MASHAHURAN MUSULMAI DA SUKA FARA KIRKIRAN AIKIN LIKITANCI A DUNIYA


Kamar yadda nayi bayani a rubutu na farko Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin waɗannan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne.
Ga kadan daga cikin irin wadannan mashahuran Musulmin da suka fara kirkiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo:
~ Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD):Mutumin kasarFarisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu
gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa.
Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu. Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da guda dari. Fitacce a cikinsu shi ne “Al-Hawi”. wanda kundin bayanai ne a kan aikin likita da ya shafi magunguna da yadda suke aiki a jikinmu.
A wani shagube da ya taba yi wa wani mai maganin ciwon ido, wanda ya kawo masa magani don ya sa a idonsa, sai ya tambaye shi da ya yi masa bayanin yadda ido ke aiki amma ya kasa, don haka ya ce maganin karya ne. Wannan ne ke mana tuni da taka-tsan-tsan wajen sayen magunguna a wurin jahilai.
~ Ali Ibn Abbas: Haly Abbas (920-994AD): Shi ma daga Farisa ya fito kuma ana ji da shi a duniyar likitanci. Ya ba da gudunmowa ta hanyar rubuta littattafai cikin harshen Larabci, wadanda suka fi bayani a kan bangaren kwakwalwa da cututtukanta da bayanan falsafar binciken kimiyya irin na zamani.
~ Abul kasim Al-Zahrawi: Abulcasis (936- 1013AD): Wanda yake Balarabe ne wanda aka haifa a kasar Spaniya. Ya yi fice wajen zama likitan tiyata na farko na zamani a duniyar Musulunci saboda kirkiro kayan aiki na leka
wurare da dama na jikin mutum da ya yi, fiye da dari biyu, wadanda daga su ne aka kera na wannan zamani.
Shi ne kuma ya fara nuna wa duniya cewa za a iya samun juna biyu a wajen mahaifa saboda tiyatar da ya sha yi a wannan bangare.
Ya zama likitan Khalifan Musulunci a kasar Andalusiya, wato Khalifa Al-Hakam kuma ya rubuta littattafai da dama a kan aikin tiyata, wanda har yanzu akan samu manhajojin a littattafan wannan zamani. Domin karin bayani, za a iya bincikar Kitabut Tasrif.
~ Abu Ali Ibn Sina: Abicenna (980-1037): Shi ma mutumin kasar Farisa ne, wanda yake da baiwar kaifin hadda da tunani mai zurfi.
Ya haddace Alkur’ani yana dan shekaru goma kacal, sa’annan ya zama likita yana dan shekara sha shida. Ya yi aikin duba marasa lafiya kyauta a wannan birni kuma ya zama babban likitan Khalifan garin.
Daga baya ya yi hijra ya nufi yamma, inda a hanya ya rubuta kundaye a kan bayanai na kula da lafiya da aikin likita, ya kuma koyar da dalibai.
Wannan kundi wanda ake kira ‘kaanun fid dibb’ an dade ana amfani da shi a jami’o’in kasashen
yamma na wancan lokaci, a matsayin littafin koyarwa.
~ Ga kuma irinsu Ishak Al-Ruhawi dan kasar Turkiya, wanda ya fara bayani a kan tarbiyyar likitoci; wato yin tsantseni da taka-tsan-tsan a kan aikin likita da hukuncin da ya kamata a ba likitoci masu ganganci da aiki a cikin littafinsa mai suna ‘Adab Al-Tabib.’ Shi ne kuma ya fara bayanin cewa kowane sabon abu aka samar a kimiyyar likita, dole a samu wasu kwararru a aikin su zurfafa bincike don tabbatar da sabon bayanin ko karyata shi.
~ Sai kuma wasu da dama irinsu malaman wadannan da muka lissafa wadanda ba su yi fice kamar dalibansu ba. Misali, malamin Al Razi, Abu Hassan Al-Tabari, wanda ya yi fice a harkar lafiyar yara.
~ Akwai kuma irinsu Abu Alhassan Ibn Al-Nafis, likitan kasar Suriya wadanda Turawa ma ba su sani ba ko kuma suka sani amma suka ki ambatonsu.
Shi ne wanda ya fara bayanin yadda jini ke zagaya jikinmu, tun kafin ma a haifi Baturen nan William Harbey, wanda suka ce shi ya fara wannan bayani.
Ya Allah ka tabbatar damu akan daidai kasa Aljannar Firdausi itace makomarmu.

واَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

ILIMIN ADDINI KO NA ZAMAI

ILMIN ADDINI KO NA ZAMANI.

“Da yawan ƴan matanmu burinsu kawai ace sunkai wani babban mataki a cikin karatun zamani saɓanin na addini, tare da cewa idan kowanne a cikinsu yana da muhimmanci gareta ma, to haƙiƙa na addinin yafi matuƙar muhimmanci a gareta, domin dashi ne zata fuskanci wanene ubangijinta a gareta”

“Ko da kuwa kina da shaidar kammala karatun zamani, amma baki da na addini, to har yanzu ke jahila ce, kuma koda kuwa kina da shaidar kammala karatun addini ɗin amma kuma baki da kunya da tarbiyya, to lallai haƙiƙa karatun ki baiyi miki albarka ba” 

“Kunya da tarbiyya, ginshiƙai ne na ɗabi’ar musulunci, duk tarin karatun ki idan kika rasa su, to haƙiƙa kin rasa babbar ƙimah a gareki, karatun zamani ko na addini kowanensu yana da muhimmanci ga rayuwarki, amma kuma duk ilmin da babu tarbiyyar musulunci a cikinsa, to haƙiƙa wannan halaka ne ga ma’abocinsa”