MASHAHURAN MUSULMAI DA SUKA FARA KIRKIRAN AIKIN LIKITANCI A DUNIYA


Kamar yadda nayi bayani a rubutu na farko Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin waɗannan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne.
Ga kadan daga cikin irin wadannan mashahuran Musulmin da suka fara kirkiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo:
~ Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD):Mutumin kasarFarisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu
gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa.
Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu. Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da guda dari. Fitacce a cikinsu shi ne “Al-Hawi”. wanda kundin bayanai ne a kan aikin likita da ya shafi magunguna da yadda suke aiki a jikinmu.
A wani shagube da ya taba yi wa wani mai maganin ciwon ido, wanda ya kawo masa magani don ya sa a idonsa, sai ya tambaye shi da ya yi masa bayanin yadda ido ke aiki amma ya kasa, don haka ya ce maganin karya ne. Wannan ne ke mana tuni da taka-tsan-tsan wajen sayen magunguna a wurin jahilai.
~ Ali Ibn Abbas: Haly Abbas (920-994AD): Shi ma daga Farisa ya fito kuma ana ji da shi a duniyar likitanci. Ya ba da gudunmowa ta hanyar rubuta littattafai cikin harshen Larabci, wadanda suka fi bayani a kan bangaren kwakwalwa da cututtukanta da bayanan falsafar binciken kimiyya irin na zamani.
~ Abul kasim Al-Zahrawi: Abulcasis (936- 1013AD): Wanda yake Balarabe ne wanda aka haifa a kasar Spaniya. Ya yi fice wajen zama likitan tiyata na farko na zamani a duniyar Musulunci saboda kirkiro kayan aiki na leka
wurare da dama na jikin mutum da ya yi, fiye da dari biyu, wadanda daga su ne aka kera na wannan zamani.
Shi ne kuma ya fara nuna wa duniya cewa za a iya samun juna biyu a wajen mahaifa saboda tiyatar da ya sha yi a wannan bangare.
Ya zama likitan Khalifan Musulunci a kasar Andalusiya, wato Khalifa Al-Hakam kuma ya rubuta littattafai da dama a kan aikin tiyata, wanda har yanzu akan samu manhajojin a littattafan wannan zamani. Domin karin bayani, za a iya bincikar Kitabut Tasrif.
~ Abu Ali Ibn Sina: Abicenna (980-1037): Shi ma mutumin kasar Farisa ne, wanda yake da baiwar kaifin hadda da tunani mai zurfi.
Ya haddace Alkur’ani yana dan shekaru goma kacal, sa’annan ya zama likita yana dan shekara sha shida. Ya yi aikin duba marasa lafiya kyauta a wannan birni kuma ya zama babban likitan Khalifan garin.
Daga baya ya yi hijra ya nufi yamma, inda a hanya ya rubuta kundaye a kan bayanai na kula da lafiya da aikin likita, ya kuma koyar da dalibai.
Wannan kundi wanda ake kira ‘kaanun fid dibb’ an dade ana amfani da shi a jami’o’in kasashen
yamma na wancan lokaci, a matsayin littafin koyarwa.
~ Ga kuma irinsu Ishak Al-Ruhawi dan kasar Turkiya, wanda ya fara bayani a kan tarbiyyar likitoci; wato yin tsantseni da taka-tsan-tsan a kan aikin likita da hukuncin da ya kamata a ba likitoci masu ganganci da aiki a cikin littafinsa mai suna ‘Adab Al-Tabib.’ Shi ne kuma ya fara bayanin cewa kowane sabon abu aka samar a kimiyyar likita, dole a samu wasu kwararru a aikin su zurfafa bincike don tabbatar da sabon bayanin ko karyata shi.
~ Sai kuma wasu da dama irinsu malaman wadannan da muka lissafa wadanda ba su yi fice kamar dalibansu ba. Misali, malamin Al Razi, Abu Hassan Al-Tabari, wanda ya yi fice a harkar lafiyar yara.
~ Akwai kuma irinsu Abu Alhassan Ibn Al-Nafis, likitan kasar Suriya wadanda Turawa ma ba su sani ba ko kuma suka sani amma suka ki ambatonsu.
Shi ne wanda ya fara bayanin yadda jini ke zagaya jikinmu, tun kafin ma a haifi Baturen nan William Harbey, wanda suka ce shi ya fara wannan bayani.
Ya Allah ka tabbatar damu akan daidai kasa Aljannar Firdausi itace makomarmu.

واَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

AQEEDAH TA ITACE MUSULUNCI

AQEEDATA

Dasunan ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

      Wasallahu Alaa man Laa Nabiyya ba’adahu Muhammadun bn Abdullah .(ﷺ) Salawatullahi Alaihi, wa Alaa Aalihi wasahbihi wasallama tasliiman khasira.

Waba’ad;
Assalamu alaikum warahmatullahi warahmatullahi wabarkatuhu, Mai karatu idan baka manta ba ada nayi Alqawwarin fadawa mai karatu mecece aqedata, dakuma matsayata dangane da halascin wakokin yabo da kirari da Haramcin kida Amusulunci.

Ⓜ Mashaa ALLAH Alkawwari yacika;
     Ni Ismail Hussaini Basalafene (Assalafy) Ne. Sala ba Kungiyace ta Aikin addini bawai Shi`anci bane. Wata al umace dake aiki akan Hani ga barna dakuma umarni da aikin Alkhairi. wacce take kuma koyi da magabata. Ainihin Kalmar Salaf tana nufin Magabata.

Salagiyya kuma tana nufin Bin tafarkin magabata. Wannan itace Al umar damuke koyi dasu na kwarai din cikinsu. Amma mu musulmaine kamar Sauran musulmi. Kuma munyi imani da Alqur`ani da hadisai kuma manzon mu shine مُحَمَّد ﷺ

Shi muke kwaikwayo a hali dakuma ayyukan.
Basai nayi bayani akan ko mene aqidah ba. Domin abaya nayi bayani akai karin bayani dan ganeda aqidar salafawa shine { (Aqeedadussalafussalih bi muwafaqati Sunnatin_nabawiyya wa Ashabuhum) (Ma ana aqidar bin tafarkin annabawa da sahabbansu) }.
   Aqidar itama Ahlussunnah ce akarkashinta akwai izala kamar yadda akasani, wadda suke da manufa iri daya dan ganeda da`awa da tsarukan karantarwa iiri daya saidai ita salafiyya kuma tafi yada da awarta ta social media fiye dana izala. ma`ana tafi dukufa wajan rubuce rubucen tarihi ta hanyar wayar da kai ga addinin musulunci da musulmai bisa yadda Zamani yakasance.  Dawayar da kan mutane Dan ganeda rayuwarsu dazamantakewarsu da Ladaftar dasu da koya masu dabarun rayuwa dawayar dasu Ga addini suyishi sukuma dabbakashi dayadashi a duniya.  Dukka sune Aikin salafawa.
Kar nazurfafa atakaice wannan itace aqidata. saikuma magana akan maulidi da kasidu masu kida da da marasa kida.

WAKOKIN YABON ANNABI
Haqiqa wakokin yabon annabi babu Kida ya halasta kaidai dolene yazama duk yaren dazakayi wakan yabon annabi dashi. yazamana kana da ilimi akan yaran sosai domin kiyaye kalmomin da zakayi amfani dosu, donyin yabon kuma dolene ka koyi ilimomi aka yaran kamar haka: ilimin balaga, Qaamusu, Ka`idojin rubutu, Ilimin Grammar, Dakuma tarihim annabin dama mawakansa  nada, domin azamanin annabi  ﷺ Anyi masa waqoqi dayawa harma ayari yake dasu na mawaka Ammafa su basuyi da kida bakuma yi sukeba Dan holewarsu ba ssunayine domin maida martani wa kafirai sai kuma domin dafawa Ga fiyayyen halittaﷺ kutambayi malamai zasu baku karin bayani akai.
    To awannan zamani namu akwai mawakan dake waqoqi nayabo amma da kida ko nace kayan sauti mabanbanta. wallahi! Tallahi!! Billahillazi La ilaha illahuwa wuce gona a kayan kida sautin shaidanune!!!

Me karatu kayi shari ah ta adalci٠
Masu wakokin yabo ayanzu musan man agun maulidi shin kaso hamsin cikin dari suna tantance me suke fada kafin su fada awakokinsu? babu shakka Amsar itace a`a.
   Muyi wa kanmu adalci waqa na ilimi wanda ba kida nayabon Annabi yahalasta amusulunci, ko muma a Tafiyarmu ta salafawa munada mawaqan yabon annabi amma basuyi da kida kuma sai an karantaddasu kuma littafai suke bugawa akuma tantancesu agaban malamai kafin suje subayar ga masu hazakar furuci su rera wakokinsu ba cinzarafi da zagi ko aibata wani ko wata aqida da ace ´yan d`ariqun sufaye da ´yan Shi`ah suma zasuyi adalci wa kawunansu dasai suma su rage msu hankalin cikinsu yakamata su daina waka da kida suyi waqa tsarkakakkiya da yabo wanda yadace da tunani mai kyau da koyarwar Addinin musulunci.
 

 BIKIN MAULIDI 

Bashakka bikin Maulidi Bai ingantaba koda ahadisine mai raunine babu, ba  ko wata yarjeniya ta wata ayari namaluman sunnah danayanzu dana da duk sun daidaita akan bai ingantaba. Hasalima suna kirantane da bidi´ah muhadatha ma`ana bidi`ah kirkirarriya. Batada tushe ko asali daga magabata, akwai hadisai dayawa wadanda suke tsawatarwa danganeda kirkira a addini. Arufai na tsawatarwa danganeda kirkira a addini. Ayanzu acikin maulidi allah ﷻ Shine kawai yasan bidi`o`in da aka kirkiro.
  Banso Raba rubutun  ba amma dolene ta saka `yan uwa kuyi hakuri muhadu arubutu nagaba mai Taken Aqeedata
   
    
 

KADA MU DEBE TSAMMANI GA UBANGIJI

ALLAH YANA DA MAFITA GAMEDA DUKKANIN WATA MATSALAR DA TAKE DAMUNKA.

Koda yaushe muna yin tunani ne akan yawan matsalolin da suke damun mu ne a rayuwa, muna mantawa da cewa lallai fa haƙiƙa Allah yana da mafita daga dukkanin kowace irin matsalar da ta dame mu a rayuwa.

A rayuwa idan muka fuskanci Allah maɗaukakin sarki, muka koma gareshi da tuba cikin nadama da ƙas-ƙantar da kai, haƙiƙa Allah zai saurare mu, zai kuma yaye mana dukkanin damuwa da take damun mu ko ba-daɗe ko ba-jima, musamman idan munyi haƙuri mun kuma toge akan biyayya ga Allah ta’ala.

Muji tsoron Allah, sai Allah ya warware mana damuwar mu, mu kauce ma saɓonsa, sai yaji ƙanmu, kada mu bari shaiɗan yayi tasiri akanmu ya shiga tsakanin mu da ubangijin mu Allah ya kuma halaka mu ƙarshe mu zamto ababen yin nadama a ranar ƙiyamah.

AREWA 24 TAMUCE

AREWA 24 TAMUCE
Faduwar Dalibai A Jarrabawar JAMB

   Sau dayawa harda wasu acikin Malamai na ta fadar cewa Kallon Shirye_Shiryen Film Series. Sune Silar Faduwar Dalibanda Sukayi JAMB A bana 2021.

Daga Alqalamin ✍️Ismail Hussaini Alpholwy

@MatanasanMarutanBauchi

       Sabanin Ra’ayi danganeda Fahimtata dakuma Wadansu damuka tattauna akan batun awani ganawar damukayi ta Online da ‘Yan uwana marubuta.
A iya fahimtarmu bakawai Kallon series bane yakayarda Mutane a jarrabawar bana ba. Duk da Cewa yana daya daga cikin abubuwa uku acikinsu. Sune Kallan film, Yawan Sauraron kida, dakuma Wasannin Wayar hannu (Games)

  Wadanda dukka wadannan abubuwa suna Faruwane ta cikin wayoyin hannuwan mu. Yadda zakasamu Mace ko na miji yana da Game Apps Sama da Goma Sha ga kuma Film Series Suma Sama da Ashirin Ga kuma wakoki na Hippop dama Jazz Music dana Hausa dama na Turanci dana Kudanci Hardana Videos na Fitsara da Lalata Tarbiyya.

   To taya yaro zai dau littafi yayi karatu, bacin ga irin wadannan Shirmen da lalacewan acikin wayarsa. Dasu zai kwana kuma yatashi kuma ba akoyar dashi Tsoron Allah ba.

   Laifin iyayene dasuke sakaci da Wayoyin Yaransu dakuma Yaran dasuka taso Basu bibiyar kafafen Alkhairi acikin wayoyin dakuma Social Media.
Dolene Mu kame daga barin abinda Zai Cutar mana da imaninmu dama Kuruciyarmu gaba daya.
Burin Turawan yamma akoda Yaushe Shine Muzama Malalata Mukasa komai Sai sun mana.

     In iyayenmu basu ankaraddamu  ba wataran Za’a iya wayar gari bazamu iyayin komaiba, Sai abinda Turawa Sukaso suyi damu, domin anriga da makara komai ayanzu nasu ake kwaikwayo. Anmanta da Cewa akwai Tsarin Rayuwa Islamiyya dakuma Christianity. Duk abinda Yahudu Sukazo dashi Shine Ake bi.

    Idan da wasu iyayen Zasu duba Profile na Socil Media na Yaranau Musamman Facebook da Twitter dakuma Istagram da Tictok Wallahil Azim sai sun farfasa Wayoyin Yaransu. Yin hakan kuma abanza ne. Don zai je ga na Abokansa.

      Mafita garemu Shine Adasawa Yara Tsoron Allah Acikin Zuqatansu kawai tahanyar Nasihohi da Addu’ar Shiriya domin Tafiya tayi Nisa. baza’a taba iya Hanasu rike wayoyi Dukansu inma babu ahannun wancan akwai ahannan wancan kuma Munsan Cewa ba’a Rowan Wuta. in aikin Shedancine kana Zaune za Akawomaka, kuma ba aganin Tsadarsa domin Akan iya Sayan plartform domin Series Film Amma daukar Nauyin Tafseer kuwa Sai cikin Azumi.

Domin Allah iyaye Akoyar da ‘ya’ya Tsoron Allah, Allah yakawo mana mafita Arayuwa.