BIYAYYA GA IYAYE

WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE        ➖➖➖➖➖➖➖➖➖                 FITOWA TA ‘DAYA

Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai* Abinda Ake Nufi da *Biyayya* Shine Kyautatawa Da Aikata Alheri da Kuma Bayar da Kyauta. A Takaice, *Biyayya* Suna ne da ya Kunshi Aikata Dukkan Wani Alheri. Kalmar *Birru* (Biyayya) Suna ne Daga Cikin Sunayen *Allah Madaukaki*, Ubangiji Yana Cewa: *{ﺇِﻧَّﺎ ﻛُﻨَّﺎ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻞُ ﻧَﺪْﻋُﻮﻩُ ﺇِﻧَّﻪُ ﻫُﻮَ ﺍﻟْﺒَﺮُّ ﺍﻟﺮَّﺣِﻴﻢُ ﴾ ‏[ ﺍﻟﻄﻮﺭ :٢٨ ‏] .}* Ma’ana: *“Lallai Mun Kasance a Baya Muna Kiransa (Bauta Masa) Lallai Shi (Allah) Mai Kyautatawa ne (Ga Bayinsa), Mai Jinqai”.* (Dur: 28). Abinda Ake Nufi da Kyautatawa Iyaye Kuma Shine: Kyautatawa Zuwa Garesu ta Hanyar Zance da Aiki da Kuma Kusanta Zuwa ga *Allah* Madaukaki. *Ubangiji* Yayi Mana Wasici da Yiwa Iyaye Biyayya a Ayoyi Masu Tarin Yawa a Cikin Alqur’ani, Wanda Hakan Kawai Ya Isa Mu Fahimci Girma da Kuma Qimar Iyaye Wadanda Sune Sila ta Zuwan Mu Gidan Duniya. *Allah ﷻ* Yana Cewa: *{ﻭَﺍﻋْﺒُﺪُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺸْﺮِﻛُﻮﺍ ﺑِﻪِ ﺷَﻴْﺌًﺎ ﻭَﺑِﺎﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﺇِﺣْﺴَﺎﻧًﺎ ﴾ ‏[ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : ٣٦]}* _Ma’ana: *“Ku Bautawa Allah Kada Ku Hadashi da Kowa (A Cikin Bauta), Kuma Iyaye Ku Kyautata Musu”*. (Nisa’i: 36)._ A Cikin Wannan Ayar Mai Albarka, Ubangiji Ya Gwama Kira Zuwa ga Kadaitashi da Bauta da Biyayya ga Iyaye da Kyautatawa Zuwa Garesu. Kuma Sau da Yawa Haka Ubangiji Yake Hada Kansa da Iyaye a Cikin Aya ‘Daya. Kamar Inda Yake Cewa: *{ﺃَﻥِ ﺍﺷْﻜُﺮْ ﻟِﻲ ﻭَﻟِﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻚَ ﺇِﻟَﻲَّ ﺍﻟْﻤَﺼِﻴﺮُ ﴾ ‏[ ﻟﻘﻤﺎﻥ : ١٤]}.* Ma’ana: *“Ka Godemin Sannan Ka Godewa Iyayenka Gareni Makoma Take”*. (Luqman:14). Har Wayau *ﷻ Allah* Yana Cewa: *{ﻭَﻗَﻀَﻰ ﺭَﺑُّﻚَ ﺃَﻟَّﺎ ﺗَﻌْﺒُﺪُﻭﺍ ﺇِﻟَّﺎ ﺇِﻳَّﺎﻩُ ﻭَﺑِﺎﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﺇِﺣْﺴَﺎﻧًﺎ ﺇِﻣَّﺎ ﻳَﺒْﻠُﻐَﻦَّ ﻋِﻨْﺪَﻙَ ﺍﻟْﻜِﺒَﺮَ ﺃَﺣَﺪُﻫُﻤَﺎ ﺃَﻭْ ﻛِﻠَﺎﻫُﻤَﺎ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻘُﻞْ ﻟَﻬُﻤَﺎ ﺃُﻑٍّ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻨْﻬَﺮْﻫُﻤَﺎ ﻭَﻗُﻞْ ﻟَﻬُﻤَﺎ ﻗَﻮْﻟًﺎ ﻛَﺮِﻳﻤًﺎ * ﻭَﺍﺧْﻔِﺾْ ﻟَﻬُﻤَﺎ ﺟَﻨَﺎﺡَ ﺍﻟﺬُّﻝِّ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﺔِ ﻭَﻗُﻞْ ﺭَﺏِّ ﺍﺭْﺣَﻤْﻬُﻤَﺎ ﻛَﻤَﺎ ﺭَﺑَّﻴَﺎﻧِﻲ ﺻَﻐِﻴﺮًﺍ *ﺭَﺑُّﻜُﻢْ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﻤَﺎ ﻓِﻲ ﻧُﻔُﻮﺳِﻜُﻢْ ﺇِﻥْ ﺗَﻜُﻮﻧُﻮﺍ ﺻَﺎﻟِﺤِﻴﻦَ ﻓَﺈِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻟِﻠْﺄَﻭَّﺍﺑِﻴﻦَ ﻏَﻔُﻮﺭًﺍ ﴾ ‏[ ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ :٢٣-٢٥}* Ma’ana: *“Ubangijinka ya Hukunta Kada a Bautawa Wani Sai Shi Kadai Kuma Iyaye a Kyautata Musu; Idan ‘Daya Daga Cikinsu Girma Yazo Masa a Wurinka Ko Duka Biyun (Mahaifi da Mahaifiya), Kada Kace Masu Tir, Kuma Kada Kayi Musu tsawa, Ka Fada Musu Zance Mai Girma (Me Dadi)……………..”.* (Isra’i: 23-25). A Wata Aya Kuma *Ubangiji* Yana Cewa: *{ﻭَﻭَﺻَّﻴْﻨَﺎ ﺍﻟْﺈِﻧْﺴَﺎﻥَ ﺑِﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻪِ ﺣُﺴْﻨًﺎ ﴾ ‏[ ﺍﻟﻌﻨﻜﺒﻮﺕ : ٨]}.* Ma’ana: *“Munyi Wasici ga Mutum da Ya Kyautatawa Mahaifansa”.* (Ankabut: 8). *Imam Ibn Kathir (rh)* Yana Cewa: “Ubangiji Ya Umurci Bayinsa da Kyautatawa Mahaifa Bayan Ya Kwadaitar da Kadaitashi da Bauta. Domin Mahaifa Sune Sababin Zuwan Mutum Duniya, Saboda Haka Sune Sukafi Dacewa da a Kyautata Musu. Mahaifi ta Hanyar Ciyar Dashi Ita Kuma Mahaifiya ta Hanyar Tausaya Mata”. *(Tafseer Ibn Kathir: v6/ p238)*. *BIYAYYA GA IYAYE SIFFAR ANNABAWA NE* ➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖ Hakika *Ubangiji* Madaukaki Ya Siffanta Wasu Daga Cikin Annabawansa da Kasancewarsu Masu Matukar Biyayya ga Iyayensu Inda Yake Cewa a Cikin Littafinsa: *{ﻳَﺎ ﻳَﺤْﻴَﻰ ﺧُﺬِ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏَ ﺑِﻘُﻮَّﺓٍ ﻭَﺁﺗَﻴْﻨَﺎﻩُ ﺍﻟْﺤُﻜْﻢَ ﺻَﺒِﻴًّﺎ * ﻭَﺣَﻨَﺎﻧًﺎ ﻣِﻦْ ﻟَﺪُﻧَّﺎ ﻭَﺯَﻛَﺎﺓً ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺗَﻘِﻴًّﺎ * ﻭَﺑَﺮًّﺍ ﺑِﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻪِ ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﺟَﺒَّﺎﺭًﺍ ﻋَﺼِﻴًّﺎ * ﻭَﺳَﻠَﺎﻡٌ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻳَﻮْﻡَ ﻭُﻟِﺪَ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﻳَﻤُﻮﺕُ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﻳُﺒْﻌَﺚُ ﺣَﻴًّﺎ ﴾ ‏[ ﻣﺮﻳﻢ : 12 – 15 ‏]}.* Ma’ana: *“Ya Yahya ka Riqe Littafi da Karfi Mun Bashi Hukunci Yana Karami# Yana Mai Biyayya ga Iyayensa be Kasance Me Girman Kai  me Sa6awa Ubangiji ba# Aminci Ya Tabbata a Gareshi Ranar da Aka Haifeshi, da Ranar da Zai Mutu da Ranar da Za’a Tasheshi Yana rayayye”.* (Maryam: 12-15). Ubangiji* Yana Cewa Game da Annabi *Isah (as): *{ﻗَﺎﻝَ ﺇِﻧِّﻲ ﻋَﺒْﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺁﺗَﺎﻧِﻲَ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏَ ﻭَﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻧَﺒِﻴًّﺎ * ﻭَﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻣُﺒَﺎﺭَﻛًﺎ ﺃَﻳْﻦَ ﻣَﺎ ﻛُﻨْﺖُ ﻭَﺃَﻭْﺻَﺎﻧِﻲ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﺍﻟﺰَّﻛَﺎﺓِ ﻣَﺎ ﺩُﻣْﺖُ ﺣَﻴًّﺎ * ﻭَﺑَﺮًّﺍ ﺑِﻮَﺍﻟِﺪَﺗِﻲ ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﺠْﻌَﻠْﻨِﻲ ﺟَﺒَّﺎﺭًﺍ ﺷَﻘِﻴًّﺎ * ﻭَﺍﻟﺴَّﻠَﺎﻡُ ﻋَﻠَﻲَّ ﻳَﻮْﻡَ ﻭُﻟِﺪْﺕُ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﺃَﻣُﻮﺕُ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﺃُﺑْﻌَﺚُ ﺣَﻴًّﺎ * ﺫَﻟِﻚَ ﻋِﻴﺴَﻰ ﺍﺑْﻦُ ﻣَﺮْﻳَﻢَ ﻗَﻮْﻝَ ﺍﻟْﺤَﻖِّ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻓِﻴﻪِ ﻳَﻤْﺘَﺮُﻭﻥَ ﴾ ‏[ ﻣﺮﻳﻢ :٣٠ -٣٤]}* Ma’ana: *“Yace Ni Bawan Allah ne An Bani Littafi Kuma an Sanyani Na Zamo Annabi# Kuma Aka Sanyani Me Albarka a Duk Inda Na Kasance Akayimin Wasici dayin Sallah da Bayar da Zakkah Matukar Ina Raye# Kuma Me Biyayya ga Mahaifiyata be Sanyani Me Taurin Kai Mara Rabo ba# Aminci Ya Tabbata a Gareni Ranar da Aka Haifeni da Ranar da Zan Mutu da Kuma Ranar da Za’a Tasheni Rayayye# Wannan Shine Isah ‘Dan Maryam, Zance Né Na Gaskiya Wanda Suke Musu”* (Maryam: 30-34). Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك*   WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE        ➖➖➖➖➖➖➖➖➖                   FITOWA TA BIYU _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_ _*KWADAITARWAR MANZON ALLAH (ﷺ) GAME DA BIYAYYA GA IYAYE*_ _Hakika *Manzon Allah(ﷺ)* Ya Kwadaitar da Wannan Al’ummah Lada da Kuma Falalar Biyayya da Iyaye Hatta Iyayen da Musulmai ba, Sannan Kuma Ya tsoratar game da Sa6a Musu, Kamar Yanda Zamu Gani a Hadisai Masu Zuwa:_ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩٍ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﺳﺄﻟﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﻠﺖ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﺃﻱ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺃﻓﻀﻞ؟ ﻗﺎﻝ : )) ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻰ ﻣﻴﻘﺎﺗﻬﺎ (( ،ﻗﻠﺖ : ﺛﻢ ﺃﻱ؟ ﻗﺎﻝ : )) ﺛﻢ ﺑﺮُّ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦِ (( ،ﻗﻠﺖ : ﺛﻢ ﺃﻱ؟ ﻗﺎﻝ : )) ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ (( ؛ ‏( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺣﺪﻳﺚ ٥٢٧ / ﻣﺴﻠﻢ ﺣﺪﻳﺚ ٨٥)}* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Mas’ud (ra)* Yace: Na Tambayi *Manzon Allah (ﷺ)* Nace: Ya Annabin Allah, Wane Aiki ne Yafi Falala? Sai Yace: *“Sallah Akan Lokacinta”.* Sai Nace Sannan Me? Sai Yace: *“Sannan Biyayya ga Iyaye”*. Sannan Nace Sai Mene? Sai Yace: *“Jihadi don ‘Daukaka Kalmar Allah”*. (Bukhari:257, Muslim:85)._ _Ya Dan Uwa Ka Duba Girman Jihadi don Daukaka Kalmar Allah, Wanda Duk Wanda Ya Mutu a Halin Jihadi Bashi da Sakamakon da ya Gaza Shiga Aljannah, Sannan Ko Hisabi Baza’ayi Musu ba Saboda Falalar Abinda Suka Mutu Akai. Tare da Haka *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Gabatar da Biyayya gareshi._ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ : ﺟﺎﺀ ﺭﺟﻞ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺎﺳﺘﺄﺫﻧﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ،ﻓﻘﺎﻝ : )) ﺃﺣﻲٌّ ﻭﺍﻟﺪﺍﻙ؟ (( ، ﻗﺎﻝ : ﻧﻌﻢ،ﻗﺎﻝ : )) ﻓﻔﻴﻬﻤﺎ ﻓﺠﺎﻫِﺪْ (( ؛ ‏( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺣﺪﻳﺚ ٣٠٠٤ / ﻣﺴﻠﻢ ﺣﺪﻳﺚ ٢٥٤٩)}.* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Amru (ra)* Yace: Wani Mutum Yaje Wurin *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Neman Ayi Masa Izinin Fita Jihadi, sai *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Shin Iyayenka Suna Raye?”* Sai Mutumin Yace Eh. Sai *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Kaje Kayi Jihadinka a Wurinsu”.* (Bukhari: 3004, Muslim: 2549)._ _*Imam Ibn Hajar Al-Asqalany (rh)* Yayi Karin Bayani Game da Wannan Hadisin Inda Yake Cewa: “Jihadi Yana Haramta Matukar Iyaye Basu Amince da Fitar ba, Amma da Sharadin Iyayen su Zamo Musulmai. Domin Yi Musu Biyayya Farillah ce ta Ainihi (Wajibi), Fita Jihadi Kuma Farillah ce ta Kifaya (Mustahabbi)”. *(Fathul Bary: V-6, p163)*_ *{ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ، ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : )) ﻻ ﻳَﺠﺰﻱ ﻭﻟﺪٌ ﻭﺍﻟﺪًﺍ ﺇﻻ ﺃﻥ ﻳﺠﺪَﻩ ﻣﻤﻠﻮﻛًﺎ ﻓﻴﺸﺘﺮﻳَﻪ ﻓﻴُﻌﺘﻘَﻪ (( ؛ ‏( ﻣﺴﻠﻢ – ﺣﺪﻳﺚ ١٥١٠)}* _An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“’Da Bazai Iya Sakawa Mahaifinsa ba Sai fa Idan Ya Samu Mahaifin ne a Matsayin Bawa, Sai Ya Siyeshi Sannan Ya ‘Yantashi”*. (Muslim: 1510)._ *{ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪٍ ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ : ﺃﻥ ﺭﺟﻠًﺎ ﻫﺎﺟﺮ ﺇﻟﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣِﻦ ﺍﻟﻴﻤﻦ، ﻓﻘﺎﻝ : )) ﻫﻞ ﻟﻚ ﺃﺣﺪ ﺑﺎﻟﻴَﻤﻦ؟ (( ، ﻗﺎﻝ : ﺃﺑﻮﺍﻱ،ﻗﺎﻝ : )) ﺃَﺫِﻧﺎ ﻟﻚ؟ (( ، ﻗﺎﻝ : ﻻ،ﻗﺎﻝ : )) ﺍﺭﺟِﻊْ ﺇﻟﻴﻬﻤﺎ ﻓﺎﺳﺘﺄﺫﻧﻬﻤﺎ، ﻓﺈﻥ ﺃﺫﻧﺎ ﻟﻚ ﻓﺠﺎﻫِﺪْ، ﻭﺇﻻ ﻓﺒَﺮَّﻫﻤﺎ (( ؛ ‏( ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ‏) ‏( ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ ﺣﺪﻳﺚ ٢٢٠٧)}.* _An Kar6o Daga *Abi-Sa’eedil Khudry (ra)*, Lallai Wani Mutum Yayi Hijirah Daga Yaman Zuwa Wurin *Manzon Allah(ﷺ)* Sai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace Dashi: *“Shin Kanada Wani a Yaman?”*. Sai Mutumin Yace: Eh Inada Iyaye na. Sai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *“Shin Su Sukayi Maka Izini?”* Sai Yace: A’a. Sai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace Dashi: *“Ka Koma Zuwa Garesu Ka Nemi Izininsu, Idan Sukayi Maka Izini Sai Kazo Kayi Jihadi. Idan Kuma Sukaqi Amincewa, to Kayi Musu Biyayya”*. (Abi-Daud: 2207)._ _An Kar6o Daga *Jabir bn Abdullah (ra)* Lallai Wani Mutum Yace: Ya *Manzon Allah (ﷺ)* Lallai Inada Dukiya da Yaro, Kuma Mahaifiya Yanason Ya Kwace Dukiyata. Sai *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Kai da Dukiyarka Ai Na Mahaifinka ne”.* (Ibn-Majah:1855)._ _*Imamud ‘Dahãwy (rh)* Yana Cewa: “Wani 6angare Na Malamai Suna Cewa: “Duk Abinda Yaro Zai Samu Nashi ne Shi Kadai Banda Mahaifinsa. Zancen da *Manzon Allah (ﷺ)* Yayi ba Yana Nuna Cewa Duk Abinda Yaro ya Mallaka Mallakin Ubansa Bane. Abinda Yake Nufi Shine Baya Kamata Ga Yaro Ya Sa6awa Mahaifinsa Saboda Wani Abu, Wajibine Yayi Masa Biyayya Gwargwadon Iko”. (Sharhu Ma’anil Ãthar Lid ‘Dahãwy: Vol. 4, P. 169)._ _Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_ *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك*  WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE        ➖➖➖➖➖➖➖➖➖                 FITOWA TA UKU _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_ _*ZANTUKAN MAGABATA NA KWARAI*_       _*GAME DA BIYAYYA GA IYAYE*_ _Idan Bamu Manta ba, a Rubutu Mu Daya Gabata Mun Fara Kawo Maganganun Magabata Na Kwarai Game da Yiwa Iyaye Biyayya. A Yau Idan Allah Ya Yarda Zamu Cigaba daga Inda Muka tsaya._ *{ﻗﺎﻝ ﻟﻘﻤﺎﻥ ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ ﻻﺑﻨﻪ : ﻳﺎ ﺑﻨﻲ، ﻣَﻦ ﺃﺭﺿﻰ ﻭﺍﻟﺪﻳﻪ ﻓﻘﺪ ﺃﺭﺿﻰ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦَ، ﻭﻣﻦ ﺃﺳﺨَﻄﻬﻤﺎ ﻓﻘﺪ ﺃﺳﺨَﻂ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦَ؛ ‏( ﺑﺮ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ – ﻷﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﺍﻟﻄﺮﻃﻮﺷﻲ ﺹ – ٣٧)}* _*Luqman* Yana Cewa ‘Dansa: *“Yakai ‘Dãna! Duk Wanda Ya Yardar da Mahaifansa, Hakika Ya Yardar da Me Rahama. Kuma Duk Wanda Ya Fusatasu, Hakika Ya Fusata Me Rahama”*. (Birrul Walidain Na Abi-Bakar ‘Dardushy: P. 8)._ _Hakika Wannan Zance Na Luqman Yayi Daidai da Zancen *Annabi* Da Yake Cewa: *“Yardan Allah Yana Cikin Yardan Iyaye, Kuma Fushin Ubangiji Yana Cikin Fushin Mahaifa”*. Saboda Haka Idan Kana Bukatar Ubangiji Ya Yarda Dakai, to ka Kyautatawa Mahaifansa Har Su Yarda Dakai. Idan Kuma Kafi Bukatar Fushin Ubangiji da Uqubarsa, to Ka Cigaba da Wulakantasu Lallai Ubangijin Shi Kuma Yana nan a Madaka._ *{ﻗﺎﻝ ﻟﻘﻤﺎﻥ ﻻﺑﻨﻪ : ﻳﺎ ﺑﻨﻲ، ﺇﻥ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦِ ﺑﺎﺏٌ ﻣﻦ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﺇﻥ ﺭﺿﻴَﺎ ﻋﻨﻚ ﻣﻀﻴﺖَ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﻭﺇﻥ ﺳﺨِﻄﺎ ﺣُﺠِﺒﺖ؛ ‏( ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ٨٠)}* _Har Wayau *Luqman* Yana Fadawa ‘Dansa Cewa: *“Lallai Mahaifa Kofa ne Daga Cikin Kofofin Aljannah, Idan Suka Yarda Dakai Zaka Zarce Aljannah. Idan Kuma Sukayi Fushi Dakai, Za’a Shamakanceka Daga Shiga Aljannah”*. (Kitabul Birr Was Sila Na *Ibn Jauzy* p. 80)._ *{ﺭﻭﻯ ﻋﺒﺪﺍﻟﺮﺯﺍﻕ ﻋﻦ ﻃﺎﻭﺱ ﺑﻦ ﻛﻴﺴﺎﻥ ﻗﺎﻝ : ﻣِﻦ ﺍﻟﺴﻨَّﺔ ﺃﻥ ﻳﻮﻗَّﺮَ ﺃﺭﺑﻌﺔ : ﺍﻟﻌﺎﻟﻢ، ﻭﺫﻭ ﺍﻟﺸَّﻴﺒﺔ، ﻭﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ، ﻭﺍﻟﻮﺍﻟﺪ، ﻗﺎﻝ : ﻭﻳﻘﺎﻝ : ﺇﻥ ﻣِﻦ ﺍﻟﺠﻔﺎﺀ ﺃﻥ ﻳﺪﻋﻮَ ﺍﻟﺮﺟﻞُ ﻭﺍﻟﺪَﻩ ﺑﺎﺳﻤِﻪ؛ ‏( ﻣﺼﻨﻒ ﻋﺒﺪﺍﻟﺮﺯﺍﻕ – ﺝ – ١١ – ﺭقم ٢٠١٣٣)}* _*Abdulrazak* Ya Ruwaito Daga *’Dawus bn Kaisãn* Yace: *“Yana Daga Cikin Sunnah a Girmama Mutane Hudu: Malami, da Mutum Me Furfura, da Shugaba da Kuma Mahaifi”*. Ya Kasance Yana Cewa: “Yana Daga Cikin Jafa’i Mutum Ya Kira Mahaifinsa da Sunansa”. (Musannaf Abdulrazaq: Vol. 11 No. 20133)._ *{ﻟﻤﺎ ﻣﺎﺗﺖ ﺃﻡ ﺇﻳﺎﺱ ﺑﻦ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺑﻜﻰ، ﻗﻴﻞ ﻟﻪ : ﻣﺎ ﻳﺒﻜﻴﻚ؟ ﻗﺎﻝ : ﻛﺎﻥ ﻟﻲ ﺑﺎﺑﺎﻥِ ﻣﻔﺘﻮﺣﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﻭﻏُﻠِّﻖ ﺃﺣﺪُﻫﻤﺎ؛ ‏( ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ – ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ٧٢)}* _A Yayin da Mahaifiya *Iyyas bn Mu’awiya* Ta Rasu Yayita yin Kuka. Sai Akace Dashi Menene Yake Sakaka Kuka? Sai Yace: *“Na Kasance Inada Kofofi Guda Biyu Budaddu Zuwa ga Aljannah, A Yau An Kulle Guda ‘Daya”.* (Kitabul Birri Was Silah Na *Ibn Jauzy*: P. 72)._ *{‏ﻗﺎﻝ ﻣﻜﺤﻮﻝ ﺍﻟﺸﺎﻣﻲ : ﺑﺮُّ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ ﻛﻔَّﺎﺭﺓٌ ﻟﻠﻜﺒﺎﺋﺮ؛ ‏( ﺷﺮﺡ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻟﻠﺒﻐﻮﻱ ﺝ – ١٣ ﺹ – ١٣)}* _*Makhul Ash-Shamy* Yana Cewa: *“Biyayya ga Iyaye Yana Kankare Manyan Zunubai”*. (Sharhu Sunnah Na Bagawy: Vol. 13, p. 13)._ *{ﻗﺎﻝ ﺳﻔﻴﺎﻥ ﺑﻦ ﻋﻴﻴﻨﺔ : ﻣَﻦ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕِ ﺍﻟﺨﻤﺲَ ﻓﻘﺪ ﺷﻜﺮ ﻟﻠﻪ، ﻭﻣﻦ ﺩﻋﺎ ﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻪ ﻋﻘﺒﻬﺎ ﻓﻘﺪ ﺷﻜﺮ ﻟﻬﻤﺎ؛ ‏( ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ – ﻻﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﺍﻟﻌﺴﻘﻼﻧﻲ – ﺝ – ٢ – ﺹ – ١٠)}* _*Sufyãn bn Uyaina* Yana Cewa: *“Duk Wanda ya Sallaci Sallolli Biyar, Hakika Ya Godewa Allah. Wanda Duk Yayiwa Iyayensa Addu’a Bayan Sallolin, Hakika Ya Godewa Iyayensa”*. (Fathul Bary: Vol. 2, P. 10)._ *{ﻗﺎﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﺤﻴﺮﻳﺰٍ : ﻣَﻦ ﻣﺸﻰ ﺑﻴﻦ ﻳﺪَﻱْ ﺃﺑﻴﻪ ﻓﻘﺪ ﻋﻘَّﻪ، ﺇﻻ ﺃﻥ ﻳﻤﺸﻲ ﻓﻴﻤﻴﻂ ﻟﻪ ﺍﻷﺫﻯ ﻋﻦ ﻃﺮﻳﻘﻪ، ﻭﻣﻦ ﺩﻋﺎ ﺃﺑﺎﻩ ﺑﺎﺳﻤﻪ ﺃﻭ ﺑﻜﻨﻴﺘﻪ ﻓﻘﺪ ﻋﻘَّﻪ، ﺇﻻ ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻝ : ﻳﺎ ﺃﺑﺖِ؛ ‏( ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ – ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ١١٧)}* _*Muhammad bn Muhairiz* Yace: *“Duk Wanda Yake Tafiya a Gaban Mahaifinsa, Hakika Ya Sa6a Masa; Sai fa Idan Ya Shiga Gaban Nasa ne Domin Kauda Abinda Zai Cutar Dashi ne. Kuma Duk WanKumYa Kira Mahaifinsa da Sunansa ko da Alkunyarsa Hakika Ya Sa6a Masa, Sai Dai Idan Zaice Ya Mahaifina”.* (Al-Birri Was Silah Na *Ibn Jauzy*: 117)._ *{ﻗﺎﻝ ﻣﺠﺎﻫﺪُ ﺑﻦ ﺟﺒﺮٍ : ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻟﻠﻮﻟﺪ ﺃﻥ ﻳﺪﻓﻊ ﻳﺪَ ﻭﺍﻟﺪﻩ ﻋﻨﻪ ﺇﺫﺍ ﺿﺮﺑﻪ، ﻗﺎﻝ : ﻭﻣَﻦ ﺷﺪ ﺍﻟﻨﻈﺮ ﺇﻟﻰ ﻭﺍﻟﺪﻳﻪ ﻓﻠﻢ ﻳَﺒَﺮَّﻫﻤﺎ، ﻭﻣَﻦ ﺃﺩﺧﻞ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺣﺰﻧًﺎ ﻓﻘﺪ ﻋَﻘَّﻬﻤﺎ؛ ‏( ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ – ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ١١٧)}* _*Mujãhid bn Jubrin* Yana Cewa: *“Baya Dacewa ga Yaro Ya Ture Hannuna Mahaifinsa a Lokacin da Yake Dukansa. Wanda Duk Ya tsananta Kallo ga Mahaifinsa, be Girmamashi ba. Duk Wanda Ya Sanyasu Damuwa, Hakika Ya Sa6a Musu”*. (Albirru Was Silah Na *Ibn Jauzy*: 117)._ _Dan Uwa Ka Duba Kaga Yanda Magabata Suke Girmama Sha’anin Mahaifa, Yanda Suke Ganin Sa6a Musu da Fusatasu Tamkar Yankan Tikitin Jahannama ne._ _Yanzu Ya Rage Gareni Dakai Mu Duba Alaqar Dake tsakanin mu da Mahaifan Mu, Shin Akwai Kyakkywan Alaqa tsakanin Mu Dasu? Idan Akwai Sai Mu dage Wajen Kara Kyautata Musu. Idan Kuma Babu Kyakkyawar Alaqa a tsakaninmu, Sai Mu Koma Mu Roqesu Gafara Kafin Lokaci Ya Qure Domin Samun tsira Anan Duniya Da Gobe Qiyama._ _*Allah Ka Sakawa Iyayenmu da Alkhairi, Wadanda Suka Rasu Kuma Ka Gafarta Musu Kasa Aljannah Ce Makomarsu*_ _Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_ *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك* WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE                        FITOWA TA HUDU _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_ _*ADDU’AR IYAYE NAGARI KARBABBA CE*_ _Lallai Yana Daga Cikin Girmamawa da Ubangiji Yayiwa Iyaye Nagari Shine Amsar Addu’arsu Nagari da ma Wanda ba Nagari ba ga ‘Ya’yansu, Musamman a Lokacin da Girma Yazo Musu. Wannan Kuma Abu ne da Yake Aukuwa Akan Idanun mu a Wannan Rayuwar Tamu ta Duniya. Hakika *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Fadakar Damu Akan Haka a Cikin Hadisai Masu Yawa, ga Kadan Daga Cikinsu:_ *{ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ، ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ”ﺛﻼﺙُ ﺩﻋﻮﺍﺕٍ ﻣﺴﺘﺠﺎﺑﺎﺕ : ﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻤﻈﻠﻮﻡ، ﻭﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻤﺴﺎﻓﺮ، ﻭﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ ﻋﻠﻰ ﻭﻟﺪﻩ“. ‏(صحيح في أدب الهفرد:٤٨٨)}* _An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)*, Daga *Annabi (ﷺ)* Yace: *“Addu’ar Guda Uku Kar6a66u ne: Addu’ar Wanda Aka Zalunta; da Addu’ar Matafiyi; da Kuma Addu’ar Mahaifi Akan ‘Dansa”.* Hadisi ne Ingantacce (Sahih Adabul Mufrad: 488)._ _*Hasanul Basary* Yana Cewa: “Addu’ar Mahaifa Tana Tabbatar da Dukiyar Yaro. Sannan Addu’ar Mahaifa Tana Sadar da Dukiya Yaro”. (Al-Birru Was-Sila Na *Ibn Jauzy*: 120- 123)._ _*YARDAN IYAYE NAGARI TANA DAGA YARDAR ALLAH*_ _Wajibi ne Mu Sani Cewa Lallai Akwai Dangantaka tsakanin Yardan Ubangiji da Kuma Amincewar Mahaifa. Saboda Hakane Ya Zam Wajibi Akan ‘Ya’ya da Su Kwadaitu Wajen Neman Yardan Mahaifansu ta Hanyar Yi Musu Biyayya a Cikin Abinda Be Sa6awa Mahalicci ba, Domin Samun Yardan Allah Anan Duniya da Gobe Kiyama. Hakika Annabin Mu Ya Shiryar Damu Haka a da Dama Daga Cikin Haidisansa:_ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮٍﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ، ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ”ﺭﺿﺎ ﺍﻟﺮﺏِّ ﻓﻲ ﺭﺿﺎ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ، ﻭﺳﺨَﻂ ﺍﻟﺮﺏِّ ﻓﻲ ﺳﺨﻂ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ“. ‏(ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ‏) ‏( ﺻﺤﻴﺢ الترمذي:١٥٤٩)}* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Amru bn Ass (ra)*, Daga *Annabi  (ﷺ)* Yace: *“Yardar Ubangiji Tana Cikin Yardan Mahaifa, Kuma Fushin Ubangiji Yana Cikin Fushin Mahaifa”*. Hadisi ne Ingantacce (Sahih Tirmizi: 1549)._ _Wannan Hadisi Dalili ne Akan Falalar Kyautatawa Mahaifa da Kuma Wajibcin Yin Hakan. Domin Aikata Hakan Shine Sababin Samin Yardan Ubangiji. Sannan Har Wayau Hadisin Yana Razanarwa Akan Sa6awa Mahaifa da Kuma Haramcin Sa6a Musu. Domin Sa6a Musun Yana Sabbabawa Mutum Haduwa da Fushin Ubangiji._ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﻗﺎﻝ : ”ﻛﺎﻧﺖ ﺗﺤﺘﻲ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻭﻛﻨﺖ ﺃﺣﺒﻬﺎ، ﻭﻛﺎﻥ ﻋﻤﺮ ﻳﻜﺮﻫﻬﺎ، ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻲ : ﻃﻠِّﻘْﻬﺎ، ﻓﺄﺑﻴﺖُ، ﻓﺄﺗﻰ ﻋﻤﺮُ ﺍﻟﻨﺒﻲَّ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺬﻛﺮ ﺫﻟﻚ ﻟﻪ، ﻓﻘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻃﻠِّﻘْﻬﺎ“. (ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ‏)( ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ ﺣﺪﻳﺚ: ٤٢٨٤)}* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Umar bn Khaddab (ra)* Yace: *“Na Kasance Inada Mata Kuma Ina Matukar Sonta, Umar Kuma Ya Kasance Baya Sonta, Sai Yace Dani: “Na Saketa,  Sai Naqi Sakinta. Sai Umar Yaje Wurin Manzon Allah (ﷺ) Ya Ambata Masa Abinda Ke Faruwa, Sai Annabi Yace Ya Saketa”*. (Abi-Daud: 4284)._ _*Fa’idah Mai Muhimmanci:* _Yakamata Iyaye Su Fahimci Cewa Wanda Ya Nemi ‘Dansa da ya Saki Matarsa *Umar bn Khaddab* ne. Ba Kowane Uba Bane Yake da Ikon Aiwatar da Abinda *Umar* Ya Nemi ‘Dansa dayi ba. Musamman Ma Idan Aka Samu Sa6ani tsakanin Mahaifin Yaro da Matar Yaron Akan Abin Duniya, Mahaifin Yaro Kamata Yayi Ya Duba Mas’alar ta Hanyar Adalci, Idan Har Matarc da Gaskiya, Wajibi ne a Tabbatar Mata da Gaskiyarta Uban Kuma Yayi Hakuri Kada Yace Zai Tursasa ‘Dansa Akan Ya Saki Matarsa. Amma Idan Laifinta Ya Sa6awa Ubangiji ne Kamar Batayin Sallah, Ko Magulmaciya ce, Kuma Anyi Mata Nasiha Taqiji, Wannan Uban Miji Yanada Iko Akan Ya Umurci ‘Dansa da ya Saki Matarsa Kamar Yanda *Umar* Yayi. Kuma Wajibi ne ‘Dan Nasa Yayi Masa Biyayya._ _Wani Mutum Ya Tambayi *Imam Ahmad bn Hambal* Cewa: Lallai Mahaifinsa Ya Umurceshi da ya Saki Matarsa, Sai *Imam Ahmad* Yace: *“Kada Ka Sake ta”*. Sai Mutumin Yace: Shin ba *Umar* Ya Umurci ‘Dansa *Abdullahi* da ya Saki Matarsa ba? Sai *Imam Ahmad* Yace: *“Ka Bari Har Sai Mahaifinka Ya Zamo Kwatankwacin Umar”*. (Al-Adabush Shar’iyya)._ _An Tambayi *Imam Ibn Taimiyya (rh)* Game da Mutumin da Mahaifiyarsa ta Umurcesa da ya Saki Matarsa. Sai. *Ibn Taimiyya* Yace: *“Baya Halatta a Gareshi da Ya Saki Matarsa, Sai dai Wajibi ne Yayi Mata Biyayya, Amma Sakin Matarsa Baya Cikin Yi Mata Biyayya”*. (Adabush Shar’i: 447)._ *{ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺪﺭﺩﺍﺀ : ﺃﻥ ﺭﺟﻠًﺎ ﺃﺗﺎﻩ ﻓﻘﺎﻝ : ﺇﻥ ﻟﻲ ﺍﻣﺮﺃﺓً، ﻭﺇﻥ ﺃﻣﻲ ﺗﺄﻣﺮﻧﻲ ﺑﻄﻼﻗﻬﺎ،ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﺪﺭﺩﺍﺀ : ﺳﻤﻌﺖُ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ : ”ﺍﻟﻮﺍﻟﺪُ ﺃﻭﺳﻂُ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻨﺔ, ﻓﺈﻥ ﺷﺌﺖَ ﻓﺄﺿِﻊْ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺒﺎﺏ، ﺃﻭ ﺍﺣﻔَﻈْﻪ“. ‏( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ: ١٥٤٨}* _An Kar6o Daga *Abi-Darda’i (ra)* Lallai Wani Mutum Yazo Masa Sai Yace: Lallai Inada Mata, Kuma Mahaifiyata ta Umurceni Dana Saketa. Sai *Abi-Darda’i* Yace: Dashi: Naji *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa: *“Mahaifa Sune Mafi Alkhairin Kofofin Aljannah. Idan Kaso Ka Tozarta Wannan Kofar, Ko Kuma Ka Kiyayeta”*. (Tirmizi: 1548)._ _Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_ *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك* IDAN KUNASO MUCI GABA SAI KUYI MANA MAGANA TA EMAIL

TARIHIN GWARGWARMAYAR KAFA IZALA

ASSASA IZALA A NIGERIA

Izala Ikon ALLA ﷻ

KADAN DAGA TARIHIN SHEIKH ISMA’ILA IDRIS BN ZAKARIYYA !!!

kamar yadda nayi maku Alqawari


     **Gwagwar mayarsa wajen Kafa Izala da Sunnah**

Sheikh Isma’ila Idris yatasone cikin al’umar nan tamu ta Nigeria, ayankin Arewa inda awannan lokacin babu wata aqida a Qasarnan bayan Dariqar Tijjaniyya, Qarqashin jagorancin sheikh Ibrahim Inyas Alkaulahy.
     To dake zamani ya Nausa tafiya tayi nisa, Al’uma tasamu kanta cikin yanayi na Cakuda addini da Son zuciya. Ana samun Malamai masu Sanya Son ransu acikin addini suna anfani dasunan Addini Suna isarda Munanan manufofinsu ga Al’uma kalar Bokanci da Sihirin Duba dama wasu Tsubbace_tsubbace su na Son Zuciya da Neman duniya.
    Wanda yaci karo da koyarwar Addinin Musulunci. Dukkan mai irin wad’annan aiki Bai tabayinsu Saiya fita a addinin Musulunci, Yazamo dukkan wanda yayi Sunansa kafiri da Nassin Aya acikin Suratu baqarah. Haqiqah bayan Wannan Akwai wasu littattafai dadama wadanda Maluma suka shigo dashi ake karantasu na Labaran mafarki da Tatsuniyoyi dasunan Adddini, Irin wadannan abubuwa dakuma makamantansu Sune maqasudin Da’awar ta Sheikh Isma’il Idris, abisa fahimtar masu kyautata masa zato.
    Da’akwai wadanda suke ganin cewa kawai yafara da’awar izala ne kawai Don Neman Suna dakuma Zagin Wasu malamai (Shehunnan ‘Dariau) dakuma Sufaye. Wanda kuma hakan kuskurene domin  Aikin Musulmi shine kyautatawa juna zato. Da Kuma nemawa juna gafara agunda akayi Kuskure danganeda Sa’banin Ra’ayi ko Fahimta.


    Zamu cigaba ta Tarihi.
    Bayan Malam Yabar aikin Soja wanda acikin Aikin nasa na Soja ya fara da’awa akan barin Tsubbu da Daura layu da makamantansu, Malam yasha tsangwama daga makiya dakuma wadanda basu da ilimi wanda basu fahimceshi ba. Ba awannan Lokaci malam yaga cewar Wannan Da’awa tasa bazata cigaba ba Har saida wata Qungiya Wacce zata Tallafa masa Danganeda samun cikar Qudirinsa na Farkadda mutane game da Sunnah Asali.
    Awannan lokacine malam ya Assasa wata Kungiya mai Suna; ”Jama’atu izalatul Bid’ah ” Ma’ana ( Gungiyar dake kawar da Bidi’ah ) Wannan Kungiya Tasa tasamu karbuwa hatta aciki ‘Yan uwa Sojoji na wannan lokaci, Saidai kuma tasamu naqasu Sosai daga Malaman wannan zamanin Musamman wadanda keda Wannan aqidar ta Tsubbace_tsubbace da Duba. Tayadda sukayita yimasa Tuggu da zagon kasa gurin Sun ga sun dakushe wannan aikin Nasa, Tare da Wargaza aikin Nasa tahanyar kirkiran karya akansa hadda cutar dashi domin Su samu Galaba akansa, Amma ahakan Allah ya Tserataddashi daga dukkan tarakunan nasu Allah ya kuma karfafa Wannan Da’awa tasa har ilayau Qugiyar izala tana nan kuma tana cigaba da aikinta wajen karantar da Al’uma bisa koyarwar magabata dakuma Tabbatar da Qur’ani da Hadisi sune tafarkin Tsira ga Bayi.
    Ahakan aka cigaba da kasancewa har takai yaje izuwa ga Malamin sa na Tauhidi Assheikh Abubakar Mahmud Gumi, Domin neman izini da Karin lamani dangane da Da’awar tasa. Awannan lokacine Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya nuna Bashi Cikakkiyar goyon baya gamida Cikatamasa Sunan Gungoyarsa da ” Wa’iqamatissunnah ”  ma’ana ( Dakuma Tsayar da Sunnah ) Wcce tazamo ” Jama’atu izalatul Bid’ah Wa’iqatissunnah ”
    Ma’an ( Qungiyar dake kawar da Bidi’a kuma take Tsayar da Sunnah )
    Domin acewarsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi; Babu Yadda za’ayi akawar da bidi’a abarta haka ba acike Gurbinta da wani abu ba, Shine Yace to sai Acike Gurbinta Da Sunnah.
    Kunga Ashe kenan ita Izala ba Fitina bace Sabanin Yadda wasu daga cikin maluman ma da basu fahimta ba, Kuma bawai Reshen addini bace kamar yadda wasu suke yimata Mummunar fahimta Har ma wasu ke ganin Cewa in baka ciki to baka cika musulmiba, wasu kuma ke Mata ganin Cewa inkan cikinta Musuluncinka da Gyara Haqiqa Dukkan Mai yiwa Wata Aqidah ta Musulunci ganin Wannan Al’amari, Alal hakika ya Jahilci Hakikanin Musulunci,
    Wannan kadan kenan daga Tarihin Sheikh Isma’ila Idris da Gwagwarmayarsa gurin kafa Izala, insha Allah Anan gaba Zan kawo muku Cigaban da iza ta Kawo Wa Musulunci da Kasarmu baki daya. In Allah mai Komai ya kaimu bayan Sallah.
    Nine naku Isma’il Hussaini Adam Alpholtawy


    Kuma Wannan Shine karshen Rubutuna danganeda Shafukan Tarihin na Bana A Hijira sheka ta 1442 Saikuma Allah ya Kaimu Almuharram Shekara ta 1443 Zan cigaba da Wannan Tarihi.
    Mai karatu ga Addu’a ta Katayani da Ameen.
    Ya ALLAH Kajiqan Mahaifina Hussaini Adam Jumba wanda Ya Rasu a irin Wannan wata Mai Alfarma kuma Aranar Idin Adhhaa, Idin Babban Sallah Allah Kajikansa Ka gafarta masa ka kai Harke Qabarinsa, Kabashi Aljannah Madaukakiya.
    Ya ALLAH Mu Zuri’arsa Da muka Rage a bayan Kasa Allah ka azurtamu da Dogora abisa Addininka, Kabamu Shahada irin tasa, kasanyamu Cikin Wadanda kake Yantawa Zuwa Aljannah.
    Ya ALLAH Ka Sitirtamu da Sutura ta Musulunci, Ka azurtamu da Arzikin imani, da Ikhlasi da Tabbatuwa akan imani, Har Mu Mutu muna masu imani Da Miqa wuya gareka Allah.
    Ya ALLAH ka daukaka musulunci da musulmai, ka Qaskantar da Kafirci da Kafirai kadirkake makiyanka makiyan addini Allah kataimaki bayinka Nagari.

Mawallafi Ismail Hussaini Adam Alpholtawy

MATSALAR TSARO A NAIJA New post 2

MATSALAR MANYANMUNE!!

Matsalar tsaro A’kasata Fitowa ta biyu (!!) ✍️Ismail Hussaini Adam

Matsalar tsaro akasar Nigeria abune mai matukar wuya amaganceta da hanzari, Domin Al’amuran Sun jima Da Cakud’ewa cikin mummunar qaddara da muka samu kanmu aciki musanman Mu Al’umar Arewa. Ansamu akasi tahanyar wasunmu suna goyon bayan ta’addanci aboye, bincki da akeyi ana kin bayyana gaskiya, Shine babban Al’amarin daya gur’bata Al’amuran tsaro A’kasarnan. Wai sai ace anrufa asiri akwai ‘yan Alfarma.

Shifa d’an ta’adda, ko mai goyon bayan ta’addanci, Koda uwarsace data haifeshine yasan zata fallasheshi, Wallahil aziim zai aikata lahira, komai Son da takemai, balle jami’an tsaro ko Masu fad’a aji na gari Wad’anda aganinsu sune Cikas d’insu aharkar dasuke ciki. Yazama wajibi akan hukumomi, Da Shuwagabannin Al’uma ta ayyadar da hukunci, akan dukkan wani mai laifi data kama, takuma yi bincike akan dukkan wanda take zargi da ta’addanci, ko goyon bayan ‘yan ta’adda. Idan Tayi bincike inya tabbata kuma tazartar da hukuncin daya dace.

Hakan shine hanya mafi sauki, Ta hanyar da za’a gyara matsalar tsaro acikin Al’uma.

WANI ABINDA MUKA MANTA

Wad’annan masu laifi da’ake kamawa da sunan ‘barayin gida da masu fasa shagunan, Idan ba’azartar masu da hukuncin daya daceba Sune ake Sayansu Su girmama, Abasu Makamai sucigaba da ta’addanci dakuma Kisan mutane, haka kurum ba gaira ba dalili.

Dole ne acire maganar Alfarma, Dukkan wanda hukunci ta haushi kawai azartar masa shine adalci. Allah yafi kowa son bayinsa Amma yana hukumtasu idan sun aikata ba daidaiba. Tayadda yakema ‘Kona wasuma domin mummunar aiki dasuka aikata. Kuma yayi umarni garemu akan mu zartar da hukunci da adalci akan dukkan wanda doka ta haushi.

Hakika Al’uma tana shiga firgici da mummunar yanayine tahanyar sakaci da’akayi da hukunta masu laifin cikinta. A Nigeria mun sami kanmu cikin wannan yanayi tahanyar Sakacin hukumominmu da shugabanninmu.

RASHIN AIKINYI GA MATASA MA QALUBALENE

Matasa babu aikinyi a kasarnan dalili kuwa Shine, manyanmu basu kishin kafa wadatattun masana’antu burinsu gina gidaje kawai da zuwa ‘kasashen waje. Taya ‘Kasan wajen suka sami Cigabane Bayan samun nagartattun Shugabanni masu kishi Suna kula da hakkin Talakawansu. Yakamata Asamarda wadatattun masana’antu tayadda za’arage masu zaman banza dakuma yan Fasa ‘kwauri akasarnan. A’kasarnan akwai arzi’ki wanda yagirmi lissafi amma kuma munfi kowa Talakawa, wannan yasamo asaline danganeda Rashin tallafin jari da aikinyi ga masu ‘karamin ‘karfi, Saudadama wasu na fara kasuwanci amma da zarar sunsami karayar arzi’ki shikenan yazama abin tausayi. Mai iyuwa ma wanin daganan yakan koma goyan bayan ta’addanci, domin yasamu dukiya koma yazamo member na ‘yan ta’adda.

ANA ZALUNTAR ‘DALIBAN KARATU

Harajin karatu awannan kasa nada wahalar Gaske, ga kuma ana matukar Cin dunduniyar ‘Dalibai tahanyar mugayen Lecturers. Kai harda keta alfarmar (Mutuncin) ‘yan mata. A iya Saninmu ga Manyanmu na yanzu Shine. Sunyi karatune akyauta kokuma cikin sauki, Amma donme suke musgunawa Mutane ayanzu? Mafiya yawan malaman yanzu burinsu shine su samu kudi Suma a’kirgasu acikin masu Arzi’kin ‘Kasa. Bawai su bada karatu ga d’alibai ba kamar yadda yake a hukunce. Wannan yasa suke neman Kudi ido rufe a governati domin cimma burikansu dakuma kirkiro wasu tsaruka mabambamta. wadanda suke da rauni da Da’kushe har’ko’kin ilimi akasarnan.

Strike da ake samu a jami’o’i da Colleges yasamo Asaline daga, Son duniyar wasu daga cikin Malamai. Dolene Govrenati tasan hanyar da zata shawo kan Wannan Al’amari. Mutane na kashe kud’ad’e masu yawa kuma Suna d’aukan dogon Zango kafin su kammala karatunsu. Duk asadin matsalar Yajin aiki (Strike). Kuma akarshe yazamo Sun gama karatu kuma sun rasa aikinyi, Tambaya anan itace, idan mutum mai raunin imani yasha wannan wahalar kuma yarasa aikinyi, Me kuke tunani Zai biyo baya?

MATSALAR ASAMACE

Manyanmu na sama Sune ke morar arzikin ‘kasarnan. Manyan Nigeria mutum daya na d’aukan ma’kudan kud’i a governatin tarayya fiyeda Lissafin mai tunani Amma Nakasansu kuwa suna shan wuya matu’ka, Amma abinda suke samu ko na man mota baya wucewa, ballema aje ga Masarufi, dakuma Suturar jikki da kayan ‘Kawar ado. Don me corruption bazai Existing atsakanin muba Alhali wasunmu naci da gumin wasu. Su kuma manta da Hakkin dake tsakaninsu na zamantakewa. A’ka’idar Zamantakewa ta mususukunci dolene kasan Ci da Shan ma’kocinka Kamar yadda zakasan na Iyalinka.

Amma ayanzu babu ruwan wani da Wani, Anyi watsi da karantarwar addini anbi yahudu kuma gashi an’bace ba akamo yahuduba kuma Ambar Allah. Wadannan ma Suna daga cikin Hanyoyi mafiya girma na sanadin Lalacewar Tsaro a Nigeria. Zanci gaba Insha Allah. Allah ya tabbatar damu akan gaskiya da shiriya.

SURATUL FATIHAT

1 – Al-Faatiha – الفاتحة 00:00 1:1 – Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.1:2 – Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;1:3 – Mai rahama, Mai jin ƙai;1:4 – Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.1:5 – Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.1:6 – Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.1:7 – Hanyar waɗanda Ka yi wa ni’ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.

MUSAN HUKUNCE_HUKJNCEN ADDININ MU

NEMAN AURE AMUSULUNCI

Dasunan Allah mai rahama maijinkai Haqiqa ANeman Aure yanada matukar amfani musan dokoki da ka idoji da hakkokin ta. AMUSULUNCI Dan kankanin Bincikena da kuma baiwar Da Allah yayi mani zanyi rubutu bisa abinda nake karantawa dakuma wadanda nake gani.

A Zamantakewarmu tayau da kullum. Neman aure. Muhimmin abune GA mutane musani kuma mukiyayesu. Zangina zantukana ne akan wannan muhimmin hadisi, ruwayar Bukhari da Muslim. Manzon Allah (s.a.w) yace “Ana Auren mace don abubuwa guda biyar 1:-kyawunta 2:-nasabar danginta 3:-addininta 4:-dukiyarta 5:-kyawu halinta Sai kuma yace kazabi ma abociyar addini zata zamomana. Yalwar hanu Abin ake cewa yalwar hanu shine zata zamo bata cutaddakai kuma bazata bari acucekaba. Dan uwa mai karatu kaga neman. Mace mai addinima nada matukar fa’ida, Idan kana Neman mace mai addini Zaka San halayenta kamar haka Haku, Kunya, Kaskantaddakai, tsoron Allah, Amana, Juriya, Kirki, mutunci da karamci. Wannan shine halayen mace mai addini, atakaice. Qa’idojin Neman Aure AMUSULUNCI :- Yazamto wacce zaka Neman tana da kamun kai. :- Yazamto tana kana sonta tana sonka son da babu tilastawa. :- Yazamto wacce kakeso tanada hankali da nutsuwa. :- Yazamto mai. Kyawun hali mai addini da tarbiyya. :- Ta zama wacce takeda nutsuwa da kamala da kyau. Ahaqiqanin gaskiya Wannan sune matakan Allah ubangiji ya daukaka musulunci da musulmi. da alkalamin Ismail Hussaini adam IHSAN Assalafy Alpholtawy Matakan Bayar da Tarbiyya Akwai matakai ko hanyoyi da ake bi wajen bayar da tarbiyya da suka haɗa da nuni, lura, umarni da kuma hani. Nuni: Abin da ake nufi da nuni a nan shi ne aikata aiki a aikace, wanda daga nan shi wanda ake tarbiyantarwa zai gani ya koya. Tirƙashi, masu iya magana sun ce; “Idan mutum ya ce zai baka riga, to duba ta jikinsa”. Wannan magana ta zo daidai da faɗin Larabawa cewa; “Maras abu baya bayar da shi”. Saboda haka dole ne mai bayar da tarbiyya ya zama mai tarbiyya. Wannan hanya ta bayar da tarbiyya ita ce mafi tasiri da kuma muhimmanci wajen bayar da tarbiyya. Saboda haka dole ne masu bayar da tarbiyya; iyaye, malaman makaranta da sauran jama’a suma su zama masu tarbiyya. Misali, dole iyaye su zama masu tsafta a aikace, kafin su dasa halin tsafta a zukatan ‘ya’yansu. Idan yaro ya tashi ya ga iyayensa suna share gida tsaf-tsaf, basa barin kwanon abinci da dauɗa, basa jefar da sutura ko’ina a ciki da wajen ɗaki, to a haka shi ma zai girma mai kula da tsafta. Kuma zai tashi shi tsafta ya sani bai san ƙazanta ba. Saboda haka da zarar ya fara zuwa makaranta malaman makaranta ba za su wahala da shi ba. Umarni da Hani (Kwaɓa): Umarni shi ne a riƙa gaya wa yaro yi kaza. Misali, idan yaro ya tsoma hannun hagu cikin kwanon abinci, ko ya riƙe abinci da hannun hagu zai kai bakinsa, sai a gaya masa cewa, wannan ba shi ne hannun cin abinci ba, ga na cin abinci nan. Da haka zai gane hannun dama dana hagu. Shi kuwa hani shi ne kore abu. A wannan gaɓar kuma yana nufin kare ko dakatar da yaro daga aikata aikin da ba mai kyau ba. A cikin wannan misalin dana kawo a sama, akwai gaurayen hani da kuma umarni. Yaro ya tsoma hannun hagu domin cin abinci, sai aka hana shi; wato aka dakatar da shi daga cigaba da amfani da hannun hagu. Sannan aka gaya masa; wato aka umarce shi da amfani da hannun dama. Lura/Kula: Lura ko kula, suna ɗaukar ma’anar saka ido a kan kai-komo na yaro; wato zirga-zirgar yara. Wannan hanya ta lura, cikamakonta shi ne kwaɓa. A nan, iyaye za su saka ido sosai game da zirga-zirgar ‘ya’yansu, duk lokacin da suka ga wata baƙuwar halayya maras kyau, sai su yi maza-maza su ɗauki matakin da ya dace tun kafin ta zama jiki. Da zarar yaro ya fara fita wajen gida domin zuwa makaranta; wato daga shekaru uku zuwa sama, to fa dole iyaye su riƙa lura da shi sosai, saboda yanzu kuma ya je ya gwamutsa da sauran yara daga gidaje barkatai. Saboda haka idan iyaye basu saka lura ba, to tarbiyyar ‘ya’yansu sai ta koma barkata TARBIYYA _Tarbiyya aba ce mai wahala, sai an dage an tashi tsayin daka sannan za’a dasa ta, ya ku Iyaye abu na farko daya kamata ku cusa a zuƙatan yaran ku, ko zuciyar yarinyar ku, ko kuma zuciyar ɗan ku Shine *TSORON ALLAH* domin samun nagartacciyar rayuwa a tare dasu da kuma tarbiyya mai kyau._ _Daga lokacin da yaro ya fara wayo, ya fara magana, yasan abincin da zai sanya a bakin sa, ko kuma abin sha to daga wannan lokacin ya kamata ku fara cusa masa jin tsoron Allah a zuciyar sa sannan su San Wane ne Manzon Allah S.W.A, Menene Matsayin sa a Wajen Al’ummar Duniya baki ɗaya da Wajen Allah.._ _ku cusawa yaran ku jin tsoron Allah ta hanyar sanar dasu ubangiji, abinda yayi umarnin a aikata da kuma abinda yayi hani a kai.kamin ku jefa yaran ku a makarantar boko ku fara tura su ta islamiya, malamai magada Annabawa nayin nasu kuma kuna yin naku to insha’Allahu tarbiyar yaran ku zata zamo mai sauƙi a wurin ku a lokacin da suka balaga suka gama mallakar hankalin kan su._ _Sa’annan ku cusawa yaran ku son ilimi na addini dana zamani Kasancewar ilimi Shine Ginshiƙin Rayuwa, hakkin kune iyaye ku bawa ƴaƴan ku ilimi wanda zai amfanar da su duniya da lahira, ba ƴaƴan ku kawai ba hatta ku iyaye yana da kyau ku samarwa kan ku ilimi. Shi ilimi haske ne mai haskaka rayuwar ɗan adam ta kowanne fanni ba kawai don neman aikin abin duniya ba..wanda mafi akasarin iyaye yanzu sun fi gina ilimin ƴaƴan su akan neman aikin abin duniya duk da cewar hakan ba laifi bane amma ya kamata mu nazartu muyi duba sose akan hakan, muyi faɗi tashi mu jajirce mu cije don ganin mun inganta rayuwar ƴaƴa da ilimi na addini domin da shine za’a tafi lahira saɓanin na duniya da inda muka same shi anan zamu bar shi._ _Sose muke tafka kuskure a rayuwar yanzu, an cusawa yara musamman mata son abin duniya, ku farka iyaye musamman iyaye mata, kin cusawa ɗiyar ki son abin duniya, kin cika rayuwar ƴar ki da burin abin duniya, kin ƙawata idanuwan ta da hangen abin cikin duniya an manta da mutuwa na tafe a kowanne lokaci. fatan ki, burin ki, mafarkin ki, jin daɗin ki, kwanciyar hankalin ki, tayi-tayi ta gama Secondary School ta Shiga Jami’a tayi degree tayi Masters Domin ta tara Muku Dukiya kuyi kuɗi duniya tasan da ɗiyar ku ko ɗan ku, ku huce takaicin duniya, hakan yana da kyau kuma ba laifi bane sai dai ta gefe guda a kwai illa, akwai matsala._ _Duk saboda wannan burin kun hana ƴar’ku aure, baku sashi a cikin lissafin da zai inganta rayuwar ƴar’ku, terming ɗin ku da terget naku shine kawai wancan duk saboda kada burdget naki ke uwa ya rushe (ga wasu iyayen). Shin idan anyi auren nan ba’a karatunne?, shin idan anyi auren nan ba’a aikinne?, shin idan tayi auren nan zai hanata dukkan muradin ki da kike son ya cika?. Kin Hanata yin Aure, ƴaƴayen mu ba duwatsu ba, b marasa lafiya, sha’awa na Damin ta, Samari kullum kawo mata hari suke, koda yaushe tana tare da su a makaran ta ko a waje, yau da gobe sai Allah ba fata ake ba, Allah ya tsare mu ya tsare mana ƴaƴayen mu._ _Mu riƙa kai zuciya nesa a kan yaran mu, duka da hantara da zagi da mummunar kalma basu zasu gyara yaro ba face ƙara lalata shi, ku dinga yawan yi masu adu’a a koda yaushe, kar ku faɗi kalma mara daɗi a kansu a lokacin da suka ɓata maku rai, don Allah iyaye mu iya bakin mu akan yaran mu, kar mu manta matsayin bakin mu akan su, fata na gari da adu’a ta gari a kansu shine dai-dai.._ _ku koyar da yaran ku da sabar masu yin sallah akan lokaci, ku koyar dasu adu’oin neman tsari da kariya kamar yanda ma’aiki ya koyar damu, ku zama masu lura da irin fina-finan da suke kallo domin kuwa shima kallo na ɓata tarbiyar yaro ya rusa duk ginin da kayi a baya, ku sabar masu da sauraran wa’azi kamar yanda ya kamata bakin ku ya saba wajen yi masu wa’azi._ _Haka Zalika ku kasance abin koyi ga yaren ku, kuyi ƙoƙarin aikata abu mai kyau tayanda zasu gani su ɗauka daga gare ku.. Ku zama masu zama da yaran ku kuna shiga cikin su domin jin matsalolin su, sannan ku zama masu sanya ido a duk abubuwan da yaran ku ke gudanarwa na yau da kullum tun kama daga kan ƙawaye, lura da irin abokan da yaro ke mu’amala dasu yana da kyau matuƙa da gaske, kuma hanya ce ta kiyaye yaron ki daga faɗawa ga miyagun abokai, idan har kun sanya ma yaro ido akan abokan tarayyar sa lalle tabbas zai ji tsoron zama da ɓata gari, zai yi duk yanda zai yi yaga yayi ƙoƙarin nisan ta da banzan abokai, fatan mu Allah ya kare mana zuri’a ya kuma shiryar dasu._ _mu guji kuma mu kiyaye bama ƙananun yaran mu da suka tasa wayar hannu, wannan waya da muke ganin ta haƙiƙanin gaskiya ba ƙaramar musiba bace, haɗari ce babba ga rayuwar ƴaƴa wallahi, don haka mu kiyaye basu waya musamman ta android a lokacin da suke da ƙarancin shekaru…. Ku zama masu sanya ido a kan shige da ficen ƴaƴan ku musamman ke uwa da kike zaune cikin gida koda yaushe, ba kowanne wuri ya kamata ku bar yaran ku suke zuwa ba, kuma ba’a koda yaushe ya kamata kuke barin su fita ba, duk da cewar rayuwar yanzu ta sauya yaran mu sunfi mu wayo da dabara… Idan dama ma da hali duk sanda ƴarki mace ta buƙaci zuwa wani wuri kiyi mata jagora, sannan ki hani yaran ki tarayya da ƙawaye barkatai._ _yake uwa ki zama mai sa’ido sosai da sosai akan ɗiyar ki mace wajen duban irin littafan hausa dana turan ci da take karantawa, ki tsoratar da ƴar’ki kiyi mata barazana da karanta littafin daya kauce hanyar kunya da tarbiyya, haka zalika idan ƴarki ta taso da sha’awar rubuta littafi shima ki tsoratar da ita ki mata baraza na ta yanda zata ji tsoro ta kuma kiyaye rubuta abinda ba shi da kyau, ki tunatar da ita cewa lalle ubangiji zai tsaida ita akan abinda ta rubuta, ki zama mai bincikar wayar ta akai-akai, ki zama ƴar jarida ga yaran ki, kisa musu ido akan duk abinda zasu samu, bi ma’ana dukkan abinda kika gani a hannun su ki sasu gaba ki titsiye su don jin daga ina suka samo shi?, taya suka same shi?, koda yaro zai ce maki ga wurin daya samu kuyi ƙoƙarin bin diddigin inda ya same su ɗin… Karku sabarwa yaron ku da riƙe kuɗi domin kuɗi na ɗaya daga cikin abinda ke rusa tarbiyar yaro._ _yake uwa ta gari, ki sanya ido akan fitar ƴarki daga gida wajen sanya sutura, ki tuna musulunci ki tuna faɗin Allah maɗaukakin sarki a cikin littafin sa mai tsarki mai girma, ki tilastata ki sabar mata da suturce jikin ta a yayin da zata fita… Idan mai sanya hijab ce ki sanya ido wurin ganin kayan data sanya aciki da kuma abinda ke ƙunshe cikin jakar hannun ta, domin wasu ƴaƴan namu kan yaudare mu da fuska biyu.. Ki hani yarinyar ki da amsar kuɗin hannun samari, ki kuma hani yaran ki da saurin miƙa hannu, ki hani yaran ki da kwaɗayi da son abin duniya._ _ya ku iyaye na gari, daga lokacin da kuka fahimci ƴaƴan ku na buƙatar aure, lalle kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, hakan shi zai hana yaɗuwar ɓarnar dake faruwa a doron ƙasar mu, ba komi ke jefe ƴaƴan mu cikin baƙincikin rayuwa ba sai wajen tauye masu hakki da muke, musamman ƴaƴa mata, don Allah iyaye da zarar kun fuskanci ƴaƴan ku na son aure kuyi masu domin shine mafita kuma shine kariyar su daga faɗawa mummunar halaka, kuma shine yayewar damuwar da za’a shiga a gaba._ _Daga ƙarshe karmu manta zamu cimma kyakykyawan burin mu ne akan tarbiyantar da yaran mu wajen yawan tunsar dasu faɗin Allah da Ma’aikin Allah._ _Ya Allah kasa mu dace, Allah kuma ya bamu ikon sauke hakkin ƴaƴan mu da Allah ya ɗora mana domin Ƴaƴa Amana ce Allah ya bamu._ Daga *® MATSALAR FYADE GA “YA” YA MATA…. KALUBANE GA IYAYE…… idan kacire yara kanana wayanda basusan fari da baqi ba wallahi sauran yan matan wasu lefinsu ne Dana iyayensu saboda gurbatar tarbiyya. Akwai Hadith na manzon Allah (saw) annabi yake cewa …. Sayaqulu fi akirizzamani nisa’un kasiyatun ariyatun. Sai annabi yace il anu hunna fa inna hunna mal ulatu, subhanallah sai yasake cewa wallahi lajidanna rihal janna, alhalin wa inna rihaha la yujadu min masiratun kaza wa kaza. To gaba daya inka duba babban matsalar wannan zamanin yanzu shine wayewa tayi yawa haka kawai yarinya takai mace iya mace Amma saita bata wasanta. a farkon fari duk bikin daza ayi saitayi anko karasa a gidan ubanwa take samo kudin Kuma dinki me daukar hankali, kaga yarinya kullum bakinta abude washa da haqora farare tass tana sheqa dariya me daukar hankali, tana tafiya tana bada style kala kala, ko makaranta zataje saita qwalqwale jiki tayi wankan siga ana tafiya tsaraici yana fita kuma wallahi iyayen suna kallo su aganinsu lokacin wance fah yayi abarta kawai taci duniyar ta ai ansan dai tunda tanada kyau Dole a aureta. To wallahi muddin diyarka ko diyarki tana irin wannan tsiyar karma gayu su afka mata kayi kumfar baki tayi suka mayar tunda dayawanku aurenma in anzo sai kuce tafara level 100 saita kammala tukunna kokuma kuce mutum yaje saiya yi gini ku bakwason haya, kokuma kuce adaidaita yake ja bazai iyaba, ko ace waye babanka daga kace malam halliru me kwado da linzami za a durama ashar akoreka. kai wallahi wa tama kidan jogo zatabi takai kanta ayi mata shi Amma daga baya sai iyayen su juya kaset din suce ai fyade ne. Dabara taragewa iyaye kuyiwa yayanku tarbiya kuyimusu aure da wuri in ansamu fitacce kunga dai auren annabi (saw) da nana Aisha Kuma ahanasu kwadayi Adena Dora musu tallah. Allah yakaremu da zuriyarmu daga dukkan sharri amin amin.