AHLUSSUNNAH MUFARKA

DA’ACE KISHIN QUNGIYANCIN MU NA ADDINI NE DA MUN WUCE HAKA ACIGABA

      Ahlussunnah Mufarka
Jiya kotu a Kaduna ta wanke Amirul Jaish na rundinar shi’ah (IMN) Ibrahim Yakubu Zakzaky daga tuhumar da Gwamnatin jihar Kaduna ta masa, biyo bayan abinda ya faru a Gazwatu Hussainiyyah Zaria da sojojin janar Buratai a 2015
Ni abinda na fahimta lokacin da Gwamnati ta gindaya masa ne kawai yayi ta sakeshi da kuma tasirin da Zakzaky yake dashi a cikin wannan Gwamnatin, amma ba wai don ta rasa hujjar da zata cigaba da tsareshi ba
Sannan bayan matakin da kotun Kaduna ta zartar, har ila yau inda ace Gwamnatin Kaduna tana da niyyar cigaba da garkame Zakzaky da tayi hakan ta hanyar daukaka kara a kotun tarayya dake Abuja, kamar yadda dokar kasa ta tanadar
Zakzaky yana da manyan mutane a Kasarnan wanda suna da tasirin da zasu iya nema masa alfarma har a gurin shugaban Kasa, idan baku sani ba Zakzaky yana da Manyan Ministoci har guda biyu a cikin wannan Gwamnatin wanda a baya har muzahara suna fita kafin a kafa Gwamnatin Buhari a 2015
Gareka Musulmi Ahlussunnah, ka sani cewa ba ruwan Gwamnatin Nigeria bane ta yaki wani mutum saboda yana dauke da akidar da ta saba da ra’ayinta, shi tsarin kundin Constitution da yake rike da tsarin gudanarwan Kasa, fada ma yake da kowace irin akida ta Musulunci
Duk abinda ya faru da Zakzaky bai da nasaba da addini ko akida, zallar siyasa ce kawai, zargi ne marar tushe da ake cewa Kasar Saudiyyah cibiyar Ahlussunnah tana da hannu a abinda ya faru da Zakzaky
Jama’ar Musulmi da muke kiyayya da shi’ah ku sani cewa akwai babban kalubale a garemu idan bamu gyara, yawan da muke dashi ba zai taba amfanar mu ba, Ya ku Ahlussunnah me zai hana kuyi irin tsarin da Zakzaky yayi har ya samu karfi da kuma tasiri da ya mallaki manyan wakilai da yake dashi a kowace ma’aikata a Gwamnatin Nigeria?
Shin Ahlussunnah kuna da tsarin da kuke daukar nauyin karatun matasa masu fikra da basira a cikinku suna zuwa Kasashen turai suna karanta Medical Doctor, Pilot, Nuclear Physics, Astronomy, Mechanical Engineering, International Law, Computer Science, Ethical Hacking, Cyber Security da sauran fannonin ilmi masu tasiri a zamani kamar yadda Zakzaky yake yi?
Shin Ahlussunnah kuna da tsarin bangare a cikin da’awar Sunnah ko kungiyar Sunnah da yake da bangare na Likitoci Ahlussunnah, bangare na Malaman makarantar boko tun daga Primary har University, bangare na jami’an tsaro, bangare na siyasa, bangare na ‘yan kasuwa, bangare na ma’aikatan Gwamnatin tarayya da na jihohi da kananan hukumomi kamar yadda Zakzaky yake da wannan tsarin?
Ahlussunnah ba mu da wannan tsarin ko guda daya, an bar Ahlussunnah a baya, an bar Ahlussunnah da yiwa juna raddi da hassada, abinda ba za’a taba samu ba kenan a cikin da’awar shi’ah a Nigeria, idan kunga bangaren RAAF suna sukar IMN Taqiyyah ne, manufarsu daya ce
Tsarin da Zakzaky yayi ba shakka idan Allah Ya bashi tsawon rai sai ya kafa Gwamnatin shi’ah a Nigeria, domin Billahi yayi kafuwar da ya wuce tunanin duk wani mai nisan tunani, na rantse da Allah inda ace da’awar shi’ah abune mai kyau da na jima da zama ‘dan shi’ah, kuma da yanzu bana Kasarnan saboda girman gudunmawa da zan bayar a tafiyar, amma shi’ah ba abune mai kyau ba
Namu jagororin sun zama ‘yan duniya, sun fara nesanta kansu da da’awar Sunnah, tsarinsu ya koma irin na ‘yan duniya kawai, sun koma karya da yaudara da zakin baki, takaicin wannan abin yana matukar sanya ni kuka da zubar da hawaye
Halin da Musulmi Ahlussunnah muke ciki a yau ya kamata ya dinga hanamu bacci, ya zamto muna tunanin hanyar da zamu bi mu gyara kuskure domin mu tunkari abokan gaban mu
Yaa Allah Ka bamu mafita na alheri Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
Daga Malam Datti Assalafiy

TARIHIN GWARGWARMAYAR KAFA IZALA

ASSASA IZALA A NIGERIA

Izala Ikon ALLA ﷻ

KADAN DAGA TARIHIN SHEIKH ISMA’ILA IDRIS BN ZAKARIYYA !!!

kamar yadda nayi maku Alqawari


     **Gwagwar mayarsa wajen Kafa Izala da Sunnah**

Sheikh Isma’ila Idris yatasone cikin al’umar nan tamu ta Nigeria, ayankin Arewa inda awannan lokacin babu wata aqida a Qasarnan bayan Dariqar Tijjaniyya, Qarqashin jagorancin sheikh Ibrahim Inyas Alkaulahy.
     To dake zamani ya Nausa tafiya tayi nisa, Al’uma tasamu kanta cikin yanayi na Cakuda addini da Son zuciya. Ana samun Malamai masu Sanya Son ransu acikin addini suna anfani dasunan Addini Suna isarda Munanan manufofinsu ga Al’uma kalar Bokanci da Sihirin Duba dama wasu Tsubbace_tsubbace su na Son Zuciya da Neman duniya.
    Wanda yaci karo da koyarwar Addinin Musulunci. Dukkan mai irin wad’annan aiki Bai tabayinsu Saiya fita a addinin Musulunci, Yazamo dukkan wanda yayi Sunansa kafiri da Nassin Aya acikin Suratu baqarah. Haqiqah bayan Wannan Akwai wasu littattafai dadama wadanda Maluma suka shigo dashi ake karantasu na Labaran mafarki da Tatsuniyoyi dasunan Adddini, Irin wadannan abubuwa dakuma makamantansu Sune maqasudin Da’awar ta Sheikh Isma’il Idris, abisa fahimtar masu kyautata masa zato.
    Da’akwai wadanda suke ganin cewa kawai yafara da’awar izala ne kawai Don Neman Suna dakuma Zagin Wasu malamai (Shehunnan ‘Dariau) dakuma Sufaye. Wanda kuma hakan kuskurene domin  Aikin Musulmi shine kyautatawa juna zato. Da Kuma nemawa juna gafara agunda akayi Kuskure danganeda Sa’banin Ra’ayi ko Fahimta.


    Zamu cigaba ta Tarihi.
    Bayan Malam Yabar aikin Soja wanda acikin Aikin nasa na Soja ya fara da’awa akan barin Tsubbu da Daura layu da makamantansu, Malam yasha tsangwama daga makiya dakuma wadanda basu da ilimi wanda basu fahimceshi ba. Ba awannan Lokaci malam yaga cewar Wannan Da’awa tasa bazata cigaba ba Har saida wata Qungiya Wacce zata Tallafa masa Danganeda samun cikar Qudirinsa na Farkadda mutane game da Sunnah Asali.
    Awannan lokacine malam ya Assasa wata Kungiya mai Suna; ”Jama’atu izalatul Bid’ah ” Ma’ana ( Gungiyar dake kawar da Bidi’ah ) Wannan Kungiya Tasa tasamu karbuwa hatta aciki ‘Yan uwa Sojoji na wannan lokaci, Saidai kuma tasamu naqasu Sosai daga Malaman wannan zamanin Musamman wadanda keda Wannan aqidar ta Tsubbace_tsubbace da Duba. Tayadda sukayita yimasa Tuggu da zagon kasa gurin Sun ga sun dakushe wannan aikin Nasa, Tare da Wargaza aikin Nasa tahanyar kirkiran karya akansa hadda cutar dashi domin Su samu Galaba akansa, Amma ahakan Allah ya Tserataddashi daga dukkan tarakunan nasu Allah ya kuma karfafa Wannan Da’awa tasa har ilayau Qugiyar izala tana nan kuma tana cigaba da aikinta wajen karantar da Al’uma bisa koyarwar magabata dakuma Tabbatar da Qur’ani da Hadisi sune tafarkin Tsira ga Bayi.
    Ahakan aka cigaba da kasancewa har takai yaje izuwa ga Malamin sa na Tauhidi Assheikh Abubakar Mahmud Gumi, Domin neman izini da Karin lamani dangane da Da’awar tasa. Awannan lokacine Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya nuna Bashi Cikakkiyar goyon baya gamida Cikatamasa Sunan Gungoyarsa da ” Wa’iqamatissunnah ”  ma’ana ( Dakuma Tsayar da Sunnah ) Wcce tazamo ” Jama’atu izalatul Bid’ah Wa’iqatissunnah ”
    Ma’an ( Qungiyar dake kawar da Bidi’a kuma take Tsayar da Sunnah )
    Domin acewarsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi; Babu Yadda za’ayi akawar da bidi’a abarta haka ba acike Gurbinta da wani abu ba, Shine Yace to sai Acike Gurbinta Da Sunnah.
    Kunga Ashe kenan ita Izala ba Fitina bace Sabanin Yadda wasu daga cikin maluman ma da basu fahimta ba, Kuma bawai Reshen addini bace kamar yadda wasu suke yimata Mummunar fahimta Har ma wasu ke ganin Cewa in baka ciki to baka cika musulmiba, wasu kuma ke Mata ganin Cewa inkan cikinta Musuluncinka da Gyara Haqiqa Dukkan Mai yiwa Wata Aqidah ta Musulunci ganin Wannan Al’amari, Alal hakika ya Jahilci Hakikanin Musulunci,
    Wannan kadan kenan daga Tarihin Sheikh Isma’ila Idris da Gwagwarmayarsa gurin kafa Izala, insha Allah Anan gaba Zan kawo muku Cigaban da iza ta Kawo Wa Musulunci da Kasarmu baki daya. In Allah mai Komai ya kaimu bayan Sallah.
    Nine naku Isma’il Hussaini Adam Alpholtawy


    Kuma Wannan Shine karshen Rubutuna danganeda Shafukan Tarihin na Bana A Hijira sheka ta 1442 Saikuma Allah ya Kaimu Almuharram Shekara ta 1443 Zan cigaba da Wannan Tarihi.
    Mai karatu ga Addu’a ta Katayani da Ameen.
    Ya ALLAH Kajiqan Mahaifina Hussaini Adam Jumba wanda Ya Rasu a irin Wannan wata Mai Alfarma kuma Aranar Idin Adhhaa, Idin Babban Sallah Allah Kajikansa Ka gafarta masa ka kai Harke Qabarinsa, Kabashi Aljannah Madaukakiya.
    Ya ALLAH Mu Zuri’arsa Da muka Rage a bayan Kasa Allah ka azurtamu da Dogora abisa Addininka, Kabamu Shahada irin tasa, kasanyamu Cikin Wadanda kake Yantawa Zuwa Aljannah.
    Ya ALLAH Ka Sitirtamu da Sutura ta Musulunci, Ka azurtamu da Arzikin imani, da Ikhlasi da Tabbatuwa akan imani, Har Mu Mutu muna masu imani Da Miqa wuya gareka Allah.
    Ya ALLAH ka daukaka musulunci da musulmai, ka Qaskantar da Kafirci da Kafirai kadirkake makiyanka makiyan addini Allah kataimaki bayinka Nagari.

Mawallafi Ismail Hussaini Adam Alpholtawy

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYAS

Tarihin Shehu Ibrahim Inyas

Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy

Dafarko dai Mai Karatu Zanfara da sunan ALLAH ﷽

Mun manta da tarihi Saikawai Labaran Duniya dakuma Kallace_Kallacen Film, Har wasu daga cikin Daliban Wannan bawan Allah din Sheikh Ibrahim Inyas mabiyansa Na Tijjaniyya Da Faidha. Basusan Tarihin Nasaba Saidai kawai Sunsan Littattafansa Wadanada yarubuta Kamarsu Kashiful Ilbasi, Dama Dawawinu_Ssittah. dama Sauran Littattafansa na Abyat.

اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

Dafarkodai Sheikh Ibrahim inyas dai Asalinsa dan kasar Sanganiyane Agarin Kaulaha. Bayan Rasuwar Mahaifinsune alokacin da Sheikh Amadu Tijjani yazo yimasu Ta’aziyya, Sai Yanemi da da abashi dakin Soro domin Larabawa basa juran Zafi. Yayansa Muhammadu Khalifa wanda Shine Magajin Mahaifinsu a fannin Khalifanci na Wannan Zawiyyan, Sai yace dashi ga dakin Ibrahim Shine Soro kuyi masa Iso dashi, Bayan Ankaisa ga Dakinne Sai Ibrahima Inyas yanemi Zai fita daga dakin. Ananne ya qaddamar Masa da Quudirinsa na zaban dakin Soro. Dominsane shi Inyas. Sunyi Maganganu dai awannan daren Ahmadu Tijjani da Ibrahim inyas Amma na bibiyi tarihohin Marubuta banga abubuwan da suka tattauna ba azancen su na wannan daren. Sai dai wasu Suna Cewa Awannan Darenne yabashi Khalifanci na Qadmin Gausiyya. Allahu akbar! Bayan Lokacin Maulidi yazagayo🕦 kowa ya hallara an dagashi (inyas) domin Gabatar da Yabo sai yayi Magana kamar haka.

ومن یحبنی ومن یرانی فی الجنة

Fassara:
Dukkan wanda yasoshi ko ya ganshi To dan Aljannah ne.

Hmm Tabdijam, Gaskiya Wannan Zance yayi Nauyi dayawa, Idan Har ya Tabbata ya fadi Wannan zance to Gaskiya ba maganan ajizanci wannan Son Zuciyane. Inkuma Qage akayi masa to malaman Dariqu kaf dinsu Makaryatane domin Wannan Zantuka nacikin Littattafan Dariqu dadama.

Bari Muci gaba da Tarihi.

Bayan Wannan zancen Nasane fa Ruwa yafara kaiwa rana, tsakaninsa da yayansa Muhammad khalifa inda yayi masa inkari gamida fusata Yace dashi. Banine khalifan Baban kuba.

Saiyace kwarai kuwa kai kahlifan Baban mune, Nikuma khalifan Amadu Tijjani, Kuma Khalifan Manzon Allah.

Daganan fa aka fara gwabza rikici cikin Sabani da rikicin Khalifanci. Wasu marubutan Suna cewa har Guba Ansakawa Inyas a Abinci kuma yaci amma bai mutuba.
An koreshi daga Garin Kaulaha ta Kasar Sanganiya, Inda yakoma Koci yakafa daular Zawiyyarsa awannan Sauran ta Gonar Koci. Sheik Ibrahima Yasha gwagwarmaya Arayuwa Sosai duk asanadin wannan muqamin nasa na Gausiyya. Amma Allah ya tseraddashi daga dukkan tuggu.

ZUWANSA NIGERIA

Sheikh Ibrahim Inyasy yazo Nigeriyane ta sanadin wani Sarkin Kano Dan Tijjaniyya wanda dayayi Rokon Allah yabashi damar Zuwa hajji Sannan yahadashi da Gausin Zamani.
Bayan Allah ya cika masa Burinsa na Zuwa Saudiyyane Sai yahadu da Sheikh Ibrahim inyas Na Kaulaha. Dagan suka Gaisa Yakuma rokeshi da Neman Alfarma na cewa yazo kasar sa ta Nigeria.

Awannan lokacin yaso zuwa Amma sai aka samu akasi akan Rikicin da duniya takeyi Na yakin duniya na biyu.
Sai bayan wannan lokacin kafin yazo Sannan yazo tareda Littattafai yarabawa malamqn Tijjaniyya na Nijeriya. Malamai Sun Sallama masa Saida malami guda dayane yayi mar tawaye.
Amma shima daga baya ya sallama.

Daga wannan lokacinne Sunansa yakarade nigeria kuma yasamu Martaba da kuma Muqami sosai daga cikin maluman cikinta mabanbanta.

Wannan Shine kadan daga Tarihin Sheikh Ibrahim Inyas Shugaban Dariqar Tijjaniyya Khalifan Sheikh Amadu Tijjani.

Muna Rokon Allah ya Dawwamar damu akan bin Tafarkin Sunnah da bin Sunnah duk wuya duk dadi Allah ka karamana ikhlasi da Istiqaama akan Shiryayyen addininka. Da bin Annabinka dakuma bin Sahabbansa Salafussalih. Allah kayi Tsira ga Manzonka Annabin Rahama. مُحَمَّد ﷺ

واَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎