TARIHIN SHEIKH ISMA’ILA IDRIS BN ZAKARIYYA !!!
**Gwagwar mayarsa wajen Kafa Izala da Sunnah***
Sheikh Isma’ila Idris
yatasone cikin al’umar nan tamu ta Nigeria, ayankin Arewa inda awannan lokacin babu wata aqida a Qasarnan bayan Dariqar Tijjaniyya, Qarqashin jagorancin sheikh Ibrahim Inyas Alkaulahy.
To dake zamani ya Nausa tafiya tayi nisa, Al’uma tasamu kanta cikin yanayi na Cakuda addini da Son zuciya. Ana samun Malamai masu Sanya Son ransu acikin addini suna anfani dasunan Addini Suna isarda Munanan manufofinsu ga Al’uma kalar Bokanci da Sihirin Duba dama wasu Tsubbace_tsubbace su na Son Zuciya da Neman duniya.
Wanda yaci karo da koyarwar Addinin Musulunci. Dukkan mai irin wad’annan aiki Bai tabayinsu Saiya fita a addinin Musulunci, Yazamo dukkan wanda yayi Sunansa kafiri da Nassin Aya acikin Suratu baqarah. Haqiqah bayan Wannan Akwai wasu littattafai dadama wadanda Maluma suka shigo dashi ake karantasu na Labaran mafarki da Tatsuniyoyi dasunan Adddini, Irin wadannan abubuwa dakuma makamantansu Sune maqasudin Da’awar ta Sheikh Isma’il Idris, abisa fahimtar masu kyautata masa zato.
Da’akwai wadanda suke ganin cewa kawai yafara da’awar izala ne kawai Don Neman Suna dakuma Zagin Wasu malamai (Shehunnan ‘Dariqu) dakuma Sufaye. Wanda kuma hakan kuskurene domin Aikin Musulmi shine kyautatawa juna zato. Da Kuma nemawa juna gafara agunda akayi Kuskure danganeda Sa’banin Ra’ayi ko Fahimta.
Zamu cigaba ta Tarihi.
Bayan Malam Yabar aikin Soja wanda acikin Aikin nasa na Soja ya fara da’awa akan barin Tsubbu da Daura layu da makamantansu, Malam yasha tsangwama daga makiya dakuma wadanda basu da ilimi wanda basu fahimceshi ba. Ba awannan Lokaci malam yaga cewar Wannan Da’awa tasa bazata cigaba ba Har saida wata Qungiya Wacce zata Tallafa masa Danganeda samun cikar Qudirinsa na Farkadda mutane game da Sunnah Asali.
Awannan lokacine malam ya Assasa wata Kungiya mai Suna; ”Jama’atu izalatul Bid’ah ” Ma’ana ( Gungiyar dake kawar da Bidi’ah ) Wannan Kungiya Tasa tasamu karbuwa hatta aciki ‘Yan uwa Sojoji na wannan lokaci, Saidai kuma tasamu naqasu Sosai daga Malaman wannan zamanin Musamman wadanda keda Wannan aqidar ta Tsubbace_tsubbace da Duba. Tayadda sukayita yimasa Tuggu da zagon kasa gurin Sun ga sun dakushe wannan aikin Nasa, Tare da Wargaza aikin Nasa tahanyar kirkiran karya akansa hadda cutar dashi domin Su samu Galaba akansa, Amma ahakan Allah ya Tserataddashi daga dukkan tarakunan nasu Allah ya kuma karfafa Wannan Da’awa tasa har ilayau Qugiyar izala tana nan kuma tana cigaba da aikinta wajen karantar da Al’uma bisa koyarwar magabata dakuma Tabbatar da Qur’ani da Hadisi sune tafarkin Tsira ga Bayi.
Ahakan aka cigaba da kasancewa har takai yaje izuwa ga Malamin sa na Tauhidi Assheikh Abubakar Mahmud Gumi, Domin neman izini da Karin lamani dangane da Da’awar tasa. Awannan lokacine Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya nuna Bashi Cikakkiyar goyon baya gamida Cikatamasa Sunan Gungoyarsa da ” Wa’iqamatissunnah ” ma’ana ( Dakuma Tsayar da Sunnah ) Wcce tazamo ” Jama’atu izalatul Bid’ah Wa’iqatissunnah ”
Ma’an ( Qungiyar dake kawar da Bidi’a kuma take Tsayar da Sunnah )
Domin acewarsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi; Babu Yadda za’ayi akawar da bidi’a abarta haka ba acike Gurbinta da wani abu ba, Shine Yace to sai Acike Gurbinta Da Sunnah.
Kunga Ashe kenan ita Izala ba Fitina bace Sabanin Yadda wasu daga cikin maluman ma da basu fahimta ba, Kuma bawai Reshen addini bace kamar yadda wasu suke yimata Mummunar fahimta Har ma wasu ke ganin Cewa in baka ciki to baka cika musulmiba, wasu kuma ke Mata ganin Cewa inkan cikinta Musuluncinka da Gyara Haqiqa Dukkan Mai yiwa Wata Aqidah ta Musulunci ganin Wannan Al’amari, Alal hakika ya Jahilci Hakikanin Musulunci,
Wannan kadan kenan daga Tarihin Sheikh Isma’ila Idris da Gwagwarmayarsa gurin kafa Izala, insha Allah Anan gaba Zan kawo muku Cigaban da iza ta Kawo Wa Musulunci da Kasarmu baki daya. In Allah mai Komai ya kaimu bayan Sallah.
Nine naku Isma’il Hussaini Adam Alpholtawy
Kuma Wannan Shine karshen Rubutuna danganeda Shafukan Tarihin na Bana A Hijira sheka ta 1442 Saikuma Allah ya Kaimu Almuharram Shekara ta 1443 Zan cigaba da Wannan Tarihi.
Mai karatu ga Addu’a ta Katayani da Ameen.
Ya ALLAH Kajiqan Mahaifina Hussaini Adam Jumba wanda Ya Rasu a irin Wannan wata Mai Alfarma kuma Aranar Idin Adhhaa, Idin Babban Sallah Allah Kajikansa Ka gafarta masa ka kai Harke Qabarinsa, Kabashi Aljannah Madaukakiya.
Ya ALLAH Mu Zuri’arsa Da muka Rage a bayan Kasa Allah ka azurtamu da Dogora abisa Addininka, Kabamu Shahada irin tasa, kasanyamu Cikin Wadanda kake Yantawa Zuwa Aljannah.
Ya ALLAH Ka Sitirtamu da Sutura ta Musulunci, Ka azurtamu da Arzikin imani, da Ikhlasi da Tabbatuwa akan imani, Har Mu Mutu muna masu imani Da Miqa wuya gareka Allah.
Ya ALLAH ka daukaka musulunci da musulmai, ka Qaskantar da Kafirci da Kafirai kadirkake makiyanka makiyan addini Allah kataimaki bayinka Nagari.





You must be logged in to post a comment.