TARIHIN SAHABBAI 001

TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI,

(manzon Allah S. A. W) “yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al’umma ta”

Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu ” usman” usman dan Amir dan Amir dan ka”abu dan sa”adu da taimu dan murratu dan ka”abu dan lu”aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka”abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya “Abdul ka” aba” daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi “Abdullahi” An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi”antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da “Atiku” shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Muhammad (S. A. W) shine yafara haduba a addinin musulunci. Shine abokin zaman kogo tare da manzon Allah na farko kuma shine nafarko cikin sahabbai goma da aka musu albishir da gidan Aljannah tun a duniya shine farkon Amirul hajji kuma yana cikin marubuta wahayin da akema Annabi Muhammad (S. A. W) An haifi Sayyidina abubakar (R. A) a makka bayan Shekara giwaye da shekaru uku (573 A. D) manzon Allah. Ya girma shi da shekaru uku. Yana cikin manyan shuwagabannin kuraishawa a lokacin jahiliya kuma a bakin manzon allah ne na kasa tun kafin aiko shi. Sau dayawa ma. Yakanje gidan shi su tattauna shine mafi sani duk larabawa game da tarihin nasabar kuraishawa. 
Kuma yakira mutane da yawa zuwa ga addinin musulunci. Biyar daga cikin su suna cikin sahabbai goma. Da aka yiwa bishara da Aljannah sune kamar haka :  
Ya sha a zaba iri – iri daga kafiran makka saboda shigar shi musulunci 
Har takai babu wani musulmai da azabtu kamar shi. Duk da irin matsananciyar azabar da suka sha suda sauran musulman farko daga kafiran makka. Bai yi kauraba zuwa kasar habasha ba. Ya tare ga manzon allah (S. A. W) lokacin kaura zuwa madina yana tare da Annabi Muhammad (S. A. W), tare suka shiga kogo kafin suwuce zuwa madina shine cukon mutane biyu da Allah ya ambata a alkur”ani in da yace : ” Idan baku taimakeshiba. ( Annabi), to ai Allah ya taimake shi yayin da kafurai suka fitar da shi ( daga makka) na biyu (mutane) biyu yayi dasuka shiga cikin kogo yake cewa da abokin shi (Abubakar)” kada kaji tsoro, Mu Hakika Allah ya na tare damu “( da taimako shi)” cikin suratul tauba:40, yayin da suka isa madina. Sayyida Abubakar, A wurin kharijatu dan zaidu. Da shi kuma manzon allah yahada su ‘yan uwantaka yayi da ya rinka hada yan’ uwantaka (ta musulunci) tsakanin mutane makka ( muhajiruna), da na madina (Ansaru) Sayyida Abubakar shine tamkar Waziri ga Annabi Muhammad (S. A. W), wajan gudanar da al’amuran daular musulunci. Mai babbar hedikwata a madina: birnin manzo,,,

Abubakar saddik ( R. A) ya dukkan yake _ yaken daukaka musulunci da yada shi da Annabi Muhammad (S. A. W) a yakin badar shine kan gaba wajan kula da wurin da manzon allah yake. Yana shir yanda yake zai gudana tare da rokon allah. har dai allah ya amsa addu’ar Annabi, ya aiko da rundunar mala”iku. Musulmai suka samu nasara. A yakin uhudu kuwa, Sayyida Abubakar. Shine jagora tsirarun Manyan sahabbai, suka gabata a filin yakin. Tare da manzon allah (S. A. W) yayin da kafurai suka tarwatsa rundunar musulmai.

Bissalam

Daga Dan Uwanku

Ismail Hussaini Alpholtawy

TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI,

Dukawa
Kasinawa
Tafawa Bakewa
Bauchi, Bauchi
Nigeria

One thought on “TARIHIN SAHABBAI 001

Comments are closed.