Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers

Nasarorin Da Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Samu Cikin Shekaru Biyu, July 2020, Zuwa July 2022

Ga wasu daga cikin nasarorin shekarar farko July 2020 zuwa July 2021;

  • Ƙungiya ta samu karɓuwa a wurin al’ummar yankin Arewa.
  • Haɗin kan Marubutan yankin Arewa.
  • Magana da murya guda a madadin dukkannin Marubutan Arewa.
  • Kare martabar yankin Arewa, da al-ummar yankin, kan ƙalubalen da suka dinga fuskanto yankin.
  • Wayar da kan al’ummar Arewa game da abubuwan da zai amfane su, da wa ‘yanda ba za su amfane suba.
  • Wayar da kan al’ummar Arewa game da kin shiga zanga-zangar EndSars, da ‘yan kudancin Najeriya suka yi a shekarar 2020 wanda ya kusan zamowa fitina.
  • Daƙile manyan labaran ƙarya kafun su yi tasiri a cikin al’umma.
  • Nasarar da ƙungiya ta yi wajan tallata “Ranar Arewa” 20 July 2020 na kowace shekara, bayan wasu masu kishin yankin sun kirkireta, don tunawa tare da jawo hankulan manyan Arewa kan dukkannin kalubalen da yankin ke fuskanta.
  • Koyawa Marubuta yadda ake rubutu, tare da saka Gasa domin zaburar da Marubutan Arewa a wasu daga cikin jihohin Arewa.
  • Jawo hankalin hukumar WAEC a shekarar 2020 kan saka lokacin zana jarabawa a daidai lokacin da musulmai suke gudanar da Ibada a ranar Jumma’a, daga karshe hukumar ta gyara lokacin.
  • Jawo hankalin gwamnatin jihar Jigawa kan ƙalubalen da talakawa zasu fuskanta, idan aka daina karatu kyauta a Jami’a mallakar jihar (Free Education) bayan majalisar jihar ta yi yunƙurin mai da tsarin biyan kuɗi mai yawa ga dukkannin daliban jihar.
  • Jawo hankalin gwamnatin Tarayya da jihohi akan Tallafawa al’ummar da iftila’in ruwa ya shafa, a jihohi da dama na Arewa a shekarar 2020 da shekara ta 2021.
  • Jawo hankalin mahukunta dake da alhakin kunnawa manoman Rani ruwa a garuruwan Bunkure, Kura, Garin Mallan, Da Garin Karfi dake jihar Kano, bayan abinda suke nomawa ya fara bushewa saboda rashin ruwa.
  • Jawo hankalin gwamnatin jihar Adamawa wajan sasanta rikicin masu sana’ar adaidaita (Keke-Napep) a garin Numan dake jihar, duba da yadda dubunnan Al-ummarmu suka dogara da sana’an.
  • Jawo hankalin gwamnatin Najeriya da na jihohi game da halin rashin tsaron da ya addabi yankinmu na Arewa.
  • Jawo hankalin ‘yan kasuwa game da halin matsin rayuwa da al-umma suke ciki, sanadin tsadar Abinci.
  • Rubuce-rubuce tare da zaburar da matasa akan su tashi su nemi sana’a domin su dogara da kansu.
  • Tallafawa daliban makaranta da robobin cin Abinci guda 100 a jihar Zamfara.
  • Nasarar samun goyon bayan manyan Arewa Sarakuna, Dattawa, da sauran manyan dake kishin yankin Arewa, wurin gudanar da ayyukan kungiyar.
  • Gudanar da manyan taruka a wasu daga cikin jihohin Arewa da dama, domin haɗin kan Marubutan Arewa, tare da ƙarfafa zumunci a tsakaninsu don fuskantar duk wani ƙalubale da ya tunkaro yankin.
  • Jawo hankalin gwamnatin Najeriya kan ta gaggauta daukan mataki akan kisan kiyashin da ake yiwa ‘yan uwanmu ‘yan Arewa dake zaune a kudancin kasar.
  • Ankarar da gwamnati game da matsalar gurbacewar ilmi a cikin al’ummah.
  • Kira kirayen ƙungiya ga gwamnati kan a kawo ƙarshen satar yara a makarantu.
  • Jawo hankulan al’ummah kan muhimmancin ilimin ‘ya’ya mata.
  • Tunatar da al’ummah da faɗakar da su na tsawon kwanaki 30 na watan Ramadan a shekarar 2021.
  • Yunƙurin kawo ƙarshen bangar siyasa a kafofin sadarwar zamani.
  • Nasarar samun shiga gidajen Radio da Television a jihohi daban daban don bayyana manufar ƙungiya da kuma alfanun kungiyar.
  • Ƙungiya ta zaburar da dubban matasan Arewa kan su nemi basussukan da gwamnatin Tarayya take bayarwa domin dogaro da kai.
  • Ƙungiya ta samu nasarar ƙulla ƙawance da ƙungiyoyi mabanbanta don ciyar da yankin Arewa gaba.

SHEKARA TA BIYU

Nasarorin da ƙungiyar “Arewa Media Writers” ta samu a cikin shekara ta biyu da kafuwarta daga July 2021, zuwa July 2022.

Ga wasu daga cikin nasarorin;

  • “Arewa Media Writers” tayi nasarar kai koken al-ummar musulman garin Obajana dake Kogi, bayan ruwan sama ya lalata tsohuwar maƙabatarsu, har sarkin Obajana Kirista Engr. Dr Idowu Isenibi, Oba Of Obajana ya baiwa musulman garin Obajana makeken Fili Hetka 10 da samun gudumuwar kudi sama da miliyan daya da rabi.
  • Ƙungiya ta wayar dakan al-ummar Arewa, tare da kira ga al-ummar Arewa da su yi ragistar katin zabe a lokuta daban daban, duba da yadda ‘yan kudancin kasar suka yi mana fintinkau.
  • Ƙungiya ta dau nauyin horar da ‘ya’yan Ƙungiyar wajan koyar da su yadda ake rijistar katin zaɓe ta yanar gizo-gizo a wasu daga cikin jihohin Arewa.
  • Ƙungiya tare da hadin guiwar babban dakin karatu na jihar Kano ta yi nasarar bawa mutane 131 horo akan loyar da su ilimin na’ura mai kwakwalwa.
  • Jami’ar koyar da harsuna ta kasa da kasa “International University of Languages” (IOUL) dake jihar Sokoto ta dau nauyin koyar da membobin kungiyar “Arewa Media Writers” ilimin sanin aikin yaɗa labarai a zamanance “Social Media in ICT” tare da basu Certificate na shaidar karbar horo.
  • Kungiya ta ziyarci tsangaya tare da raba kayan tsaftace muhalli da kayan shayi a babban birnin Tarayya Abuja.
  • Ƙungiya ta bada gudummuwa wurin ganin an raunata jaridar “Sahara Reporters” kan batanci da ta yiwa Annabi (SAW) da yankinmu na Arewa, wanda har yau bata da wo cikin hayyacinta ba.
  • Ƙungiya ta jawo hankalin gwamnati kan gyaran asibitin garin Garun Babba, dake karamar hukumar Garun Malam a jihar Kano, wanda shugaban karamar hukumar ya dau nauyin gyarawa.
  • Ƙungiya ta wayar da kan al’ummar Arewa game da abubuwan da zai amfane su, da wa ‘yanda ba zai amfane suba akan rayuwar yau da kullum.
  • Ƙungiya ta yi tattaki zuwa Abuja, ta kaiwa shugabannin hukumomin tsaron Najeriya budaddiyar wasika kan halin da al-ummar Arewa suke ciki na rashin tsaron da ya addabi wasu yankunan dake yankin, tare da jawo hankalin su da su ƙara zage damtse don ganin an kawo ƙarshen rashin tsaron da ya addabi yankin.
  • Kungiya ta yi nasarar turawa shugaban kasar Najeriya buɗaɗɗiyar wasiƙa, ta gidajen jaridun DAILY Trust, Blueprint, VOA Hausa, da sauran manyan jaridun ƙasar, kan halin da al-ummar Arewa suke ciki na rashin tsaron da ya addabi wasu yankunan dake yankin, tare da jawo hankalin shugaban ƙasar da ya ƙara zage damtse don ganin gwamnatin shi ta kawo ƙarshen rashin tsaron da ya addabi yankin.
  • Ƙungiya ta yi Nasarar rubuta Littafi mai suna “RAYUWAR SAMARI DA ‘YANMATA A SOCIAL MEDIA” wanda aka yi bikin kaddamar dashi a watan junairun shekara ta 2022.
  • Ƙungiya tayi nasar gudanar da taron bita akan amfani da kafofin sadarwar zamani a jihar Filato.
  • Ƙungiya ta ja hankalin matasan Arewa a lokuta da dama, tare da wayar da kansu akan su guji bangar siyasa, don gobensu tayi kyau.
  • Ƙungiya tayi nasarar rubuta littafi mai suna “matar bahaushe” dake dauke da darusa iri-iri, anyi akayi bikin kaddamar dashi a jihar Jigawa.
  • Ƙungiya tayi nasarar horar da membobinta “Excos” reshen jihar Sokoto na tsawon kwanaki uku “3 Days Seminer” akan yadda ake rubutu.
  • Ƙungiya ta gudanar da rubuce-rubucen jan-hankali masu yawa a gidajen jaridu da kafofin sada zumunta, game da cin kashin da ake yiwa ‘yan uwanmu ‘yan Arewa dake zaune a kudancin Najeriya.
  • Kungiya ta yi nasarar horar da marubutan Arewa sama da 500 game da yadda ake aikin jarida da rubutu a kafofin sada zumunta, tare da basu takaddar shaidar karɓar horo (certificate) wanda yanzu haka yake gudana. Insha’Allah kungiyar “Arewa Media Writers” za ta gudanar da irin wannan seminar din a kowace jiha dake Arewacin Najeriya, don horar da dukkannin masu amfani da kafofin sada zumunta a kokarin kungiyar, na tsaftace harkar rubuce-rubuce a kafofin sada zumunta.
  • Ƙungiya ta gudanar da Rubuce-rubuce masu amfani ga al-ummar Arewa, da ba za su ƙirgu ba, tun daga watan July na shekarar 2020 da aka kafata har zuwa yanzu July shekarar 2022.

Mamallakin Wannan Kafa Tareda Alhakin Sanya Rubutu Gamida Hada Manhajar (Appllication).

Danna Maballin da Aka Sanya Manhajar Tarihi, Domin Saukewa Yanzu.

Edited by

(Paper Presentation Committee)

Abdulrahman Suleiman Zaria

Chairaman

Muhammad Kwairi Waziri

Secretary

@Coded Prints 08137556140

Ameera Yusuf Duguri

Treasurer

Huzaifa Ayuba

Member

Bashir Abubakar Gombe

Member

Walida Hussaini

Member


Shared By

ISMAIL HUSSAINI ALPHOLTAWY

Member

Hakkin Sanyawa Awannan Pejin tareda Mallakar Peijin