sannan Wasu kuma Zasu Balle Sukuma dabam, Sunzamo Uku Kuma Duk yayi bayaninsu wanda Duk maihangen Nesa Cikin Sahabbai Yaganosu, Kuma Sune matsalar musulmi, Daman Annabi ﷺ yafada Insun Bayyana Akashesu Kada Abarsu Domin Sudin fitinace Ga Alumar Musulmi, Wadda kuma Aliyyu Ya Aiwatar da Wannan Aikin Na Yakarsu kamar Yadda Annabi ﷺ Yabada wasici, Cewar AYakansu Akwai Lada Mai Dumbin Yawa Daga Bakin Annabin ALLAH ﷺ Sannan Yace Idan Za Ayakesu  Ayimusu Kisan Kiyashi (Ankashe Su Dukka) Danhaka  Sayyadina Aliyu (R. A) Ya yakesu kuma Yakashe Kasho Casa’in Da Biyar Cikin Darinsu Saura Kuma Suka gudu.
Sunefa Masu Da’awa Akan cewa Babu Gofnati Babu Hukunci Saina ALLAH, Wanda Har Sayyida Aliyu Ya turamusu Abdullahi Dan Abbas, Domin Yayi Musu Wa’azi, Domin Sunce Aya Suke Nema Ba ruwansu da Shugabancin Wane Ko hukuncin Wane, Sannan Kuma Su Basa bin Wata Gafnati Tsakanin Aliyyu Ko Mu’awuya Ba ruwansu da Kowa.
     Anyi Nasarar Wasu Sun Tuba Sun Amince Sun koma Rindinar Gofnati, Tayadda Wasu kuma Suka Tangare Suka Nuna Girman Kai daga Nanne Sayyadina Aliyyu Yaganefa Sune Wadanda Annabi Yake ta bada Misalinnan Fa, Dagananne Sayyadina Aliyyu Ya Daura Damarar Yaki dasu Domin Yagano Su Yakashe mafi Yawansu, Wasu kuma suka Gudu, Wadanda Suka gudu Suka Tsira Sune Sukayita Yakin Sunkuru Ga Musulmai, Snayimusu Dauki ‘Daid’ai Haryakaiga Sun Kashe Sayyadina Aliyu (R. A) Da Asuba Yafito Yana Tashin Mutane Su Fito Domin Suyi Sallahr Asubahi, Wanda Yakashe Shi Shine Abdullahi Bn Muljum Domin Suna Ganin Su Sayyidina Aliyyu  sun kafirta Saikuma yakama Da’awar Cewa In ankasheshi Yayi Shahada.

Wannan Shine Matsalar Da Musulmi Suka taba Samu Gameda Shugabanci Kuma Shine Dalilin Shahadar Sayyadina Aliyyu Dakuma Dalha Da Zubair Rahmatullahi Alaihim Ajmain.

Kuma Siffar Khawarijawa Kenan: Tawaye wa Aqidar Mutane da Gofnati Da Daukan Makami Akan Al’umar Musulmi.

HAKIKA AN TAUYE HAKKIN AL’UMMAR AREWA

Ma’aikatar cikin gida (Ministry of Interio) karkashin jagorancin Minista Ra’uf Aregbesola ta fitar da sakamo na jahohin Nigeria matasa wadanda suka samu nasaran daukar su aiki domin cike gurbi a hukumomin tsaro na Civil Defence, Correctional, Fire Service da Immigration
Amma a cikin wannan sakamon an cuci yankin jihohin Arewa, an danne musu hakkinsu, kashi 99 cikin 100 na wadanda aka daukesu aikin daga Inyamurai ne sai Yarbawa, tsakani da Allah me ya kawo Sunan Ikechukwu jihar Jigawa?
Kuma a haka wakilan Arewa zasu zuba ido ba zasuyi magana ba?
Wato an mayar da ‘yan Arewa saniyar ware, an mayar damu marassa amfani kawai, amfanin ‘yan Arewa sai lokacin zabe yayi azo neman kuri’ah ana watsa mana hatsi daga cikin mota kamar kaji muna caccaka
Mu dai Arewa an barmu da yiwa juna hassada da kyashi da munafurci, mutanen kudu sun mayar da hankali wajen kokarin gina ‘yan uwan su, sun mamaye dukkan ma’aikatu dake babban birnin tarayya Abuja, har a cikin jihohin Arewa inda ya kamata a ga sunan Hausawa sai dai aga sunan Inyamuri, saboda sun fimu hadin kai da son juna ba tare da nuna banbanci ba
Wannan babban kalubale ne wa Ministocin Nigeria ‘yan Arewa, ya kamata ku dauki darasi da abinda Ma’aikatar cikin gida tayi, ku dena nuna tsoro ko shakkar masu zagi da suka, tabbas kuma zaku iya yin abinda Minista Ra’uf Aregbesola yayi a ma’aikatunku idan an tashi diban aiki, shugaba Muhammadu Buhari yayi iya bakin kokarinsa da ya baku mukami, saura kuyi abinda ya dace
Allah Ka taimaki Arewa da ‘yan Arewa Amin

AHLUSSUNNAH MUFARKA

DA’ACE KISHIN QUNGIYANCIN MU NA ADDINI NE DA MUN WUCE HAKA ACIGABA

      Ahlussunnah Mufarka
Jiya kotu a Kaduna ta wanke Amirul Jaish na rundinar shi’ah (IMN) Ibrahim Yakubu Zakzaky daga tuhumar da Gwamnatin jihar Kaduna ta masa, biyo bayan abinda ya faru a Gazwatu Hussainiyyah Zaria da sojojin janar Buratai a 2015
Ni abinda na fahimta lokacin da Gwamnati ta gindaya masa ne kawai yayi ta sakeshi da kuma tasirin da Zakzaky yake dashi a cikin wannan Gwamnatin, amma ba wai don ta rasa hujjar da zata cigaba da tsareshi ba
Sannan bayan matakin da kotun Kaduna ta zartar, har ila yau inda ace Gwamnatin Kaduna tana da niyyar cigaba da garkame Zakzaky da tayi hakan ta hanyar daukaka kara a kotun tarayya dake Abuja, kamar yadda dokar kasa ta tanadar
Zakzaky yana da manyan mutane a Kasarnan wanda suna da tasirin da zasu iya nema masa alfarma har a gurin shugaban Kasa, idan baku sani ba Zakzaky yana da Manyan Ministoci har guda biyu a cikin wannan Gwamnatin wanda a baya har muzahara suna fita kafin a kafa Gwamnatin Buhari a 2015
Gareka Musulmi Ahlussunnah, ka sani cewa ba ruwan Gwamnatin Nigeria bane ta yaki wani mutum saboda yana dauke da akidar da ta saba da ra’ayinta, shi tsarin kundin Constitution da yake rike da tsarin gudanarwan Kasa, fada ma yake da kowace irin akida ta Musulunci
Duk abinda ya faru da Zakzaky bai da nasaba da addini ko akida, zallar siyasa ce kawai, zargi ne marar tushe da ake cewa Kasar Saudiyyah cibiyar Ahlussunnah tana da hannu a abinda ya faru da Zakzaky
Jama’ar Musulmi da muke kiyayya da shi’ah ku sani cewa akwai babban kalubale a garemu idan bamu gyara, yawan da muke dashi ba zai taba amfanar mu ba, Ya ku Ahlussunnah me zai hana kuyi irin tsarin da Zakzaky yayi har ya samu karfi da kuma tasiri da ya mallaki manyan wakilai da yake dashi a kowace ma’aikata a Gwamnatin Nigeria?
Shin Ahlussunnah kuna da tsarin da kuke daukar nauyin karatun matasa masu fikra da basira a cikinku suna zuwa Kasashen turai suna karanta Medical Doctor, Pilot, Nuclear Physics, Astronomy, Mechanical Engineering, International Law, Computer Science, Ethical Hacking, Cyber Security da sauran fannonin ilmi masu tasiri a zamani kamar yadda Zakzaky yake yi?
Shin Ahlussunnah kuna da tsarin bangare a cikin da’awar Sunnah ko kungiyar Sunnah da yake da bangare na Likitoci Ahlussunnah, bangare na Malaman makarantar boko tun daga Primary har University, bangare na jami’an tsaro, bangare na siyasa, bangare na ‘yan kasuwa, bangare na ma’aikatan Gwamnatin tarayya da na jihohi da kananan hukumomi kamar yadda Zakzaky yake da wannan tsarin?
Ahlussunnah ba mu da wannan tsarin ko guda daya, an bar Ahlussunnah a baya, an bar Ahlussunnah da yiwa juna raddi da hassada, abinda ba za’a taba samu ba kenan a cikin da’awar shi’ah a Nigeria, idan kunga bangaren RAAF suna sukar IMN Taqiyyah ne, manufarsu daya ce
Tsarin da Zakzaky yayi ba shakka idan Allah Ya bashi tsawon rai sai ya kafa Gwamnatin shi’ah a Nigeria, domin Billahi yayi kafuwar da ya wuce tunanin duk wani mai nisan tunani, na rantse da Allah inda ace da’awar shi’ah abune mai kyau da na jima da zama ‘dan shi’ah, kuma da yanzu bana Kasarnan saboda girman gudunmawa da zan bayar a tafiyar, amma shi’ah ba abune mai kyau ba
Namu jagororin sun zama ‘yan duniya, sun fara nesanta kansu da da’awar Sunnah, tsarinsu ya koma irin na ‘yan duniya kawai, sun koma karya da yaudara da zakin baki, takaicin wannan abin yana matukar sanya ni kuka da zubar da hawaye
Halin da Musulmi Ahlussunnah muke ciki a yau ya kamata ya dinga hanamu bacci, ya zamto muna tunanin hanyar da zamu bi mu gyara kuskure domin mu tunkari abokan gaban mu
Yaa Allah Ka bamu mafita na alheri Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
Daga Malam Datti Assalafiy