GODIYA TA GA ALLAH BUWAYI


Ban Shan Sigari Ban Shan Moringa
Ban Shan 200 Kayan zamani Ban Leqa taga
Kayan Wani bai idona Ni nai ga Katanga
Shiga Sha`anin Wani banayi Cikin Garinga
Bana da Abokin Hamayya koda A Singa
Ni Ba Alfaharifa Nake Ba Sunce Banda Siga
Kawai Dan Bana Kula Mai haukar Marashin Balaga
Burina tarayya Damai Son Mutane ko a Daga
Komai Wuya Bai mantawa da Allah Garinga

Buwayi Jallah ne Yatsareni ga Dukkan Wauta
Shi ya Nufa Bana Daukan kayan wani Sata
Kuma Ya Horemin Baiwar Neman Azurta
Cikin Tsafta da Ilimi Babu Son Zuciyata
Meyakai Hakan Rabone ga Tambayata

Ga baiwa Basira nasam rabauta
Shin Wazai Samu Ilimi Kamata
Yakuma Tsarkaka ba Tozarta
DaSanin Falsafar duniyata
Cikin Nema Ba Qazanta
Kuma Yasan Hanyoyin Rabauta
Amma Dan Gudun Duniyata
Naki Duba Nai Nazarta
Da kyawun hali Ba Mugunta
Mutan Gari Na nufata da Cuta
Na Bisu da Kyawun Hali Mai tsafta
Kullum Cikin dare Har Safiyata
Bana Nufin Sharri dan Gabata

Matukar Jallah Yarubuta Zan Azurta
Ina Ruwana damai Duban Duniyata
Yai ta Qunci Cikin rai karya Huta
Yaitayi Dan Shine Zai Qaranta
Bamai Hanawa Koda da Cuta

Zasu barni In wala har na Huta
Duk Rintsi nafada Zan Azurta
Indai Buwayine ya Qadarta
Dan Shike Ayyada Qaddarata

Cikin Mafarki
Wallahi Cikin Mafarki Naganta
tana ta Raki
Tana fadin wai Nayi karatu Najita
Nabada Maki
Ahakan fa Nabata Maki na Sota
Taminni Kirki
Asalinta Naduba nayi Nazarta
So ne da Ba Raki
Asalin Furuci yasaka Nai Zumunta

Muryarta da Dad`i
Dana jishi Yasanya Na ´Dimauta
Nayi Matta Gargad`i
Abokina Nura Yagoyan Baya Gareta
Abin yasakani Zumud`i
Wallahi Da Murmushi fa Afuskarta
Dahakan naji Dad`i
Furucinta da Sanyi Nayi Nazarta

Zanen Zabo Da Shi Aka ganta
Kukan Kura Jawabi Najigata
Ra`ayin wani Babu Ni acikinta
Burina In Tabbatar da Halinta
Intana da Kirki Ni Zan Sota
Dama Na Ganta azahiri na Ganinta
Sannan Nafurta Abinnan na Huta
Na Kalmar Soyayya Zan Kirata
Sanna Nabita Da Furicin Qaunata

Na Yarda tana da Halin Kwarai
Domin na jita Garai Garai
Sannan Siffanta Sarai Sarai
Ba Mai Kinta Idan da Rai
Girma Zan Bata Cikin Tirai
Zafin Qaunarta idan da Rai
Zai Bi Jikina ya  Yata´b´ba Rai

Mai gaskiya Shi Ake gudu Awannan zamani

Mara Gaskiya madubin A’uma Oh na Bani

Indai Daranka Ayanzu kasha kallon gini

Wai Ta Tarbiya agidan giyane Jan Rini

Ga Zamani yayo Muni Maqurar Sani

In Laddabi Akayima To kai kasani

Bawanda Zaimaka banza inkai tini

Inmacce ce taga Kudine ko sabon zani

Ko ko Abinci takeso agareka kayo sani

Dan mai Bara da Rikon kwarya To kasani

Barar Zamani da Baki Akeyinsa da Bude zani

Kaima Kasani Ga Mai Kod’aka aran Yini

Amarsuce Take Wautar kukan dadi mundai Sani

Banza Nasha Na Wuni Da Qishi na Tuntuni

Bazanci Banza ba Ace Nakwan Dana sani