•••°°°TARBIYAR MATASA°°°•••
Godiya ta tabbata ga ALLAH madaukakin sarki, Tsira da amincin ALLAH su tabbata ga fiyayen Halitta, kuma cikamakin ANNABAWA DA MANZANNI, shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa tare da mabiya sunnah har zuwa ranar qarshe.
Bayan haka ‘yan uwana ina mai farin cikin gabatar muku da wannan muhadara wanda na sanya mata taken ★TARBIYAR MATASA★ badon wai na iya ba, ba kuma don nuna qwarancewa ba a’a kawai dai ina ganin ya kamata mu rinqa tattaunawa abisa matsalolin rayuwarmu ta yau da kullum.
•••WANENE MATASHI???•••
MATASHI shine (Almukallab) wato baligi wanda shari’a ta hau kansa, shine wanda idan yayi aiki Nagari za’a rubuta masa ladan aikinsa haka kuma idan yayi mummuna nan ma za’a rubuta masa abunda ya aikata acikin littafinsa.

°FARKON ABINDA YAKE WAJABA AKAN MATASHI° Farkon abinda yake wajaba akan matashi shine yayi imani da ALLAH ma’ana ya kadaita ALLAH shi kadai ya kuma shaida Muhammad bawan ALLAH ne kuma Manzon sa ne (SAW), kuma yayi imani da littatafanda ALLAH ya sauqar kuma yayi imani da qaddara mai kyau da maras kyau, kuma ya san da cewa akwai kwanciyar kabari akwai kuma tambayoyin cikin kabari akwai tashin alqiyama akwai hisabi akwai sakamako akwai tsallaka siradi, akwai wuta akwai aljannah. Kuma ya san cewa duniya gidan aro ce, lahira ita ce gida na gaskia ya kuma kyautatawa mahaifansa, kuma ya tsaida ibadarsa kamar yadda aka umurci dan Adam.
••TA YAYA ZAI ZAMA NAGARI GA AL`UMMA???••
Dole ne sai matashi ya kiyaye abubuwa muhimmai na rayuwa wa enda matuqar yana son ya zamanto matashi daga cikin matasa ingantattu kuma nagartattu, sai ya kiyaye addininsa, sai ya kasance mai Hakuri, mai ladabi, mai biyayya, mai neman ilimi, mai kauracewa alfasha, mai girmama na gaba dashi, mai tunani kafin aiwatar da wani abu mai neman shawara kafin gabatar da wani abu, mai sada zumunci mai yawan tausayi, mai gudun duniya, mai dogaro da kansa da neman abun kansa ta hanyar halak, wadannan abubuwa da muka lissafa sune zasu karfafa ★TARBIYAR MATASA★.
Ita dai TARBIYA ta samo asali ne daga tushen iyaye, Tarbiya tana ginuwa ne daga samun uwa tagari domin ita ke kasancewa makaranta ga ‘yayanta. Shiyasa Annabi MUHAMMAD (SAW) yayi umurni da a auri mace ma’abociyar addini domin kasancewar saita san addini sannan tasan yadda zata yi ta tarbiyantar da ‘yayanta.
A yau mun wayi gari Tarbiyar Matasanmu yana gur6acewa ta hanyoyi da dama a wannan zamani da muke ciki.★TARBIYAR MATASA★ tana samun matsala daga manyan mutane walau masu siyasa walau sarakuna ta hanyar amfani da matasa a wannan lokaci da suke yi na haddasa gaba da qiyayya a tsakani, da yin qoqarin aiki da matsa wajen basu makamai don kashe musu abokan gabansu wannan ba daidai bane. Ya kamata MATASA suyiwa kansu fada kuma su duba duk sanda aka umurce su da kai hari na kisa ba zaka ga daya daga cikin ‘yayan wanda suka tura su don ta’addancin ba, saboda haka mai zai sa su tsaya suna kashe junansu???, bayan ALLAH (SWT) yana cewa acikin suratul Anfaal: ( FATTAQULLA WA ASLIHU ZATA BAINIKUM WA’ADILLAHA WARASULAHU INKUNTUM MU’AMINEEN). Ma’ana:- (kuji tsoron ALLAH kuma ku daidaita tsakaninku kuma kubi ALLAH da Manzonsa idan kun kasance muminai)
Kuma ALLAH (SWT) ya qara cewa acikin suratul Hujurat :- (INNAMAL MU’UMINUNA IKHWATUN FA ASLIHU BAINA AKAWAIKUM WATTAQULLAHA LA’ALLAKUM TURHAMUUN). Ma’ana :- (su muminai yan’uwan juna ne don haka idan wani abu ya faru, to ku daidaita tsakaninku kuma kuji tsoron Allah ko a jiqanku) to saboda me matasa zasu rinqa kashe junansu.

•MATSALOLIN MATASA A YAU•
Yau an wayi gari MATASA sune shaye shaye, batsa duk wani abunda bayida kyau sai a samu MATASA ne suke aikata shi. Alal haqiqa ana samun iyayenda suke yiwa yaransu cikakkiyar tarbiya amma daga bisani sai yaran sufi karfinsu. Ba wani abu bane ke kawo haka illa zamantakewa na rayuwa a wurare guda (4) GIDA, MAKARANTA, KAN HANYA, ABOKAI wadannan abubuwa suke kawo illoli ga ★TARBIYAR MATASA★ a wannan qarni a wannan zamani da muke ciki.
Cudanyar Mata da Maza tana daga cikin hanyar lalacewar ★TARBIYAR MATASA★ musamman MATA zaku ga mace don tana ganin ta girma tana ganin tsayinta yayi daidai dana mahaifiyarta, tana ganin ta hadu da abokai na banza masu fure mata kunnuwa, to wallahi ki sani duk wani taqama da kikeyi a rayuwa da sanya damammun kaya masu fidda surorinki a bayyane tare da yin tozo da kanki kamar tozon raqumi wanda ake qira da a cuci gara saboda kina jin ke kin balaga kina jin tashe yana tashi a tare dake to wallahi kiji tsoron ALLAH. Domin Annabi MUHAMMAD (SAW) yace (Mata mafi yawansu ma’abota wuta ne, kuma Manzon ALLAH (SAW) Ya siffanta mata nau’i nau’i da ya gani acikin wutan jahannama, Wallahi Mata abun tausayi ne amma sai suka zama masu bijirewa baiwar da ALLAH yayi musu suka tsiri koyi da yahudawa da nasara. Abun mamaki wai Yarinya tasa Hijab har qasa ta fita sai kaji tace maka kunya take ji saboda tsantsar koyi da yahudawa.
Mafi yawan MATASA basa bada hankalinsu wajen karatun Addini kowa ka ta6a Boko, musamman mata zaku ga akan karatun boko tamkar zata kashe kanta, amma idan aka bincika wata zaka samu ko farillan al’awala bata sani ba, amma idan ka tambayeta Geography, Biology, chemistry zata yita kawo maka tamkar a qwaqwalwarta aka gina su, Haba Matasa !!!
Ina qara jan Hankalin ‘yan uwana Matasa dasu kiyaye Tarbiyarsu, su kula da rayuwarsu kada su shagala da wannan duniyar domin Annabi (SAW) yace: Duniya kurkukun Mumini ce kuma aljannar kafiri ce) Muslim ne ya ruwaito wannan Hadeeth din.
Kuma Manzon ALLAH (SAW) yayi qiran Matasa da cewa:- Yaku taron samari duk wanda yake da iko acikinku to yayi aure don yafi rintse ido kuma yafi kame farji, wanda kuma bai samu iko ba to na hore shi da yin azumi domin shi yana kashe sha’awa) (Bukhari da Muslim da Tirmizi da Abu Dawud da Nasa’i suka ruwaito wannan hadeethin). Ina Qara qira ga ‘yanuwana Matasa dasu kasance masu neman abun Hannunsu, ma’ana su kasance masu sana’a, domin fadin ALLAH (SWT) acikin suratul Naba’i :- (WAJA’ALNAN NAHARA MA’ASHA) ma’ana:- (Mun sanya muku rana domin ku fita ku nemi abinci). Kuma Manzon ALLAH (SAW) yace (ALLAH yana son mumini mai riqe da sana’a saboda ALLAH. Manzon Allah Ya qara cewa:- (Mafificiyar sana’a ita ce sana’ar mai akikin hannu idan yayi adalci) (Ahmad ne ya ruwaito wannan hadeeth din a musnadinsa).
Haka kuma bayani yaxo daga cikin Hadithin Abu-Huraira cewa an tambayi Manzon ALLAH (SAW) cewa wace sana’a ce tafi dadi??? Sai Manzon ALLAH (SAW) yace aikinda mutum yake yi da hanunsa da dukkan wani ciniki ingantacce (Ahmad ne ya ruwaito shi). Saboda haka ya kamata MATASA su kwadaitu ga yin sana’a kuma ayi sana’ar saboda ALLAH. Ina kuma qara qira ga ‘yanuwana matasa har da dukkan dan ‘adam da su guji KARYA, ZINA, SHANGIYA, ANNAMIMANCI, KASHE JUNA, GIBA (GULMA), RASHIN TAUSAYI, CACA, SON DUNIYA, YAUDARA da dai sauransu. Ina ganin wannan shine dan abunda ALLAH ya iyar dani wajen kawowa game da ★TARBIYAR MATASA★ ina kuma roqon ALLAH ya qara shiryar damu a bisa hanya madaidaiciya yasa muyi kyakykyawar qarshe.
Ina kuma roqon ALLAH dukkan abunda muka fada daidai ya hadamu gaba daya acikin ladan, abunda muka fada bisa kuskure kuma ALLAH ya gafarta mana daman ALLAH shine ya sani ba muba.

Daga:
Yar Uwarku
Faridah Bintu Salis
(Bintus~Sunnah)
You must be logged in to post a comment.