AKAFA DAULAR MUSULUNCI DOMIN A TACE MASU SON ZICIYA A ADDINI

MUSULMI ATASHI AKAFA DAULA DAN SAMUN INGANTACCEN RAYUWA

inji Shahararren malamin salafiyyannan Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria.
   Hakika shugaba yayi wadannan maganganu da shawarwarin agurare Ma bambanta da majalisai dadama. Domin nuni garemu ga hanyar tsira. Dakuma koyi da magabata. Don samun rayuwa Mai inganci, da zamantakewar rayuwa Mai tsafta. Ba kamar yadda wasu ke daukar zancen awata mahanga. Da tunani irinta miyagun mutani ba.
Ga zancen malam;
Tsokaci kan batun malam:
    Saidai haryanzu banji wani shahararren mutum daga cikin malamai ko shugabanni daga cikin musulmiba wanda ke karfafa Zancen. Duk da cewar maganan maganice na ciwon dayake damun musulmin duniya baki daya. Saidaima wasu daga cikin miyagun mutane dasuke fassara zancen da wani salo nadaban, tayadda suke kokarin cire ma’anar maganan na hakika su shigoda wani al’amari nadabam.
    Gadai Maganan da malam yayi;
Mal. Yace ”Yakamata musulmi su kafa daula Dan gujewa hadarin dake gabansu, na miyagun hare_haren yahudawa”
Abinda malam ke nufi anan shine.
Shi cigaban addini dole saida kafa  daula dakuma tabbatar da Shari’ah. domin tabbatar da Shari’ah shiyake saukakewa mutani  hanyar rayuwa Mai inganci. Shi Kuma kafa daula shine hanya mafi sauki Wanda zai tabbatarwa da mutani yancinsu. Tayadda gudanarwar rayuwar Musulmi zaizamto tsararrene, Ga Shugabanninsu. Koda aharkar da’awace da karantarwa, zai kasancene karkashin wannan hukumace, matukar lamarin addini za’a karantar.
   Ko kataba tunanin meyasa Turawan yamma suke gaba da Musulunci? To ga ansarka;
  Burinsu aduniya yazamto babu Mai iko saisu, tayadda zasuyi dukkan abinda sukeso batareda wani yayi musu inkariba.
   Shi kuma musulunci akodayaushe Adalci yake tabbatarwa ga mutane. Haka kuma idan akace za’a kaddamar da Shari’ah za agusar da Al’adunsu asanya abinda Allah yahukunta Wanda kuma yasha bamban da son Zuciyarasu. Kuma Shine ainihin adalci, duk mai inkari akan haka yadauki Alqur’ani yakaranta, Zaiga tsagwaran adalci. Sa’banin son zuciya dakuma Zalincin turawa na constitution, wanda muke anfani dashi amatsayin hukunci ayanzu. Dashi suke amfani su saka dukkan wata son zuciyar na burin dasuke so su cimma akasanku saisu fake dacewa sunkawo muku tsarin hukuman, dana shugabanci kuma wai Afadinsu shine dokokin kasa wadanda za’ayi amfani dasu. Wanda ahakikanin gaskiya akwai duk abinda muke bukata acikin Alqur’ani da Bible. Nadaga tsarin rayuwa dana shugabanci, domin wannan shine dokar Allah wanda ya shinfidasu ga bayinsa.

Idan mukayi dubi ga maslahar kafa daula kuwa. Misali mafi sauki Shine Inda zamuyi dubi ga Al’umomin damuke rayuwa acikinta.
        Abinda zamu lura anan dai shine Kowace kasa tanada sojoji dasuke karkashinta tareda shugabanni mabambanta. Shugabannin nan sune ke tsara dukkannin doka da tsarukan cigaban kasar. To inaga musulunci. Wanda danshi mukazo duniyar kuma yatara makiya kota ina. Inbabu shugabanci bazamu Taba sanin ina muka dosaba. Saidai muta dimuwa da fagabniya tayadda zasu cigaba da kashemu dakuma kiranmu dasunan yan ta’adda. Idan da zakayi bincike kashi saba’in da biyar cikin Dari (75%) Na mutanen da yan ta adda ke kashewa ayanzu Musulme ake kashewa. Amma kuma musulmi ake daura wa Alhakin kisan, dakuma Kiran musulunci da Sunan addinin ta’addanci da ‘yan ta’adda. Domin Akan samu wasu lalatattu da basusan mecece hakikanin addiniba, Suna fakewa da sunan jihadi Suna ta’addancinsu abisa son zuciyarsu. Don wata maslahar rayuwarsu ta duniya. Kuma suna kiran kansu musulmi, Sabida Musulmi basuda manya hukumance waanda dazata karyata wannan al’amarin yasaka, ake tafiya ahaka batare da angyaraba.

     Indagaske musulmaine yan ta addan danme za ake kashemu Kamar kisan kiyashi. Adasa boma_bomai akona masallatanmu dasunan ta addanci. Kawai Rashin Tabbatar da daulane dakuma Rashin samar da daularma gabaki daya. Tayadda wasu zasu fake dasunan jihadi suna kashemu sa’Annan akuma daura alhakin kisan agaremu. Don rashin samun wadanda zasuyi jagora gurin fada da Al’amarin acikin hukumomin duniya.
        Kada rayuwar holewa na turawan yamma yaburgeka ka manta da addininka ko police kasamu amatakin hukuma, Matukar kai musulmine kaji aranka aikin musulunci zakayi. Inzamu dukufa dakawunanmu duk yawan kafiran duniya koda sun nunkamu sau dubune basu isa suyimana abinda Allah bai So Ba, Sai abinda Allah yanufa akanmu shine zai samemu. Kada abin duniyarsu ya tsole maka ido har ka aminta da wani mummunar manufarsu akan Al’umar musulmi. Koda Kai ba musulmi bane to inba ayankinsu kakeba to hakika Kai abin Hari ne garesu kuma sai sunyakeka ta kowani bangare na rayuwa.
   Abin Lura garemu musulmi.
Allah yafada mana acikin Alqur’ani. Wadannan mutane bazasu gusheba suna yakarmu ta kowani ‘bangare harsai munyi ridda munbar addininmu. Kuma kada mumanta da Cewa Su wadannan kosu kyautata ko Akasin Hakan, Allah yayi alkawarin basu duniya Don ita duniya ta kowace, Lahirace ta Wanda Allah yazaba. Kuma duk Wanda yanemi duniya zaisamu. Amma abinda muka sani Su musulmi sunada iyaka awajen nemansu. ba nema mukeyi ta kowani bangareba. Tayadda mukan bambance halal da Haram wannan yasa arzikin musulmi yasha bamaban da turawan yamma dama sauran Al’umomin duniya. haka tsarin rayuwarmu shima ya bambanta dasauran wasu addinai.
Daga Alqalamin
✍️Ismail Hussaini Adam Assalafy
Whatsapp: 09047958802
Instagram: ismailhussein511
Email: hussainiismail257@gmail.com
     ALLAH kadaukaka musulunci da musulmi, ka qasqantar da kafirci, da kafirai, ka dirkake maqiyanka maqiya addininka kataimaki bayinka na qwarai.
4/Ramadhan/1442 Hijiri
16/April/2021 Miladi

KADA MU DEBE TSAMMANI GA UBANGIJI

ALLAH YANA DA MAFITA GAMEDA DUKKANIN WATA MATSALAR DA TAKE DAMUNKA.

Koda yaushe muna yin tunani ne akan yawan matsalolin da suke damun mu ne a rayuwa, muna mantawa da cewa lallai fa haƙiƙa Allah yana da mafita daga dukkanin kowace irin matsalar da ta dame mu a rayuwa.

A rayuwa idan muka fuskanci Allah maɗaukakin sarki, muka koma gareshi da tuba cikin nadama da ƙas-ƙantar da kai, haƙiƙa Allah zai saurare mu, zai kuma yaye mana dukkanin damuwa da take damun mu ko ba-daɗe ko ba-jima, musamman idan munyi haƙuri mun kuma toge akan biyayya ga Allah ta’ala.

Muji tsoron Allah, sai Allah ya warware mana damuwar mu, mu kauce ma saɓonsa, sai yaji ƙanmu, kada mu bari shaiɗan yayi tasiri akanmu ya shiga tsakanin mu da ubangijin mu Allah ya kuma halaka mu ƙarshe mu zamto ababen yin nadama a ranar ƙiyamah.

UWA TA GARI

UWA TAGARI SA’AR YA’YA.

“Wallahi dukkanin wani jin daɗin da kake dashi a wannan duniyar matuƙar aka ce baka mori uwa ba, baka yi sa’ar samun uwa tagari ba, to haƙiƙa jin daɗinka ragagge ne”

“Dukkanin uwar da zata yawaita addu’ar alkhairi ga ƴa’ƴanta, zata kame bakinta daga zagi da aibanta su da kuma tsinuwa a garesu, to haƙiƙa wannan itace uwa tagari ga ƴa’ƴanta kuma mai bawa al’umma kariya ce, domin idan ta tsine musu ba iya ita kaɗai zasu dama ba, hatta jama’ar waje suma sai sun addabe su, sabida ita tsinuwar uwa akan ƴa’ƴanta haƙiƙa ba ƙaramar illa bace, sannan kuma idan tayi musu addu’ar alkhairi suka zama na ƙwarai to lallai ba iya ita kaɗai zata mora ba, hatta ma jama’ar waje sai sun amfana dasu, sabida haka ki zamto uwa tagari ga ƴa’ƴanki”

“Lallai uwa tagari bata la’antar ƴa’ƴanta, kana kuma bata la’antar na wasu, domin dukkanin uwar da zatayi riƙo da ɗabi’ar la’antar ƴa’ƴan wasu, to haƙiƙa wataran itama za’a la’anci nata, koda kuwa ba’a la’anci natan ba, to watarana da kanta zata la’ance su tunda bakinta ya saba da la’antar na wasu, amma idan ta zamto tagari mai yawan addu’a ga ƴa’ƴanta, to haƙiƙa inshaa Allahu sai Allah ya basu kariya a duk inda suke saidai idan jarabawar Allah ta sauka a garesu gameda wani ibtila’in rayuwar”

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYAS

Tarihin Shehu Ibrahim Inyas

Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy

Dafarko dai Mai Karatu Zanfara da sunan ALLAH ﷽

Mun manta da tarihi Saikawai Labaran Duniya dakuma Kallace_Kallacen Film, Har wasu daga cikin Daliban Wannan bawan Allah din Sheikh Ibrahim Inyas mabiyansa Na Tijjaniyya Da Faidha. Basusan Tarihin Nasaba Saidai kawai Sunsan Littattafansa Wadanada yarubuta Kamarsu Kashiful Ilbasi, Dama Dawawinu_Ssittah. dama Sauran Littattafansa na Abyat.

اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

Dafarkodai Sheikh Ibrahim inyas dai Asalinsa dan kasar Sanganiyane Agarin Kaulaha. Bayan Rasuwar Mahaifinsune alokacin da Sheikh Amadu Tijjani yazo yimasu Ta’aziyya, Sai Yanemi da da abashi dakin Soro domin Larabawa basa juran Zafi. Yayansa Muhammadu Khalifa wanda Shine Magajin Mahaifinsu a fannin Khalifanci na Wannan Zawiyyan, Sai yace dashi ga dakin Ibrahim Shine Soro kuyi masa Iso dashi, Bayan Ankaisa ga Dakinne Sai Ibrahima Inyas yanemi Zai fita daga dakin. Ananne ya qaddamar Masa da Quudirinsa na zaban dakin Soro. Dominsane shi Inyas. Sunyi Maganganu dai awannan daren Ahmadu Tijjani da Ibrahim inyas Amma na bibiyi tarihohin Marubuta banga abubuwan da suka tattauna ba azancen su na wannan daren. Sai dai wasu Suna Cewa Awannan Darenne yabashi Khalifanci na Qadmin Gausiyya. Allahu akbar! Bayan Lokacin Maulidi yazagayo🕦 kowa ya hallara an dagashi (inyas) domin Gabatar da Yabo sai yayi Magana kamar haka.

ومن یحبنی ومن یرانی فی الجنة

Fassara:
Dukkan wanda yasoshi ko ya ganshi To dan Aljannah ne.

Hmm Tabdijam, Gaskiya Wannan Zance yayi Nauyi dayawa, Idan Har ya Tabbata ya fadi Wannan zance to Gaskiya ba maganan ajizanci wannan Son Zuciyane. Inkuma Qage akayi masa to malaman Dariqu kaf dinsu Makaryatane domin Wannan Zantuka nacikin Littattafan Dariqu dadama.

Bari Muci gaba da Tarihi.

Bayan Wannan zancen Nasane fa Ruwa yafara kaiwa rana, tsakaninsa da yayansa Muhammad khalifa inda yayi masa inkari gamida fusata Yace dashi. Banine khalifan Baban kuba.

Saiyace kwarai kuwa kai kahlifan Baban mune, Nikuma khalifan Amadu Tijjani, Kuma Khalifan Manzon Allah.

Daganan fa aka fara gwabza rikici cikin Sabani da rikicin Khalifanci. Wasu marubutan Suna cewa har Guba Ansakawa Inyas a Abinci kuma yaci amma bai mutuba.
An koreshi daga Garin Kaulaha ta Kasar Sanganiya, Inda yakoma Koci yakafa daular Zawiyyarsa awannan Sauran ta Gonar Koci. Sheik Ibrahima Yasha gwagwarmaya Arayuwa Sosai duk asanadin wannan muqamin nasa na Gausiyya. Amma Allah ya tseraddashi daga dukkan tuggu.

ZUWANSA NIGERIA

Sheikh Ibrahim Inyasy yazo Nigeriyane ta sanadin wani Sarkin Kano Dan Tijjaniyya wanda dayayi Rokon Allah yabashi damar Zuwa hajji Sannan yahadashi da Gausin Zamani.
Bayan Allah ya cika masa Burinsa na Zuwa Saudiyyane Sai yahadu da Sheikh Ibrahim inyas Na Kaulaha. Dagan suka Gaisa Yakuma rokeshi da Neman Alfarma na cewa yazo kasar sa ta Nigeria.

Awannan lokacin yaso zuwa Amma sai aka samu akasi akan Rikicin da duniya takeyi Na yakin duniya na biyu.
Sai bayan wannan lokacin kafin yazo Sannan yazo tareda Littattafai yarabawa malamqn Tijjaniyya na Nijeriya. Malamai Sun Sallama masa Saida malami guda dayane yayi mar tawaye.
Amma shima daga baya ya sallama.

Daga wannan lokacinne Sunansa yakarade nigeria kuma yasamu Martaba da kuma Muqami sosai daga cikin maluman cikinta mabanbanta.

Wannan Shine kadan daga Tarihin Sheikh Ibrahim Inyas Shugaban Dariqar Tijjaniyya Khalifan Sheikh Amadu Tijjani.

Muna Rokon Allah ya Dawwamar damu akan bin Tafarkin Sunnah da bin Sunnah duk wuya duk dadi Allah ka karamana ikhlasi da Istiqaama akan Shiryayyen addininka. Da bin Annabinka dakuma bin Sahabbansa Salafussalih. Allah kayi Tsira ga Manzonka Annabin Rahama. مُحَمَّد ﷺ

واَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎