GWARGWADON IMANINKA GA ALLAH.



“Shi imani ga bawa yana tsufa kuma yana sabunta, yana raguwa kuma yana ƙaruwa”

“Yana tsufa ko raguwa da yawan saɓon Allah, sannan kuma yana sabunta ko ƙaruwa da biyayya ga Allah

“A lokacin da Allah ta’ala yaso nufarka da alkhairi, sai ya jarabceka a rayuwarka sannan kuma ya baka damar cin wannan jarabawar don ya sauƙaƙa maka hanyar shiga aljannah”

“Gwargwadon imaninka ga Allah gwargwadon jarrabawarsa gareka, bawa baya zama mai cikakken imani ga Allah har sai sanda ya haƙurtar da kansa abisa jarabawowin da Allah buwayi yake jarabtarsa dasu a rayuwarsa ya kuma jure bai gaza cin wannan jarabawar ba, lallai kada mu manta! Tabbas dukkanin girman wata jarabawa, tana tareda girman kyakkyawan sakamako a gurin Allah, ya Allah ka jarabcemu daidai imanin mu”