AHLUSSUNNAH MUFARKA

DA’ACE KISHIN QUNGIYANCIN MU NA ADDINI NE DA MUN WUCE HAKA ACIGABA

      Ahlussunnah Mufarka
Jiya kotu a Kaduna ta wanke Amirul Jaish na rundinar shi’ah (IMN) Ibrahim Yakubu Zakzaky daga tuhumar da Gwamnatin jihar Kaduna ta masa, biyo bayan abinda ya faru a Gazwatu Hussainiyyah Zaria da sojojin janar Buratai a 2015
Ni abinda na fahimta lokacin da Gwamnati ta gindaya masa ne kawai yayi ta sakeshi da kuma tasirin da Zakzaky yake dashi a cikin wannan Gwamnatin, amma ba wai don ta rasa hujjar da zata cigaba da tsareshi ba
Sannan bayan matakin da kotun Kaduna ta zartar, har ila yau inda ace Gwamnatin Kaduna tana da niyyar cigaba da garkame Zakzaky da tayi hakan ta hanyar daukaka kara a kotun tarayya dake Abuja, kamar yadda dokar kasa ta tanadar
Zakzaky yana da manyan mutane a Kasarnan wanda suna da tasirin da zasu iya nema masa alfarma har a gurin shugaban Kasa, idan baku sani ba Zakzaky yana da Manyan Ministoci har guda biyu a cikin wannan Gwamnatin wanda a baya har muzahara suna fita kafin a kafa Gwamnatin Buhari a 2015
Gareka Musulmi Ahlussunnah, ka sani cewa ba ruwan Gwamnatin Nigeria bane ta yaki wani mutum saboda yana dauke da akidar da ta saba da ra’ayinta, shi tsarin kundin Constitution da yake rike da tsarin gudanarwan Kasa, fada ma yake da kowace irin akida ta Musulunci
Duk abinda ya faru da Zakzaky bai da nasaba da addini ko akida, zallar siyasa ce kawai, zargi ne marar tushe da ake cewa Kasar Saudiyyah cibiyar Ahlussunnah tana da hannu a abinda ya faru da Zakzaky
Jama’ar Musulmi da muke kiyayya da shi’ah ku sani cewa akwai babban kalubale a garemu idan bamu gyara, yawan da muke dashi ba zai taba amfanar mu ba, Ya ku Ahlussunnah me zai hana kuyi irin tsarin da Zakzaky yayi har ya samu karfi da kuma tasiri da ya mallaki manyan wakilai da yake dashi a kowace ma’aikata a Gwamnatin Nigeria?
Shin Ahlussunnah kuna da tsarin da kuke daukar nauyin karatun matasa masu fikra da basira a cikinku suna zuwa Kasashen turai suna karanta Medical Doctor, Pilot, Nuclear Physics, Astronomy, Mechanical Engineering, International Law, Computer Science, Ethical Hacking, Cyber Security da sauran fannonin ilmi masu tasiri a zamani kamar yadda Zakzaky yake yi?
Shin Ahlussunnah kuna da tsarin bangare a cikin da’awar Sunnah ko kungiyar Sunnah da yake da bangare na Likitoci Ahlussunnah, bangare na Malaman makarantar boko tun daga Primary har University, bangare na jami’an tsaro, bangare na siyasa, bangare na ‘yan kasuwa, bangare na ma’aikatan Gwamnatin tarayya da na jihohi da kananan hukumomi kamar yadda Zakzaky yake da wannan tsarin?
Ahlussunnah ba mu da wannan tsarin ko guda daya, an bar Ahlussunnah a baya, an bar Ahlussunnah da yiwa juna raddi da hassada, abinda ba za’a taba samu ba kenan a cikin da’awar shi’ah a Nigeria, idan kunga bangaren RAAF suna sukar IMN Taqiyyah ne, manufarsu daya ce
Tsarin da Zakzaky yayi ba shakka idan Allah Ya bashi tsawon rai sai ya kafa Gwamnatin shi’ah a Nigeria, domin Billahi yayi kafuwar da ya wuce tunanin duk wani mai nisan tunani, na rantse da Allah inda ace da’awar shi’ah abune mai kyau da na jima da zama ‘dan shi’ah, kuma da yanzu bana Kasarnan saboda girman gudunmawa da zan bayar a tafiyar, amma shi’ah ba abune mai kyau ba
Namu jagororin sun zama ‘yan duniya, sun fara nesanta kansu da da’awar Sunnah, tsarinsu ya koma irin na ‘yan duniya kawai, sun koma karya da yaudara da zakin baki, takaicin wannan abin yana matukar sanya ni kuka da zubar da hawaye
Halin da Musulmi Ahlussunnah muke ciki a yau ya kamata ya dinga hanamu bacci, ya zamto muna tunanin hanyar da zamu bi mu gyara kuskure domin mu tunkari abokan gaban mu
Yaa Allah Ka bamu mafita na alheri Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
Daga Malam Datti Assalafiy