YARANTA DA SON SUCIYA NA YAN SOCIAL MEDIA

BA’A ADDINI DA SON ZUCIYA !!! Ana addine da abinda yazo ashari’a Shi Hidimar Addini ba irinta Siyasa bace. Dan Allah idan baka saniba kadaina kutse acikin lamarin. Bana jin dadin irin wadannan abubuwan da mukeyiwa juna, Wallahil aziim idan wadanda ba musulmiba sukaga irin wadannan Musanya da Cin mutuncin da mukeyiwa junan mun, dadi sukeji. Idan kasan baka da ilimi awani zancen daka tsinkaya a Audio, na lamari addini ko A social media kada kace zakayi Raddi direct. Nasan baza ka rasa malamin da ka yadda dashi ba ayankinka, kamata yayi kaje ya warwarema lamarin, inda kuskuren yake saikayi Contact da mai Wannan jawabin. kuyi magana ta fahimta dashi Agunsa zakasami karin bayani, daga nan sai ka sam hujja. Haka ake magance mummunar zance kuma in yanada kuskurema me iyuwa ya koma kan wannan jawabin nasa yayi gyara kokuma ya warware abinda yashigewa duniya duhu. Wannan zai zamo ka kawar da barna, in barnanne inkuma rashin fahimtace To kaga kaima kasami Sabon ilimi Dan Allah Mutane mudunga kyautatawa junan mu zato. 📝#Dan_Arewa

MATSALAR TSARO A NAIJA new post 1

BABA YAKASA MATASALAR TSARO AKASATA

Leave the issue that he has doing well kawai muce Baba yakasa. Abin na Bu’katar Tunani ne. Idan zamuyi adalci wa kanmu kuma mufadi gaskiya, Wallahi matsalar tsaro a nigeria, kasawar kayan aikin Jami’an tsaron governati ce. bawai ina nufin bata da karfin yaqarsu ba, kawai taki tayi abinda yadacene dan ganeda lamarin. Tahanyar nazari dakuma bawa jami’ai kayan aiki dakuma da nauyi da bada tallafi ga iyalin duk wanda yarasa Ransa akan yaki da ‘Yan ta’adda. Kullum al’amuran kara rikicewa yakeyi, Tambayata anan itace: Waishin su ‘yan ta’addannankam aljanune, kokuma aljanune suke basu kayan aikine. Wadanda dasuke amfani dasu, Kama daga ci shansu har zuwa makamai dasuke amfani dasu, dakuma man da suke sakawa a ababen hawansu. da’akwai alamar tambaya anan gun! Shin anya acikinmu babu masu daukan nauyinsu? kokuma makiyanmu ne ke basu mafaka da tallafi? Idan akwai kuwa suwaye wadannan mataimakan nawu? Kuma a ina suke? Are the citizens of nigeria? Or they are in another countries? Shin nigeria anya batada makiyan boye na cikin gida da waje? In akwai to suwaye kuma a ina suke? Amsar wadannan maganganu nawa suna nan acikin wannan kalmomi guda uku. #BABA_A_BINCIKA Gadai ni abinda na bincika da kuma hasashen tunanina. Dafarko dai ina zargin Turawan yamma, bisa wasu kwararan dalilai guda biyar ( hudu ) danganeda dambaruwar dake faruwa a Arewa ( daya ) kuwa danganeda abinda ya faru na End Sers a kudu, ga dalilan kamar haka. 1. Kungiyoyin da addancin da ake jinginasu dasunan Musulmi, wadanda kuma ayankunan Musulmi suke. tayadda suke kashesu suna kuma korarsu daga gidaddajinsu. Idan musulmin gaskiyane ba dan gwangilaba, abinda zasuyi koyi dashi, shine Alqur’ani da hadisan manzon Allah. A alqur’ani da hadisi abinda ake nufi da hakikanin jihadi shine, yada addinin musulunci. Kuma ni naga arewa mafi yawansu musulmine. Idan gaskiyane kudanci ai shine guri mafi karancin musulmi, dan me ba’akai Jihadin can ba? Amsa Sharrine na turawan yamma inda suke amfani da masu raunin addini, suna ida nufinsu domin su samu damar samun hanyar shiga kasarmu. Nazari Duba abinda yafaru akasashen Gabas ta tsakiya, danganeda larabawa Sunnah, da kuma Sauran Qabilun Shi’awa, na yanki Fakistan, Iran da Iraqi .da kuma Cecenistan, Afghanistan, Dimashqi, dakuma wasu yankuna na Syria (Shaam) dama sauran kasashen na gabas ta tsakiya. Suma turawan yammane sukayi amfani dawasu bangare masu rauni acikinsu na (‘yan ta’adda). Suka wargaza kasan sa’annan suka lalata Arzikin dake cikinta, har wayau kasashen dukkansu alalace suke. Misalin kamar irin ta nigeria ce, suma daga rikicin kabilaci suka fara, saikuma rikicin yanki, akazo rikicin Aqeeda, daga karshe aka dawo dana yanki, har izuwa yau bala’i suke kan Tafkawa akasashennan nasu. 2. Dalilin na biyu dayasa nake zargin turawan yamma shine; Kashe maluman addinin musulunci da Pastoci masu gaskiya da akeyi, akan don suna wayar wa mutane kai dan ganeda Sharrukan yahudawa, Duk wanda yake karanta Bibble ko Qur’ani yanajin yadda Allah yake kiran yahudawa, dakuma zarginsu, akan sauya Littafi dakuma Nuna finkarfi da zalunci akan mutane. Acikin Alqur’ani Allah yanuna mana haqiqanin kiyayyar da sukeman dakuma son mallakar duniya, dasuke so akanmu da mamaya. yadda Allah yake cewa (s.w.a). ”Bazasu gusheba suna yakarku Tako wata ‘bangare harsai kun Ridda kunbar addininku” Wa’iyazu billah kokai Christa ne, kasani kaima basu barkaba inda suke batanci akan Nana Maryamu (Mary). dakuma sukarta da Qazafin zina, da kuma kisan gillah dasukeyiwa ‘Yan addinin Christa kafin zuwan Hitla. Wallahi matsalar duniya ayanzu sune yahudawa Allah kayimana maganinsu. 3. Dalili na uku kuwa shine: yadda ake ayyana wasu wadanda sune jigogin nigeria ayanzu Cikinsu harda Ministan Sadarwa da Tattali ta kasa watau Isah Ali Ibrahim fanmi. Ana ayyadasu amatsayin wadanda za’a hara nan gaba. tareda hallakasu da karyar ta’addanci kamar yadda yafaru awadancan kasashen, Na gabas tatsakiya, inda akatabin masu hikima da fasahar tsaro da tattalin arzikinsu akayi ta kashewa, da sunan yaki da ta’addanci. 4. Dalili na hudu kuwa shine Yadda ake samun makamai ahannun ‘yan ta’addan Nigeria: har yana fin na Jami’an tsaron governati. Wanene ke bawa ‘yan ta’adda makamai haka yadda kasan ba aduniyarnan suke samuba. To Wallahil Azim koda Aljanune suke basu inbabu Munafinci da Gilli da Tuggu. Wallahi za’asan Suwaye. Wadanda ke basu makamai. Masu basu kuwa sune ‘yan world totalirial government. kuma sune wadanda sukeson ahada duniya karkashin mallakin Mulki guda. Wadanda suka sha Alwashin gamawa da dukkan wata Al’uma dasuke ganin zai kawo musu cikas, gurin cimma burikansu na mulkan duniya. Domin a imaninsu shine babu wata rayuwa bayan ta duniya, balle sakamako yabiyo baya. Tayadda suke anfani da ‘Yan ta’adda dakuma salon tsarin ta’addanci, da babu irinsa kamar kirkiran gungiyoyin Shan jini, dakuma na Zubaddda jini. wato kashe halittu abayan kasa, tahanyar amfani da makamai, da kwayoyi, dakuma ma abubuwan ci, dana sha, harda suturar sakawa dakuma iskar damuke She’ka. Kuma wadannan Mutane Sanannune aduniya. kuma suna da Cibiya tasu Me zaman kansnta. inda suke Aiwatarda munanan manufofinsu, kama daga Mulkin mallaka, dakuma sa baki aharkokin tsaron kasashen duniya. Wadannan kad’an kenan daga cikin kananan Burikansu, kafin manyan su bayyana dakuma cikar ‘Kudirinsu. Muna rokon Allah yakarya Wannan daula, yakuma wulakanta mambobinta gaba dayansu. Allah yadirkakesu yataimaki bayinsa Nagari. 5. Dalili na biyar kuma na karshe a dalilaina daga cikin wadannan dalilan Shine. Faruwar EndSers dakuma wanzuwa da tasirin da sukayi a Nigeria. ayankin Kudancinta, Sun yi tasiri wajan Illata muhallan wasu, da Shaguna, da kwantina, da kona kone. Hakika babu shakka masu wadannan mummunar manufa, sunada wakilansu akowace kasa, inda suke amfani dasu, Su hura wutar rigima da tashin hankali, da Hatsaniya tareda tallafawa wani sashi acikinsu. Da taimaka musu da makamai kamar dai yadda yake faruwa. Hakika Sunyi abinda sukayi na Zalinci. Harda suka kuma kara ingiza yan Arewa suma su motsa. Sai kuma Allah yasanya musu saukin rai. tareda nuna rashin yarda domin ‘bata kasane. Ahakikanin gaskiya gidajan juna muke rusawa, kuma masana’antun ‘yan uwa muke konawa kuma illar mu zata shafa, tayadda daga baya zamuzo mu ciza yatsa, muyi Allah wadai da Lamarin Mu da kanmu. Idan da Za a kama rikicin a Arewa dakuwa Sabuwar masifa ta kara aukuwa acikin kasa. daga nan sai sukawo tallafin magunguna da abinci. Muna Ci muna Mutuwa. Ga matsalar tsaro kuma, Sai su kawo Jami’ansu na kungiyar World totalirial goverment. Za’a kawosu suci gaba da kashemu dasunan yaki dayan ta’adda. Har awargaza kasanmu kamar yadda yafaru agabas ta tsakiya. Kuma sunfara da al’umar Musulmine domin musulmi sunfi yasa. Kuma sunfi karfi. Amma idan sunjiyo kan kawo zasu afka. Don haka #Mukula. Nigeria maza da mata manya da yara Christians and Muslims ayi hattara. # Qaalu_Bale_garemu Muyita Rokon Allah yakawo mana mafita Amma saina gyara ka gyara Mun gyara Kun gyara Sun gyara. Allah yakaremu, kataimakemu da gyara.

RAYIWAR YAN MATA

📝 QALUBALE GA RAYUWAR ‘YAN MATA ✍️ ******* GABATARWA *******

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu mai karatu.

Zanyi wannan rubutunne don nuni zuwaga yan uwana maza, domin kusan wa zaku auro ku kawo cikin gidanku, amatsayin abokiyar zama. Mata kuma su san dawa zasuyi qawance don gudun faďawa akomar halaka. Inda hali kutsaya kukaranta gabaki ďaya, domin zaka/zaki k’aru kuma inshaa Allahu zaku rabauta da waďannan zantuka nawa.

Ina bukatan addu’arku Allah ya haskaka qabarin mahaifina, dana mai karatu idan kuma suna raye, Allah yasa mugama dasu lafiya yakuma basu rabon cikawa da imani. Allah ka albarkaci rayuwar lahaifiyata da ayyukan alkhairi daku mumaďin gabaki ďaya.

‘YAN MATAN JAMI’A

Allah sarki rayuwarsu gwanin birgewane, saidai kuma abin tausayine awani bangaren, tayadda zaka samesu mafi yawancinsu akwai tsaftar jiki dana tufi. sannan sun san yakamata matuka, Saidai wasu acikinsu suna son yin aure kuma Suďin sun kame kansu. amma rashin dama takansa wasu acikinsu afkawa izuwa ga zina, Allah yakare. Hakan yana faruwane don rashin samun dama daga iyayensu. Zasu fidda gwani amma sai suce sam sai kin kammala karatu, sun manta da wasiyyar manzon Allah (s.a.w). Wasu kuma suna sheke ayarsune kawai tahanyar biyan bukatarsu ga maza, aduk sadda sha’awarsu ta motsa. Wasu kuma na fama da jimamin rayuwa tayadda suke fama da fuskantar barazanar lecturers lalatattu, da yunkuri batamasu tarbiyya da fansar jarrabawarsu da mutuncinsu. Iyaye ayi hattara zaku iya shiga wuta akan hakkin ‘ya’yayenku don rashin sadaukar musu da hakkinsu daya rataya akanku

‘YAN MATAN LUNGU

Idan akace matan lungu: sune mata masu talle akan titi, dakuma lungu da sashen unguwanni da sakokin ma’aikata, da shaguna (Kwantinan) kasuwanni. irin wadannan matan, idan basu sami kulawar tarbiyyaba sunfi kowasu mata sharri. Domin awani bangaren sukan ‘boye kamarsu suyi kama da mutanen kikrki amma sam bahakan bane azahirance. Kuma mafi yawanci acikinsune ake samun masu sace_sace, da bin maza bayan sunyi aure. domin sun saba da rike kudi masu kauri ahannayensu, ayayin budurcinsu. Hakazalika wasu acikin sunma suna saida budurcinsu kafin aure, a son zuciyarsu kokuma ara’ayin iyayensu mata. Ko uwayen goyensu na bariki. tayadda sukan taradda wulakanci agun mazajensu, dalilin rashin budurci bayan sunyi aure, hakan yake tursasu fita karuwanci bayan aure, ko sata wa mazansu na aure.

‘YAN MATAN BARIKI

Irin wadannan matan basuda mutunci. wanda su kansu sun yadda da hakan, kuma suna iya furtawa da kansu cewa su marasa kunyane amma daga fitsararrun cikinsu. Irin wadannan matan sukan tasone aguri mai lalacewar tarbiyya.

A gunda iyayensu ke zaune babu tarbiyya kuma iyayen basu kulawa da tarbiyyarsu. kuma babu addini agunda suke zaune. Saidai holewa da sha’anin duniyanci dakuma ta’ada, da muta kabbaranci. Ga uwa uba rashin dattako don ko waye ‘yar bariki zata zaki asalinsa ko da kuwa shugaban unguwarsune ko sarkin gari. Wadannan matan ko acikin garine shigarsu daban take sune Manzon Allah (s.a.w) yayimanz ishara dasu acikin hadisi ruwayar bukhari da muslim ” Akwai wasu nau’in mutane da Annabi baigansuba amma zasuzo anan gaba yake fadawa sahabbansa. Yace dasu dukkan wadannan mutane ‘yan wutane. ” na farko dai shugabanni azzalumai yake nufi kokuma masu hukunci da zalinci. nabiyu kuma yace; wasu matane zaku gansu da kaya ajikinsu amma tsaraicinsu na waje suna tafiya suna karairaya jiki, sa’annan kawunansu kamar tozon rakumi, yace kuma bazasu shiga aljannaba, kuma bazasu ta’ba jin kanshin aljannah ba. Domin awani qaulin anajin kamshin aljanna a tsahon tafiyar shekaru dari biyu ko dari biyar.” Allah kakare ‘ya’yanmu da ‘ya’yan ‘yan uwanmu daga Gurbacewar tarbiya.

‘YAN MATAN ASALI

Allah sarki wadannan sune abin tausayi, kuma sune masu wahala, kuma sune masu rabauta duniya da lahira. Tayadda suke fitowa daga gida na mutunci, iyayensu nagartattune su kuma kamammune. Sukan rike budurcinsu iya jimawar da zasuyi gabanin suyi aure. dashi suke samun martaba da nagartar zamantakewarsu ta aure. Kuma kafin suyi aure basu koda cakuduwane cikin maza ballema suyi wani mummunr mu’amala da namiji, hartakai ga sun zubadda mutuncinsu da budurcinsu. Suna matukar Kula ha hakkokin dake kansu na addini dana zamantakewar rayuwa. sune Allah ya ambacesu acikin Alqur’ani yadda yake cewa a Suratul_ahzab. surah ta-33 Aya ta:35 ”Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli’u maza da mãsu tawãlĩu mãtã da mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma.”

Hakika mata masu addini sune mafi dacewa ga dukkanin wani ďa namiji musulmi. Kuma sune zakasamesu masu kyakkyawan hallayya dakuma tsaftatacciyar budurcin wanda babu kazanta acikinsa.

Duk da cewar kwaciyar aure na rana daya tak, yana wanke dattin kazantar bariki, duk jimawar da akayi dashi. Amma kuma duk da hakan kazanta bariki, yakan sanya zargi atsakanin ma’aurata, Zargi na har abada. Musamman ma yazamanto shima mijin mutumin banzane.

Allah karabamu da danasanin duniya da hasarar lahira. Ameen Dukkannin wanda yakaranta wannan rubutun nawa ya sanya aransa shima zai bada gudun mawa wajen gyara yau da goben Al’umar mususulmi kusani acikin addu’arku dani da mahaifana. Albarkacin wannan wata mai albarka ta Raladhana.

INGANCIN ZUQATAN BAYI

INGANCIN ZUCIYA!!! ***************************************** Hakika gyaran zuciya itace maqasudin kar´bar aiki. Da Akwai Ayoyi da hadisai ingantttu dake nuna jinjina ga ayyukan bayi amma dukkansu suna yabawane akan tsarkin zuciya domin shine (sababin karbar aikin). Hakazalika. ibadar da Allah yafisoma, ~Maqasudinsa zuciyace watau (Azumi).

Shi Azumi ALLAHﷻ (s.w.a) Shine kadai keda hakikanin gasgata maiyinsa, Saikuma Zuciyar maiyinsa, Sa`annan kuma ma ALLAHﷻ shi da kansa yake cewa yana son masu tuba damasu tsarki Ma´ana masu tsarkake zuciyoyinsu daga bari munanan ayyuka. Da ayyukan da aka kyamata. Gashinan in arabic text إن الله یحب التوابین ویحب المتطهری Manzon ALLAH ﷺyana cewa إن فی الجسد مضغة إذا صلحت صلح الجسد کله وإذا فسدة فسد الجسد کله علی وهی القلب Arufai kuyimin afuwa nai muku Shisshigi inda kuskere atusaddani. Dan Adam ajizine ALLAHﷻShine masani. dafatan anyi Juma`ah lafiya

MATAKAN TARBIYYA GUDA UKU


MATAKAN TARBIYYA
Daga. Alqalamin Ismail Smart
Dasunan ALLAH Mai RAHAMA Mai JINKAI.
Haqiqa tarbiyya dolece a addinin mu na musulunci musan man ma na iyalanka/ki
Domin ALLAH MADAUKAKI yana cewa:

یا أیهاالذین آمنو قو أنفسکم وأهلیکم نارا وقودها الناس والحجارة
        Awannan aya ALLAH yayi umarni ga Muminai dasu Kare kansu da iyalansu daga wata wutta Wanda yakasance makamashinta mutane ne dakuma duwatsu.
ALLAH UBANGIJI katsaremu amin  ya RABBI. Awannan ‘Bangaren Nakeson nayi rubutu  domin yan uwa musulmai su anfana.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI ya dafamin
MATAKIN FARKO
(Neman Aure zuwa da yakai 5yrs)
Dole Akan kowa Idan yazo neman aure
Yanemi Mai addini Da hali nagari Da kakkyawar zuciya. Ba kawai kyawun fuskaba ko wani martaba ko nasabar Abokin zama ba. Kuma yazamto anyi auren tanasonsa yana sonta.
Domin hakanne Zaisa suji dadin zamantakewarsu ta Aure Kuma hakan Zaisa yayansu sutaso dason junansu Da Bin doka ko umarnin Da akayi masu. Domin kada yazamto uwa tace fari uba yace Bahakaneba Baki yake. Bayan haka
Yazama dole asakawa yaro kakkyawar suna alokacin dayake jinjiri. Yazama dole ka karantar Da matanka tsarin tarbiyyar addinin musulunci ko kasa akarantar da ita Awannan sahar kokuma MA kafin wannnan lokacin. Ma’ana kafin ta sami d’a (yara).
Domin kaso saba’in Cikin Dari (70%) Na Tarbiyyar cikin Gida maqasudinsa na uwace. Yazama dole takasance Mai Lura da Meke gudana me sukeso me yakamata suyi ko so Bari duk wadannan uwace takeda hakkin koyar da yaranta.
Dakuma koyardasu Ibaadaat Kamar Sallah Azumi Dakuma koyamusu karatun Alqur’ani da tilawarsa dama haddarsa. Har sukai 10yrs  Kafin daga bisani Sai Aturasu  Islamiya. Sucigaba da karatu daneman ilimin addini. Hakan zaisa sutaso da ganin girman iyayansu. Dama duk wanda yagirmesu tayadda basai ance ga malam waneba kafin sudaina abinda sukeyi.
MATAKI NA BIYU
(Daga 5yrs zuwa 15 to 18yrs)
Dolene akan iyaye su San abokanan yayansu, Susan Kuma menene alaqarsu dasu Domin duk kyawun tarbiyyar dakasamu agida abokai sukan wargazashi, matsawar dakayi abota da marasa tarbiyya koda baka zama tamkarsu ba. Zaka rudu da wani hali acikin munanan halayyarsu.
Yazama dole iyaye su bawa yayansu tarbiyyar addini da wayewar rayuwa tahanyar sanaddasu yadda zasuyi addini da hikimomin tsara rayuwa bisa kykkyawar tsari. Kamar koyamusu dabarun kare kai da addu’o’in neman tsari da kariya. Da sanardasu tarihohi Wanda zasu sami hikima da, wa’azozi acikinsa. Domin abinciken masana kwakwalwar dan adam sun yarda akan cewa kwakwalwar dan adam takan bude da adana bayanai alokacin da mutum yake dan shekaru takwas (8) zuwa Sha biyar (15) koda haddane mutum yafi nutsuwa dashi awannan lokacin Inhar kaga yaro ya natsu awannan lokacin to tabbas ana kyautata zaton shiryayye ne. Inkuma ya kangare kuwa yanada wuyar shiryuwa Yakamata iyaye sudunga zama da yaransu suna zantawa dasu domin suji damuwoyi da bukatunsu, Harsu san tahanyar da zasu bullo musu gurin bada shawara ko kore musu matsalarsu tarayuwa.
MATAKI NA UKU NAKARSHE
(Daga 15/18yrs. zuwa auraddasu)
Yakamata iyaye su lura da yayansu su san menene wane/wacce tafi/yafi kwarewa akai saisu dage gurin nema masu mafita ta hanyar basu tallafi ko jari domin samun damar gudanar da harkokin rayuwarsa cikin sauki batare da yana zauneba saidai kullum abashi.
      Domin hakan yana kashe zuciyar mutum yazanto baya iya kafuwa da kansa balle ma har yagina wasu. Saidai kullum a bani_bani sai kuma bin abokai da yawace yawacen banza da hofi, da bin bangar siyasa, wadda daga karshe ke jawo mutum yakoma ta’asa da ‘barna acikin al’uma kokuma ma yakama shaye_shaye da bin mugaye mutane. Duk adalilin rashin aikin yi. ALLAH ya tsaremu da zuri’armu baki daya.
       Rashin aikinyi na daya daga cikin abubuwa mafi girma wanda suke lalata  tarbiyya arayuwar mutane.
Allah ka bawa iyayen mu hakurin zama damu kasauke musu hanyar dazasu tarbiyyantar damu tarbiyya ta Addinin musulunci, ALLAH kajikan maifina kahaskaka qabrinsa.