HAKIKA AN TAUYE HAKKIN AL’UMMAR AREWA

Ma’aikatar cikin gida (Ministry of Interio) karkashin jagorancin Minista Ra’uf Aregbesola ta fitar da sakamo na jahohin Nigeria matasa wadanda suka samu nasaran daukar su aiki domin cike gurbi a hukumomin tsaro na Civil Defence, Correctional, Fire Service da Immigration
Amma a cikin wannan sakamon an cuci yankin jihohin Arewa, an danne musu hakkinsu, kashi 99 cikin 100 na wadanda aka daukesu aikin daga Inyamurai ne sai Yarbawa, tsakani da Allah me ya kawo Sunan Ikechukwu jihar Jigawa?
Kuma a haka wakilan Arewa zasu zuba ido ba zasuyi magana ba?
Wato an mayar da ‘yan Arewa saniyar ware, an mayar damu marassa amfani kawai, amfanin ‘yan Arewa sai lokacin zabe yayi azo neman kuri’ah ana watsa mana hatsi daga cikin mota kamar kaji muna caccaka
Mu dai Arewa an barmu da yiwa juna hassada da kyashi da munafurci, mutanen kudu sun mayar da hankali wajen kokarin gina ‘yan uwan su, sun mamaye dukkan ma’aikatu dake babban birnin tarayya Abuja, har a cikin jihohin Arewa inda ya kamata a ga sunan Hausawa sai dai aga sunan Inyamuri, saboda sun fimu hadin kai da son juna ba tare da nuna banbanci ba
Wannan babban kalubale ne wa Ministocin Nigeria ‘yan Arewa, ya kamata ku dauki darasi da abinda Ma’aikatar cikin gida tayi, ku dena nuna tsoro ko shakkar masu zagi da suka, tabbas kuma zaku iya yin abinda Minista Ra’uf Aregbesola yayi a ma’aikatunku idan an tashi diban aiki, shugaba Muhammadu Buhari yayi iya bakin kokarinsa da ya baku mukami, saura kuyi abinda ya dace
Allah Ka taimaki Arewa da ‘yan Arewa Amin