ARBA UNA ANNAWAWI

Hadisi Na 2

عن عمر رضي الله تعالى عنه أيضاً قال: بينما نحن جلوس عند رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم إذ طلع علينا رجل شديد بياض الثياب شديد سواد الشعر لا يرى عليه أثر السفر ولا يعرفه منا أحد، حتى جلس إلى النبي صلى الله عليه وسلم فأسند ركبتيه إلى ركبتيه ووضع كفيه على فخذيه وقال: يا محمد أخبرني عن الإسلام، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: الإسلام أن تشهد أن لا إله إلا الله وأن محمداً رسول الله، وتقيم الصلاة، وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان، وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلاً قال: صدقت، فعجبنا له يسأله ويصدقه.قال: فأخبرني عن الإيمان، قال أن تؤمن بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر، وتؤمن بالقدر خيره وشره، قال: صدقت، قال: فأخبرني عن الإحسان، قال أن تعبد الله كأنك تراه، فإن لم تكن تراه فإنه يراك،قال: فأخبرني عن الساعة، قال ما المسئول عنها بأعلم من السائل، قال: فأخبرني عن أماراتها، قال أن تلد الأمة ربتها، وأن ترى الحفاة العراة العالة رعاء الشاء يتطاولون في البنيان ثم انطلق فلبثت ملياً ثم قال يا عمر أتدري من السائل؟ قلت: الله ورسوله أعلم، قال فإنه جبريل أتاكم يعلمكم دينكم» .رواه مسلم.

An karbo daga sayyidina Umar kuma, Sayyidina Umar yace; wata rana muna zaune awajen manzon Allah s.a.w, sai wani mutum ya bullo muna yana da tsananin farin tufafi, yana da tsananin bakin gashi, ba’a ganin alamar tafiyar a tare dashi, kuma babu wanda ya sanshi a cikin mu (Sahabbai), har ya zauna wajen manzon s.a.w ya hada gwiwowinsa zuwa ga guwayyun Annabi , ya dora tafin hannayensa akan cinyarsa sannan sai yace; yakai Muhammad ka bani labari gameda addinin musulunci, sai manzon Allah s.a.w yace: “Abinda a addinin musulnci shine; ka shaida cewa babu wani abin da ya cancanta a bautawa in banda Allah, kuma ka shaida cewa Muhammad manzon Allah ne, ka tsaida Sallah, ka bada zakka, ka azumci watan ramadana, ka ziyarci dakin Allah, idan hanya ta sauwaka gareka”. Sai yace; ka fadi gaskiya sai mukayi mamakin wannan mutumen, shi yake tambayar manzon Allah kuma yana gasagatashi, sai yace; ka bani labari gameda Imani, sai manzon Allah yace “kayi Imani da Allah, kayi Imani da mala’ikunsa, da littaffansa, da manzanninsa, da ranar karshe, kuma kayi Imani da kaddara Alkhairinsa da sharrinsa, sai mutumen yace ka fadi gaskiya, sai yace ka bani labari gameda Ihsan (kyautatawa), sai Annabi yace “ka bautawa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa, to Shi Allah yana ganinka”, sai yace ka bani labari gameda sa’ar karshe(ta duniya), sai manzon Allah yace “wanda ake tambaya baifi mai tamabaya sani ba”, sai yace to ka bani labarin Alamominta, sai Annabi yace “baiwa zata haifi uwar gijiyarta, zaka ga huntaye, marar sa sutura, talakawa (wadanda basuda takalma da sutura isassu), masu kiwon dabbobi, suna gasa wajen gina manya manyan gidaje, sai Umar yace; sai wannan mutumen ya tafiya tai, sai na jira wani dan lokaci, sannan Annabi yace man “yakai Umar shin ko kasan wannan mai tambayar?” sai nicce Allah da manzonsa su sukafi sani, sai Annabi yace “ai mala’ika Jibirila ne, yazo muku ne domin ya karantar daku addininku” [Muslim ya ruwaitoshi]

My recent post