NASIHOHIN RAYUWAR

IDAN KAJI TSORON ALLAH ZAI BAKA MAFITA.

Hausawa suka ce bin Allah maganin wayyo Allah, tabbas hakane, lallai idan mutum yabi Allah kuma yaji tsoron sa, ya bauta masa, ya kuma kaucewa saɓa masa, to haƙiƙa bazai koka ba, kuma lallai Allah zai sanya masa hanya madaidaiciya wacce zai bita ɗoɗar ba tareda ya karkace ba”

“A rayuwar ka idan ka kasance mai yawan jin tsoron Allah abisa dukkanin ilahirin lamuranka, to lallai Allah ɗin zai baka mafita daga dukkanin wani ƙunci, bala’i da masifu, kuma zai azurta ka ta hanyoyi mabanbanta waɗanda baka san su bama, amma sharaɗin ɗaya ne, shine sai kaji tsoron Allah kuma ka guji dukkanin nau’ukan saɓon Allah”

Allah ta’ala yace: Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (yaji tsoron Allah) Allah zai sanya masa mafita. () Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma’ishinsa. Lallai Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama’auni ga dukan kõme.
aT-Talaaq 2-3

HAKIKA AN TAUYE HAKKIN AL’UMMAR AREWA

Ma’aikatar cikin gida (Ministry of Interio) karkashin jagorancin Minista Ra’uf Aregbesola ta fitar da sakamo na jahohin Nigeria matasa wadanda suka samu nasaran daukar su aiki domin cike gurbi a hukumomin tsaro na Civil Defence, Correctional, Fire Service da Immigration
Amma a cikin wannan sakamon an cuci yankin jihohin Arewa, an danne musu hakkinsu, kashi 99 cikin 100 na wadanda aka daukesu aikin daga Inyamurai ne sai Yarbawa, tsakani da Allah me ya kawo Sunan Ikechukwu jihar Jigawa?
Kuma a haka wakilan Arewa zasu zuba ido ba zasuyi magana ba?
Wato an mayar da ‘yan Arewa saniyar ware, an mayar damu marassa amfani kawai, amfanin ‘yan Arewa sai lokacin zabe yayi azo neman kuri’ah ana watsa mana hatsi daga cikin mota kamar kaji muna caccaka
Mu dai Arewa an barmu da yiwa juna hassada da kyashi da munafurci, mutanen kudu sun mayar da hankali wajen kokarin gina ‘yan uwan su, sun mamaye dukkan ma’aikatu dake babban birnin tarayya Abuja, har a cikin jihohin Arewa inda ya kamata a ga sunan Hausawa sai dai aga sunan Inyamuri, saboda sun fimu hadin kai da son juna ba tare da nuna banbanci ba
Wannan babban kalubale ne wa Ministocin Nigeria ‘yan Arewa, ya kamata ku dauki darasi da abinda Ma’aikatar cikin gida tayi, ku dena nuna tsoro ko shakkar masu zagi da suka, tabbas kuma zaku iya yin abinda Minista Ra’uf Aregbesola yayi a ma’aikatunku idan an tashi diban aiki, shugaba Muhammadu Buhari yayi iya bakin kokarinsa da ya baku mukami, saura kuyi abinda ya dace
Allah Ka taimaki Arewa da ‘yan Arewa Amin

HADIN KANMU HANYAR TSIRARMU

💾📱📚

Ismail Hussaini Alpholtawy

  Rayuwa ta ishemu Wa’azi
Malamai kuji tsoron Allah wajen Karantarwa kada kusa Son Zuciya. Domin tsira da mutuncinku aduniya da tsira da imani aran Qiyama

Dalibai muji tsoron Allah, Mufahimci junananmu Yayin Sa’bani, Kada Muce komai Malam  wane yafada Gaskiya ce, Binciken Yafi Sauraron Mu yawa.

Muyi riko da Tsarin Allah Mugirmama junan mu kada Murarraba, Rabuwa A Al’uma fitinace, Yawan jayayya yanasanya Masu Son zuciya yad’a ‘Barna kuma yakan sa Wasu gaba da juna Bisa Rashin Dalili.

Mukula Da amanar junan mu gun jaddada Sa’bani, Muyawaita zantawa da juna domin warware Sa’bani mukula da Wadanda ke son tada fitina a Addini Sud’in wawayene kuma jahilai, danganeda Harkokin Addini Basusan komai ba Sai musu da Cinzarafin Malamai.

Akowace aqeeda akan iya Samun masu mummunar manufa da Kuma Son zuciya. Babbar matsalar rayuwa Shine aiki da Jahilci, dakuma Son Zuciya.

Mu Janye Gaba da juna danganeda bambamcin aqeedah. Meyin hakan Bai fahimci addini ba Son duniya da Son zuciya Shiyake sa Mutum yakasa Barin Mummunar Aqeeda da Mummunar halaye a rayuwa da Addini.

Addinin mu yatanadar mana komai, Bamu Bukatar wata hujja idan Nassi ya inganta. Maluman mu nada da Yanzu Sun mana gata.

daga Matsala ta Kunno kai Sai mubude littafi. Idan muka Zauna Kushe littafan mu da muzantashi. Zamu wayi gari Muna Qauracewa gareshi. Har yazamto mun Halaka kamar Yahudu da Nasara.

Idan Munji gyara Muntabbata gyara ce to yazama wajibi mugyara, Kada Mutsaya Sauraron Ra’ayin Wane ko Matsayar wani Malami, Kowani ‘Dan adam ajizine, Malam Wane Ba Annabi bane Yakan iyayin Kuskure Ko Qarancin Tunani.

Addini dayace Sa’bani Sharri ce kuma fitinace, Hanyar gujemata Shine bincike da Neman Ilimi. Da Gujewa Rudin Duniya dakuma Komawa ga Allah ﷻ.

Idan kai ba malami bane kadaina katsalandan aharkar Fatawa ko Matsayar malamai, Yin hakan Shike janyo d’alibi yaraina Hatta malamin dake karantar dashi.

Malamai Su hada kansu Domin kaucewa yawan Sa’bani, Rashin Zantawa da juna shikesa malamai Sa’bani wani abinma labari kakeji daga ‘Dalibanka wani kuma Baka gama jin Kammalallen saba. Yazama dole Dole muyi Bincike.

Idan kasabawa Maluman dakake tare dasu kadauka kaine akan Kuskure, Ko baka fahimcesuba Kuma kana kyutatamasu zato amma ayimaka gamsasshiyar bayani. Amma idan Kaki kuwait Shaid`an Zai Rinjayeka Ko da akan Gaskiya kake. Domin Kurama takan Cinye Dabbar da ta Ke´bene.

Laifin Wani baya shafan wani agun mu mu ‘Yan adam, Kada Wani wanda ba aqeedarku daya ba yayi magana kayanke hukuncin Dukka aqeedar haka suke. A`a Shidai haka yake amma akwai Wasu nakirki acikinsu.

‘Dalibai Mudunga Girmama maluman mu, Munemi ilimi ba Son shaharaba. Babu amfanin ilimi idan bai zamo hanyar Tsirarmu ranar Lahiraba.

Idan wani yahalaka Sanadinka kana da Kaso cikin Sakamakon da za’a Qaddamar masa.

Idan Hasashen Mutane gaskiyace! Tabbas akwai wadanda ke kar’bo kwangila domin ‘Bata Addini. Amma kuskurene muyi Jam’i, Dole akwai wadanda da gaske suke Kuma Sunada yaqinin Tabbatuwar su akan Gaskiya Suke.

Dole ne Mu martaba Magabatan mu, Idan Munga kuskurensu mu nema masu gafara. Mudaina Tonan Silili ga ‘Yan uwanmu, Idan za’ayi tonon silili wa kowa Babu mai tsira Gaban Allah.

Munbar koyarwar addini, Mundauki Al’adar yahudawa, Amaganganun Mu komai yazo furtawa Muke babu Tantancewa. Muna da Laifi amma hangen na wasu yahanamu neman Afuwar Namu.

Muyo ‘Da’ah Cikin umarnin Annabi nadaga abinda yazo cikin Alqur’ani da Hadisi, Muhanu daga abinda ya tsawatar, Mubautawa Allah cikin Koyarwarsa ﷺ.

Kada mu yarda da Munanan kalaman da ake furtawa ga Sahabbansa رضی الله عنهم ورضو عنه, Hakan zai iya taba darajarsa ﷺ, Mud’auka Cewa Ma’kiya addinine Suke Kokarin raba kawunan mu.

Inmunga Matsala a Alaqarmu ta Aqeeda Muzauna Muwarware mukoma ga Allah musamu mafita. Na tabbata rayuwar mu zata Sauya.

Bissalam Nine naku Ismail Hussaini Alpholtawy

***SA’KON FA’DAKARWA GA AL’UMAR MUSULMI ****

      **lokaci yaquremana** 

     Idan Har a kullum zamu dinga Nisantar Wa’azine dan ana fad’an abinda Yasha Bamban da Ra’ayinmu to Tabbas Zamu Rinqa Nesantar Haske muna Tutsa kanmu cikin Duhun Jahilci, da kafirci,

     Idan Har Sai abinda yayi daidai da Da Ra’ayoyin Mutane Za a Ayyadar aduniya, Tabbas da Wuta ba ayitaba Sai Aljannah inkuwa anyisuma Ko da anzo Duniya babu mai bin Allah.

    Yawancin Mutane Tunatarwa takan Zakke Musu, yayinda Suka tuno da Me zasu tarar a Filin hisabi, Sai imaninsu ga Allah yaqaru, Inkuwa ankoma Shagalin Duniya Kuwa, Allah ma Wasu mantawa suke da Wujudinsa.

   Idan har Zamuce Wai dan Malami yafadi Sabanin Ra’ayin mu, yazamo mutumin banza to Tabbas imani a azuciyar mu zatai wahalar dasuwa. Domin ayyukanmu munana sunfi Yawa, Sukuma Malamai burinsa mu rage.

    Bai zamo dole ace wai Dukkan abinda Zuciya ta natsu dashi yazama Alkhairiba Iyakar Allah shine abinda yahana, koman Jahilcin Dan Adam, daga yashigo Da’irar Allah ta Haramci, na abinda yaqetare iyaka, Yasanta Saidai ya zakkemata domin Son zuciyarsa.

    Kamar Kid’a ma aiya haramta amma muna Saurara kuma yanayi mana dadin ji. Ammafa haramunne. Kuma ma na sanyamu Shagala da Barin Aikin Alkhairi.
   
    Kowani dadi inhar zai hanamu, ko ya nesantamu da jin dadin Lahira Allah kamusanya mana Shi da Mafi alkhairi, Kaine masanin Sirrin asirin Sansanin Sararin Sababin Alkhairan Duniya da Qiyama.

    Mun manta da Yunqurin Shaid’anu akanmu, Muyi nazarin hakan cikin Rayuwa: Sau dadama abinda Allah yahanemu
Zuciyar mu tafison Mu’aikata, Bisa Rud’i da Rinjayar Shed’anun duniya.

      Bai zamo Lallai ba ace; ko Wani abinda Yayi mana dadi Yazama shine halal ba, Tabbas Halal shine abinda yazamo akwai yardar ubangiji acikinsa Babu Shakku bare kokonto.

      Yawan Fad’a da gaskiya yanasa Qeqashewar zuciya, Tabbas idan kaji Gaskiya koda abakin Abokin gabankane, yi kokari ka Kar’beta amatsayinta na Gaskiya, Inkuwa kaqita kuma kana so ka mayar da ita abin ‘kyama, to Tabbas  Zaka Sha Mamakin duniya, Domin Sunan Allah kake yaqa wato Al_Haqqu.

     Ai kuwa dama zaka Qaryata Gaskiyar MA ayarjemaka bisa yadda kake da iko cikin mutane, daga baya Idan gaskiya tabayyana zakasha Kunya, Idan ma Allah yasoka da Shiryuwa ne Saika gyara, inkuwa bakada da rabon haka, Kamutu Ayimaka Hisabi na ‘Batar da Mutane dakuma Aikata Mummunar aiki.

   Dama habaicinnan damuke yawanyi wa juna, da Zagin Juna A Social Media, Amatsayin Sa’banin Ra’ayi ko aqeeda, Da ayoyin Qur’ani muke yad’awa haka da babu ayar da zaka Duba baka Sametaba a Internet. Ko Hadisan Annabi.

     Muyi Tarayya daku wajen yada ilimi na Addinin Musulunci musamu lada sa’bani bazai ta’ba qarewaba A Addini matukar zamu dawwama cikin yiwa juna Raddi da Jahilci. Muyawaita yiwa junar mu NASIHA.

   Wai ko Munmanta da Cewar mu Musulmai ne, Akwai Ranar fa dazata zo Zamuyi Kewar inama adawo damu Duniya Muyi koda Tasbihi guda dayane Mumutu, Dakuwa Munso hakan. Amma babu dama ankulle kofar Nadama da Aiki, Sakamako kawai ake ba Qaqqautawa.

  Kamar Misalin Jarabawar Duniya ce; Sai Ranar raba Result Saikace Ka manta Maths da English baka Baka karasa Amsaba abaka dama kaje ka gyara aikuwa lokaci kam yakure.

    Allah ka Albarkanci Rayuwar mu da ayyukan Nagarta Dakuma zuciya mai imani da dawwama a imani Har mu samu Rabo Aranar Sakamako. Allah kajikan iyayenmu matattu.

    Naraye Allah ka qara Masu Lafiya da imani da Tabbatuwa Akan imanin Har Mu samu rabo na Lahira Mu dasu Muyi Tarayya cikin Samun  kyakkyawan Sakamako anan duniya da Gobe Qiyama.

** KYAWUN FATANA GA AL’UMAR MUSULMI**

    Nayi nazari cikin tsarin Rayuwar Malumanmu na Musulunci, acikin Kyautata zatona danayi Garesu da kyakkyawan Fata sai na hango Maluman mu na Najeriya acikin Da’irar Son Ma’ki da kishin Sahabbansa da Iyalan gidansa

   Inada Lissafin yatiqe dai Munrabene Cikin aqidu Domin Nuna Kishi ahalarar Soyayya
Tayadda ‘Dariqu Suke jaddada So da Girmama waliyyai da Shehunai da Sharifai da Sufaye Domin kasancewarsu Masoya kuma dangi Jinin Fadima Yar Ma’aiki

Sukuwa Ahlussunnah kishinasu ya Ta’allaqane Akan Hidimtawa wa Da’irar Ibada bisa Tafarkin Sunnah da gyara Ibadoji da kiyaye hakkin Annabi da Alqur’ani da Kore Shubuha a Addini

Haka masu jaddada kishin Ahlulbaiti (Ahlul Kusa’i) Suma dai Soyayyace Ragamar su cikin Nuna Hidimtawa wa Sayyada Fadima ‘Yar Ma’ki da Zuri’ar Gidanta Abangaren Sayyadina Ali Allah yakaramasa Yarda

Tabbas gida d’aya Muke karkashin inuwa guda Muke, Matsalar da faruwa acikinmu itace wasunmu na aiki da Jahilci da kuma Son zuciya bisa Siyasar Masu Neman Duniya da gurbata Addini. Masha Allah, Malamai na ya’kar tsarin da salon tsarin Tabbatar da Sunnah gami da kore  Shubuha da qarfafa Shari’ar Musulunci, Muma muzamto wakilan Musulunci kada musanya ido haka kurum muna kallonsu Kamar Telabijin, Ayi muji dadi dan anyi Nasara Akan Ma’kiya Muyi dariya,
    Idan an kore Kazantar wasu To mu abinda yakamata Muyi shine ina datti yake ajikinmu muma Muyi kokari mu wanke, Dan kuwa Malumanmu Tabbas zasu Shud’e kuma Duniya na kara Gur’bata ga kuma Mummunar nufin Yahudawa da Nasara. Muyi Kokarin gyarawa kuma mu ankarar da juna danganeda Zamantakewa da Ibadoji.
  Tabbas Malamai gatarin sarane agaremu kuma tsanin hawane mai qarfi bisa haryar tsira da Digar tono asiran ma’bb’bugar Alkhairai. Inhar mukayi sakaci suka Shud’e bamuda Masu maye Guraben su Tabbas Munyi Kuskure Mafi girma, Ina mukeda yaqinin Tabbatuwa, Yaushe Za’amaimaita Kamarsu Sheikh Ismail Idris da Kuma Ja’afar da Albani.
   Ya za’ayi Duniya tamance da ginshiqannanan namu watau Khulafa’Urrashidun, Ina za’ayi jagorori Kamarsu wadanda burinsu Kullum cigaban Addini. Akwai ire_irensu Wadanda ban ambata ba Ammafa Sun Shud’e Wadanda sukayi hidima ajanibin Ma’aiki da Halarar Tsaftace Al’uma daga Jahilci da Duhun kafirci.
    Saidai kuwa Jimamin mu Kullum Shine; Gamu karkashin inuwar Rumfa guda amma Wasu na Kokarin Jijjige rumfar ga barazanar Abokan Gaban dake tunkaran mu, hakan na faruwane ta silar Wasu wawayen cikin mu da bisa Siyasar Masu Son zuciya da marasa hankalinmu.
  
  ** Mecece mafita?**
   Mafita agaremu Shine komawa ga Allah dakuma hadin kai wajen aikin Alkhairi da ya’da Addini da bawa Addinin kariya takowace ‘Bangare tareda aiki da ilimi wajen da Yad’a ilimin, Malami kuwa Yatsaya amatsayin na Fannin dayasani. Allah ne Masanin komai, Bai aikin Musulmi bane Yanke hukunci da Jahilci ko Son zuciya.
    Wani Tunani dake Zuwa cikin zuciyata Mai cikeda mamaki gamida Amsarta, Itace;

     Anya Kiristoci? Yaya Sukeji ko kallon Al’amuran mu na yawan Sa’bani?
   Kwatsam Saina amsa da cewa, Ai mu Munada yaqinin munakan Gaskiya Saidai binta yayi mana wahala bisa Rinjayar Shed’anu da kuma kasawa ta Dan Adam. Su kuwa kullum wa Duniya kadai Sukewa hidima, Sunbar Addininsu ba tsari Matansu Na fita yawo tsirara ba Mutunci Kamar rayuwar dabbobi, Mukuma Kullum burinmu Ya’kar Irin Wadannan tsarikan mukeyi, Mamakin danake garesu Kullum Shine Rashin Kulawa dasukewa ‘Ya’yansu dasukeyi Shigar banza Kamar Basu da Addini Na Tabbata Addinin Kiristanci bai karantar da hakan ba.

**Godiyar mu ga Allah Musulmi **
Addinin mu yagamamana komai kuma mun riski ilimi da Dukkan wata falalar rayuwa da Tsarin Zamantakewa da ingantacciyar Rayuwa da tarbiyya dukkan mai akasin Kyawun hali da dabi’u tabbas yakauce ne wa koyarwar addini.

**Kira ga Dalibai matasa**

          Yan uwana Matasa Dalibai!!! Murabu da malamai Abangaren wa’azantarwarsu Muzauna amajalisi akoyar damu Ibadoji da Tsaftace Rayuwa gamida tarihohin Shiryarwa Mugujewa Shagalar Rayuwa da rudin Duniya Munemi halali kurum akasuwancinmu.
    Mukuma tayasu wajen Yad’a karatuttuka a Social Media tahanyar Recording and Sharing Audio da Video da Pictures quotes gamida Rubuce Nasihohi da Wallafa manhajoji da Websites  da Rubuta Text wa ‘Yan uwa da abokan Arziqi. Domin sanya ilimin Addini cikin duniyar Network da yaqar Shubuhar mutane da wautarsu na Zagin Malamai da Hauka.
    Sannan hakan zaisanya Mu tanadar babban Guziri wa Yan baya, Domin kada Su iske bamu bar musu kyakkyawan koyiba Sai tarin Shubuha gamida Sa’bani, hakan zaisa Masu raunin imani acikinsu Kokonta cikin imani dama Shakku a Addini matukar Basu tarar da abinda zai Qarfafesu na matsaya gudaba Abin koyi. Ya Allah Kaqaramana imani da Ikhlasi da Tabbatuwa Akan imanin Harmu sameka muna Sallamawa gareka Allah karabamu Da Riya da Son zuciya.
  Allah kajikan Magabatan mu Mukuwa Allah kabamu Shahada.

RAYIWAR YAN MATA

📝 QALUBALE GA RAYUWAR ‘YAN MATA ✍️ ******* GABATARWA *******

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu mai karatu.

Zanyi wannan rubutunne don nuni zuwaga yan uwana maza, domin kusan wa zaku auro ku kawo cikin gidanku, amatsayin abokiyar zama. Mata kuma su san dawa zasuyi qawance don gudun faďawa akomar halaka. Inda hali kutsaya kukaranta gabaki ďaya, domin zaka/zaki k’aru kuma inshaa Allahu zaku rabauta da waďannan zantuka nawa.

Ina bukatan addu’arku Allah ya haskaka qabarin mahaifina, dana mai karatu idan kuma suna raye, Allah yasa mugama dasu lafiya yakuma basu rabon cikawa da imani. Allah ka albarkaci rayuwar lahaifiyata da ayyukan alkhairi daku mumaďin gabaki ďaya.

‘YAN MATAN JAMI’A

Allah sarki rayuwarsu gwanin birgewane, saidai kuma abin tausayine awani bangaren, tayadda zaka samesu mafi yawancinsu akwai tsaftar jiki dana tufi. sannan sun san yakamata matuka, Saidai wasu acikinsu suna son yin aure kuma Suďin sun kame kansu. amma rashin dama takansa wasu acikinsu afkawa izuwa ga zina, Allah yakare. Hakan yana faruwane don rashin samun dama daga iyayensu. Zasu fidda gwani amma sai suce sam sai kin kammala karatu, sun manta da wasiyyar manzon Allah (s.a.w). Wasu kuma suna sheke ayarsune kawai tahanyar biyan bukatarsu ga maza, aduk sadda sha’awarsu ta motsa. Wasu kuma na fama da jimamin rayuwa tayadda suke fama da fuskantar barazanar lecturers lalatattu, da yunkuri batamasu tarbiyya da fansar jarrabawarsu da mutuncinsu. Iyaye ayi hattara zaku iya shiga wuta akan hakkin ‘ya’yayenku don rashin sadaukar musu da hakkinsu daya rataya akanku

‘YAN MATAN LUNGU

Idan akace matan lungu: sune mata masu talle akan titi, dakuma lungu da sashen unguwanni da sakokin ma’aikata, da shaguna (Kwantinan) kasuwanni. irin wadannan matan, idan basu sami kulawar tarbiyyaba sunfi kowasu mata sharri. Domin awani bangaren sukan ‘boye kamarsu suyi kama da mutanen kikrki amma sam bahakan bane azahirance. Kuma mafi yawanci acikinsune ake samun masu sace_sace, da bin maza bayan sunyi aure. domin sun saba da rike kudi masu kauri ahannayensu, ayayin budurcinsu. Hakazalika wasu acikin sunma suna saida budurcinsu kafin aure, a son zuciyarsu kokuma ara’ayin iyayensu mata. Ko uwayen goyensu na bariki. tayadda sukan taradda wulakanci agun mazajensu, dalilin rashin budurci bayan sunyi aure, hakan yake tursasu fita karuwanci bayan aure, ko sata wa mazansu na aure.

‘YAN MATAN BARIKI

Irin wadannan matan basuda mutunci. wanda su kansu sun yadda da hakan, kuma suna iya furtawa da kansu cewa su marasa kunyane amma daga fitsararrun cikinsu. Irin wadannan matan sukan tasone aguri mai lalacewar tarbiyya.

A gunda iyayensu ke zaune babu tarbiyya kuma iyayen basu kulawa da tarbiyyarsu. kuma babu addini agunda suke zaune. Saidai holewa da sha’anin duniyanci dakuma ta’ada, da muta kabbaranci. Ga uwa uba rashin dattako don ko waye ‘yar bariki zata zaki asalinsa ko da kuwa shugaban unguwarsune ko sarkin gari. Wadannan matan ko acikin garine shigarsu daban take sune Manzon Allah (s.a.w) yayimanz ishara dasu acikin hadisi ruwayar bukhari da muslim ” Akwai wasu nau’in mutane da Annabi baigansuba amma zasuzo anan gaba yake fadawa sahabbansa. Yace dasu dukkan wadannan mutane ‘yan wutane. ” na farko dai shugabanni azzalumai yake nufi kokuma masu hukunci da zalinci. nabiyu kuma yace; wasu matane zaku gansu da kaya ajikinsu amma tsaraicinsu na waje suna tafiya suna karairaya jiki, sa’annan kawunansu kamar tozon rakumi, yace kuma bazasu shiga aljannaba, kuma bazasu ta’ba jin kanshin aljannah ba. Domin awani qaulin anajin kamshin aljanna a tsahon tafiyar shekaru dari biyu ko dari biyar.” Allah kakare ‘ya’yanmu da ‘ya’yan ‘yan uwanmu daga Gurbacewar tarbiya.

‘YAN MATAN ASALI

Allah sarki wadannan sune abin tausayi, kuma sune masu wahala, kuma sune masu rabauta duniya da lahira. Tayadda suke fitowa daga gida na mutunci, iyayensu nagartattune su kuma kamammune. Sukan rike budurcinsu iya jimawar da zasuyi gabanin suyi aure. dashi suke samun martaba da nagartar zamantakewarsu ta aure. Kuma kafin suyi aure basu koda cakuduwane cikin maza ballema suyi wani mummunr mu’amala da namiji, hartakai ga sun zubadda mutuncinsu da budurcinsu. Suna matukar Kula ha hakkokin dake kansu na addini dana zamantakewar rayuwa. sune Allah ya ambacesu acikin Alqur’ani yadda yake cewa a Suratul_ahzab. surah ta-33 Aya ta:35 ”Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli’u maza da mãsu tawãlĩu mãtã da mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma.”

Hakika mata masu addini sune mafi dacewa ga dukkanin wani ďa namiji musulmi. Kuma sune zakasamesu masu kyakkyawan hallayya dakuma tsaftatacciyar budurcin wanda babu kazanta acikinsa.

Duk da cewar kwaciyar aure na rana daya tak, yana wanke dattin kazantar bariki, duk jimawar da akayi dashi. Amma kuma duk da hakan kazanta bariki, yakan sanya zargi atsakanin ma’aurata, Zargi na har abada. Musamman ma yazamanto shima mijin mutumin banzane.

Allah karabamu da danasanin duniya da hasarar lahira. Ameen Dukkannin wanda yakaranta wannan rubutun nawa ya sanya aransa shima zai bada gudun mawa wajen gyara yau da goben Al’umar mususulmi kusani acikin addu’arku dani da mahaifana. Albarkacin wannan wata mai albarka ta Raladhana.

BAYAN RAYUWAN DUNIYA AKWAI RAYUWA BAYAN MUTUWA

GASKIYA AKWAI MATTSALA!!!!


Sau nawa kake zama domin Bincike ko sauraron Yadda zaka gyara Ibadarka?????
         Sau dadama idan na kadaita sai nayita tunani dan ganeda lammarin gudanar addini agun wasun mu. Zakaji mutum nakiran kansa musulmi amma farillan alwala ma bai sani balle in ta ‘baci ya gyara farillan sallah ma bai saniba balle inyayi Rafkanuwa yagyara. Ko na wanka ballema ilimin gyaransu.
    Wayyoooni duniya ina zaki damune kowa kagani abinci kawai yake nema kokuma yadda zai huta ko yadda zaiji dadin duniya gaba. Saidai kash itakuma tafiyarnan da take gaban mu batta da rana. Kawai zuwa take kwatsam kara zube ba zato ba tsammani.
    To taya zamu tara guzirin komawa ga mahaliccin mu domin samun hujja garemu aranar sakamako?
    Ansa
    Mukoma munemi ilimin addini mugyara ibadu da mu’amalarmu kafinnan musami hanyar tsira. Wani abin ban takaici shine yawanci mukan jahilci lammarin addini bawai don rashinsaba sai don aqidanci. Mutum baida karatun komai jahilin kauye afagen addini amma saikaji na karyata abubuwan da malamai ke fada dan ganeda hukuncin halasci ko haramcin wani al Amarin addini. Dalili kuwa shine don aqidarsu ta banbanta, Alhali baida hujja ta aya ko hadisi data karyata al’amarin dalili kawai don malumansu basayi yan abiyari (inbasu wane bazamuyiba).
    Wannan shi ake kira da shi’anci ashari’ar musulunci ma’ana raba kan al’umar musulmi. Tahanyar sabawar fahimta ko mazhaba. Abubuwan da kejawo haka sune:
    _Jahilci
    _Son zuciya
    _Son shahara
    _Munafinci
          ***JAHILCI***
    Idan jahilci yayi naso (katutu) azuciyar mutun saikaga na karyata koma mene ne addini ni kuma in yayi shugabanci zai dinga shirme yayita kawo jahilci alammuran dasunan gyara daga karshe zaiyita kokarin fada da malamai idan suna fada masa gaskiya. Jahilci nasa girman kai da hassada matukar maishi na tare da masu ilimi kuma akayi rashin sa’ah yawuce su wata daukakaka tarayuwa.
       ***SON ZUCIYA***
Idan mutum nada son zuciya komai aka fada bazaibiba sidai yakowo tasa abi. Koda tasa hanyar me raunice zai toge yadage akan sai anbi tasa daga karshe in anki zai fara neman mabiya daga baya saikaji ya Fidda tasa sabon kungiyar daban ko juma yafandare yayi reshe akungiyarsa daban.
    ****SON SHAHARA****
    Mafiya yawanci anfi samu daga wanda suka ‘Danyi karatu amma bamai nisaba sunason taka hawa mai nisa amma kafarsu baikaiba. Burinsu dai komai zai wakana yazam anyishi harda furucinsu. Amma basuda cikakken ilimi abangaren irin wadannan ywanci akansamu masu kyakkyawar manufa amma rashin ilimi mai nisa yana wargaza manufar nasu.
    Yakai dan uwa shawarata gareka katsaya iya matsayin ka kabar abinda Bakasaniba.
    Masu hikima nacewa Bansaniba shima wani yankin ilimine.
   
      *****MUNAFINCI****
    Akwai wasu burinsu kawai azagi musulunci da musulmai. Zasu tsaya kai da fata su tabo wannan aqidan da wata ta daban, Harsu haddasa wata rigima tsakanin musulmai wadannan basuda wata kyakkyawar manufa akan musulmai wasunma bamusulmai bane burinsu su wargaza wata shiri ko wata tanadi wacce musulmai sukeyi, ko don su raba kawunan al’umar musulmi.
    Allah katsaremu daga sharrin makirai da fajiran munakan addini.
    Allah yamayar da makircin garesu dasu da wanda suke sasu.
    Allah kabudemana kwakwalenmu don gujewa afkawa rudanin addini.
    Allah  kabawa maluman mu damar isar mana da gaskiyar koyi na Addini.