MU KIYAYE ALLAH NIDA KU

Ismail Hussaini Adam

Bazamu Kauce Shari`ah Ba
Duk Wuya Bazamu rabe ba
Kunci Bazaisa Mu Sarye ba
Balle Wuya ba Mutuwa ba
Duk Rintsi Bazamu Rabe ba

Dan Arzikinka Ga Bayi Allah Tabbatar Mana Alkhairinka

Duniya Ba`a Zauna ba
Rayuwa ba Mutuwa ba
Zamani Ba Namutum ba
Arzikin ba Nakun ba
Iyawuya Ninakine Zainaba

Ya Zul jalalu Kaduba Isarmu Kabamu  Iyawar dan Tasirinka

Dafamana ya Rabbana
Ka iyamana ya Jalla na
Da Isarka ne Khaliqa na
Rayuwarmu Arzuq Na
Bi Izzatuka Ya Ahya Na

Ka Nuna Isarka Cikin Ayyukan Bayi Ka Tabbatar Da Samuwarka

Ya Arhamrrahimina
Ya Alimul Alamina
Ya Khairul Munzalina
Ya Fatihul Raziqina
Ya Alimussirruna

Alhayyul Qayyumu Bamu ikon Tuba Kayima duniya da Lahirarmu Tsari Ya Mai Tsarkin Tsarkaka

MATAN ZAMANI AYI HATTARA

  Duk iya Gyaran Bakanike Bazai Iya Maida Tsoho Izuwa Sabo ba, Komai Zaiyi Lallabene.

“Babu wanda zai so siyan abu sabo a kwali sai yaje gida ya bude ya tarar duk ya koke ko kuma yaga wani alamu da ke alamta cewa wani yayiamfani da abun kafin shi.

Wani zai iya daurewa ya cigaba da amfani daabun a haka amma ba da daďin rai ba,wani kumazai fusata ya mayar da abun inda ya siyo ne donyaji dalilin da zaa sayar masa da second hand amatsayin sabo,

Kada a rudu da rudin zamani don shi dai mutunci madara ne, don haka sai a kula!
Allah Ya shirya mu da zuri’ar mu gaba daya.”

Aishatu Bint Shafili

19 June 2021

  • Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers
    Nasarorin Da Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Samu Cikin Shekaru… Read more: Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers
  • TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI
    ══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁… Read more: TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI
  • ZATIN UBANGIJI
    SHAUQI CIKIN AL AMARIN GAIBIYYA Kasantuwar Ubangiji A Buya Bai… Read more: ZATIN UBANGIJI
  • GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI
    Ban Shan Sigari Ban Shan MoringaBan Shan 200 Kayan zamani… Read more: GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI
  • KUJI TAUSAYIN MARAYAN ALLAH
    Bansan me Nayi mussu baNufata da Sharri suke basu barniba… Read more: KUJI TAUSAYIN MARAYAN ALLAH
  • FASAHAR ZAMANI
    Menene capacitor?  Dauki masu gudanar da wutarlantarki guda biyu (abubuwan da suka bari Wutarlantarki ta ratsa su) sai ka raba su da insulator(kayan da ba su barin wuta ya ratsa sosai) sai kayi capacitor: wani abu da zai iya adanamakamashin wutar lantarki. Kara makamashinlantarki ga mai iya aiki shi ake kira caji ; fitar dakarfin daga mai iya aiki shi aka sani dadischarging. Capacitor yana dan kama da baturiya, amma yanada wani aiki daban. Baturiya na amfani dasinadarai don adana makamashin lantarki da sake shi a hankalita hanyar zagaye; wani lokaci (a yanayin agogonkwata) zai iya daukar shekaru da dama. Mai iyaaiki yana sakin karfinsa da sauri-sau da yawa acikin sakanni ko kasa da haka. Idan kana daukanhoton flash, misali, kana bukatar kyamararka don samar da babban burst na haskea cikin fraction na sakan daya. Wani mai iko daaka hađe da bindigogin flash na ‘yan sakanni taamfani da makamashi daga batirin kyamararka.(Yana daukar lokaci kafin caji capacitor shi yasayawanoci dole ka jira kadan.) Da zarar an caji maikarfin, zai iya sakin duk karfin nan take ta hanyarxenon flash bulb. Zap! What is a capacitor?Take… Read more: FASAHAR ZAMANI
  • MU KIYAYE ALLAH NIDA KU
    Bazamu Kauce Shari`ah BaDuk Wuya Bazamu rabe baKunci Bazaisa Mu… Read more: MU KIYAYE ALLAH NIDA KU

HANYAR KUTSE TA SIYASAR YAHUDAWA

Alpholtawy

  • May 20,2021
  • Gabatarwa Dukkan Yabo ya Tabbata ga Allah ﷻ Wanda yayi Rana, Da wata, yayi Halittun Duniya da Dukkan Abinda Yafaru Iyawarsane. Muna yabamasa, Muna Godiya Agareshi, Daya Sanyamu Cikin Aluma wacce take Mafificiya. Wacce tazamo Mafi daraja daga Cikin Alumomin da Allah Yake Sanyawa adoron Kasa, Karkashin Manzo Mafi Daraja Cikin Manzanninsa Mafiya Daukaka Annabi Muhammadﷺ . Muna Godemasaﷻ daya Sanyamu Musulmi Kuma Masu Kokarin Neman Sanin Gaskiya Dakuma Bincike Akan abinda Zai Zama Hanyar Tsira Agaremu. Bayan haka; hakika Ban Wallafa Wannan Rubutu nawa Domin Cin Zarafin Kowa ba Sai Dan Fayyace Haqiqanin Abinda Allah ne Yamana Ishara Cikin Littafinsa Mai Tsarki Karkashin Ayoyi dayawa Amma Zangina Rubutuna akan Wannan ayoyine Guda biyu Wadanda Suke Bayani Karara Akan Siyasar Dunya watau Dilomasiyya Fadisa Yahudu da Nasara Basa Yarje Muku Harsai kunbi Tafarkinsu Dakuma Fadinsa ´´Bazasu Gujeba Suna Yakarku Harsai Kunbar Addininku Insun Samu IkoAmma Kuma Ubangiji Yafada mana Wadanda Suka Fi Gaba Da Musulunci Dakuma Wadanda Suke da Sassaucin Ra`ayi Inda Yake Cewa ﷻ ´´Zakasamu Mafiya Kusancin Soyayya ga Wadanda Sukayi Imani, Sune Wadanda Suke Riya Cewa Lallai mune Nasara Saboda Acikinsu Akwai Malaman Qissisin da Ruhban Wadannan Ayoyi da Makamanatansu Sune Babban Abinda Zagina Maqala ta Akai, Haqiqa Ubangiji ﷻ Shine ya Sansu, Kuma shidin Yafimu Sanin Halayemsu, Shiyasa Shi da Kansa Yake Bayyana Mana Halinsu, Kuma Yayimana Gargadi Akan cewa kada Muyarda Mubi Tafarkinsu, Domin Sudin Daga Wadanda Ubangiji Yayi Fushi dasu Saboda Kin Aiki da Gaskiya ne, Sai kuma Batattu Wadanda Suka Ki Sunemi Ilimin Da Zasu Fayyace Gaskiya, Wannan Shi Yahukumta Dolene Kanemi Ilimi, Kuma Dolene Kayi Aiki Da Iliminka Wajen Neman Lahira, Inkuwa Baka nema ba Bakada uziri agun Ubangiji, domin Yafada mana Kuma Inkasamu Bakayi Aiki bama, Shima Qalubalene Domin zai iya Zama Hujja akanka, Fatanmu Ubangiji Yabamu Ikon Aiki da Ilimin da Yabamu Yakuma Bamu ilimi na Tsoronsa da Aiki dominsa Yahore mana Sanin Gaskiya Da Aiki Da Ita. Mawallafi ✍️ Ismail Hussaini Alpholtawy Website alpholtawy.jw.Lt Tsikaci; Banyi Wannan Rubutu Domin Cin Zarafin Wani ko keta Mutuwacin wataba. Nayishine Domin fahimtar da Wasu wadanda Suka Jahilci Lamarin Diplomasiyya Na Yanzu, Tayadda Aka kasa gane Menene manufar mamayar Turawa Dakuma Illar dasuke Jefawa Al’uma, Misali Mafi girma Irin ‘Barnar rayuka dasuka haifar a Gabas ta Tsakiya dasunan Rikicin Aqeedah dakuma Addini. Lamarin Zai Karene Akan Gida Kuma Yankinmu Africa Tayadda Suka Maidamu Bayi Kuma Suke Sa Muna kashe Junarmu Domin Biyan Bukatunsu.
  • MAQALA TA FARKO Bayanin Suwaye YAHUDAWA
    MAQALA TA BIYU Kutsen YAHUDAWA a Gabas Ta Tsakiya
    MAQALA TA UKU Illar dasuke Yiwa Larabawa Na Mulkin Kama Karya
    MAQALA TA HUDU Illar Dasuke Yiwa Africa Ayanzu
    MAQALA TA BIYAR Hanyoyin dasuke Bi Don Kutsewa Duniya
    Zanyi Bayaninsu Daya Bayan Daya INSHAALLAH Inafatan Mai KARATU Bazai Gajiya ba, Zan takaita Rubutun Nawa Domin Ina Sanyawa A Social Media Dan yazama nasayashi a Post Guda Daya.
    MAQALA TA FARKO
    Bayanin Suwaye Yahudawa Dukkan Mai bibiyan Tarihi Kokuma Wanda yake Karanta ALQUR’ANI Basai Anyimasa dogon jawabi ba, Yasan YAHUDAWA Sufarsu Ahali Saidai Ayanzu Idan Zamu Nemi Saninsu Zamuce Mutanen da 👉Hitila Ya Yakesu 🔥. Wad’anda Ayanzu Sukafi Rayuwa awadannan Kasashen kamar Haka; US, UK, Canada, France, Germany, Italy, Portugal, Turkey da sauransu. Wad’anda Suke a Yammacin Duniya Kuma Suna da Karfin Iko Tayadda Yazama Kaso Saba’in da Biyar Cikin Dari (75%) Na duniya Su Suke juyata Da ikonsu na Salon Mulkin kama Karya Dakuma Zalnci Hakan yafaru ne Dalilin Mugun halinsu Na Tusa Talauci Da Ta’addanci Wa Dukkan Kasar dasukaga Zata yimusu Tawaye Harsai Sunkarya Daukarta. Mai Karatu Na iya Tambaya Shin Menene ikonsu Da Gadara? **Amsarka itace:— Sunada Karfi Iko aduniya Sunada Kudi Wanda Sunhada Wad’annnan Abubuwane tahanyar Tanadin da Suke fata na Kare Kansu a Yaki Idan ta fado Musu domin Gamai bibiyan Tarihi yaji Yadda aka Tarwatsamusu Daula A Yakin Duniya ta Biyu akayi Kusan Karar Dasu Adoron Kasa. Wannan Dalili yasa Suka kulla kawance da Junansu Suka Kuma fara Tattali da Tara Makamai da Kutse Cikin kowace Al’uma domin Suyada Kansu aduniya Dan Subazama Takowani Shashi, Suna da Qungiyo Ayanzu kamar haka; 👉NATO (North Atlantic Treaty Organization 👉CSTO (Collective Security 👉G7 (Group of Seven) 👉EU (European Union) Sannan Suntara Makamai Ba Adadi Sunada Karfi Fiyeda sanin ‘Dan Adam, Kuma Zasu iya Tunkarar kowa Aduniya, insuka farwa kasa To ALLAH ne Kawai Gatanta Amma Babu Mahaluqinda ya isa Yatsayar musu Da Aniyarsu Sai ALLAH Saikuma In Ansamu Masharranta Irinsu. Muna Rokon **Ubangiji ** yatsaremu daga Sharrin YAHUDAWA.
    MAQALA TA BIYU
    Kutsen yahudawa a Gabas Ta Tsakiya Wannan Maqalar zata iya Zama izina kokuma nace Hannunka Mai Sandan ga Hukumomi Dakuma Shugabannin Africa. Haqiqa Larabawa Sundauki YAHUDAWA amatsayin Aminai Kuma Mataimaka, Wanda Aminci yakai alakar Auratayya Tashiga Tsakaninsu Tayadda Suna Auren juna Kamar Yadda Addinin Musulunci yasawwaqe. Tofa Saidai Awannan zamanin Juyin Yanyi Yacanza al’amuran, Tayadda Yahudawa Suke Amfani dawannan HANYAR Suna Sanya Gaba da Tsanar juna Wa YAHUDAWA Tahanyar Cusawa ‘ya’yansu mata Suna Koyamusu Yadda Zasu Sanya Mijin Daya Auri Bayahudiya Yakori Dansa Ko Kaninsa kowani Nasa Wadda Yake Karakashinsa Saboda Sharri irinna Matayen YAHUDAWA dasuka Auro, Kuma hakan Koyine daga Iyayensu domin Acewarsu Hakan Shine Zai fara Karya Daular Larabawa Domin Awannan Lokacin babu Daular datake Qalubale agaresu kamar Larabawa Domin Sunfi Kusa dasu kuma Sune Al’uma mafi yawa Awannan Lokacin. Wannan Shine Farkon Faruwar Rushe Daular Larabawa.
    ,MAQALA TA UKU
    Illar dasuke Yiwa Larabawa Na Mulkin Kama Karya Bayan Sun Karya Karfinta da mata Sai kuma Suka Fara Yakar Tattalin Arzikinta Tahanyar Yanke Huldar Kasuwancinsu da Kasashen Duniya. Ga GA’bar Tambaya! Taya Zasu yanke Huldar Kasuwancinsu da Kasashen Duniya? Amsar mu Anan itace;— Sunyi Amfani da Wasu ‘Yan Gidan Gofnatin da Larabawa ke Mulka Wad’annan Wad’anda Yayunsu da Iyayen Gidansu Suka Kora Sukayi Amfani Dasu Wajen Kirkiran Qungiyoyin Ta’addanci domin Suyi Kamfen din ‘Bata Wannan Daular datayi Sanandin Barinsu Gari daganan YAHUDAWA Suka Karfafa Wad’annan Qungiyoyi na Ta’addanci Suka Taramusu Kudade da Makamai Suka Dinga Ruguza Al’uma Gefe Guda Kuma YAHUDAWA Suna Shigowa Suna Bada Magunguna Masu Illa Dasunan Tallafi Suna Kashe Al’umar da Gubar magani ‘yan Ta’adda sunayi Da Bindiga da Bomabomai. Sannan A’bangaren Gofnati Sunshiga Da Zimmar Zasu Taimaki Gofnatin Amma Suna bata Bashin Makamai Sannan dahakan Sukayi Amfani Suka karya Wannan Daular Suka Ruguza Himma da Mafarkin Wadannan Shuwagabannin Har ila Yau Kasashen Larabawar Gabas ta Tsakiya Suna Cikin halin Tausayawa da Alhini da Kuncin Rayuwa da Halin Tausayawa
    . MAQALA TA HUDU
    Yadda Suke Wanzar da Shirin Kutse Cikin Al’umar dasuke So! Suna yin Wannan ayyuka nasune tahanyar damuka ambata abaya, da mata Dakuma Tsirar da Tsiro na ‘Yan Ta’adda daga Cikinku Wanda Hakan Zaibasu Daman Saida Makamai Akasarku, Tayadda Zasu Sami Damar Shiga Gofnatin Kasarku daganan sai su Karya Tattalin Arzikin Kasarku. Sannan Daga Baya Suma Sufara Shigowa suna Baku Guba dasunan Magani. Tabbas Akwai Wani Mummunar aiki Wanda YAHUDAWA Suke Shiryuwa Wanda Wannan Tafi Shafan Wad’anda Suke Musulmi Domin Acewarsu Bisa bincike dasuke Aiwatar wa ”Nan Da ‘yan Wasu Shekaru Duniya da Mulkin ta Zaikoma Hannun Musulmi Wannan Dalili Yasa Suke Kirkiran Wasu Qungiyoyi Wad’anda Suke Fada da Rusa Tsarin Musulunci Dakuma Hadin kansu Dama Uwa uba Tunkud’esu Akan Turbarsu ta Imani Da Ubangiji ALLAH izuwa Ga Bautan Aljanu da Kaucewa Hukumcin Ubangiji Izuwa Hukumci na son Zuciya Maras Tushe Da Asali. Tambayar dayakamata Me Karatu yayi; Taya Suke Aiwatar da Wad’annan ayyuka kuma me Suke So Su cimma kuma Menene Qungiyoyinda Suke Kirkiran? Suna Aikinne Kaitsaye Domin Rushe Bautar Ubangiji Dakuma Hani akan Aikin Da Littattafan Ubangiji Sannan, Domin Burinsu Sumulki Duniya Amma hakan Bazai yiwuba Matukar Mutane sunada Tsarin rayuwa Da Addini Domin Hakan Zaihanasu Samun Cikakken iko Dakuma Dama, Saboda Haka Aikin da Zasuyi nafarko Shine Raba Mutane da Addini, Ba Musulunci kadaiba; Dukkan Addinin dasukaga yanada Littattafi Burinsu Su Sanyawa Mabiyansa Rauni Tayadda Zasuyi Amfani da Matsalolin Aqidar Addinin Suhaddasa Rigima daga Baya kuwa Su fara Yiwa Malamanku Kisan Gilla dasunan Suna kawo Sabanin ADDINI.
    MAQALA TA BIYAR
    Kammalawa da Bayanin Hanyoyin dasuke Bi Don Kutsewa Duniya Dukkan Godiya ta Gabbata Ga Ubangiji Mahalicci, Mai Hukumci Bisa Adalci Mai Karamci Baya Butulci Sassauci Baya Ha’inci. Masani Mai Bada Kyautar Komai Mai Yadda Yaso Ayanda Yaso Ko Anaso Ko Ba’aso, Salati Da Aminci Sutabbata Ga Shugaba Ja Gaba Mai Martaba Annabi (S. W. A.) Da Iyalan gidansa mataye da Yayayensa Da Sahabbansa Ubangiji kayimusu Aminci Aminci mai Yawa. Bayan Haka Wannan Maqala Itace ta Kammalawa Kuma Zankara Haskamana Wasu Abebenda Zamu kara Lura Dasu Muma Mudau Izina Sannan Mukula DA Sha’anin YAHUDAWA Dakuma Kokarin Gujewa Turbarsu ta Munafurci Dayaudara.
    👉Muyi Hakuri da Junanmu muna Tsayuwa Domin Neman Fahimtar Juna Yayin Rikicin Addini ko Qabilanci. 👉Kada Shigar Tsaraici Na Matan YAHUDAWAn Yamma ya rudeka Ka Kwaso Bala’i Wa Kasarku. 👉Kuyi Kokarin Koran Tsarin Rayuwarsu DA Al’adunsu Na Dabbanci Kuyi Hukumci da Littattafanku. 👉Kutabbatar Kuna Rike DA Tarihin Duniya Awulkanci Wani Lokaci idan Fitina Ta Auku Ku Nemi Maslaha daga Tarihin Al’umomin Bayanku. 👉Kada Kubar ‘ya’yanku Akasashen Turawan Yamma Kawai Suna Karatun Boko Batareda Koyar Dasu Addini ba. 👉Kutabbatar Kuna Kwatanta Aiki Tsarin Addininku Domin Gujewa Sa’banin Zamani. 👉Kada Kukarbi Wani Tallafin Magani Ko Abinci Daga Garesu Harasai Masana Daga Kasarku Sun Tantance. 👉Kada Kuyarda Kukarbi Bashi daga Garesu Duk Matsin Rayuwa Saidai Idan Zakuyi Trade By Barter. 👉Ku Sanya Masana Akan Dukkan Wasu Muqaman Gofnati Ba Jahilaiba Kuma Masu Addini Ba ‘Yan Duniya ba. Akwai Dalilai Dayawa Amman Zantsaya Anan Domin Kada Rubutun Nawa Yazamto Najashi Yayi Yawa Anan Nake Cewa Daku Bissalam. Nine Naku Ismail Hussaini Alpholtawy

MASHAHURAN MUSULMAI DA SUKA FARA KIRKIRAN AIKIN LIKITANCI A DUNIYA


Kamar yadda nayi bayani a rubutu na farko Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin waɗannan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne.
Ga kadan daga cikin irin wadannan mashahuran Musulmin da suka fara kirkiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo:
~ Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD):Mutumin kasarFarisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu
gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa.
Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu. Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da guda dari. Fitacce a cikinsu shi ne “Al-Hawi”. wanda kundin bayanai ne a kan aikin likita da ya shafi magunguna da yadda suke aiki a jikinmu.
A wani shagube da ya taba yi wa wani mai maganin ciwon ido, wanda ya kawo masa magani don ya sa a idonsa, sai ya tambaye shi da ya yi masa bayanin yadda ido ke aiki amma ya kasa, don haka ya ce maganin karya ne. Wannan ne ke mana tuni da taka-tsan-tsan wajen sayen magunguna a wurin jahilai.
~ Ali Ibn Abbas: Haly Abbas (920-994AD): Shi ma daga Farisa ya fito kuma ana ji da shi a duniyar likitanci. Ya ba da gudunmowa ta hanyar rubuta littattafai cikin harshen Larabci, wadanda suka fi bayani a kan bangaren kwakwalwa da cututtukanta da bayanan falsafar binciken kimiyya irin na zamani.
~ Abul kasim Al-Zahrawi: Abulcasis (936- 1013AD): Wanda yake Balarabe ne wanda aka haifa a kasar Spaniya. Ya yi fice wajen zama likitan tiyata na farko na zamani a duniyar Musulunci saboda kirkiro kayan aiki na leka
wurare da dama na jikin mutum da ya yi, fiye da dari biyu, wadanda daga su ne aka kera na wannan zamani.
Shi ne kuma ya fara nuna wa duniya cewa za a iya samun juna biyu a wajen mahaifa saboda tiyatar da ya sha yi a wannan bangare.
Ya zama likitan Khalifan Musulunci a kasar Andalusiya, wato Khalifa Al-Hakam kuma ya rubuta littattafai da dama a kan aikin tiyata, wanda har yanzu akan samu manhajojin a littattafan wannan zamani. Domin karin bayani, za a iya bincikar Kitabut Tasrif.
~ Abu Ali Ibn Sina: Abicenna (980-1037): Shi ma mutumin kasar Farisa ne, wanda yake da baiwar kaifin hadda da tunani mai zurfi.
Ya haddace Alkur’ani yana dan shekaru goma kacal, sa’annan ya zama likita yana dan shekara sha shida. Ya yi aikin duba marasa lafiya kyauta a wannan birni kuma ya zama babban likitan Khalifan garin.
Daga baya ya yi hijra ya nufi yamma, inda a hanya ya rubuta kundaye a kan bayanai na kula da lafiya da aikin likita, ya kuma koyar da dalibai.
Wannan kundi wanda ake kira ‘kaanun fid dibb’ an dade ana amfani da shi a jami’o’in kasashen
yamma na wancan lokaci, a matsayin littafin koyarwa.
~ Ga kuma irinsu Ishak Al-Ruhawi dan kasar Turkiya, wanda ya fara bayani a kan tarbiyyar likitoci; wato yin tsantseni da taka-tsan-tsan a kan aikin likita da hukuncin da ya kamata a ba likitoci masu ganganci da aiki a cikin littafinsa mai suna ‘Adab Al-Tabib.’ Shi ne kuma ya fara bayanin cewa kowane sabon abu aka samar a kimiyyar likita, dole a samu wasu kwararru a aikin su zurfafa bincike don tabbatar da sabon bayanin ko karyata shi.
~ Sai kuma wasu da dama irinsu malaman wadannan da muka lissafa wadanda ba su yi fice kamar dalibansu ba. Misali, malamin Al Razi, Abu Hassan Al-Tabari, wanda ya yi fice a harkar lafiyar yara.
~ Akwai kuma irinsu Abu Alhassan Ibn Al-Nafis, likitan kasar Suriya wadanda Turawa ma ba su sani ba ko kuma suka sani amma suka ki ambatonsu.
Shi ne wanda ya fara bayanin yadda jini ke zagaya jikinmu, tun kafin ma a haifi Baturen nan William Harbey, wanda suka ce shi ya fara wannan bayani.
Ya Allah ka tabbatar damu akan daidai kasa Aljannar Firdausi itace makomarmu.

واَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

TARBIYAR MATASA

•••°°°TARBIYAR MATASA°°°•••

Godiya ta tabbata ga ALLAH madaukakin sarki, Tsira da amincin ALLAH su tabbata ga fiyayen Halitta, kuma cikamakin ANNABAWA DA MANZANNI, shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa tare da mabiya sunnah har zuwa ranar qarshe.
Bayan haka ‘yan uwana ina mai farin cikin gabatar muku da wannan muhadara wanda na sanya mata taken ★TARBIYAR MATASA★ badon wai na iya ba, ba kuma don nuna qwarancewa ba a’a kawai dai ina ganin ya kamata mu rinqa tattaunawa abisa matsalolin rayuwarmu ta yau da kullum.

•••WANENE MATASHI???•••
MATASHI shine (Almukallab) wato baligi wanda shari’a ta hau kansa, shine wanda idan yayi aiki Nagari za’a rubuta masa ladan aikinsa haka kuma idan yayi mummuna nan ma za’a rubuta masa abunda ya aikata acikin littafinsa.

°FARKON ABINDA YAKE WAJABA AKAN MATASHI° Farkon abinda yake wajaba akan matashi shine yayi imani da ALLAH ma’ana ya kadaita ALLAH shi kadai ya kuma shaida Muhammad bawan ALLAH ne kuma Manzon sa ne (SAW), kuma yayi imani da littatafanda ALLAH ya sauqar kuma yayi imani da qaddara mai kyau da maras kyau, kuma ya san da cewa akwai kwanciyar kabari akwai kuma tambayoyin cikin kabari akwai tashin alqiyama akwai hisabi akwai sakamako akwai tsallaka siradi, akwai wuta akwai aljannah. Kuma ya san cewa duniya gidan aro ce, lahira ita ce gida na gaskia ya kuma kyautatawa mahaifansa, kuma ya tsaida ibadarsa kamar yadda aka umurci dan Adam.

••TA YAYA ZAI ZAMA NAGARI GA AL`UMMA???••
Dole ne sai matashi ya kiyaye abubuwa muhimmai na rayuwa wa enda matuqar yana son ya zamanto matashi daga cikin matasa ingantattu kuma nagartattu, sai ya kiyaye addininsa, sai ya kasance mai Hakuri, mai ladabi, mai biyayya, mai neman ilimi, mai kauracewa alfasha, mai girmama na gaba dashi, mai tunani kafin aiwatar da wani abu mai neman shawara kafin gabatar da wani abu, mai sada zumunci mai yawan tausayi, mai gudun duniya, mai dogaro da kansa da neman abun kansa ta hanyar halak, wadannan abubuwa da muka lissafa sune zasu karfafa ★TARBIYAR MATASA★.
Ita dai TARBIYA ta samo asali ne daga tushen iyaye, Tarbiya tana ginuwa ne daga samun uwa tagari domin ita ke kasancewa makaranta ga ‘yayanta. Shiyasa Annabi MUHAMMAD (SAW) yayi umurni da a auri mace ma’abociyar addini domin kasancewar saita san addini sannan tasan yadda zata yi ta tarbiyantar da ‘yayanta.
A yau mun wayi gari Tarbiyar Matasanmu yana gur6acewa ta hanyoyi da dama a wannan zamani da muke ciki.★TARBIYAR MATASA★ tana samun matsala daga manyan mutane walau masu siyasa walau sarakuna ta hanyar amfani da matasa a wannan lokaci da suke yi na haddasa gaba da qiyayya a tsakani, da yin qoqarin aiki da matsa wajen basu makamai don kashe musu abokan gabansu wannan ba daidai bane. Ya kamata MATASA suyiwa kansu fada kuma su duba duk sanda aka umurce su da kai hari na kisa ba zaka ga daya daga cikin ‘yayan wanda suka tura su don ta’addancin ba, saboda haka mai zai sa su tsaya suna kashe junansu???, bayan ALLAH (SWT) yana cewa acikin suratul Anfaal: ( FATTAQULLA WA ASLIHU ZATA BAINIKUM WA’ADILLAHA WARASULAHU INKUNTUM MU’AMINEEN). Ma’ana:- (kuji tsoron ALLAH kuma ku daidaita tsakaninku kuma kubi ALLAH da Manzonsa idan kun kasance muminai)
Kuma ALLAH (SWT) ya qara cewa acikin suratul Hujurat :- (INNAMAL MU’UMINUNA IKHWATUN FA ASLIHU BAINA AKAWAIKUM WATTAQULLAHA LA’ALLAKUM TURHAMUUN). Ma’ana :- (su muminai yan’uwan juna ne don haka idan wani abu ya faru, to ku daidaita tsakaninku kuma kuji tsoron Allah ko a jiqanku) to saboda me matasa zasu rinqa kashe junansu.

•MATSALOLIN MATASA A YAU•
Yau an wayi gari MATASA sune shaye shaye, batsa duk wani abunda bayida kyau sai a samu MATASA ne suke aikata shi. Alal haqiqa ana samun iyayenda suke yiwa yaransu cikakkiyar tarbiya amma daga bisani sai yaran sufi karfinsu. Ba wani abu bane ke kawo haka illa zamantakewa na rayuwa a wurare guda (4) GIDA, MAKARANTA, KAN HANYA, ABOKAI wadannan abubuwa suke kawo illoli ga ★TARBIYAR MATASA★ a wannan qarni a wannan zamani da muke ciki.
Cudanyar Mata da Maza tana daga cikin hanyar lalacewar ★TARBIYAR MATASA★ musamman MATA zaku ga mace don tana ganin ta girma tana ganin tsayinta yayi daidai dana mahaifiyarta, tana ganin ta hadu da abokai na banza masu fure mata kunnuwa, to wallahi ki sani duk wani taqama da kikeyi a rayuwa da sanya damammun kaya masu fidda surorinki a bayyane tare da yin tozo da kanki kamar tozon raqumi wanda ake qira da a cuci gara saboda kina jin ke kin balaga kina jin tashe yana tashi a tare dake to wallahi kiji tsoron ALLAH. Domin Annabi MUHAMMAD (SAW) yace (Mata mafi yawansu ma’abota wuta ne, kuma Manzon ALLAH (SAW) Ya siffanta mata nau’i nau’i da ya gani acikin wutan jahannama, Wallahi Mata abun tausayi ne amma sai suka zama masu bijirewa baiwar da ALLAH yayi musu suka tsiri koyi da yahudawa da nasara. Abun mamaki wai Yarinya tasa Hijab har qasa ta fita sai kaji tace maka kunya take ji saboda tsantsar koyi da yahudawa.
Mafi yawan MATASA basa bada hankalinsu wajen karatun Addini kowa ka ta6a Boko, musamman mata zaku ga akan karatun boko tamkar zata kashe kanta, amma idan aka bincika wata zaka samu ko farillan al’awala bata sani ba, amma idan ka tambayeta Geography, Biology, chemistry zata yita kawo maka tamkar a qwaqwalwarta aka gina su, Haba Matasa !!!
Ina qara jan Hankalin ‘yan uwana Matasa dasu kiyaye Tarbiyarsu, su kula da rayuwarsu kada su shagala da wannan duniyar domin Annabi (SAW) yace: Duniya kurkukun Mumini ce kuma aljannar kafiri ce) Muslim ne ya ruwaito wannan Hadeeth din.
Kuma Manzon ALLAH (SAW) yayi qiran Matasa da cewa:- Yaku taron samari duk wanda yake da iko acikinku to yayi aure don yafi rintse ido kuma yafi kame farji, wanda kuma bai samu iko ba to na hore shi da yin azumi domin shi yana kashe sha’awa) (Bukhari da Muslim da Tirmizi da Abu Dawud da Nasa’i suka ruwaito wannan hadeethin). Ina Qara qira ga ‘yanuwana Matasa dasu kasance masu neman abun Hannunsu, ma’ana su kasance masu sana’a, domin fadin ALLAH (SWT) acikin suratul Naba’i :- (WAJA’ALNAN NAHARA MA’ASHA) ma’ana:- (Mun sanya muku rana domin ku fita ku nemi abinci). Kuma Manzon ALLAH (SAW) yace (ALLAH yana son mumini mai riqe da sana’a saboda ALLAH. Manzon Allah Ya qara cewa:- (Mafificiyar sana’a ita ce sana’ar mai akikin hannu idan yayi adalci) (Ahmad ne ya ruwaito wannan hadeeth din a musnadinsa).
Haka kuma bayani yaxo daga cikin Hadithin Abu-Huraira cewa an tambayi Manzon ALLAH (SAW) cewa wace sana’a ce tafi dadi??? Sai Manzon ALLAH (SAW) yace aikinda mutum yake yi da hanunsa da dukkan wani ciniki ingantacce (Ahmad ne ya ruwaito shi). Saboda haka ya kamata MATASA su kwadaitu ga yin sana’a kuma ayi sana’ar saboda ALLAH. Ina kuma qara qira ga ‘yanuwana matasa har da dukkan dan ‘adam da su guji KARYA, ZINA, SHANGIYA, ANNAMIMANCI, KASHE JUNA, GIBA (GULMA), RASHIN TAUSAYI, CACA, SON DUNIYA, YAUDARA da dai sauransu. Ina ganin wannan shine dan abunda ALLAH ya iyar dani wajen kawowa game da ★TARBIYAR MATASA★ ina kuma roqon ALLAH ya qara shiryar damu a bisa hanya madaidaiciya yasa muyi kyakykyawar qarshe.
Ina kuma roqon ALLAH dukkan abunda muka fada daidai ya hadamu gaba daya acikin ladan, abunda muka fada bisa kuskure kuma ALLAH ya gafarta mana daman ALLAH shine ya sani ba muba.

Daga:
Yar Uwarku
Faridah Bintu Salis
(Bintus~Sunnah)