Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers

Nasarorin Da Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Samu Cikin Shekaru Biyu, July 2020, Zuwa July 2022

Ga wasu daga cikin nasarorin shekarar farko July 2020 zuwa July 2021;

  • Ƙungiya ta samu karɓuwa a wurin al’ummar yankin Arewa.
  • Haɗin kan Marubutan yankin Arewa.
  • Magana da murya guda a madadin dukkannin Marubutan Arewa.
  • Kare martabar yankin Arewa, da al-ummar yankin, kan ƙalubalen da suka dinga fuskanto yankin.
  • Wayar da kan al’ummar Arewa game da abubuwan da zai amfane su, da wa ‘yanda ba za su amfane suba.
  • Wayar da kan al’ummar Arewa game da kin shiga zanga-zangar EndSars, da ‘yan kudancin Najeriya suka yi a shekarar 2020 wanda ya kusan zamowa fitina.
  • Daƙile manyan labaran ƙarya kafun su yi tasiri a cikin al’umma.
  • Nasarar da ƙungiya ta yi wajan tallata “Ranar Arewa” 20 July 2020 na kowace shekara, bayan wasu masu kishin yankin sun kirkireta, don tunawa tare da jawo hankulan manyan Arewa kan dukkannin kalubalen da yankin ke fuskanta.
  • Koyawa Marubuta yadda ake rubutu, tare da saka Gasa domin zaburar da Marubutan Arewa a wasu daga cikin jihohin Arewa.
  • Jawo hankalin hukumar WAEC a shekarar 2020 kan saka lokacin zana jarabawa a daidai lokacin da musulmai suke gudanar da Ibada a ranar Jumma’a, daga karshe hukumar ta gyara lokacin.
  • Jawo hankalin gwamnatin jihar Jigawa kan ƙalubalen da talakawa zasu fuskanta, idan aka daina karatu kyauta a Jami’a mallakar jihar (Free Education) bayan majalisar jihar ta yi yunƙurin mai da tsarin biyan kuɗi mai yawa ga dukkannin daliban jihar.
  • Jawo hankalin gwamnatin Tarayya da jihohi akan Tallafawa al’ummar da iftila’in ruwa ya shafa, a jihohi da dama na Arewa a shekarar 2020 da shekara ta 2021.
  • Jawo hankalin mahukunta dake da alhakin kunnawa manoman Rani ruwa a garuruwan Bunkure, Kura, Garin Mallan, Da Garin Karfi dake jihar Kano, bayan abinda suke nomawa ya fara bushewa saboda rashin ruwa.
  • Jawo hankalin gwamnatin jihar Adamawa wajan sasanta rikicin masu sana’ar adaidaita (Keke-Napep) a garin Numan dake jihar, duba da yadda dubunnan Al-ummarmu suka dogara da sana’an.
  • Jawo hankalin gwamnatin Najeriya da na jihohi game da halin rashin tsaron da ya addabi yankinmu na Arewa.
  • Jawo hankalin ‘yan kasuwa game da halin matsin rayuwa da al-umma suke ciki, sanadin tsadar Abinci.
  • Rubuce-rubuce tare da zaburar da matasa akan su tashi su nemi sana’a domin su dogara da kansu.
  • Tallafawa daliban makaranta da robobin cin Abinci guda 100 a jihar Zamfara.
  • Nasarar samun goyon bayan manyan Arewa Sarakuna, Dattawa, da sauran manyan dake kishin yankin Arewa, wurin gudanar da ayyukan kungiyar.
  • Gudanar da manyan taruka a wasu daga cikin jihohin Arewa da dama, domin haɗin kan Marubutan Arewa, tare da ƙarfafa zumunci a tsakaninsu don fuskantar duk wani ƙalubale da ya tunkaro yankin.
  • Jawo hankalin gwamnatin Najeriya kan ta gaggauta daukan mataki akan kisan kiyashin da ake yiwa ‘yan uwanmu ‘yan Arewa dake zaune a kudancin kasar.
  • Ankarar da gwamnati game da matsalar gurbacewar ilmi a cikin al’ummah.
  • Kira kirayen ƙungiya ga gwamnati kan a kawo ƙarshen satar yara a makarantu.
  • Jawo hankulan al’ummah kan muhimmancin ilimin ‘ya’ya mata.
  • Tunatar da al’ummah da faɗakar da su na tsawon kwanaki 30 na watan Ramadan a shekarar 2021.
  • Yunƙurin kawo ƙarshen bangar siyasa a kafofin sadarwar zamani.
  • Nasarar samun shiga gidajen Radio da Television a jihohi daban daban don bayyana manufar ƙungiya da kuma alfanun kungiyar.
  • Ƙungiya ta zaburar da dubban matasan Arewa kan su nemi basussukan da gwamnatin Tarayya take bayarwa domin dogaro da kai.
  • Ƙungiya ta samu nasarar ƙulla ƙawance da ƙungiyoyi mabanbanta don ciyar da yankin Arewa gaba.

SHEKARA TA BIYU

Nasarorin da ƙungiyar “Arewa Media Writers” ta samu a cikin shekara ta biyu da kafuwarta daga July 2021, zuwa July 2022.

Ga wasu daga cikin nasarorin;

  • “Arewa Media Writers” tayi nasarar kai koken al-ummar musulman garin Obajana dake Kogi, bayan ruwan sama ya lalata tsohuwar maƙabatarsu, har sarkin Obajana Kirista Engr. Dr Idowu Isenibi, Oba Of Obajana ya baiwa musulman garin Obajana makeken Fili Hetka 10 da samun gudumuwar kudi sama da miliyan daya da rabi.
  • Ƙungiya ta wayar dakan al-ummar Arewa, tare da kira ga al-ummar Arewa da su yi ragistar katin zabe a lokuta daban daban, duba da yadda ‘yan kudancin kasar suka yi mana fintinkau.
  • Ƙungiya ta dau nauyin horar da ‘ya’yan Ƙungiyar wajan koyar da su yadda ake rijistar katin zaɓe ta yanar gizo-gizo a wasu daga cikin jihohin Arewa.
  • Ƙungiya tare da hadin guiwar babban dakin karatu na jihar Kano ta yi nasarar bawa mutane 131 horo akan loyar da su ilimin na’ura mai kwakwalwa.
  • Jami’ar koyar da harsuna ta kasa da kasa “International University of Languages” (IOUL) dake jihar Sokoto ta dau nauyin koyar da membobin kungiyar “Arewa Media Writers” ilimin sanin aikin yaɗa labarai a zamanance “Social Media in ICT” tare da basu Certificate na shaidar karbar horo.
  • Kungiya ta ziyarci tsangaya tare da raba kayan tsaftace muhalli da kayan shayi a babban birnin Tarayya Abuja.
  • Ƙungiya ta bada gudummuwa wurin ganin an raunata jaridar “Sahara Reporters” kan batanci da ta yiwa Annabi (SAW) da yankinmu na Arewa, wanda har yau bata da wo cikin hayyacinta ba.
  • Ƙungiya ta jawo hankalin gwamnati kan gyaran asibitin garin Garun Babba, dake karamar hukumar Garun Malam a jihar Kano, wanda shugaban karamar hukumar ya dau nauyin gyarawa.
  • Ƙungiya ta wayar da kan al’ummar Arewa game da abubuwan da zai amfane su, da wa ‘yanda ba zai amfane suba akan rayuwar yau da kullum.
  • Ƙungiya ta yi tattaki zuwa Abuja, ta kaiwa shugabannin hukumomin tsaron Najeriya budaddiyar wasika kan halin da al-ummar Arewa suke ciki na rashin tsaron da ya addabi wasu yankunan dake yankin, tare da jawo hankalin su da su ƙara zage damtse don ganin an kawo ƙarshen rashin tsaron da ya addabi yankin.
  • Kungiya ta yi nasarar turawa shugaban kasar Najeriya buɗaɗɗiyar wasiƙa, ta gidajen jaridun DAILY Trust, Blueprint, VOA Hausa, da sauran manyan jaridun ƙasar, kan halin da al-ummar Arewa suke ciki na rashin tsaron da ya addabi wasu yankunan dake yankin, tare da jawo hankalin shugaban ƙasar da ya ƙara zage damtse don ganin gwamnatin shi ta kawo ƙarshen rashin tsaron da ya addabi yankin.
  • Ƙungiya ta yi Nasarar rubuta Littafi mai suna “RAYUWAR SAMARI DA ‘YANMATA A SOCIAL MEDIA” wanda aka yi bikin kaddamar dashi a watan junairun shekara ta 2022.
  • Ƙungiya tayi nasar gudanar da taron bita akan amfani da kafofin sadarwar zamani a jihar Filato.
  • Ƙungiya ta ja hankalin matasan Arewa a lokuta da dama, tare da wayar da kansu akan su guji bangar siyasa, don gobensu tayi kyau.
  • Ƙungiya tayi nasarar rubuta littafi mai suna “matar bahaushe” dake dauke da darusa iri-iri, anyi akayi bikin kaddamar dashi a jihar Jigawa.
  • Ƙungiya tayi nasarar horar da membobinta “Excos” reshen jihar Sokoto na tsawon kwanaki uku “3 Days Seminer” akan yadda ake rubutu.
  • Ƙungiya ta gudanar da rubuce-rubucen jan-hankali masu yawa a gidajen jaridu da kafofin sada zumunta, game da cin kashin da ake yiwa ‘yan uwanmu ‘yan Arewa dake zaune a kudancin Najeriya.
  • Kungiya ta yi nasarar horar da marubutan Arewa sama da 500 game da yadda ake aikin jarida da rubutu a kafofin sada zumunta, tare da basu takaddar shaidar karɓar horo (certificate) wanda yanzu haka yake gudana. Insha’Allah kungiyar “Arewa Media Writers” za ta gudanar da irin wannan seminar din a kowace jiha dake Arewacin Najeriya, don horar da dukkannin masu amfani da kafofin sada zumunta a kokarin kungiyar, na tsaftace harkar rubuce-rubuce a kafofin sada zumunta.
  • Ƙungiya ta gudanar da Rubuce-rubuce masu amfani ga al-ummar Arewa, da ba za su ƙirgu ba, tun daga watan July na shekarar 2020 da aka kafata har zuwa yanzu July shekarar 2022.

Mamallakin Wannan Kafa Tareda Alhakin Sanya Rubutu Gamida Hada Manhajar (Appllication).

Danna Maballin da Aka Sanya Manhajar Tarihi, Domin Saukewa Yanzu.

Edited by

(Paper Presentation Committee)

Abdulrahman Suleiman Zaria

Chairaman

Muhammad Kwairi Waziri

Secretary

@Coded Prints 08137556140

Ameera Yusuf Duguri

Treasurer

Huzaifa Ayuba

Member

Bashir Abubakar Gombe

Member

Walida Hussaini

Member


Shared By

ISMAIL HUSSAINI ALPHOLTAWY

Member

Hakkin Sanyawa Awannan Pejin tareda Mallakar Peijin

TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
                       GABATARWA
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
                            ﷽
Dukkan Yabo da Godiya Su Tabbata gin Ubangiji Allah Madaukakin Sarki, Wamda Yayi Komai da Kowace Iriyar Halitta Kuma yakyautata Surarmu Yabamu Tagomashi Yasnyamu Musulmi, Muna Gode Masa Bisa Wadannan Falala da Baiwar Arziqi Muna Salati da Sallamawa ga Fiyayyen Halitta Mai Tarin Matsayi da Girman Daraja Annabi Muhammad, Tsira da aminci Sutabbata agreshi da Iyalan Gidansa Da Sahabbansa, Da Dukkan Wadanda Suka bi Kyakkyawar Tafarkinsa Madaidaici Har izuwa Ranar Sakamako.

     Godiya Ta Musamman ga Iyayena da Malamaina, Wadanda Sukayi Dawainiya Dani Wajen Gina Rayuwata domin Tayi inganci Ina Rokon Ubangiji Yakarawa Rayuwarsu Albarka, Dani Dasu da masu Karatu Allah Yahadamu Agidan Aljannah Alfarmar Rahamarka Allahﷻ.
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
           ✍️Ismail Hussaini Adam
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

════ ❁✿❁ ══❁✿❁══ ❁✿❁ ══❁✿❁                                   
❁✿❁ ❁✿❁ALPHOLTAWY❁✿❁ ❁✿❁
════ ❁✿❁ ══❁✿❁══ ❁✿❁ ══❁✿❁

                       SHINMFIDA
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

_Tarbiyya Abace mai wahala, sai an dage an tashi tsayin daka sannan za’a dasa ta, ya ku Iyaye abu na farko daya kamata ku cusa a zuƙatan yaran ku, ko zuciyar yarinyar ku, ko kuma zuciyar ɗan ku Shine <TSORON ALLAH.
Domin samun nagartacciyar rayuwa a tare dasu da kuma tarbiyya mai kyau.

_Daga lokacin da yaro ya fara wayo, ya fara magana, yasan abincin da zai sanya a bakin sa, ko kuma abin sha to daga wannan lokacin ya kamata ku fara cusa masa jin tsoron Allah a zuciyar sa sannan su San Wane ne Manzon Allah S.W.A, Menene Matsayin sa a Wajen Al’ummar Duniya baki ɗaya da Wajen Allah.._
_ku cusawa yaran ku jin tsoron Allah ta hanyar sanar dasu ubangiji, abinda yayi umarnin a aikata da kuma abinda yayi hani a kai.kamin ku jefa yaran ku a makarantar boko ku fara tura su ta islamiya, malamai magada Annabawa nayin nasu kuma kuna yin naku to insha’Allahu tarbiyar yaran ku zata zamo mai sauƙi a wurin ku a lokacin da suka balaga suka gama mallakar hankalin kan su._
_Sa’annan ku cusawa yaran ku son ilimi na addini dana zamani Kasancewar ilimi Shine Ginshiƙin Rayuwa, hakkin kune iyaye ku bawa ƴaƴan ku ilimi wanda zai amfanar da su duniya da lahira, ba ƴaƴan ku kawai ba hatta ku iyaye yana da kyau ku samarwa kan ku ilimi. Shi ilimi haske ne mai haskaka rayuwar ɗan adam ta kowanne fanni ba kawai don neman aikin abin duniya ba..wanda mafi akasarin iyaye yanzu sun fi gina ilimin ƴaƴan su akan neman aikin abin duniya duk da cewar hakan ba laifi bane amma ya kamata mu nazartu muyi duba sose akan hakan, muyi faɗi tashi mu jajirce mu cije don ganin mun inganta rayuwar ƴaƴa da ilimi na addini domin da shine za’a tafi lahira saɓanin na duniya da inda muka same shi anan zamu bar shi._
_Sose muke tafka kuskure a rayuwar yanzu, an cusawa yara musamman mata son abin duniya, ku farka iyaye musamman iyaye mata, kin cusawa ɗiyar ki son abin duniya, kin cika rayuwar ƴar ki da burin abin duniya, kin ƙawata idanuwan ta da hangen abin cikin duniya an manta da mutuwa na tafe a kowanne lokaci. fatan ki, burin ki, mafarkin ki, jin daɗin ki, kwanciyar hankalin ki, tayi-tayi ta gama Secondary School ta Shiga Jami’a tayi degree tayi Masters Domin ta tara Muku Dukiya kuyi kuɗi duniya tasan da ɗiyar ku ko ɗan ku, ku huce takaicin duniya, hakan yana da kyau kuma ba laifi bane sai dai ta gefe guda a kwai illa, akwai matsala._
_Duk saboda wannan burin kun hana ƴar’ku aure, baku sashi a cikin lissafin da zai inganta rayuwar ƴar’ku, terming ɗin ku da terget naku shine kawai wancan duk saboda kada burdget naki ke uwa ya rushe (ga wasu iyayen). Shin idan anyi auren nan ba’a karatunne?, shin idan anyi auren nan ba’a aikinne?, shin idan tayi auren nan zai hanata dukkan muradin ki da kike son ya cika?. Kin Hanata yin Aure, ƴaƴayen mu ba duwatsu ba, b marasa lafiya, sha’awa na Damin ta, Samari kullum kawo mata hari suke, koda yaushe tana tare da su a makaran ta ko a waje, yau da gobe sai Allah ba fata ake ba, Allah ya tsare mu ya tsare mana ƴaƴayen mu._
_Mu riƙa kai zuciya nesa a kan yaran mu, duka da hantara da zagi da mummunar kalma basu zasu gyara yaro ba face ƙara lalata shi, ku dinga yawan yi masu adu’a a koda yaushe, kar ku faɗi kalma mara daɗi a kansu a lokacin da suka ɓata maku rai, don Allah iyaye mu iya bakin mu akan yaran mu, kar mu manta matsayin bakin mu akan su, fata na gari da adu’a ta gari a kansu shine dai-dai.._
_ku koyar da yaran ku da sabar masu yin sallah akan lokaci, ku koyar dasu adu’oin neman tsari da kariya kamar yanda ma’aiki ya koyar damu, ku zama masu lura da irin fina-finan da suke kallo domin kuwa shima kallo na ɓata tarbiyar yaro ya rusa duk ginin da kayi a baya, ku sabar masu da sauraran wa’azi kamar yanda ya kamata bakin ku ya saba wajen yi masu wa’azi._
_Haka Zalika ku kasance abin koyi ga yaren ku, kuyi ƙoƙarin aikata abu mai kyau tayanda zasu gani su ɗauka daga gare ku.. Ku zama masu zama da yaran ku kuna shiga cikin su domin jin matsalolin su, sannan ku zama masu sanya ido a duk abubuwan da yaran ku ke gudanarwa na yau da kullum tun kama daga kan ƙawaye, lura da irin abokan da yaro ke mu’amala dasu yana da kyau matuƙa da gaske, kuma hanya ce ta kiyaye yaron ki daga faɗawa ga miyagun abokai, idan har kun sanya ma yaro ido akan abokan tarayyar sa lalle tabbas zai ji tsoron zama da ɓata gari, zai yi duk yanda zai yi yaga yayi ƙoƙarin nisan ta da banzan abokai, fatan mu Allah ya kare mana zuri’a ya kuma shiryar dasu._
_mu guji kuma mu kiyaye bama ƙananun yaran mu da suka tasa wayar hannu, wannan waya da muke ganin ta haƙiƙanin gaskiya ba ƙaramar musiba bace, haɗari ce babba ga rayuwar ƴaƴa wallahi, don haka mu kiyaye basu waya musamman ta android a lokacin da suke da ƙarancin shekaru…. Ku zama masu sanya ido a kan shige da ficen ƴaƴan ku musamman ke uwa da kike zaune cikin gida koda yaushe, ba kowanne wuri ya kamata ku bar yaran ku suke zuwa ba, kuma ba’a koda yaushe ya kamata kuke barin su fita ba, duk da cewar rayuwar yanzu ta sauya yaran mu sunfi mu wayo da dabara… Idan dama ma da hali duk sanda ƴarki mace ta buƙaci zuwa wani wuri kiyi mata jagora, sannan ki hani yaran ki tarayya da ƙawaye barkatai._
_yake uwa ki zama mai sa’ido sosai da sosai akan ɗiyar ki mace wajen duban irin littafan hausa dana turan ci da take karantawa, ki tsoratar da ƴar’ki kiyi mata barazana da karanta littafin daya kauce hanyar kunya da tarbiyya, haka zalika idan ƴarki ta taso da sha’awar rubuta littafi shima ki tsoratar da ita ki mata baraza na ta yanda zata ji tsoro ta kuma kiyaye rubuta abinda ba shi da kyau, ki tunatar da ita cewa lalle ubangiji zai tsaida ita akan abinda ta rubuta, ki zama mai bincikar wayar ta akai-akai, ki zama ƴar jarida ga yaran ki, kisa musu ido akan duk abinda zasu samu, bi ma’ana dukkan abinda kika gani a hannun su ki sasu gaba ki titsiye su don jin daga ina suka samo shi?, taya suka same shi?, koda yaro zai ce maki ga wurin daya samu kuyi ƙoƙarin bin diddigin inda ya same su ɗin… Karku sabarwa yaron ku da riƙe kuɗi domin kuɗi na ɗaya daga cikin abinda ke rusa tarbiyar yaro._
_yake uwa ta gari, ki sanya ido akan fitar ƴarki daga gida wajen sanya sutura, ki tuna musulunci ki tuna faɗin Allah maɗaukakin sarki a cikin littafin sa mai tsarki mai girma, ki tilastata ki sabar mata da suturce jikin ta a yayin da zata fita… Idan mai sanya hijab ce ki sanya ido wurin ganin kayan data sanya aciki da kuma abinda ke ƙunshe cikin jakar hannun ta, domin wasu ƴaƴan namu kan yaudare mu da fuska biyu.. Ki hani yarinyar ki da amsar kuɗin hannun samari, ki kuma hani yaran ki da saurin miƙa hannu, ki hani yaran ki da kwaɗayi da son abin duniya._
_ya ku iyaye na gari, daga lokacin da kuka fahimci ƴaƴan ku na buƙatar aure, lalle kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, hakan shi zai hana yaɗuwar ɓarnar dake faruwa a doron ƙasar mu, ba komi ke jefe ƴaƴan mu cikin baƙincikin rayuwa ba sai wajen tauye masu hakki da muke, musamman ƴaƴa mata, don Allah iyaye da zarar kun fuskanci ƴaƴan ku na son aure kuyi masu domin shine mafita kuma shine kariyar su daga faɗawa mummunar halaka, kuma shine yayewar damuwar da za’a shiga a gaba._
_Daga ƙarshe karmu manta zamu cimma kyakykyawan burin mu ne akan tarbiyantar da yaran mu wajen yawan tunsar dasu faɗin Allah da Ma’aikin Allah._
_Ya Allah kasa mu dace, Allah kuma ya bamu ikon sauke hakkin ƴaƴan mu da Allah ya ɗora mana domin Ƴaƴa Amana ce Allah ya bamu.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
                 ASALIN TARBIYYA
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

Kalmar tarbiyya, ararriyar kalma ce daga Larabci (التربية aka Hausantar da ita. Kalma ce magamaiya, wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta renon jikin yaro; hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa, tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a, a al’ummance da kuma ɗaiɗaiku.

Ƙololin buƙatar tarbiyya ita ce gina cikakken mutum mai amfanar da kansa da kuna waninsa.

Bisa la’akari da wannan faffaɗar ma’ana da wannan kalma take da ita, rubutun zai taƙaitu ne wajen yin magana a kan abin da ya shafi ruhi da kuma cuɗanya. Zai yi magana bakin gwargwado a kan ma’anar tarbiyya, manufarta, amfaninta, masu bayar da ita, jerin wasu kyawawan halaye da kuma yadda Bahaushe yake bayar da tasa tarbiyyar, da sauransu bakin gwargwadon iyawa.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Ma’anar Tarbiyya
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

Saboda zamowar kalmar tarbiyya mai tushe a Larabci, zan kawo ma’anarta a Larabce da cewa, “Ita ce ayyukan ɗaukakowar halittu, wato ƙarawa mutum mutumtaka domin ya samu kaiwa cikakkiyar daraja matabacciya a jiki da aiki da ruhi da kuma cuɗanya”, Abu Hamza (2013). Daga wannan ma’ana za mu iya fahimtar cewa, tarbiyya reno ce. Saboda dukkan abubuwan nan da aka ambata suna ƙunshe cikin reno. Shi kuwa reno ana yin sa ne mataki-mataki. Sai dai ya fi zafi a tsakanin ranar farko ta haihuwa zuwa shekara uku. A wannan tsakanin komai yi wa mutum ake yi.  Ɗawainiyoyin suna fara raguwa ne bayan an yaye mutum wato daga watanni 15 na haihuwa zuwa shekaru 2. Daga wannan mataki yawancin yara sukan fara yi wa kawukansu wasu abubuwan kamar ci da sha da sauran ƙananan abubuwan rayuwa.

Daga wannan mataki na yaye kuma, sai a shiga kiwonsa, da ma’ana ta lura da zirga-zirgarsa ƙut-da-ƙut har zuwa kamar shekaru 5 ko 6, idan zai kai kansa mahallaka ko dai a ce da shi bari, ko kuma a je a ɗauke shi ko a janye shi da sauransu.

Idan ya haura shida kuma, to ya fara kai wa matakin da zai fara cuɗanya da wajen gida, sai kuma ya shiga makaranta. A makarantar ma renonsa ake yi, saboda a koyar da shi ne alaƙoƙin da suka shafi rayuwarsa ta duniya da kuma ta lahira, iya tsawon karatunsa da ma rayuwar baki ɗaya.

Saboda haka idan muka koma kan waccar ma’ana ta tarbiyya muka ciro kalmomin cewa, ayyuka ne da ke ɗaukaka halitta, za mu gan su cikin wannan ɗan taƙaitaccen bayani game da reno da na yi.

Ana kuma iya cewa, tarbiyya ita ce horas da yaro kyawawan halaye domin ya zama mutum nagari. Ko kuma a ce, hanya ce ta nuna wa yaro yadda zai tashi da kyawawan halaye ababen yabo a cikin jama’a.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Manufar Tarbiyya
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Babbar manufar tarbiyya ita ce samar da mutum mai kyawawan halaye ababen yabo domin ya zama mai amfanar da kansa da kuma waninsa.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Amfanin Tarbiyya
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Amfanin tarbiyya ba zai ƙidayu ba, amfaninta na ƙarshe; wato maƙurar amfanin nata shi ne mutum ya samu kansa a gidan Aljana a lahira, a nan duniya kuma ya zama son kowa, ƙin wanda bai samu ba.Waɗannan gajiyoyi da za a ci; duniya da lahira, su ne maƙura, sai kuma wasu ɗaiɗaikun abubuwa da zan lissafo kamar haka:

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Tsarkake Halaye: Tarbiyya tana tsarkake halayen mutum ya zama mai kyawawan halaye.
Sauƙin Rayuwa: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya rayu, rayuwa mai sauƙi. Saboda zamowarsa mai wadatar zuci.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Farin Ciki: Mutum mai cikakkiyar tarbiyya akan same shi cikin annashuwa a mafiya yawan lokutansa. Saboda koda wani abu can gefe ya ɓata masa rai, to yasan idan ya zo yin hulɗa da wani wanda abin bai shafe shi ba, sai ya danne wancan ɗacin a ransa shi kaɗai.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Girma da Ɗaukaka: Kyakkyawar tarbiyya tana ɗaukaka darajar mutum a idon mutane a nan duniya, haka nan ma a wajen Ubangiji Mai Girma da Buwaya.
Kwarjini: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya zama mai kwarjini.
Matakan Bayar da Tarbiyya.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Akwai matakai ko hanyoyi da ake bi wajen bayar da tarbiyya da suka haɗa da nuni, lura, umarni da kuma hani.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Nuni: Abin da ake nufi da nuni a nan shi ne aikata aiki a aikace, wanda daga nan shi wanda ake tarbiyantarwa zai gani ya koya. Tirƙashi, masu iya magana sun ce; “Idan mutum ya ce zai baka riga, to duba ta jikinsa”. Wannan magana ta zo daidai da faɗin Larabawa cewa; “Maras abu baya bayar da shi”. Saboda haka dole ne mai bayar da tarbiyya ya zama mai tarbiyya.
Wannan hanya ta bayar da tarbiyya ita ce mafi tasiri da kuma muhimmanci wajen bayar da tarbiyya. Saboda haka dole ne masu bayar da tarbiyya; iyaye, malaman makaranta da sauran jama’a suma su zama masu tarbiyya. Misali, dole iyaye su zama masu tsafta a aikace, kafin su dasa halin tsafta a zukatan ‘ya’yansu. Idan yaro ya tashi ya ga iyayensa suna share gida tsaf-tsaf, basa barin kwanon abinci da dauɗa, basa jefar da sutura ko’ina a ciki da wajen ɗaki, to a haka shi ma zai girma mai kula da tsafta. Kuma zai tashi shi tsafta ya sani bai san ƙazanta ba. Saboda haka da zarar ya fara zuwa makaranta malaman makaranta ba za su wahala da shi ba.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
Umarni da Hani (Kwaɓa): Umarni shi ne a riƙa gaya wa yaro yi kaza. Misali, idan yaro ya tsoma hannun hagu cikin kwanon abinci, ko ya riƙe abinci da hannun hagu zai kai bakinsa, sai a gaya masa cewa, wannan ba shi ne hannun cin abinci ba, ga na cin abinci nan. Da haka zai gane hannun dama dana hagu.
Shi kuwa hani shi ne kore abu. A wannan gaɓar kuma yana nufin kare ko dakatar da yaro daga aikata aikin da ba mai kyau ba. A cikin wannan misalin dana kawo a sama, akwai gaurayen hani da kuma umarni. Yaro ya tsoma hannun hagu domin cin abinci, sai aka hana shi; wato aka dakatar da shi daga cigaba da amfani da hannun hagu. Sannan aka gaya masa; wato aka umarce shi da amfani da hannun dama.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════Lura/Kula: Lura ko kula, suna ɗaukar ma’anar saka ido a kan kai-komo na yaro; wato zirga-zirgar yara. Wannan hanya ta lura, cikamakonta shi ne kwaɓa. A nan, iyaye za su saka ido sosai game da zirga-zirgar ‘ya’yansu, duk lokacin da suka ga wata baƙuwar halayya maras kyau, sai su yi maza-maza su ɗauki matakin da ya dace tun kafin ta zama jiki.
Da zarar yaro ya fara fita wajen gida domin zuwa makaranta; wato daga shekaru uku zuwa sama, to fa dole iyaye su riƙa lura da shi sosai, saboda yanzu kuma ya je ya gwamutsa da sauran yara daga gidaje barkatai. Saboda haka idan iyaye basu saka lura ba, to tarbiyyar ‘ya’yansu sai ta koma barkatai.

═════ ❁✿❁MATAKAN TARBIYYA══════ ❁✿❁

Dasunan ALLAH Mai RAHAMA Mai JINKAI.
Haqiqa tarbiyya dolece a addinin mu na musulunci musan man ma na iyalanka/ki
Domin ALLAH MADAUKAKI yana cewa:

ﯾﺎ ﺃﯾﻬﺎﺍﻟﺬﯾﻦ ﺁﻣﻨﻮ ﻗﻮ ﺃﻧﻔﺴﮑﻢ ﻭﺃﻫﻠﯿﮑﻢ ﻧﺎﺭﺍ ﻭﻗﻮﺩﻫﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻭﺍﻟﺤﺠﺎﺭﺓ
Awannan aya ALLAH yayi umarni ga Muminai dasu Kare kansu da iyalansu daga wata wutta Wanda yakasance makamashinta mutane ne dakuma duwatsu.
ALLAH UBANGIJI katsaremu amin ya RABBI. Awannan ‘Bangaren Nakeson nayi rubutu domin yan uwa musulmai su anfana.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI ya dafamin.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════MATAKIN FARKO
(Neman Aure zuwa da yakai 5yrs)
Dole Akan kowa Idan yazo neman aure
Yanemi Mai addini Da hali nagari Da kakkyawar zuciya. Ba kawai kyawun fuskaba ko wani martaba ko nasabar Abokin zama ba. Kuma yazamto anyi auren tanasonsa yana sonta.
Domin hakanne Zaisa suji dadin zamantakewarsu ta Aure Kuma hakan Zaisa yayansu sutaso dason junansu Da Bin doka ko umarnin Da akayi masu. Domin kada yazamto uwa tace fari uba yace Bahakaneba Baki yake. Bayan haka
Yazama dole asakawa yaro kakkyawar suna alokacin dayake jinjiri. Yazama dole ka karantar Da matanka tsarin tarbiyyar addinin musulunci ko kasa akarantar da ita Awannan sahar kokuma MA kafin wannnan lokacin. Ma’ana kafin ta sami d’a (yara).
Domin kaso saba’in Cikin Dari (70%) Na Tarbiyyar cikin Gida maqasudinsa na uwace. Yazama dole takasance Mai Lura da Meke gudana me sukeso me yakamata suyi ko so Bari duk wadannan uwace takeda hakkin koyar da yaranta.
Dakuma koyardasu Ibaadaat Kamar Sallah Azumi Dakuma koyamusu karatun Alqur’ani da tilawarsa dama haddarsa. Har sukai 10yrs Kafin daga bisani Sai Aturasu Islamiya. Sucigaba da karatu daneman ilimin addini. Hakan zaisa sutaso da ganin girman iyayansu. Dama duk wanda yagirmesu tayadda basai ance ga malam waneba kafin sudaina abinda sukeyi.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════MATAKI NA BIYU
(Daga 5yrs zuwa 15 to 18yrs)
Dolene akan iyaye su San abokanan yayansu, Susan Kuma menene alaqarsu dasu Domin duk kyawun tarbiyyar dakasamu agida abokai sukan wargazashi, matsawar dakayi abota da marasa tarbiyya koda baka zama tamkarsu ba. Zaka rudu da wani hali acikin munanan halayyarsu.
Yazama dole iyaye su bawa yayansu tarbiyyar addini da wayewar rayuwa tahanyar sanaddasu yadda zasuyi addini da hikimomin tsara rayuwa bisa kykkyawar tsari. Kamar koyamusu dabarun kare kai da addu’o’in neman tsari da kariya. Da sanardasu tarihohi Wanda zasu sami hikima da, wa’azozi acikinsa. Domin abinciken masana kwakwalwar dan adam sun yarda akan cewa kwakwalwar dan adam takan bude da adana bayanai alokacin da mutum yake dan shekaru takwas (8) zuwa Sha biyar (15) koda haddane mutum yafi nutsuwa dashi awannan lokacin Inhar kaga yaro ya natsu awannan lokacin to tabbas ana kyautata zaton shiryayye ne. Inkuma ya kangare kuwa yanada wuyar shiryuwa Yakamata iyaye sudunga zama da yaransu suna zantawa dasu domin suji damuwoyi da bukatunsu, Harsu san tahanyar da zasu bullo musu gurin bada shawara ko kore musu matsalarsu tarayuwa.

══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════MATAKI NA UKU NAKARSHE
(Daga 15/18yrs. zuwa auraddasu)
Yakamata iyaye su lura da yayansu su san menene wane/wacce tafi/yafi kwarewa akai saisu dage gurin nema masu mafita ta hanyar basu tallafi ko jari domin samun damar gudanar da harkokin rayuwarsa cikin sauki batare da yana zauneba saidai kullum abashi.
Domin hakan yana kashe zuciyar mutum yazanto baya iya kafuwa da kansa balle ma har yagina wasu. Saidai kullum a bani_bani sai kuma bin abokai da yawace yawacen banza da hofi, da bin bangar siyasa, wadda daga karshe ke jawo mutum yakoma ta’asa da ‘barna acikin al’uma kokuma ma yakama shaye_shaye da bin mugaye mutane. Duk adalilin rashin aikin yi. ALLAH ya tsaremu da zuri’armu baki daya.
Rashin aikinyi na daya daga cikin abubuwa mafi girma wanda suke lalata tarbiyya arayuwar mutane.
Allah ka bawa iyayen mu hakurin zama damu kasauke musu hanyar dazasu tarbiyyantar damu tarbiyya ta Addinin musulunci, ALLAH kajikan maifina kahaskaka qabrinsa.

`YAN UWANA MATASA!!! MU KOMA GA ALLAH
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

   Rayuwar Matashi abin tausayine, Kana fama da Quruciya Ga kuma bakin Al`uma akanka. Idan za`afadi Damuwar Al`uma Dari, Kaso  Chasa’in da Biyar (95) Na Matasa ne.
         Qalubale Garemu Matasa, Ban cire kainaba domin nima cikin Quruciya nake.
Tabbas Muna Fuskantar Qalubalen rayuwa daga ´Bangaren zamantakewa, Har da Ibada. Saidai Raunin zuciya kuwa ya danganta da Yadda mutum yataso, Wahala ko Qunci, Tarbiyya ko Akasin hakan (Garari), Riskar iyaye da Rai ko Tashin Maraici. Idan Kasamu yin Makaranta Fani’ima (Haka akeso) In MA bakasamu ba Kaidai kada Kabar Neman ilimin Addini Domin Shidin Yalwatacce NE. Ako Ina akwaishi Amma kayi Takatsan_tsan Maluman da  Kake Saurara. KADA kabi Maison Zuciya.
Dukkan Wadannan Matsololin Rayuwa ce, Kirata Agaremu Shine, Mugane inane hanyar tsira kuma mecece mafita ta rayuwar mu, Ina Muka fito, Ina Zamuje, Me zamu Riska, Ina Tafiyar zata Tiqe?

MATASA BAYIN ALLAH NE
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

Kada Mushagaltu da Rudin Rayuwar duniya, Ko kuma Yanayin juyin Rayuwa yasanya Mu ´Bata Rayuwar mu da Shaye_shaye, ko Ta`addanci, ko Daba, Da zama `Yan Iskan gari.
       Mugyara Rayuwarmu tahanyar kaucewa had`arurrukan da Suka shafi aikata Munanan Laifuka, Mutuna Cewa Allah yake bada arziki, kuma Shike bada lokaci dakuma damar Amfanar Arzikin namu. Zamu iya tarawa ahanyar ‘Barna (Haram) Amma mu mutu, bamu ciba kuma Hisabinta Nanan Akan mu.
Zamu iya shiga Matsalar Rayuwa, Mugur´bata Rayuwar mu da Shaye_shaye ko garari Sanadiyyar wani, ko wata Mattsala, Mun manta cewa ga Allah za a koma kuma akwai hisabi, Shifa Allah ako ina Mukayi kuka Yana jinmu. Idan Ka Shiga Mummunar Hali Mu tuna da ALLAH. Sannan Mu dunga Yawan Ambaton Allah d`in kada Muce zamu Sha kwaya, ko Mu Kunna Sigari, Yi Hakan kamar An watsa maka Kashine ka Wanke da Kwata. ‘Barna bata Kawar da ‘Barna.

Mu waita yin Istigfari, Wata Qila Jarrabawace ta Yawan zunubin mu, Allah yakeso ya kankare mana. Allah ya yafe mana Yakuma ´Dauramu akan Shiriyar Addininsa, Yakuma Tseratar damu daga Tabewa da Halaka, Allah ka Albarkanci Iyayenmu, da Malumanmu, da Yayunmu, da Kannen mu, Damu kanmu, Wadanda Suka Rasu a Gafartamasu Musamman Mahaifina Allah kajikansa Da Rahama

KUYI TARBIYYAR ZUCIYOYIN ‘YA’YAYENKU DA ‘KANNENKU!!!
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
══════ ❁✿❁ ═══════════ ❁✿❁
Zaku gyara Ahaliku Masu Zuwa
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

      Malaman Tarbiyya Sukace Idan Yaro yana ‘karami Daga Haihuwarsa Har Yakai Shekaru Bakwai (7), Ba’a Dukansa Ko Yimasa Mummunar Tsawar Dazai Ta’ba Zuciyarsa Domin Awannan Lokaci Yanada raunin  Zuciya. Sannan Dolene Yazama Ana Kula dashi ta Dukkan Yadda Zai Shiga Ko Fitarsa Sannan adunga Kyautata masa Suturarsa Ma’ana Kada Adunga  Sanya Masa Sai Sutura ta Mutunci Da Kamala, Kuma Dolene Iyaye Sudinga Sa Ido Akan Ayyukansa Da Yanayin Kitsonta Ko Askinsa.
     Bugu Da Qari Iyaye Dolene akansu Sudinga Lura da  Yanayin Himmarsa Abangaren Sana’a Ko Karatunsu, Hakazalika Awannan Lokaci Ba’a Barinsa Yayi Ko Tayi Tafiya Mai Nisa! Wanda Zaizamo an Wuni Ba’a Ganshi Ko Anganta ba, Saidai Idan Makarantane Domin Sunce Awannan lokaci Yaro Kamar Sarkine Ko Shugaban Kasa Tsakaninsa Shi Da Iyayensa, ( Shine Sarki Iyayensa Fadawansa).
   Sannan Sukace Idan Yaro Ya Haura Shekaru Goma (10 Yrs): Babu Laifi Za’a iya Dukansa Idan Yayi Laifi Mai Girma Amma ba Dukan Dazai Cutar da fatarsa ba ko Yadugunzuma Zuciyarsa ba, Kuma Dalilin Dukansa/tan Zai Zamo Daliline Na Ana Ladaftar dashi Bawai Anayi bane Domin Abata ransa, ko Dan Abata Ran Mahaifansa Ba. Idan Har Antarbiyyantar Da Yaro ma Daga Farko Da Lallami Sukace ”Zaiyi wahala Yazama Sai Andakeshi Kafin Ya Ladaftu” Wai Kafin Yayi Abinda akeso.

  Idan Kuwa Yaro Ko yarinya Sunkai Shekaru Sha Biyar Zuwa  Sha Shida (15–16), To Awannan Lokacin Yazama Abokin Hira Da Abokin Harka, Ma’ana Za’akoyar dashi Sabgogin Rayuwa Kamar karfafashi Abangaren Abinda yafi Karfi Na Karatunsa Ko Sa’ana Ko Dukkansu, Sannan Idan macece do Dolene akoyarda ita Kula Da Dawainiyar Gida Da Hidimar Daya Shafi abinci dadai Wasu Hidimomin Dasuka Shafi Rayuwar Gida, Sa’annan Yana dakyau Iyaye Su Dinga Shawari Dasu Awannan Lokacin. Domin Tantance Zurfin Tunaninsu Da Hankalinsu, Kuma hakan zaisa suma idan suna Bukatar shawara Suma Suzo Garesu, Domin Sunsan Iyayensu Suna girmama tunaninsu Kuma Suma Suna Nemansu Da Shawarwari, Idan  Har Iyaye suka Kuskure Awannan Lokaci To Tabbas Zasuyi Asarar Kaso Mafi Yawa  Na Morar ‘Yayansu, Domin Awannan Lokaci ne ‘YA’YA Suka Fara Fuskantar Dawainiyar Rayuwa Wacce take Iya Zama Nasara Ko Akasinta, Kuma Awannan lokaci Suke Bukatar Anusar Dasu Ahanya Domin Samun Ingantacciyar Rayuwar Da Suma Zasu Tarbiyyantar Da Wasu.

      Awannan Lokaci Kuma Ana Bukatar Iyaye Sudinga Nusar Dasu D a Nasiha, Ba Mummunar magana Hatta Daga Yayu; ( Ba Tir, Allah wadai, Allah tsine, Kayi/kinyi Asara, Allah Ya’isa) Dolene Yayu Da Iyaye Su tsare Harsunansu Daga furta irin Wadannan kalmomi Da Makamantansu Ga ‘Ya’yansu, domin Suna Tasiri Wajen Tarwatsa Rayuwar Yara Duk Tarbiyyanda Suka Samu Bazai Anfanesuba, Zaicutar Dasu Kuma Yakan Shafi Dukkan Sashin Rayuwarsu, Abinda yadace Na Furuci Tsakanin Iyaye Da Yara Ko Yayu Da Kannensu Sune: Sanya Albarka Da Yafiya Da Abinda Zai Faranta Rayukan Juna, Kada Kuyi Sakaci Da Neman Afuwar Juna Dakuma Yafewa Juna Hatta Idan ma Ba Laifin Da Ya Bayyana, Domin Yafiya Tsakanin Iyaye Da ‘Ya’yansu Ko Yayu Da ‘Kannensu ( Man Motan Nasara Ce) Matukar Babu Shi Nasarar Yara Bata Samuwa.

  Daga Karshe Nasiha ta Ga IYAYE Da YAYU Amatsayina Na ‘Da itace;
Dan Allah IYAYE Kuriqemu Amatsayin Amana, Sannan Kusani Sakacinku Damu Zai Iya Kailu Wuta Dukanmu Subhanallah, ALLAH yakare! Kusani Awannan Zamanin Dolene Iyaye Da Yayu Sudinga Lura Wayoyin ‘Ya’yansu ko Qannensu, Haka Kwatsam Kace Wane/Wance; Bani Aron Wayarka Ko Wayarki Ka/ki Ciremin PinCode d’in, Kada Kuji Nauyin Hakan inkunyi Sakaci Kuwa Lahirarku ce Da Tamu Zata ‘Baci, Subhanallah Kada Muzo Alahira Muna La’antar Juna! Wa’iyazu BILLAAHI!!!
Allah Yatsare.
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════
✍️Ismail Hussaini Alpholtawy
══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════

ZATIN UBANGIJI

SHAUQI CIKIN AL AMARIN GAIBIYYA

Kasantuwar Ubangiji A Buya Bai zama tawaya Ga Imanin Mai imani Sai dai Yana kara imanine ga Mai imani Yayin da Yake Halarto da Imani Azuciyar Mara shi Matukar ya Kasance Mai Nazarin Lissafin Hangen Nesa da tunani Mai Zurfi.

Imani Gatane  da Yanci na Samar da Sukuni Azucikatan Bayi gamida Samuwar Hasken Zuciya dana Ruhi, Wanda Yazamo Tasirin Samuwar Kyakkyawar Rayuwa Mai Inganci Aduniya dakuma Samun Kyakkyawar Sakamako Bayan Mutuwa.
Wannan Duk darajace da Muqami amma ga Wanda Ya Gasgata Ubangiji Kuma yake Tsoran sa, Shi kadai Baya Tsoron Sharri Sai abinda Ubangijiﷻ Yanufa Shi zai Iya faru Gareshi arayuwa.

Ubangiji ya Boye Zatinsa Na Wanzuwar Siffarnan tasa Madaukakiya, Yayi mana gata Ya Bayyana Mana ilimin Saninsa ta Hanyar Turomana Da Annabawa, Ya Rayamu bisa rayuwa Ingantacciyaya, Bamu kasance Cikin dimuwa da Makantacciyar Zuciya ba.

   Makauniyar Rayuwa itacee Rashin gane Waye Ubangiji Hakan ke tabbatar dakai Ahalaka da Tabewa Kasantuwar hakan zai sanya Maka Kaskantar da Kanka ga Abida Shine yakamata ya Girmamaka, Akasin Hakan Kuwa zai sana Ka koma kana Nema Agun Wanda Saika bashi kake kuma Rokonsa.

  Ka Kaskantar da kanka ga ubangiji da Qaramin Aikinka ga Mai Halittawa Kuma ka Rage burinka ga Duniya Domin Hidima da Bada lokaci cikin Bautawa Maqaginka domin Gyara wa  Rayuwarka na Gaba.

KUJI TAUSAYIN MARAYAN ALLAH

Bansan me Nayi mussu ba
Nufata da Sharri suke basu barniba

Nayi kukan Zuciya
Har na Ido Hawayena Basu fad’i ba

Ganinan na Sarqafe
Igiyar suce Suka ya’ban nashiga fargaba

Ba Mai Karni Ni
Inhar JALLAH bai Qadarinsa akaina Ba

Zasuyi dana Sani
Biyar Dasuke fatansu Bazai Cini ba

Natashi Da Safiya
Qadarin gobe Bazan Sanshi ba

Tafiyar Tayi Nisa
Garin danaje Basu Sanni ba

Nasamu Masauki
Agidan danake Ba’aso Ganina Agefe ba

Suna So Muyi Fira
Kuma Zancena Bazasu Suqi Jinta ba

Gareni Sun Tako
Mararina Suke Kullum basu Barniba

Ya Rabbi Ka nufa
Gani Zamanin da ake Gudun Mai gaskiya

Ya Mai Raya Rayayyen Marayan Daya Rayu Cikin rayuwa da Ruwayar Maruwaita Rayayyun Ruhi da Ra’ayin Ribar Rabauta A Ranar Ramawa Ramammun Ruhanan da suka Rayu Cikin Ramawa Rayayyen Rai Ra’ayinta Randa Ba’a Raina Rukunin Ribatar Raunin Ruwayar Rayayyu.

Ismail Hussaini Adam

Alpholtawy

JAWABAI MUHIMMAI

FASAHAR ZAMANI

Menene capacitor? 

Dauki masu gudanar da wutarlantarki guda biyu (abubuwan da suka bari Wutarlantarki ta ratsa su) sai ka raba su da insulator(kayan da ba su barin wuta ya ratsa sosai) sai kayi capacitor: wani abu da zai iya adanamakamashin wutar lantarki. Kara makamashinlantarki ga mai iya aiki shi ake kira caji ; fitar dakarfin daga mai iya aiki shi aka sani dadischarging.

Capacitor yana dan kama da baturiya, amma yanada wani aiki daban. Baturiya na amfani dasinadarai don

adana makamashin lantarki da sake shi a hankalita

hanyar zagaye; wani lokaci (a yanayin agogonkwata) zai iya daukar shekaru da dama. Mai iyaaiki yana sakin karfinsa da sauri-sau da yawa acikin sakanni ko kasa da haka. Idan kana daukanhoton flash, misali, kana bukatar

kyamararka don samar da babban burst na haskea cikin fraction na sakan daya. Wani mai iko daaka hađe da bindigogin flash na ‘yan sakanni taamfani da makamashi daga batirin kyamararka.(Yana daukar lokaci kafin caji capacitor shi yasayawanoci dole ka jira kadan.) Da zarar an caji maikarfin, zai iya sakin duk karfin nan take ta hanyarxenon flash bulb. Zap!

What is a capacitor?
Take two electrical conductors (things that let
electricity flow through them) and separate them with an insulator (a material that doesn’t let electricity flow very well) and you make a capacitor: something that can store electrical energy . Adding electrical energy to a capacitor is called charging ; releasing the energy from a capacitor is known as discharging.
Photo: A small capacitor in a transistor radio circuit.
A capacitor is a bit like a battery , but it has a different job to do. A battery uses chemicals to store electrical energy and release it very slowly through a circuit; sometimes (in the case of a quartz watch) it can take several years. A capacitor generally releases its energy much more rapidly—often in seconds or less. If you’re taking a flash photograph, for example, you need your camera to produce a huge burst of light in a fraction of a second. A capacitor attached to the flash gun charges up for a few seconds using energy from your camera’s batteries. (It takes time to charge a capacitor and that’s why you typically have to wait a little while.) Once the capacitor is fully charged, it can release all that energy in an instant through the xenon flash bulb . Zap!

JAWABANMU MUHIMMAI