IDAN KAJI TSORON ALLAH ZAI BAKA MAFITA.
–
Hausawa suka ce bin Allah maganin wayyo Allah, tabbas hakane, lallai idan mutum yabi Allah kuma yaji tsoron sa, ya bauta masa, ya kuma kaucewa saɓa masa, to haƙiƙa bazai koka ba, kuma lallai Allah zai sanya masa hanya madaidaiciya wacce zai bita ɗoɗar ba tareda ya karkace ba”
–
“A rayuwar ka idan ka kasance mai yawan jin tsoron Allah abisa dukkanin ilahirin lamuranka, to lallai Allah ɗin zai baka mafita daga dukkanin wani ƙunci, bala’i da masifu, kuma zai azurta ka ta hanyoyi mabanbanta waɗanda baka san su bama, amma sharaɗin ɗaya ne, shine sai kaji tsoron Allah kuma ka guji dukkanin nau’ukan saɓon Allah”
–
Allah ta’ala yace: Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (yaji tsoron Allah) Allah zai sanya masa mafita. () Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma’ishinsa. Lallai Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama’auni ga dukan kõme.
aT-Talaaq 2-3
–