
AMFANIN SABAYA A JIKIN YA”MACE
*DR ABDULWAHAB GONI BAUCHI*
Idan Mutum Ya Hadawa Matarsa (SABAYA) Yana Da Matuqar Ta’asiri a Jikin Ya”Mace Kuma Yana Haifar Mata Da Ababe Uku a Jikinta Akwai Matar Da Idan Tana Shayarwa Zakaga Kamar Ta Fito Daga Gidan Yari Wata Jikinta Yana Zubewa Ruwan Nononta Yana Lalacewa
*Nafarko Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Zai Taimaka Wajen Dawo da Halittan Da Allah Yai Mata Jikinta Nonon Bazai Zube Ba
*Na Biyu Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Jikinta Zaiyi Laushi Kamar Kwalabiya
*Na Uku Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Da zarar ta Haihu Irin Ramar Da Mata Keyi Baza Tayi Ba
Kuma Ruwan Nononta Zai Qara Yawa Sannan Bazai Lalace Ba Kuma Yaron Data Haifa Allah Zai Kareshi Daga Dangin Cututtuka
Kuma Hatta Magidanci Idan Yasha Yana Qara Masa Lafiya Da Kuma Kuzari a Jikinsa
MEYA KAMATA ASAMO WAJEN HADA SABAYA TASU KAMAR HAKA:
*Al Kama 1Mudu
*Danyen Shinkafa 1Mudu
*Waken Suya 1Mudu
*Ridi ½Mudu
*Hulba ½Mudu
*Gyada Mai Bargo/Kamfala
*Madara
*Zuma
YA ZA’A HADASU SHINE:
Ridi Da Gyada Ana Hadasu Wuri Guda Ridi a Soyashi Yadda Ake Kantu, Gyadar A Soyata Yadda Ake Quli Quli, Shinkafa Da Alkama Ana Jiqasu Tsawon 5hour Sai a Shanya Da Laima a Jikin Sai a Hadasu Wuri Guda
Da Ridin Da Gyadar Da Al Kama Da Hulba Da Shinkafar Sai a Niqa Matarka Tin Tana Da Ciki Ya Kamata Ka Fara Bata Har Zuwa Haihuwa Kaga Yadda Zatai Da Yaronta Kuma Nononta Dana Shayarwa Ko Bata Shayarwa Bazai Canza Ba Da Ikon Allah
TO YA AKE SHANSA
Yadda Ake Dama Kunu Haka Ake Damashi Sai Dai Idan aka Zuba Ruwan Zafi Ana Iya Maidashi Kan Wuta,
Sukace Karta Wuce Cokali Uku a Rana Musamman Cikin Babban Cokali Idan Kuma Harda Magidancin Sai a Sanya Cokali Shida
Su Kace Amma Idan Mace Bata Da Aure Kada Tasha Domin Yana Qara Sha’awa Kuma Yana Qara Yawan Nono Ma’ana Yafi Dacewa Da Matar Datake Shayarwa Domin Samun Ingancin Lafiyar Jikinta Don Kada Ya Zube
Kuyi Amfani Da Wannan Link Din Domin Samun Magunguna a Sauqaqe

- Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media WritersNasarorin Da Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Ta Samu Cikin Shekaru Biyu, July 2020, Zuwa July 2022… Read more: Nasarorin Ƙungiyar Arewa Media Writers
- TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════ ══════ ❁✿❁ ═════ ❁✿❁ ═════ … Read more: TARBIYYAR ‘YA’YA AMUSULUNCI
- ZATIN UBANGIJISHAUQI CIKIN AL AMARIN GAIBIYYA Kasantuwar Ubangiji A Buya Bai zama tawaya Ga Imanin Mai imani… Read more: ZATIN UBANGIJI
ALLAH ﷻ Yasa mu amfana dash
ماشاءاللہ
You must be logged in to post a comment.