ALAKAR SHEIKH DR AHMAD GUMI DA MASU GARKUWA DA MUTANE
Kada kayanke Hukunci Sai Ka karanta Dukka
Bayan da Gwamnatin Nigeria karkashin jagorancin Maigirma shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari Maigaskiya ta dauke service network a jihar Zamfara domin sojoji su gudanar da aiki na musamman akan masu garkuwa da mutane da suka samo asali daga yankin Zamfara suka yadu zuwa wasu jihohin Arewa
Ance Sheikh Dr Ahmad Gumi yace bai kamata Gwamnatin Nigeria ta kyale sojoji suna ruwan wuta ta sama da kasa akan sansanonin barayin dajin Zamfara ba suna hallakasu mazansu da matansu da yaransu, Malam yace kamata yayi Gwamnatin Nigeria ta yiwa barayin afuwa kamar yadda ta yiwa tsagerun Niger Delta afuwa
Fadin wannan maganar naga jama’a suna ta kokarin cin mutunci da zagin Sheikh Dr Ahmad Gumi, har ma wasu suna kira cewa a kamashi, wai yana goyon bayan barayin bindiga, wannan ne ya bani karfin gwiwa domin nayi wannan rubutun
A hakikanin gaskiya duk wanda ya zargi Sheikh Dr Ahmad Gumi da alaka da ‘yan bindiga ko tarayya cikin ayyukansu na ta’addanci to mai wannan zargin idan har ba makiyin Musulunci bane idan ance yana da kwakwalwar jakuna ba laifi bane
Dr Ahmad Gumi sulhu yake jagoranta, kamar yadda aka taba samun wadanda ba Musulmai ba suka jagoranci sulhu tsakanin Gwamnatin Nigeria da tsagerun Niger Delta, aka taba samu har da turawa makiyanmu makiya addinin mu suka jagoranci sulhu tsakanin Gwamnatin Nigeria da ‘yan Boko Haram kan musayen ‘yan matan Chibok
Kowa ya tsaya yayi tunani, shin menene ya faru muka wayi gari fulanin jeji makiyaya suka dauki bindiga suka zama barayin jeji masu garkuwa da mutane?
Wanda bai san abinda ya faru ba to ga cikakken bayani
(1) Rashin adalci na wasu jami’an tsaron Gwamnatin Nigeria Azzalumai maciya amana shi ya tunzura fulanin jeji suka dauki makami suka zama ‘yan ta’addan dole
Wato idan wasu azzaluman jami’an tsaro suka shiga jeji neman barayin shanu, duk wani bafulatani da aka gani yana kiwo sai a kamashi ko a harbeshi a kora shanunsa, ana kashe iyayensu akan idon su, ana kama matansu ana musu fyade a kan idon su, wannan yasa sukace tunda bamuyi komai ba ana kashe mu ana kwace mana shanu to bari mu dauki makami muyi ta’addancin da tushe domin daukar fansa
Wallahi wannan shine farkon abinda ya jawo fulanin jeji suka zama ‘yan ta’adda, marigayi Alhaji Ali Kwara ya tabbatar da wannan a hiran da VOA Hausa tayi dashi, su kansu manyan Kwamandojin barayin daji sun tabbatar da wannan zalunci da wasu jami’an tsaron Gwamnati suka musu a farko, shi ya kaisu zama ‘yan ta’adda a yau
(2) Sannan sai sakaci da Musulmai sukayi: wato aka ki shiga jeji a karantar da fulani addini aka barsu cikin bakin duhu na jahilci, ‘yan bazata (Missionary) suka shiga suka canza musu addini, Faransa ta shiga ta karkashin kasa ta basu makami, Boko Haram da Ansaru suka hada kai dasu suka fara zubar da jinin al’umma ba gaira babu dalili
A takaice wannan shine abinda ya faru, sannan a ilmin tsaro an kasa nau’ukan ta’addanci gida hudu:
Cikin na’ukan ta’addanci guda hudu, uku daga cikinsu suna da saukin magancewa, kuma ilmin tsaro ya tabbatar da ana iya yin sulhu da su imbanda wanda suke ta’addanci akan akida ta addini wanda suke fatan su mutu a kai.
Fulanin jeji suna ta’addanci ne akan daukar fansa, ashe za’a iya yin sulhu da su idan sulhun za’ayi da gaske
An gwada yin sulhu da wasu barayin jeji amma ba’a sanya gaskiya a ciki ba, kuma rashin gaskiya yafi yawa daga bangaren Gwamnati, an sanya yaudara ne saboda ana da wata boyayyar manufa ga zaman lafiya da tsaron Arewacin Nigeria, wannan shine abinda Sheikh Dr Ahmad Gumi yake ta kokarin fahimtar da al’ummar mu
Ni da ku mun sani cewa Sheikh Dr Ahmad Gumi abinda yakeyi ba wai yanayi don biyan bukatar kansa da na iyalansa bane, shi a yadda yake yanzu har ya koma ga Allah Gwamnatin Nigeria zata bashi tsaro a duk inda zai je ya dawo, don haka yanayi ne saboda ni da kai ‘dan uwa talaka wanda bamu kai matsayin da za’a bamu sojoji da ‘yan sanda suyi gadin mu ba har karshen rayuwa
Idan akwai kuskure cikin kokarinnda Dr Ahmad Gumi yake na ayi sulhu to bai wuce guda daya ba, zanyi bayani a rubutu na gaba Insha Allah
Muna fatan Allah Ya tsare mana Sheikh Dr Ahmad Gumi, Allah Ya kawo mana sauki da mafita a tsaron Nigeria
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum