ARBA UNA ANNAWAWI

Hadisi Na 2

عن عمر رضي الله تعالى عنه أيضاً قال: بينما نحن جلوس عند رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم إذ طلع علينا رجل شديد بياض الثياب شديد سواد الشعر لا يرى عليه أثر السفر ولا يعرفه منا أحد، حتى جلس إلى النبي صلى الله عليه وسلم فأسند ركبتيه إلى ركبتيه ووضع كفيه على فخذيه وقال: يا محمد أخبرني عن الإسلام، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: الإسلام أن تشهد أن لا إله إلا الله وأن محمداً رسول الله، وتقيم الصلاة، وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان، وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلاً قال: صدقت، فعجبنا له يسأله ويصدقه.قال: فأخبرني عن الإيمان، قال أن تؤمن بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر، وتؤمن بالقدر خيره وشره، قال: صدقت، قال: فأخبرني عن الإحسان، قال أن تعبد الله كأنك تراه، فإن لم تكن تراه فإنه يراك،قال: فأخبرني عن الساعة، قال ما المسئول عنها بأعلم من السائل، قال: فأخبرني عن أماراتها، قال أن تلد الأمة ربتها، وأن ترى الحفاة العراة العالة رعاء الشاء يتطاولون في البنيان ثم انطلق فلبثت ملياً ثم قال يا عمر أتدري من السائل؟ قلت: الله ورسوله أعلم، قال فإنه جبريل أتاكم يعلمكم دينكم» .رواه مسلم.

An karbo daga sayyidina Umar kuma, Sayyidina Umar yace; wata rana muna zaune awajen manzon Allah s.a.w, sai wani mutum ya bullo muna yana da tsananin farin tufafi, yana da tsananin bakin gashi, ba’a ganin alamar tafiyar a tare dashi, kuma babu wanda ya sanshi a cikin mu (Sahabbai), har ya zauna wajen manzon s.a.w ya hada gwiwowinsa zuwa ga guwayyun Annabi , ya dora tafin hannayensa akan cinyarsa sannan sai yace; yakai Muhammad ka bani labari gameda addinin musulunci, sai manzon Allah s.a.w yace: “Abinda a addinin musulnci shine; ka shaida cewa babu wani abin da ya cancanta a bautawa in banda Allah, kuma ka shaida cewa Muhammad manzon Allah ne, ka tsaida Sallah, ka bada zakka, ka azumci watan ramadana, ka ziyarci dakin Allah, idan hanya ta sauwaka gareka”. Sai yace; ka fadi gaskiya sai mukayi mamakin wannan mutumen, shi yake tambayar manzon Allah kuma yana gasagatashi, sai yace; ka bani labari gameda Imani, sai manzon Allah yace “kayi Imani da Allah, kayi Imani da mala’ikunsa, da littaffansa, da manzanninsa, da ranar karshe, kuma kayi Imani da kaddara Alkhairinsa da sharrinsa, sai mutumen yace ka fadi gaskiya, sai yace ka bani labari gameda Ihsan (kyautatawa), sai Annabi yace “ka bautawa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa, to Shi Allah yana ganinka”, sai yace ka bani labari gameda sa’ar karshe(ta duniya), sai manzon Allah yace “wanda ake tambaya baifi mai tamabaya sani ba”, sai yace to ka bani labarin Alamominta, sai Annabi yace “baiwa zata haifi uwar gijiyarta, zaka ga huntaye, marar sa sutura, talakawa (wadanda basuda takalma da sutura isassu), masu kiwon dabbobi, suna gasa wajen gina manya manyan gidaje, sai Umar yace; sai wannan mutumen ya tafiya tai, sai na jira wani dan lokaci, sannan Annabi yace man “yakai Umar shin ko kasan wannan mai tambayar?” sai nicce Allah da manzonsa su sukafi sani, sai Annabi yace “ai mala’ika Jibirila ne, yazo muku ne domin ya karantar daku addininku” [Muslim ya ruwaitoshi]

My recent post

KADA MU DEBE TSAMMANI GA UBANGIJI

ALLAH YANA DA MAFITA GAMEDA DUKKANIN WATA MATSALAR DA TAKE DAMUNKA.

Koda yaushe muna yin tunani ne akan yawan matsalolin da suke damun mu ne a rayuwa, muna mantawa da cewa lallai fa haƙiƙa Allah yana da mafita daga dukkanin kowace irin matsalar da ta dame mu a rayuwa.

A rayuwa idan muka fuskanci Allah maɗaukakin sarki, muka koma gareshi da tuba cikin nadama da ƙas-ƙantar da kai, haƙiƙa Allah zai saurare mu, zai kuma yaye mana dukkanin damuwa da take damun mu ko ba-daɗe ko ba-jima, musamman idan munyi haƙuri mun kuma toge akan biyayya ga Allah ta’ala.

Muji tsoron Allah, sai Allah ya warware mana damuwar mu, mu kauce ma saɓonsa, sai yaji ƙanmu, kada mu bari shaiɗan yayi tasiri akanmu ya shiga tsakanin mu da ubangijin mu Allah ya kuma halaka mu ƙarshe mu zamto ababen yin nadama a ranar ƙiyamah.

UWA TA GARI

UWA TAGARI SA’AR YA’YA.

“Wallahi dukkanin wani jin daɗin da kake dashi a wannan duniyar matuƙar aka ce baka mori uwa ba, baka yi sa’ar samun uwa tagari ba, to haƙiƙa jin daɗinka ragagge ne”

“Dukkanin uwar da zata yawaita addu’ar alkhairi ga ƴa’ƴanta, zata kame bakinta daga zagi da aibanta su da kuma tsinuwa a garesu, to haƙiƙa wannan itace uwa tagari ga ƴa’ƴanta kuma mai bawa al’umma kariya ce, domin idan ta tsine musu ba iya ita kaɗai zasu dama ba, hatta jama’ar waje suma sai sun addabe su, sabida ita tsinuwar uwa akan ƴa’ƴanta haƙiƙa ba ƙaramar illa bace, sannan kuma idan tayi musu addu’ar alkhairi suka zama na ƙwarai to lallai ba iya ita kaɗai zata mora ba, hatta ma jama’ar waje sai sun amfana dasu, sabida haka ki zamto uwa tagari ga ƴa’ƴanki”

“Lallai uwa tagari bata la’antar ƴa’ƴanta, kana kuma bata la’antar na wasu, domin dukkanin uwar da zatayi riƙo da ɗabi’ar la’antar ƴa’ƴan wasu, to haƙiƙa wataran itama za’a la’anci nata, koda kuwa ba’a la’anci natan ba, to watarana da kanta zata la’ance su tunda bakinta ya saba da la’antar na wasu, amma idan ta zamto tagari mai yawan addu’a ga ƴa’ƴanta, to haƙiƙa inshaa Allahu sai Allah ya basu kariya a duk inda suke saidai idan jarabawar Allah ta sauka a garesu gameda wani ibtila’in rayuwar”

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYAS

Tarihin Shehu Ibrahim Inyas

Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy

Dafarko dai Mai Karatu Zanfara da sunan ALLAH ﷽

Mun manta da tarihi Saikawai Labaran Duniya dakuma Kallace_Kallacen Film, Har wasu daga cikin Daliban Wannan bawan Allah din Sheikh Ibrahim Inyas mabiyansa Na Tijjaniyya Da Faidha. Basusan Tarihin Nasaba Saidai kawai Sunsan Littattafansa Wadanada yarubuta Kamarsu Kashiful Ilbasi, Dama Dawawinu_Ssittah. dama Sauran Littattafansa na Abyat.

اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

Dafarkodai Sheikh Ibrahim inyas dai Asalinsa dan kasar Sanganiyane Agarin Kaulaha. Bayan Rasuwar Mahaifinsune alokacin da Sheikh Amadu Tijjani yazo yimasu Ta’aziyya, Sai Yanemi da da abashi dakin Soro domin Larabawa basa juran Zafi. Yayansa Muhammadu Khalifa wanda Shine Magajin Mahaifinsu a fannin Khalifanci na Wannan Zawiyyan, Sai yace dashi ga dakin Ibrahim Shine Soro kuyi masa Iso dashi, Bayan Ankaisa ga Dakinne Sai Ibrahima Inyas yanemi Zai fita daga dakin. Ananne ya qaddamar Masa da Quudirinsa na zaban dakin Soro. Dominsane shi Inyas. Sunyi Maganganu dai awannan daren Ahmadu Tijjani da Ibrahim inyas Amma na bibiyi tarihohin Marubuta banga abubuwan da suka tattauna ba azancen su na wannan daren. Sai dai wasu Suna Cewa Awannan Darenne yabashi Khalifanci na Qadmin Gausiyya. Allahu akbar! Bayan Lokacin Maulidi yazagayo🕦 kowa ya hallara an dagashi (inyas) domin Gabatar da Yabo sai yayi Magana kamar haka.

ومن یحبنی ومن یرانی فی الجنة

Fassara:
Dukkan wanda yasoshi ko ya ganshi To dan Aljannah ne.

Hmm Tabdijam, Gaskiya Wannan Zance yayi Nauyi dayawa, Idan Har ya Tabbata ya fadi Wannan zance to Gaskiya ba maganan ajizanci wannan Son Zuciyane. Inkuma Qage akayi masa to malaman Dariqu kaf dinsu Makaryatane domin Wannan Zantuka nacikin Littattafan Dariqu dadama.

Bari Muci gaba da Tarihi.

Bayan Wannan zancen Nasane fa Ruwa yafara kaiwa rana, tsakaninsa da yayansa Muhammad khalifa inda yayi masa inkari gamida fusata Yace dashi. Banine khalifan Baban kuba.

Saiyace kwarai kuwa kai kahlifan Baban mune, Nikuma khalifan Amadu Tijjani, Kuma Khalifan Manzon Allah.

Daganan fa aka fara gwabza rikici cikin Sabani da rikicin Khalifanci. Wasu marubutan Suna cewa har Guba Ansakawa Inyas a Abinci kuma yaci amma bai mutuba.
An koreshi daga Garin Kaulaha ta Kasar Sanganiya, Inda yakoma Koci yakafa daular Zawiyyarsa awannan Sauran ta Gonar Koci. Sheik Ibrahima Yasha gwagwarmaya Arayuwa Sosai duk asanadin wannan muqamin nasa na Gausiyya. Amma Allah ya tseraddashi daga dukkan tuggu.

ZUWANSA NIGERIA

Sheikh Ibrahim Inyasy yazo Nigeriyane ta sanadin wani Sarkin Kano Dan Tijjaniyya wanda dayayi Rokon Allah yabashi damar Zuwa hajji Sannan yahadashi da Gausin Zamani.
Bayan Allah ya cika masa Burinsa na Zuwa Saudiyyane Sai yahadu da Sheikh Ibrahim inyas Na Kaulaha. Dagan suka Gaisa Yakuma rokeshi da Neman Alfarma na cewa yazo kasar sa ta Nigeria.

Awannan lokacin yaso zuwa Amma sai aka samu akasi akan Rikicin da duniya takeyi Na yakin duniya na biyu.
Sai bayan wannan lokacin kafin yazo Sannan yazo tareda Littattafai yarabawa malamqn Tijjaniyya na Nijeriya. Malamai Sun Sallama masa Saida malami guda dayane yayi mar tawaye.
Amma shima daga baya ya sallama.

Daga wannan lokacinne Sunansa yakarade nigeria kuma yasamu Martaba da kuma Muqami sosai daga cikin maluman cikinta mabanbanta.

Wannan Shine kadan daga Tarihin Sheikh Ibrahim Inyas Shugaban Dariqar Tijjaniyya Khalifan Sheikh Amadu Tijjani.

Muna Rokon Allah ya Dawwamar damu akan bin Tafarkin Sunnah da bin Sunnah duk wuya duk dadi Allah ka karamana ikhlasi da Istiqaama akan Shiryayyen addininka. Da bin Annabinka dakuma bin Sahabbansa Salafussalih. Allah kayi Tsira ga Manzonka Annabin Rahama. مُحَمَّد ﷺ

واَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

AREWA 24 TAMUCE

AREWA 24 TAMUCE
Faduwar Dalibai A Jarrabawar JAMB

   Sau dayawa harda wasu acikin Malamai na ta fadar cewa Kallon Shirye_Shiryen Film Series. Sune Silar Faduwar Dalibanda Sukayi JAMB A bana 2021.

Daga Alqalamin ✍️Ismail Hussaini Alpholwy

@MatanasanMarutanBauchi

       Sabanin Ra’ayi danganeda Fahimtata dakuma Wadansu damuka tattauna akan batun awani ganawar damukayi ta Online da ‘Yan uwana marubuta.
A iya fahimtarmu bakawai Kallon series bane yakayarda Mutane a jarrabawar bana ba. Duk da Cewa yana daya daga cikin abubuwa uku acikinsu. Sune Kallan film, Yawan Sauraron kida, dakuma Wasannin Wayar hannu (Games)

  Wadanda dukka wadannan abubuwa suna Faruwane ta cikin wayoyin hannuwan mu. Yadda zakasamu Mace ko na miji yana da Game Apps Sama da Goma Sha ga kuma Film Series Suma Sama da Ashirin Ga kuma wakoki na Hippop dama Jazz Music dana Hausa dama na Turanci dana Kudanci Hardana Videos na Fitsara da Lalata Tarbiyya.

   To taya yaro zai dau littafi yayi karatu, bacin ga irin wadannan Shirmen da lalacewan acikin wayarsa. Dasu zai kwana kuma yatashi kuma ba akoyar dashi Tsoron Allah ba.

   Laifin iyayene dasuke sakaci da Wayoyin Yaransu dakuma Yaran dasuka taso Basu bibiyar kafafen Alkhairi acikin wayoyin dakuma Social Media.
Dolene Mu kame daga barin abinda Zai Cutar mana da imaninmu dama Kuruciyarmu gaba daya.
Burin Turawan yamma akoda Yaushe Shine Muzama Malalata Mukasa komai Sai sun mana.

     In iyayenmu basu ankaraddamu  ba wataran Za’a iya wayar gari bazamu iyayin komaiba, Sai abinda Turawa Sukaso suyi damu, domin anriga da makara komai ayanzu nasu ake kwaikwayo. Anmanta da Cewa akwai Tsarin Rayuwa Islamiyya dakuma Christianity. Duk abinda Yahudu Sukazo dashi Shine Ake bi.

    Idan da wasu iyayen Zasu duba Profile na Socil Media na Yaranau Musamman Facebook da Twitter dakuma Istagram da Tictok Wallahil Azim sai sun farfasa Wayoyin Yaransu. Yin hakan kuma abanza ne. Don zai je ga na Abokansa.

      Mafita garemu Shine Adasawa Yara Tsoron Allah Acikin Zuqatansu kawai tahanyar Nasihohi da Addu’ar Shiriya domin Tafiya tayi Nisa. baza’a taba iya Hanasu rike wayoyi Dukansu inma babu ahannun wancan akwai ahannan wancan kuma Munsan Cewa ba’a Rowan Wuta. in aikin Shedancine kana Zaune za Akawomaka, kuma ba aganin Tsadarsa domin Akan iya Sayan plartform domin Series Film Amma daukar Nauyin Tafseer kuwa Sai cikin Azumi.

Domin Allah iyaye Akoyar da ‘ya’ya Tsoron Allah, Allah yakawo mana mafita Arayuwa.