MUKULA DA DUNIYA

Ismail Hussaini Alpholtawy

AN BAMU ILIMI KYAUTA! MUN WATSAR! MUN SAYI JAHILCI DA KU’DINMU!

  Shin Mecece Makomarmu?
Halaka, Tabewa, Ko Asara !!!
ALLAH ﷻ Katsaremu.

        Shirmen Yahudu Muka Dauka Muka Shagaltu Da Abinda Ke Cutar da Rayukanmu, Na Shagaltuwa da Kida, Wakoki, da Kallace_Kallae, Mun Bar Da’irar Tsira Hanyar da Ake Rayar Da zuciyoyinmu Ana kashe Mana Kasala, Taskar Sani Dangujewa Jahilci Rumbum Asirai (Quran da Hadisan Annabi (S.A.W) }. Shiyasa Yahudu Ke Juya Zuciyoyinmu Yadda Sukaga dama

Zan Gina Wannan Rubutun Nawa Ta Hanyar Tuna baya, Atarihin Rayuwata Inda Abaya Na kasance Mai Sanin Darajar Kaina, Allah Ya Yassaremin Rayayyiyar Zuciya Tun Ina Karamina.
     Afannin ilimi babu Bajimta da Dalibi Zaiyi Amakaranta wacce zata gagareni (Ilimin Addini Dana Zamani) Balle Tafi Karfina. Yadda na zamo Fitila Atsakaninmu Dalibai Yasa Rayuwata Ta Bunkasa, Duk da halin Rashin Dama Amma Ina Alfahari dakaina, Akanyi kuma Tunkaho dani Akowace Sansani.
    Nakusan Yin Sakaci Bisa Samun damar Da ta Yanke min Buri, Alokacinda Ban Cika Hankaliba, Balle tunani Ya zakkemin. Kwatsam Sai Rauni Yafara Fisgata Bisa Ta’bar’barewar Zamani,  Nakasar Shagaltuwa Yafara Tabin Jinina Yafara Samin Kasala, Dakyar Na farka Daga Baccina. Lokaci ‘Kalilan Naji Shagalar Tawa Amma Sai da Nad’auki Dogon Zango Kafin Na Gyara Saitin Akalata, Dayardar Allah Saitin Ma’ajin Bayanaina Ayanzu Sun Kankama Tunda Hankali Yakusa Fara Zuwa (22Yrs Ba Wasaba), Tabbas fa Ashe Kowa Nada Hankali, Amma Aiki da Hankali Sai Da Dafawar Ubangiji.

To Taya Ubangijin Zai Dafa Mana Bayan Mun Butulce Masa?
Nidai (Ismail) Yarone,
Ina Manyan  Suke?‍‍
   Kutayani Duba Ance Kunada Hangen Nesa

Ni na Tabbata Bin Tafarkin Ma’aiki Da Yawan Ibada Itace Ke Raya Zuciyar Dukkan Wani dan Adam, Ba Shagalin Duniya Da Sha’anonin Rayuwa Na Shagala Ba.
Inka Kauracewa Shirmen Duniya Komai Ka Nema Agun Allah kuwa, Abinda ka Nema da kansa Zai kawo Kansa Wallahi Basaika wahalar da Gangar Jikinka ba. ALLAH Ne Yasanar Damu Hakan.
Duba Hadisul_Qudsi, Zakaga Ga Hujjana.

    Dalibi, Danuwa, Yaruwa, Aboki, Yana, Yayata, Iyayena, Yan Uwana Musulmi Ga Shawari Kyauta!!!

Mu Kauracewa Mummunar Dabiar Shagala Na Haukar Yahudawa Musamman Sauraron Kida Da Kallon Film Wai Domin Shagala Dan Cire Damuwa Abanzane, ‘ Wallahi ‘Karin Damuwa Nema’ Domin Acikinsa Ake Sauya Tunaninmu, Ake Kwashe Kaso Mafi Yawa Na Lokutan dayakamata Muyi Ibadojinmu Kuma Yana Disashemana Kaifin ‘Kwa’kalenmu, Ka dauki Littafan karatu Su Zamo Abinda kake Goge Hawayen Damuwoyinka Da Dawo Farinciki Idan ya gujemaka, Gamaiyin Hakan Kuwa Tabbas Ribarsa Babu Adadi.

Samun Sau’kin Rayuwa,
Gujewa halakar  Yahudawa,
Raya zuciya da cire Damuwa,

Fayyace Dukkan Mattsala,
Barin Sansani Na Jahilci zalla,
Fidda Jinyar jiki dama Kalsala,

Cire wa Kai Son Duniya,
Tarewa Atafarkin Shiriya,
Kaji Zancen Gobe Yau har jiya,

Babu Cutar Rai Ba Tsangwama,
Zallar Gaskiya ba Gardama,
Asalin Zance ba tantama,

Ba Ra’ayi Ga Sirrin warwara,
Alkairine  Ga Sanin Fikira,
Cire kwadayi da Takura,

Inkana Neman Zallar Tsarkaka,
Tarin lada Kuma Ga Haskaka,
Bi Islam Addininnannaka,

Wallahi Komai Akwai Amusulunci, Rashin Neman Na Addinine Yasa Muke Kwaikwayon Yahudu, Mutanen Da Dasu da Dabbobi Babu Maraba Mu’amalolinsu Kamar na Dabbobi,
Zina Agunsu Adoce,
Zubar da Jini Aikin sune,
Cin Hakikkin Wani Gatane,
Kin Bautar Allah Burinsune,
Raba Kan Mutane Halinsune,
Son Zuciya Agurinsu damane,
Shan Kayan Maye Dad’in sune,

      Amma Annabinmu Ya Nesanta Kuma Yatsawatar Garemu Akan Irin Wadannan Munanan Ayyukan Nasu. Tsarkinsa Ta Tsarkaka da Tsaftar Tsammanin Tsular Tsiyar dasuke Tsalawa Domin Tsageranci, Tsafatar Tsarkin Tsarkakakken Tsariran damai Tsari Ya tsareshi Ta Tsarkaka daga tsiyar Tsokanar da Tsagerun Tsinannun Yahudu Suke Tsulamasa.

Muna Sonka Annabinmu!!!
Masani, Lamani, Tsani, Sansani,
Ma’aiki, Sadauki, Tafki,
Jagaba, Shugaba,
Annabi.

مُحَمَّد ﷺ

         
Sirrin Yahudu Kenan Daga Alpholtawy (IHSAN) Writer