Nasarorin Da Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Samu Cikin Shekaru Biyu, July 2020, Zuwa July 2022 Ga wasu daga cikin nasarorin shekarar farko July 2020… Read more: Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers
SHAUQI CIKIN AL AMARIN GAIBIYYA Kasantuwar Ubangiji A Buya Bai zama tawaya Ga Imanin Mai imani Sai dai Yana kara imanine ga Mai imani Yayin… Read more: ZATIN UBANGIJI
Ban Shan Sigari Ban Shan MoringaBan Shan 200 Kayan zamani Ban Leqa tagaKayan Wani bai idona Ni nai ga KatangaShiga Sha`anin Wani banayi Cikin GaringaBana… Read more: GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI
Bansan me Nayi mussu baNufata da Sharri suke basu barniba Nayi kukan ZuciyaHar na Ido Hawayena Basu fad’i ba Ganinan na SarqafeIgiyar suce Suka ya’ban… Read more: KUJI TAUSAYIN MARAYAN ALLAH
TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI,
(manzon Allah S. A. W) “yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al’umma ta”
Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu ” usman” usman dan Amir dan Amir dan ka”abu dan sa”adu da taimu dan murratu dan ka”abu dan lu”aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka”abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya “Abdul ka” aba” daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi “Abdullahi” An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi”antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da “Atiku” shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Muhammad (S. A. W) shine yafara haduba a addinin musulunci. Shine abokin zaman kogo tare da manzon Allah na farko kuma shine nafarko cikin sahabbai goma da aka musu albishir da gidan Aljannah tun a duniya shine farkon Amirul hajji kuma yana cikin marubuta wahayin da akema Annabi Muhammad (S. A. W) An haifi Sayyidina abubakar (R. A) a makka bayan Shekara giwaye da shekaru uku (573 A. D) manzon Allah. Ya girma shi da shekaru uku. Yana cikin manyan shuwagabannin kuraishawa a lokacin jahiliya kuma a bakin manzon allah ne na kasa tun kafin aiko shi. Sau dayawa ma. Yakanje gidan shi su tattauna shine mafi sani duk larabawa game da tarihin nasabar kuraishawa. Kuma yakira mutane da yawa zuwa ga addinin musulunci. Biyar daga cikin su suna cikin sahabbai goma. Da aka yiwa bishara da Aljannah sune kamar haka : Ya sha a zaba iri – iri daga kafiran makka saboda shigar shi musulunci Har takai babu wani musulmai da azabtu kamar shi. Duk da irin matsananciyar azabar da suka sha suda sauran musulman farko daga kafiran makka. Bai yi kauraba zuwa kasar habasha ba. Ya tare ga manzon allah (S. A. W) lokacin kaura zuwa madina yana tare da Annabi Muhammad (S. A. W), tare suka shiga kogo kafin suwuce zuwa madina shine cukon mutane biyu da Allah ya ambata a alkur”ani in da yace : ” Idan baku taimakeshiba. ( Annabi), to ai Allah ya taimake shi yayin da kafurai suka fitar da shi ( daga makka) na biyu (mutane) biyu yayi dasuka shiga cikin kogo yake cewa da abokin shi (Abubakar)” kada kaji tsoro, Mu Hakika Allah ya na tare damu “( da taimako shi)” cikin suratul tauba:40, yayin da suka isa madina. Sayyida Abubakar, A wurin kharijatu dan zaidu. Da shi kuma manzon allah yahada su ‘yan uwantaka yayi da ya rinka hada yan’ uwantaka (ta musulunci) tsakanin mutane makka ( muhajiruna), da na madina (Ansaru) Sayyida Abubakar shine tamkar Waziri ga Annabi Muhammad (S. A. W), wajan gudanar da al’amuran daular musulunci. Mai babbar hedikwata a madina: birnin manzo,,,
Abubakar saddik ( R. A) ya dukkan yake _ yaken daukaka musulunci da yada shi da Annabi Muhammad (S. A. W) a yakin badar shine kan gaba wajan kula da wurin da manzon allah yake. Yana shir yanda yake zai gudana tare da rokon allah. har dai allah ya amsa addu’ar Annabi, ya aiko da rundunar mala”iku. Musulmai suka samu nasara. A yakin uhudu kuwa, Sayyida Abubakar. Shine jagora tsirarun Manyan sahabbai, suka gabata a filin yakin. Tare da manzon allah (S. A. W) yayin da kafurai suka tarwatsa rundunar musulmai.
Ban Shan Sigari Ban Shan MoringaBan Shan 200 Kayan zamani Ban Leqa tagaKayan Wani bai idona Ni nai ga KatangaShiga Sha`anin… Read more: GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI
Menene capacitor? Dauki masu gudanar da wutarlantarki guda biyu (abubuwan da suka bari Wutarlantarki ta ratsa su) sai ka raba su da insulator(kayan da ba su barin wuta ya ratsa sosai) sai kayi capacitor: wani abu da zai iya adanamakamashin wutar lantarki. Kara makamashinlantarki ga mai iya aiki shi ake kira caji ; fitar dakarfin daga mai iya aiki shi aka sani dadischarging. Capacitor yana dan kama da baturiya, amma yanada wani aiki daban. Baturiya na amfani dasinadarai don adana makamashin lantarki da sake shi a hankalita hanyar zagaye; wani lokaci (a yanayin agogonkwata) zai iya daukar shekaru da dama. Mai iyaaiki yana sakin karfinsa da sauri-sau da yawa acikin sakanni ko kasa da haka. Idan kana daukanhoton flash, misali, kana bukatar kyamararka don samar da babban burst na haskea cikin fraction na sakan daya. Wani mai iko daaka hađe da bindigogin flash na ‘yan sakanni taamfani da makamashi daga batirin kyamararka.(Yana daukar lokaci kafin caji capacitor shi yasayawanoci dole ka jira kadan.) Da zarar an caji maikarfin, zai iya sakin duk karfin nan take ta hanyarxenon flash bulb. Zap! What is a capacitor?Take two electrical conductors (things that letelectricity flow through them) and separate… Read more: FASAHAR ZAMANI
Kanun bayannai
Nasabar Sa
Iyayen Sa
Haihuwar Sa
Aiko Shi
Hijirar Sa zuwa Madina
Yaƙoƙinsa
Matan Sa
Yayayen Sa
Masu yi masa hidima na musamman
Muhammad Annabi ne kuma Manzo ne wato ma’aikin Allah Madaukakin Sarki. Allah Ya aiko shi domin ya tabbatar da addinin da Annabawan da suka gabace shi suka koyar, Kamar Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Annabi Isah da dukkannin sauran Annabawan Allah (tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gare su) Annabi Muhammad (s.a.w) shine cikamakon Annabawa, wato Annabin karshe wanda daga kansa babu wani annabin Allah. Dukkan wanda yayi ikirarin annabta bayan zuwan Annabi Muhammad (s.a.w) to karya yake. Shine kuma ya hada kan dukkan larabawa suka dunkule waje daya, tare da daidaita yan adam ta hanyar koyarwar sa da Alkue’anin da yazo da shi.
Nasabar Sa
Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗɗalibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam. Manzon Allah ne. Khataman-Nabiyyin da addinin Musulunci.
Iyayen Sa
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) ‘yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abu-Qasim, Abu Ibrahim.
Laƙabinsa:
Al-Musɗafa (zababben Allah) yana da sunaye da suka zo a cikin Ƙur’ani Mai Girma kamar, Khataman-Nabiyyin, da Al-Ummi da Al-Muzzammil da Al-Muddassir da An-Nazir da Al-Mubin da Al-Karim da An-Nur da An-Niˁima da Ar-Rahma da Al-ˁAbdu da Ar-Ra’uf da Ar-Rahim da Ash-Shahid da Al-Mubasshir da An-Nazir da Ad-Da’i da sauransu.
Haihuwar Sa
An haifi Annabi Muhammad (s.a.w) a wajen shekara ta 570Miladiyya. Mahaifinsa shine Abdullahi ya rasu kafin haihuwar Sa. Mahaifiyar sa Amina itama ta rasu lokacin da yake dan shekara shida a [[duniya]. Haka yasa kakan sa Abdul-Mudallib ya rike shi har zuwa lokacin daya rasu, lokacin Annabi Muhammad (s.a.w) yana dan shekara takwas a duniya. Daga nan sai kawun sa Abu-Talib yaci gaba da rikon sa. Abu-Talib ya taimaka ma Manzon Allah (s.a.w) sosai a rayuwar sa.
Aiko Shi
Kogon Hira, wajen da aka fara wa Annabi WahayiAikoshi: An aiko shi a Makkah 27 Rajab yana ɗan shekara arba’in. Koyarwarsa Ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan-uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.
Mu’ujizozinsa
Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Ƙur’ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa. Kiransa Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makkah a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.
Hijirar Sa zuwa Madina
Bayan Tsanani da takurawar Kafuran Makkah akan Annabi Muhammad (s.a.w) da wadanda sukayi inami da shi yayi yawa, sai Allah Yayi ma Manzon Sa da sauran Wadan da sukayi imani da shi izinin akan suyi kaura daga garinsu na haihuwa wato birnin Makka zuwa wani garin daban na wati Madina. Mutanen birnin Madina kuwa sunyi matukar murna da zuwan sa garin su kuma sun bashi kyakkyawan masauki. Sanna kuma sukayi imani dashi suka shiga AddiMusulunci. A farkon Hijira dai Shi Annabi da kansa dakuma babban aminin sa kuma na farko wajen imani dashi wato Sayyadina Abubakar Sukayi tasu hijirar tare. Sannan sauran musulmai sukayi ta bin bayansu daya bayan daya. Kaurar Annabi (s.a.w) daga Makka zuwa Madina shine ake kira Hijira kuma shine farkon kalandar Musulunci.
Yaƙoƙinsa
Inaso Mai Karatu Yayi haquri, Wannan Babi Zamu daukeshi amatsayin Darasinmu na Gaba
إن شاء الله
Matan Sa
Annabin Musulunci Muhammad Ya auri mata goma sha daya, ga Jerin sunayen su.
Khadijah(Kubura ‘yar kuwailadu)
Saudat
A’ishah(‘yar Abubakar )
Hafsah(‘yar Umar)
Zainab(‘yar Kuzaimata)
hindatu(ummu salama)
Zainab(‘yar jahshin)
juwairiyya
ramlat
safiyya
maimunah
Yayayen Sa
Ammominsa: Tara ne, su ‘ya’yan ˁAbdul-Muɗɗalib ne: Al-Haris da Zubair da Abu Ɗalib da Hamza da Al-Ghaidaq da Dirar Al-Muqawwam da Abu Lahab da ˁAbbass. Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Aminah da Ummu Hakima da Barra da Atiqa da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirul-Mu’minina Ali ɗan Abi Ɗalib (a.s) da Hasan ɗan ˁAli da Hussain ɗan ˁAli da ˁAliyyu ɗan Husaini da Muhammad ɗan ˁAli da Jaˁfar ɗan Muhammad da Musa ɗan Jaˁfar da ˁAli ɗan Musa da Muhammad ɗan ˁAli da ˁAli ɗan Muhammad da Alhassan ɗan ˁAli da Muhammad ɗan Hassan Mahadi (a.s).
Masu yi masa hidima na musamman
Mai tsaron ƙofarsa: Anas ɗan Malik. Mawaƙinsa: Hassan ɗan Sabit, da ˁAbdullahi ɗan Rawahata, da Ka’abu ɗan Malik. Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da ˁAbdullahi ɗan Ummu Maktum da Saˁad Al-Kirdi. Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah! Tsawon rayuwarsa: shekaru 63. Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23. Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.
Wajan da ya yi wafati: Madinah.
Inda aka binne shi: Madinah a Masallaci Maɗaukaki Mai Alfarma. Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne ƙarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari’arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kaɗai ce shari’ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa ƙarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaɗai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ɗaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W): Shi ne Muhammad ɗan ˁAbdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu ‘yar Wahab. An haife shi a Makkah ranar juma’a goma sha bakwai ga watan Rabi’ul awwal bayan ɓollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).
An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana ɗan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makkah ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaƙi . Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makkah a lokcin akwai jama’a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saƙon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: “Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta” . A lokacin tunda mutanen Makkah mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riƙa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa’adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: “Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni” . Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane ƙalilan, na farkonsu Imam ˁAli sannan sai matarsa Khadijah (A.S) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S). Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madinah wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya daɗu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari’arsa Mai Sauƙi Mai Hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madinah har suka fi dukkan duniya da addini na sama da waɗanda ba na sama ba. Kuma an samu yaƙoƙi masu yawa a Madinah kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga maƙiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zaɓar ɓangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waɗanda ake kashewa daga ɓangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaƙoƙinsa tamanin da wani abu, wato; waɗanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu ba. Mutuwa Mai Zafin Gaske Tun lokacin da aka aiko Annabi da saƙo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Ƙur’ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a haɗa shi kamar yadda yake a yau ɗin nan. Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu’amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.
Idan Mutum Ya Hadawa Matarsa (SABAYA) Yana Da Matuqar Ta’asiri a Jikin Ya”Mace Kuma Yana Haifar Mata Da Ababe Uku a Jikinta Akwai Matar Da Idan Tana Shayarwa Zakaga Kamar Ta Fito Daga Gidan Yari Wata Jikinta Yana Zubewa Ruwan Nononta Yana Lalacewa
*Nafarko Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Zai Taimaka Wajen Dawo da Halittan Da Allah Yai Mata Jikinta Nonon Bazai Zube Ba *Na Biyu Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Jikinta Zaiyi Laushi Kamar Kwalabiya *Na Uku Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Da zarar ta Haihu Irin Ramar Da Mata Keyi Baza Tayi Ba
Kuma Ruwan Nononta Zai Qara Yawa Sannan Bazai Lalace Ba Kuma Yaron Data Haifa Allah Zai Kareshi Daga Dangin Cututtuka
Kuma Hatta Magidanci Idan Yasha Yana Qara Masa Lafiya Da Kuma Kuzari a Jikinsa
MEYA KAMATA ASAMO WAJEN HADA SABAYA TASU KAMAR HAKA: *Al Kama 1Mudu *Danyen Shinkafa 1Mudu *Waken Suya 1Mudu *Ridi ½Mudu *Hulba ½Mudu *Gyada Mai Bargo/Kamfala *Madara *Zuma
YA ZA’A HADASU SHINE: Ridi Da Gyada Ana Hadasu Wuri Guda Ridi a Soyashi Yadda Ake Kantu, Gyadar A Soyata Yadda Ake Quli Quli, Shinkafa Da Alkama Ana Jiqasu Tsawon 5hour Sai a Shanya Da Laima a Jikin Sai a Hadasu Wuri Guda
Da Ridin Da Gyadar Da Al Kama Da Hulba Da Shinkafar Sai a Niqa Matarka Tin Tana Da Ciki Ya Kamata Ka Fara Bata Har Zuwa Haihuwa Kaga Yadda Zatai Da Yaronta Kuma Nononta Dana Shayarwa Ko Bata Shayarwa Bazai Canza Ba Da Ikon Allah
TO YA AKE SHANSA Yadda Ake Dama Kunu Haka Ake Damashi Sai Dai Idan aka Zuba Ruwan Zafi Ana Iya Maidashi Kan Wuta, Sukace Karta Wuce Cokali Uku a Rana Musamman Cikin Babban Cokali Idan Kuma Harda Magidancin Sai a Sanya Cokali Shida
Su Kace Amma Idan Mace Bata Da Aure Kada Tasha Domin Yana Qara Sha’awa Kuma Yana Qara Yawan Nono Ma’ana Yafi Dacewa Da Matar Datake Shayarwa Domin Samun Ingancin Lafiyar Jikinta Don Kada Ya Zube
Kuyi Amfani Da Wannan Link Din Domin Samun Magunguna a Sauqaqe
IDAN KAJI TSORON ALLAH ZAI BAKA MAFITA. – Hausawa suka ce bin Allah maganin wayyo Allah, tabbas hakane, lallai idan mutum yabi Allah kuma yaji tsoron sa, ya bauta masa, ya kuma kaucewa saɓa masa, to haƙiƙa bazai koka ba, kuma lallai Allah zai sanya masa hanya madaidaiciya wacce zai bita ɗoɗar ba tareda ya karkace ba” – “A rayuwar ka idan ka kasance mai yawan jin tsoron Allah abisa dukkanin ilahirin lamuranka, to lallai Allah ɗin zai baka mafita daga dukkanin wani ƙunci, bala’i da masifu, kuma zai azurta ka ta hanyoyi mabanbanta waɗanda baka san su bama, amma sharaɗin ɗaya ne, shine sai kaji tsoron Allah kuma ka guji dukkanin nau’ukan saɓon Allah” – Allah ta’ala yace: Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (yaji tsoron Allah) Allah zai sanya masa mafita. () Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma’ishinsa. Lallai Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama’auni ga dukan kõme. aT-Talaaq 2-3 –
Ma’aikatar cikin gida (Ministry of Interio) karkashin jagorancin Minista Ra’uf Aregbesola ta fitar da sakamo na jahohin Nigeria matasa wadanda suka samu nasaran daukar su aiki domin cike gurbi a hukumomin tsaro na Civil Defence, Correctional, Fire Service da Immigration Amma a cikin wannan sakamon an cuci yankin jihohin Arewa, an danne musu hakkinsu, kashi 99 cikin 100 na wadanda aka daukesu aikin daga Inyamurai ne sai Yarbawa, tsakani da Allah me ya kawo Sunan Ikechukwu jihar Jigawa? Kuma a haka wakilan Arewa zasu zuba ido ba zasuyi magana ba? Wato an mayar da ‘yan Arewa saniyar ware, an mayar damu marassa amfani kawai, amfanin ‘yan Arewa sai lokacin zabe yayi azo neman kuri’ah ana watsa mana hatsi daga cikin mota kamar kaji muna caccaka Mu dai Arewa an barmu da yiwa juna hassada da kyashi da munafurci, mutanen kudu sun mayar da hankali wajen kokarin gina ‘yan uwan su, sun mamaye dukkan ma’aikatu dake babban birnin tarayya Abuja, har a cikin jihohin Arewa inda ya kamata a ga sunan Hausawa sai dai aga sunan Inyamuri, saboda sun fimu hadin kai da son juna ba tare da nuna banbanci ba Wannan babban kalubale ne wa Ministocin Nigeria ‘yan Arewa, ya kamata ku dauki darasi da abinda Ma’aikatar cikin gida tayi, ku dena nuna tsoro ko shakkar masu zagi da suka, tabbas kuma zaku iya yin abinda Minista Ra’uf Aregbesola yayi a ma’aikatunku idan an tashi diban aiki, shugaba Muhammadu Buhari yayi iya bakin kokarinsa da ya baku mukami, saura kuyi abinda ya dace Allah Ka taimaki Arewa da ‘yan Arewa Amin
You must be logged in to post a comment.