WAHABIYANCI DABAN DA MU’UTAZILANCI
WAHABIYANCI:
Shine Takaituwa Akan Tafarkin Sunnah, Da Bin Nassin Alqur’ani Da Hadisan Manzon ALLAH (ﷺ). Abisa Koyarwar Magabata Na kwarai, Da Kuma Nema Musu Gafara, Tareda Ayyadar da Hukuncin Tsarkake Zuciya Daga Hawan Nafsu (Bin Son Zuciya).
Mu Bama Kushe Dariqar Kowa, Inhar Basu Ta’ba Nassi Ba.
Kada Kabari Son Rai Yasa Kayi Abinda Zai Kaucewa Shari’ah, Abisa Furucine Ko aikin Ibada! Inkayi Haka Kazamo Mu’utazilah,
سبحان الله ماشاءالله لا حول ولا قوة إلا باالله العلی العظم
SAHABBAI SUNE MANYAN WALIYYAN ALLAH
Musulmin Kwarai Baya Gaba Da Waliyyai Kuma Waliyyai: Sune Mabubbugan Sanin Asiran Ulumu Nakara Fad’a Muku, Idan Sahabi Yayi Maka Sharhi! Saikaji kamar Kana Gurin Akayi Zancen, Kaji Waliyyin Gaskiya, Kuma Sahabbai Sun Tsarkaka daga Bin Son Zuciya, Da kuma Ikirarin ‘Kir’kira (Basayin Bid’a), Ko Shigoda Son Zuciyarsu Cikin Addinin Allah.
Subhanallah
Kaji Auliya’ULLAHI Masana Tasarrufin Harshen Masoyina Annabi ﷺ. Daku Muke Taqama Mu Kore Dukkan Wata ‘Barna Da Son Zuciyarmu, Mu Dasa Wa Zu’katanmu Koyi Da Shariar Manzon Allah ﷺ.
GA SIFFAR WALIYYAI AHADISI
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إن الله تعالى قال: من عادى لي ولياً فقد آذنته بالحرب، وما تقرب إلى عبدي بشئ أحب إلي مما افترضته عليه، ولا يزال عبدي يتقرب إلي بالنوافل حتى أحبه، فإذا أحببته كنت سمعه الذي يسمع به وبصره الذي يبصر به ويده التي يبطش بها ورجله التي يمشي بها، ولئن سألني لأعطينه، ولئن استعاذني لأعيذنه» . رواه البخاري.
An karbo daga Abu Hurairata Allah yakaramasa yarda, ya ce: Manzon Allah s.a.w ya ce: hakika Allah Madaukakin Sarki ya ce: Wanda ya yi gaba da masoyina (Waliyyi), to Ha’ki’ka na yi masa Shelan yaki da ni. Kuma bawana bai gushe ba yana neman kusanci a gare ni, da nafilfilu, Har sai na So shi. Idan kuwa na So shi, To Sai na kasance ni ne jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da kuma hannunsa da yake jim’ka (taba wani abu) dashi, da kuma kafafuwansa da yake tafiya dasu. Kuma wallahi idan ya rokeni, wallahi sai na bashi, kuma wallahi idan ya nemi tsarina, wallahi sai na tsareshi”. [Buhari ne ya rawaito shi]
‘KARIN HASKE
Kunga Kenan Waliyyi Shine wanda Yatsare Hukuncin Allah Cikin Ji da Gani, Gamida Sauran Ayyukansa Duk Zaiyi Koyine da Wanda ALLAH ﷻ ya Aminta Dashi. Wanda Yazo A Alqurani Ko Hadisan Manzon Allahﷺ,
‘Dauki Hadisai Kwafin Wahabiyawa Ba Sharrace_Sharracen Shi’awa Ba, Ka Kwashi Romon Ilimomi Afanni Mabambanta.
Yahudawan Dasuke Sa Wasu Suna Karyata Hadisai, Wallahi Suma Anan Su ka Samo Ilimomin Kimiyyar ‘Kira da Dana Yad’a Bayanai. Ya Isheka Misali: Dukkan Manyan Ka’idoji ( Principles Dakuma Law’s Da Theory’s Sanannu ) Na Cikin Ilimin Kimiyya (Science) Duk Zakasamu Na Musulmaine.
Muguntar Yahudu Shine: Mudaina Karanta Hadisai da Ayoyin ALLAH. Suna ‘Kyashin Kada Mun Wuce su Da Sanin Fasaha, Shine Sukeson Mu Kyamaci Littafan Namu, Domin Murasa Madafa.
AMATSAYINKA NA MUSULMI MENENE RIBARKA IDAN KA KUSHE WAHABIYAWA???
Idan Kaji Ana cewa Aikin Banza, Shine Wanda Ke Zagin Ahlussunnah da Wahabiyanci.
Dolenkane Bin Tafarkin Magabatan kwarai Amatsayin ka Na Musulmi , Domin Hanyar Ce Kadai Wacce Zata Sadaka Da Manzan ALLAH ﷺ﴿.
Wahabiyanci Tafarkin Tsira Ne Shine Bin Annabi dama Asahabu Rasulallahi ﷺ.
Domin Sahabbai ALLAH Yakara Musu Yarda: Sune Manyan Waliyyai, Arufai Masana Tarbiyyar Shiriya Ta Abal Qasim Nurun Ala Nurun ﷺ, Muhammadurrasulallah ﷺ.
Idan Kabisu Kabuta, Da ka Kauce Kuwa Ka Halaka.
Zaka Afkane Cikin Qiyayya da Gaba da ABOKANAN Annabin ALLAH ﷺ, Katabbata Cikin Halaka Da Ta’bewa, Ka Koma Yiwa Yahudawa Hidima, Idan Ka ‘Kyamaci Hadisan Annabi ﷺ Kuwa Zaja Girmama Maganganun Yahudu, Mai Cikeda Son Zuciya Da Halakarwa Dakuma Ta’bewa. Yahudu Kullum Kiransu ga Rushe Addinine Tahanyar Amfani da Masu Raunin Addini.
Mudage Mu Kaucewa Manhajinsu, Mu Cire Kamanceceniyar Siffantuwa dasu Cikin ayyukanmu Mai kama Da Tasu, Mu Bi Sunnah Ta Annabi ﷺ.
Itace Hanyar Tsira.
WAHABIYANCI BAIZAMO KHAWARIJANCI BA
INNA LILLAHI WA’ INNA ILAIHI RAJI’UN!!!
TABBAS AQIDANCI BISA JAHILCI ZAIKAI WASUNMU GA HALAKA!!!
Wa’iyazu Billah, Hasbunallahu Wani’imal Wakil.
Dalilin Wannan Ba’asin Nawa Shine: Yadda Naga ko Naji Wasu daga cikin, ‘Yan uwa Musulmi Suna Alaqanta Ahlussunnah da Khawarijawa, Sai Yanzu Nafahimci Dalilin Kisan Malaman Mu da’akeyi haka Kurum. Kuma akayi Shiru Musamman Ja’afar da Albani, Rahmatullahi Alaihim Ajma’in.
Subhanallah Mudai Ahlussunnah, Mun Barranta daga Khawarijanci da Sifofin dama kuke ambatowa, Duk dacewar Bahakan nema Annabi ﷺ Yamisalta ba, Mu Ke da Hadisan Kuma Munsan Sifar! Kuyi Ladabi Asanar daku Sirrikan.
Dan Allah Mudaina Amfani da abinda Ma’kiyan Musulunci ke amfani dashi, Muna Aibanta Junanmu, Domin Hakan Zai Jawo Rabuwar Kan Al’umar Musulmi, Nidai Nasan A Iya Fahimtata ‘Yan Ta’adda Masu Jihadinnan Na Gefen Gari! Damuke dasu Ayanzu Sune Ragowar Khawarij.
Tab ‘Di Jam Babban Magana Kai Mu Ko ‘Yan Shi’ar Najeriya Masu Sukarsu acikinmu Saidai Su Sokesu Dasunan: Ahlul bagyi ‘Yan Tawaye wa Governati Da Shari’ah Amma ba Khawarij ba A Bisa Adalci, Dalilin Kuwa Dayasa Muke Kiran Mafiyawan ‘Dariqu Da Mu’utazilawa Shine: Karbar Shari’a Daga Wasun SAHABBAI (R.A).
Sune ‘SUHUFAYE‘ Wad’anda Kuma Suna Daidai, Suna Kuskure Wasuma Sukan Sanya Ra’ayoyin Su Acikin Addini, Sukuwa SAHABBAI Adalaine, Shari’ar Abal Qasim Itace Shari’ar Su Hukmatan Wa Taufiqan Bi Qaulihi Amalihi ( A Hukumce da Manhaji Bisa Maganganunsa Da Ayyukansa ).
Kuma Akanta Muke ‘Karkashin Jagorancin Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahhab, Shiyasa Ake Cewa Damu Wahabiyawa, Amma Shi Ibn Abdulwahhab Ba Shugaba Bane Shidai Mainuni Ne Ga Hanyar Aqidan Bin Sahabbai Dakaucewa Mu’utazilanci, Kuma ‘Mu Bama Zagin SAHABBAI Kuma Bama Kar’bar Shari’ar Da Batazo Daga Annabi ﷺ Ba.
Insha Allahu Agaba Zanyi Rubutu danganeda, Suwaye Khawarij? Da kuma Bambancinsu da Ahlul bagyi. Karkashin Wasu Lectures Na Malam Dr. Mansur Isa Yalwa.
Allah Yayimana Jagorancin.

You must be logged in to post a comment.