

SUWAYE KHAWARIJ???
khawarij
Sune Mutanen da Banbancin Aqida Ko Maslahar Rayuwa Tasanya Suke Kafirta Shashin Wasu Bangare daga Cikin Musulmi Bisa Ko Da Ilimi Ko Babu Kuma Suna Kisa, Wacce takai Har Suka ‘Dauki Makami Suna Ya’kar Musulmi Suna Kashesu Kuma Suna Halartar da Jinanansu, Wanda hakan Yasamo Asaline: Daga Tsatson Wani Mutum Mai Suna Zul Khuwaisirah Attamimi.
سبحان الله
Wanda Bayan Anyi Yakin Hunain
Bayan anyi Sulhul Hudaibiyya
Ansamu Ganima ayakin Hunain, Manzan Allah ﷺ Yazo Rabo, Sai Munafukai Suka Fara Gutsiri Tsoma Cikin Zancensu Suna zargin cewa Annabi ﷺ Bazaiyi Adalci ba, Suna Wannan Tattaunawar Tasu Cikin Ayarinsu na Munafukai Sai Wannan Mutum Mai Rashin kunya ( Zulkhuwaisirah Attamimi)
Yace: Shifa Saiyaje Yasameshi Danme Baza afadamasa Gaskiya ba Cewar Su Annabi ﷺBazaiyi Adalci ba.
Bayan Hakane Wannan mutumin Mara Mutunci Yazo Kan Annabi Cikin Yanayi na Rashin Kunya Yana Cewa: Da Annabin ”Kaji Tsoron Allah Kayi Adalci” Wa’iyazu Billah ALLAH Ka La’anci Khawarij Makasa Dangi da Sahabban Manzan ALLAH ﷺ.
Cikin Sanyin Murya Annabi Yace Dashi ”Yanzu Inbanyi Adalci ba Waye Zaiyi Adalci ” ﷺ.
Nan da Nan Sayyadina Umar Yazare Takobi Yace: Ya Rasulalllah Barni Insare Wuyarsa Sai Annabi Yace Dashi: ”Barshi Koka Kasheshi Yana da Tsatso, kuma Wasu Zasu Bayyana a Karshen Zamani Makamantansa, Wadanda Idan kaga Sallahr Su Saika Raina Taka, Komai Sukan yi Na Addini fiye da yadda kuke Zato, Amma kuma Suna Fita Daga Addinin Kamar Yadda kibiya Ke Fita daga cikin Baka, Annabi ﷺ Yayi ta Bada Misalinsu kafin Karshen rayuwar sa, Yadda Yakara da cewa Zakagansu Suna Da kananan Shekaru, Kuma Suna Karanta Alqur’ani Amma Bai Wuce Makoshinsu (Ma’ana Babu Alamun Sanyashi Cikin Ayyukansu).
Kuma Suna da Tsantsan Rashin kunya da Nuna Tsantsaini Akan Duniya, Sunada Wofantattun ‘kwa’kwale (Abu Kad’an Yakan iya Canza Tunaninsu).
Sannan Suna Kafirta Kowa Wanda Baibin Bayansu, Idan Fitinarsu Ta tashi Za Su rin’ka Kashe Musulmi Suna Barin Kafirai, Suna da Jayayya dakuma Rashin Amintaka da Yan uwansu Musulmi, Amma Ba Ruwansu da Kafirai, Burinsu Kullum inane Musulmi Yayi Ba Daidai ba (Bin Diddigin Musulmi).
Kuma Burinsu Akullum Nasu Itace Turba Inzaka zamo Mafi Tsoron Allah agun Kowa Inbaka Cikinsu Kai Ba Musulmi Bane agunsu Dan Haka Idan Sun Bayyana Ku Kashesu Ku kashesu Ku kashesu.
Bayan Zamani yayi Nisa Kuwa Sai Wadannan Mutane Suka Bayyana Danhaka Suka Fara Sa’insa da Gofnatin Musulunci Tun Azamanin Sayyadina Umar (R. A) Alamun Hakan Tafara Bayyana, Amma Basu Ware Kansuba, Sun Fara Bayyana kansune cikin Munanan Halayyar su Wanda Annabi ﷺ Ya Ambata, Ananne Suka Fara Nuna Adawarsu Da Tawayensu ga Gofnatin Musulunci Haryakai ga Sun Fara Gutsiri Tsoma Ga Shugabancin Gofnatin Na Sayyadina Umar.
Aganinsu Umar Yana Tsanantawa Gurin Hukunci Tayadda Akasamu Wani acikinsu Mai Suna: Abu Lu’uLu’il Majusi Ya Sokeshi Sayyadina Umar (R. A) Da Wu’ka Acikinsa, Wanda Wannan Itace tazamo Jinyar da Tayi Sanadin Shahadarsa.Bayan Shahadar Sayyina Umar (R. A).
Sai Sayyadina Usman Yacigaba Da Khalifanci, Wadda dama Annabi ﷺ yafada Wa Sayyadina Usman Cewa: Zaiyi Shahadane Tahanyar hakurin da Zaiyi Yayin Wata Musiba Da Zata Shafeshi, Hakurinsa Itace Maslahar Al’uma Sannan kuma itace Zata Kaishi Aljannah, Zaiga Musiba Akarshen rayuwarsa Dan haka Saiyayi hakuri, Inji Annabi Muhammad ﷺ Saboda haka: Bayan Ya Sami Nasarar Zamowa Khalifa, Sai ya Umarce Mutanen Sa cewa Kada Wani Ya Tunkari Mutanen da Duk Sukazo Domin Niman Ransa. Domin Tunawa Da Wasiyyar Manzan Allah ﷺ Domin Yasan Cewa Shahadace Karshen Rayuwar sa, Kuma Hakan Zai Farune Tahanyar Wasu Daga cikin Musulmi.
Dan Hakane Har Suka Samu Suka Hauro Katangar gidansa, Suka Sameshi na Karanta Alqur’ani Sukayita Saransa Harsai da Jininsa Ya Zuba Akan Alqur’ani Alhali Yana Azumi, Amma Ko Daga Kansa Baiyi ba Haryakai ga Yayi Shahada Sukuwa Suka Fice daga ciki Gidan Sukayi Tafiyarsu, Sunyi Masa Wannan Ta’addancine: Domin Aganinsu Suna Ganin Cewa Yana ‘Daura Danginsane Kad’ai Amuqaman Gofnatin, Kuma ‘Yan Qabilarsane Danhaka Dangoginsane da Gofnatin, Sukuma Sunfison Dangin Manzan ALLAH ﷺ.
Amma hakikanin Gaskiya itace Zalunci Ne kawai Da Tayarda Rikici wa Addinin Musulunci.
Sannan kuma Sai Wadannan Mutanen dake Inkarin Mulkin Na Sayyadina Usman (R. A): Suka Nemi Sayyadina Aliyyu (R. A) Daya Maye Gurbinsa, Acewarsu Yacigaba da Khalifanci Da Jagorancin Musulmi,
Sukayita Kurarashi Da Wasu Dadin Baki Amma Sayyadina Aliyu Yaki Amincewa, Domin Acewarsa Yanajin Kunyan ALLAH Akan Wannan Al’amari, Ankashe Wanda ALLAH da Mala’ikunsa sukejin Kunyarsa, Dan haka Shi Da’awa Yasaba Abarshi Yayi Da’awarsa Azabi Wani Yayi Shugabanci. Sai da Wasu Daga Cikin Manyan Masu Fad’a aji na Sahabbai Suka Sa Baki Sannan Sayyadina Aliyu Ya Amince.
Dalilin Daya’ki Amince wa Kuwa: Shine Yana Ganin Cewa Bayadda Za’ayi Ayi Wa Sayyadina Usman Wannan ‘Danyan Aikin Bai Dauki mataki ba, Sannan Kuma Ace Ya Zamto Anbashi Ragamar Shugabanci Kunsan Aliyyu Kadanga Ne: Kasar Yaki Dan Baffan Manzan ALLAHﷺ Aganinsa Ankatse Masa Dukkan Wata Damarsa ta Ganin Ya ‘Dauki Mataki Danganeda Al’amarin Matukar Aka Bashi Ragamar Mulki.

Bayan Ya amince da Yarjejeniyar Zama Khalifane: Domin magance dakuma daidaita Tsakanin Matsalar Musulmi Domin Khawarij Suna Sonsa Sannan kuma Sauran Sahabbaima Shine Za’binsu, Domin Su Wadannan Mutane Sunce Babu Wanda Zaiyi Jagoranci Awannan Lokacin Sai Shi Sayyidina Aliyyu. Kuma Wasu daga cikin Mutanen kirki acikin SAHABBAI Suma Sungoyi Bayansa. Awannan Lokaci Yaga Maslahar Al’umar kawai Itace Ya Rungumi ‘Kaddara Ya Cigaba da Khalifanci.
Bayan Ya Amince da Hakan Ya Kuma Samu Mubaya’ah daga Dukkan SAHABBAI, Sai Kuma Suka ‘Kara Kunna Wata Sabuwar Rigima, Ta Cewar Sai Ankamo Wadanda Suka Kashe Sayyadina Usman, Domin A Aiwatarwa Musu Da Hukuncin Alhali Kuwa Babu Wanda Yasan Su waye Suka Kasheshi.
Daganan Sai Suka Fara Rura Wutar Rigima Tsakanin Musulumi Na Yankin Madina, Har Rikicin Yafara Shafan Wasu Daga Cikin Sassan Sauran ‘kasashen Musulmi, Wanda Har Wasu Daga cikin SAHABBAI Masu Kyakkyawan Manufa Sanda Wannan Rikici Yaritsa dasu, Wasu Kuma Suka ‘Ki Sanya Baki cikin Rikicin, Wanda Harda da Matan Annabi ﷺ Wadda Dama Suna Madina aka Kashe Sayyadina Usman, Lokacin Sunzo Hajji ‘Kar’kashin Jagorancin Aishatu (R. A). Dasauran Matan Manzan Allah ﷺ Duk Sun Daidaita Akan Cewa Sayyadina Aliyu Yafara Bincike Ya Hukunta Wadanda Sukayi Wannan ‘Danyan Aikin. Shikuwa Sayyadina Aliyyu Burinsa Daidaita Al’amarin Shugabanci Kafin Tsara Yadda Gofnati Zata Gudana, Kafinnan Sai Ya Fara Bincike.
Daganan Bayan Haka Aka Kai Koken Zuwaga Mu’awuya Tahanyar Wadannan Munafukan, Wadda Shikuma Sayyadina Usman Yakasance ‘Dan Uwan Mu’awuya Ne najini, Sai Shima Mu’awuya Yace Bazai Yi Mubaya’a ga Aliyyu ba Harsai Ya Zartar Da Hukuncin ga Wadanda Suka Kashe Usman. Kasancewar Mu’awuya Shima Gofnane Agarin Basra A’kasar Sham Siriya Watau Iraqi Ayanzu.
ALLAHU Akbar Yau ga Ranar Manzan ALLAH ﷺ Ina Ma Ace yana Cikin Duniyar!!! Wallahi Nasan Wannan Ba Komai Bane Agunsa ﷺ Cikin Sakanni Zaiyi Maganin Matsalar ﷺ.
Daganan fa Sai Labari Ya Riski ‘Dalha Bn Ubaidullah, Cewa Akwai Matsala A Can Basra Inda Mu’awuya (R. A) Yake Mulki, Domin Mu’awuya (R. A) Shi da Mutanen sa Sunce Bazasuyi Mubaya’ah ba ga Aliyu.
Sannan Madina Tayi Zafi, Rikici Yayi Yawa, Aliyyu Kuma Yakoma (Kufa) Can Ta Yankin Da Mu’awuya Yake Mulki, Domin Mutanen Kufa Sunce Da Aliyyu Yazo Yankinsu Su Sun Aminta dashi, Kuma Sunada Babbar Daula Danhaka Yabar Madina Domin MadinaRikici Yayi Yawa, Yazo Gurinsu, Zasu Bashi Cikakken Goyon Baya Yakafa Daular Musulunci Awannan Yankin, Ya zamo Itace Cibiyar Musulunci Wanda Shugaban Musulmi Yake Cikinta Amaimakon Madina ta Asali Afarko.
Sannan Yacigaba Da Dukkan Wata Qudiri dakuma Aikin Shugabancinsa Zasu Dafa Masa Har abinciko Wadanda Suke Kokarin Rushe Daular.
‘Dalha Bn Ubaidullah da Zubairu Bn Awwam Manyane Daga Cikin Manyan Zaratan Sojojin Manzan ALLAH ﷺ Suma Suka Koma Makka Sai Suka Hadu Da Nana Aisha.
Domin Suma kansu Yayi Zafi Tunaninsu Ya Bambanta dana Sayyadina Aliyu (R. A) Cewar Suna Ganin Yakamata Sayyadina Aliyu yafara Kama Wadanda Sukayi Wannan Mummunar Aiki, Domin Yaji Dadin Mulkinsa Dakuma Magance Matsalar Munafukai dasuke i’kirarin Cewa Harda Hadin Bakinsa Aka Kashe Sayyadina Usman (R. A)
Bayan Sayyadina Aliyu Yakoma Kufa Kuma Ita Kufa Wata Babban Jihace Akasar Iraqi Wanda Har ayanzu Tana Cikin Manyan Daulolin Kasar, Ananma Sai Sayyadina Mu’awuya Yace Bazai Ta’ba Yarda da Khalifancin Sayyadina Aliyu (R. A) Ba Harsai ya Binciko Wadanda Suka Kashshi.
Akan hakan Kuwa Yasa Shi Mu’awuya Yakiyimasa Mubaya’a Domin Sa’banin Ra’ayin dake Tsakanin Su, Sannan Haryakai ga ‘Dalha Bn Ubaidullah Da Azzubair Bn Awwam Suka Taso Daga Makka da Nufin Cewa, Dole Ne Sai Sun Shiga Cikin Matsalarnan Tahanyar: Yin Sulhu Tsakanin Mu’awuya da Sayyadina Aliyu (R. A) Kafin Asamu Maslaha.
Bayan Sun sami Matsaya Danganeda Shawarwarinsu Saikuwa Suka Shirya Domin Zuwa Sulhu Kasar Iraqi Aisha Ma Tace Hankalinta Bazai Kwanta ba Ga Ahalin Gidan Annabi Muhammad ﷺ Cikin Wani Hali Danhaka Sai Yabisu, Sai Kuwa Suka Sauka A Basra Inda Mu’awuya Yake Mulki, Domin Neman Sa daya Janye Akan Yayi Mubaya’a Wa Sayyadina Aliyu, Awannan Lokaci Ne Munafukai Suka So Rura Wutar Gaba Tsakanin ‘Dalha, Aisha, da Zubair (R. A) Da Gulman Cewa Su AISHATU DA ‘DALHA DA ZUBAIR sunje Gun Mu’awuya Ne Domin Suna Goyon Bayan Mu’awuya.
Shikuwa Sayyadina Aliyu Ai Ba Wawa bane Rainon Manzan ALLAH ﷺ Ba Wasa Bane, Yafi Karfin Zugon Munafukai Kuma Ashe Yagane Akwai Munafukai Masu Rura Wutar Rigima, Saiya Aiki wani Daga Cikin Manyan Zaratan Kwamanadan Sojojin Manzan ALLAH ﷺ Qa’aqa’a Bn Attamimi.
Domin Ya Binciko Masa Menene ake ciki Domin Kada Ya Yanke Hukuncin ABisa Rashin Sanin Hakikanin Abinda yake Gaskiya, Sai Kuwa Yazomasa Da Labarin Cewar Ai Sunzo Yin Sulhu Ne.
Sai Sayyadina Aliyu Yace Aikuwa Baici tazama ba Dolene Yajema Kawai Caan Ayi Sulhun (Yaje Basra) Ayi Acan Domin Ga Manyan Mutanen dayake Jin Nauyin su Acan Basra. Agefe Guda Kuwa Wadannan Mutane Masu Mummunar Manufar Sunanan Suna ta Kullace_Kullacensu.
Lokacin da Suka Sami Labarin Cewa Sayyadina Aliyu Yatafi Zaije Sulhu Da Mu’awuya Kuwa: Sai Suka Fara Tunanin Yadda Zasu Wargaza Wannan Sulhun Yazamo Ba’ayi Shiba. Domin Sun Tabbatar dacewar Anayin Sulhu Kan Al’umar Musulmi Zai Hadu Kuma Za’akamosu Ahukuntasu. Shine Suka Rabu Gida Biyu, D’aya Sukaje Basra.
Bayan Sayyadina Aliyyu Yakama Hanya Tareda Rundunarsa Wadanda Sukace Bazasu Bari Yatafi Shidayaba Dole Sai sunbishi Domin kare Ransa da Lafiyarsa. Hakan Kuwa sukayi Suna tafiyane Sai Dare Yayi Musu Ahanya Sai Kuwa Ya Yada Zango Da Rudunar Mutane Dubu Ashirin A wani Guri domin Dare Yayi Dan Su Huta Sai Safiya Acigaba da Tafiya. Cikin Dare Sai Wadannan Munafukai Wadanda suka Kasu Gida Biyu: Domin Cimma Mummunar Manufarsu ta Wargaza Sulhu, Wani Bangaren Suka Zo wa Rundunar Sayyadina Aliyyu Suna Kashesu Suna Saransu Wasu Bangare kuwa Suka Je Ga Sayyadina Mu’awuya AKasarsa Suna Kashe Sojojin said Suna Cewa Ba Maganar Sulhu. Nanma Gun Rindinar Sayyadina Aliyu Suka Kama Saran Sojojin Sa Suna Cewa Babu Sulhu, Daganan Kuma Suka Hade Guri Guda Aka Kama Yaki Musulmi da Musulmi, Ana Kisan Juna ba tareda Ansan Dalilin Yin hakan ba Kowa Na Saran Dan Uwansa Amma Baisan Daliliba Sudai Sunsan Cewa Hari Aka Kawowa Kowanne daga cikin su.
Nagartattun Cikinsu Wasuma Basusaniba Wasu kuwa Sunki shiga Yakin Haka kuma Wadanda Suka shiga ma Sunayine Domin Kare Kansu Domin Su aganinsu Kamar Ankawo Musu Harine.
Awannan Rikicinne aka Kashe Zubair da Dalha Sannan Wasu daga Cikin Sojojin Aliyyu Sune Suka Kashesu Domin Rashin Sanin Hakikanin Me Yakawosu, Yankin Mu’awuya Aganinsu Sune Suka Ruruta Wutar Rigimar, Wani Daga Cikin Sojojin Aliyu Yasamu Azzubair Ibnl Awwam Yana bacci Yadauki Takobinshi Yakasheshi da Ita, Sannan Kuma Ya dauki Takobin Yakaiwa Sayyadina Aliyyu Domin Nuna Bajintarsa Ga Sayyadina Aliyyu,
Da Sayyadina Aliyyu Yaga Wannan Takobi Sannan Wannan Mutumi Yace Dashi Wannan Takobin Dan Awwam ne Da ita Na Kasheshi Dan Sune Suka ruruta Wutar Rigimarnan, Sai Sayyadina Aliyyu Ya Fashe da Kuka Yana Cewa Shin Kasan Hidimar da Wannan Takobi Tayi wa musulunci kuwa?
Da Wannan Takobine Akayi Gadin Manzan Allah ﷺLokacin da akayi Yakin Khandaq, Annabi ﷺ Baya Samun Bacci Azzubair Shike Gadin Annabi ﷺ Haryasamu Yin Bacci. Manzan ALLAH ﷺ Yakira Azzubair da Hawariyyinsa, Domin Yace dukkan Annabi Yanada hawariyawa Nikuwa hawariyina Shine azzubair.
Sannan Shima Dalha Ibn Ubauidullah Shima Awannan Yakinne aka kasheshi tahanyar Harbin Kibiya Da akayi masa, Sayyadina Aliyyu (R. A) Yafada wa Sayyadina Hassan (R. A) Yace dashi ”Lokacin da ‘Dalha Yazo Cikawa Yace Dani, Abin Baiyi Masa Dad’iba Domin Sunzo Sulhu Maimakon Sulhu Kuma Sai Ankama Kashe Juna.
Sayyadina Aliyyu Yana yaki yana kuka Yana Fadin wai Meyafarune!!!.
Bayan Anyi Wannan Yaqinne Sai Sayyadina Aliyyu yace: ”Zamu koma Kufa Domin Abin Baimana Dadin Ji da Ganiba” Aisha Kuwa Da taji Abinda Yafaru hankalinta yatashi Sai Tace Zata Koma Gida, sai Aka Sanya Wasu Rudina Karkashin Jagorancin Mu’awuya (R. A) Sukayi Rakiyarta Gamida Wasu Guziri.
Munafukai kuwa dasukaji haka Har Wani Yafara cewa Aidama Ance Kaza_kaza akanta, Da Sayyadina Aliyyu yaji Haka Saiyasa aka kama wannan Mutumin aka tubeshi akayimasa bulalan ‘Kazafi Na Haddi, Sannan Yace Dashi Wannan itace matar Annabi ﷺ Aduniya kuma Qiyama.
Dagananne Aka Samu Bangarorinnan Na ‘Yan Tawaye Ahlul Bagyi ‘Bangaren Su (Mu’awuya), Dakuma ‘Bangaren Masu Gofnati Su (Sayyadina Aliyyu), Da Munafukai Masu Fad’a Da Dukkan Tsarin Sune (Khawarij), wadanda Dama Annabi Yafadesu Cewa Akwai Wasu Bangarori Biyu Masu Gaskiya Zasu Yaki Juna, Sannan Wasu kuma Zasu Balle Sukuma dabam, Sunzamo Uku Kuma Duk yayi bayaninsu wanda Duk maihangen Nesa Cikin Sahabbai Yaganosu, Kuma Sune matsalar musulmi, Daman Annabi ﷺ yafada Insun Bayyana Akashesu Kada Abarsu Domin Sudin fitinace Ga Alumar Musulmi, Wadda kuma Aliyyu Ya Aiwatar da Wannan Aikin Na Yakarsu kamar Yadda Annabi ﷺ Yabada wasici, Cewar AYakansu Akwai Lada Mai Dumbin Yawa Daga Bakin Annabin ALLAH ﷺ Sannan Yace Idan Za Ayakesu Ayimusu Kisan Kiyashi (Ankashe Su Dukka) Danhaka Sayyadina Aliyu (R. A) Ya yakesu kuma Yakashe Kasho Casa’in Da Biyar Cikin Darinsu Saura Kuma Suka gudu.
Sunefa Masu Da’awa Akan cewa Babu Gofnati Babu Hukunci Saina ALLAH, Wanda Har Sayyida Aliyu Ya turamusu Abdullahi Dan Abbas, Domin Yayi Musu Wa’azi, Domin Sunce Aya Suke Nema Ba ruwansu da Shugabancin Wane Ko hukuncin Wane, Sannan Kuma Su Basa bin Wata Gafnati Tsakanin Aliyyu Ko Mu’awuya Ba ruwansu da Kowa.
Anyi Nasarar Wasu Sun Tuba Sun Amince Sun koma Rindinar Gofnati, Tayadda Wasu kuma Suka Tangare Suka Nuna Girman Kai daga Nanne Sayyadina Aliyyu Yaganefa Sune Wadanda Annabi Yake ta bada Misalinnan Fa, Dagananne Sayyadina Aliyyu Ya Daura Damarar Yaki dasu Domin Yagano Su Yakashe mafi Yawansu, Wasu kuma suka Gudu, Wadanda Suka gudu Suka Tsira Sune Sukayita Yakin Sunkuru Ga Musulmai, Snayimusu Dauki ‘Daid’ai Haryakaiga Sun Kashe Sayyadina Aliyu (R. A) Da Asuba Yafito Yana Tashin Mutane Su Fito Domin Suyi Sallahr Asubahi, Wanda Yakashe Shi Shine Abdullahi Bn Muljum Domin Suna Ganin Su Sayyidina Aliyyu sun kafirta Saikuma yakama Da’awar Cewa In ankasheshi Yayi Shahada.
Wannan Shine Matsalar Da Musulmi Suka taba Samu Gameda Shugabanci Kuma Shine Dalilin Shahadar Sayyadina Aliyyu Dakuma Dalha Da Zubair Rahmatullahi Alaihim Ajmain.
Kuma Siffar Khawarijawa Kenan: Tawaye wa Aqidar Mutane da Gofnati Da Daukan Makami Akan Al’umar Musulmi.

جزاكم الله خيرا و احسن الجزء
LikeLike