WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE ➖➖➖➖➖➖➖➖➖ FITOWA TA ‘DAYA
Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai* Abinda Ake Nufi da *Biyayya* Shine Kyautatawa Da Aikata Alheri da Kuma Bayar da Kyauta. A Takaice, *Biyayya* Suna ne da ya Kunshi Aikata Dukkan Wani Alheri. Kalmar *Birru* (Biyayya) Suna ne Daga Cikin Sunayen *Allah Madaukaki*, Ubangiji Yana Cewa: *{ﺇِﻧَّﺎ ﻛُﻨَّﺎ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻞُ ﻧَﺪْﻋُﻮﻩُ ﺇِﻧَّﻪُ ﻫُﻮَ ﺍﻟْﺒَﺮُّ ﺍﻟﺮَّﺣِﻴﻢُ ﴾ [ ﺍﻟﻄﻮﺭ :٢٨ ] .}* Ma’ana: *“Lallai Mun Kasance a Baya Muna Kiransa (Bauta Masa) Lallai Shi (Allah) Mai Kyautatawa ne (Ga Bayinsa), Mai Jinqai”.* (Dur: 28). Abinda Ake Nufi da Kyautatawa Iyaye Kuma Shine: Kyautatawa Zuwa Garesu ta Hanyar Zance da Aiki da Kuma Kusanta Zuwa ga *Allah* Madaukaki. *Ubangiji* Yayi Mana Wasici da Yiwa Iyaye Biyayya a Ayoyi Masu Tarin Yawa a Cikin Alqur’ani, Wanda Hakan Kawai Ya Isa Mu Fahimci Girma da Kuma Qimar Iyaye Wadanda Sune Sila ta Zuwan Mu Gidan Duniya. *Allah ﷻ* Yana Cewa: *{ﻭَﺍﻋْﺒُﺪُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺸْﺮِﻛُﻮﺍ ﺑِﻪِ ﺷَﻴْﺌًﺎ ﻭَﺑِﺎﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﺇِﺣْﺴَﺎﻧًﺎ ﴾ [ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : ٣٦]}* _Ma’ana: *“Ku Bautawa Allah Kada Ku Hadashi da Kowa (A Cikin Bauta), Kuma Iyaye Ku Kyautata Musu”*. (Nisa’i: 36)._ A Cikin Wannan Ayar Mai Albarka, Ubangiji Ya Gwama Kira Zuwa ga Kadaitashi da Bauta da Biyayya ga Iyaye da Kyautatawa Zuwa Garesu. Kuma Sau da Yawa Haka Ubangiji Yake Hada Kansa da Iyaye a Cikin Aya ‘Daya. Kamar Inda Yake Cewa: *{ﺃَﻥِ ﺍﺷْﻜُﺮْ ﻟِﻲ ﻭَﻟِﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻚَ ﺇِﻟَﻲَّ ﺍﻟْﻤَﺼِﻴﺮُ ﴾ [ ﻟﻘﻤﺎﻥ : ١٤]}.* Ma’ana: *“Ka Godemin Sannan Ka Godewa Iyayenka Gareni Makoma Take”*. (Luqman:14). Har Wayau *ﷻ Allah* Yana Cewa: *{ﻭَﻗَﻀَﻰ ﺭَﺑُّﻚَ ﺃَﻟَّﺎ ﺗَﻌْﺒُﺪُﻭﺍ ﺇِﻟَّﺎ ﺇِﻳَّﺎﻩُ ﻭَﺑِﺎﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﺇِﺣْﺴَﺎﻧًﺎ ﺇِﻣَّﺎ ﻳَﺒْﻠُﻐَﻦَّ ﻋِﻨْﺪَﻙَ ﺍﻟْﻜِﺒَﺮَ ﺃَﺣَﺪُﻫُﻤَﺎ ﺃَﻭْ ﻛِﻠَﺎﻫُﻤَﺎ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻘُﻞْ ﻟَﻬُﻤَﺎ ﺃُﻑٍّ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻨْﻬَﺮْﻫُﻤَﺎ ﻭَﻗُﻞْ ﻟَﻬُﻤَﺎ ﻗَﻮْﻟًﺎ ﻛَﺮِﻳﻤًﺎ * ﻭَﺍﺧْﻔِﺾْ ﻟَﻬُﻤَﺎ ﺟَﻨَﺎﺡَ ﺍﻟﺬُّﻝِّ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﺔِ ﻭَﻗُﻞْ ﺭَﺏِّ ﺍﺭْﺣَﻤْﻬُﻤَﺎ ﻛَﻤَﺎ ﺭَﺑَّﻴَﺎﻧِﻲ ﺻَﻐِﻴﺮًﺍ *ﺭَﺑُّﻜُﻢْ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﻤَﺎ ﻓِﻲ ﻧُﻔُﻮﺳِﻜُﻢْ ﺇِﻥْ ﺗَﻜُﻮﻧُﻮﺍ ﺻَﺎﻟِﺤِﻴﻦَ ﻓَﺈِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻟِﻠْﺄَﻭَّﺍﺑِﻴﻦَ ﻏَﻔُﻮﺭًﺍ ﴾ [ ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ :٢٣-٢٥}* Ma’ana: *“Ubangijinka ya Hukunta Kada a Bautawa Wani Sai Shi Kadai Kuma Iyaye a Kyautata Musu; Idan ‘Daya Daga Cikinsu Girma Yazo Masa a Wurinka Ko Duka Biyun (Mahaifi da Mahaifiya), Kada Kace Masu Tir, Kuma Kada Kayi Musu tsawa, Ka Fada Musu Zance Mai Girma (Me Dadi)……………..”.* (Isra’i: 23-25). A Wata Aya Kuma *Ubangiji* Yana Cewa: *{ﻭَﻭَﺻَّﻴْﻨَﺎ ﺍﻟْﺈِﻧْﺴَﺎﻥَ ﺑِﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻪِ ﺣُﺴْﻨًﺎ ﴾ [ ﺍﻟﻌﻨﻜﺒﻮﺕ : ٨]}.* Ma’ana: *“Munyi Wasici ga Mutum da Ya Kyautatawa Mahaifansa”.* (Ankabut: 8). *Imam Ibn Kathir (rh)* Yana Cewa: “Ubangiji Ya Umurci Bayinsa da Kyautatawa Mahaifa Bayan Ya Kwadaitar da Kadaitashi da Bauta. Domin Mahaifa Sune Sababin Zuwan Mutum Duniya, Saboda Haka Sune Sukafi Dacewa da a Kyautata Musu. Mahaifi ta Hanyar Ciyar Dashi Ita Kuma Mahaifiya ta Hanyar Tausaya Mata”. *(Tafseer Ibn Kathir: v6/ p238)*. *BIYAYYA GA IYAYE SIFFAR ANNABAWA NE* ➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖ Hakika *Ubangiji* Madaukaki Ya Siffanta Wasu Daga Cikin Annabawansa da Kasancewarsu Masu Matukar Biyayya ga Iyayensu Inda Yake Cewa a Cikin Littafinsa: *{ﻳَﺎ ﻳَﺤْﻴَﻰ ﺧُﺬِ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏَ ﺑِﻘُﻮَّﺓٍ ﻭَﺁﺗَﻴْﻨَﺎﻩُ ﺍﻟْﺤُﻜْﻢَ ﺻَﺒِﻴًّﺎ * ﻭَﺣَﻨَﺎﻧًﺎ ﻣِﻦْ ﻟَﺪُﻧَّﺎ ﻭَﺯَﻛَﺎﺓً ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺗَﻘِﻴًّﺎ * ﻭَﺑَﺮًّﺍ ﺑِﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻪِ ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﺟَﺒَّﺎﺭًﺍ ﻋَﺼِﻴًّﺎ * ﻭَﺳَﻠَﺎﻡٌ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻳَﻮْﻡَ ﻭُﻟِﺪَ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﻳَﻤُﻮﺕُ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﻳُﺒْﻌَﺚُ ﺣَﻴًّﺎ ﴾ [ ﻣﺮﻳﻢ : 12 – 15 ]}.* Ma’ana: *“Ya Yahya ka Riqe Littafi da Karfi Mun Bashi Hukunci Yana Karami# Yana Mai Biyayya ga Iyayensa be Kasance Me Girman Kai me Sa6awa Ubangiji ba# Aminci Ya Tabbata a Gareshi Ranar da Aka Haifeshi, da Ranar da Zai Mutu da Ranar da Za’a Tasheshi Yana rayayye”.* (Maryam: 12-15). Ubangiji* Yana Cewa Game da Annabi *Isah (as): *{ﻗَﺎﻝَ ﺇِﻧِّﻲ ﻋَﺒْﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺁﺗَﺎﻧِﻲَ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏَ ﻭَﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻧَﺒِﻴًّﺎ * ﻭَﺟَﻌَﻠَﻨِﻲ ﻣُﺒَﺎﺭَﻛًﺎ ﺃَﻳْﻦَ ﻣَﺎ ﻛُﻨْﺖُ ﻭَﺃَﻭْﺻَﺎﻧِﻲ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﺍﻟﺰَّﻛَﺎﺓِ ﻣَﺎ ﺩُﻣْﺖُ ﺣَﻴًّﺎ * ﻭَﺑَﺮًّﺍ ﺑِﻮَﺍﻟِﺪَﺗِﻲ ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﺠْﻌَﻠْﻨِﻲ ﺟَﺒَّﺎﺭًﺍ ﺷَﻘِﻴًّﺎ * ﻭَﺍﻟﺴَّﻠَﺎﻡُ ﻋَﻠَﻲَّ ﻳَﻮْﻡَ ﻭُﻟِﺪْﺕُ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﺃَﻣُﻮﺕُ ﻭَﻳَﻮْﻡَ ﺃُﺑْﻌَﺚُ ﺣَﻴًّﺎ * ﺫَﻟِﻚَ ﻋِﻴﺴَﻰ ﺍﺑْﻦُ ﻣَﺮْﻳَﻢَ ﻗَﻮْﻝَ ﺍﻟْﺤَﻖِّ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻓِﻴﻪِ ﻳَﻤْﺘَﺮُﻭﻥَ ﴾ [ ﻣﺮﻳﻢ :٣٠ -٣٤]}* Ma’ana: *“Yace Ni Bawan Allah ne An Bani Littafi Kuma an Sanyani Na Zamo Annabi# Kuma Aka Sanyani Me Albarka a Duk Inda Na Kasance Akayimin Wasici dayin Sallah da Bayar da Zakkah Matukar Ina Raye# Kuma Me Biyayya ga Mahaifiyata be Sanyani Me Taurin Kai Mara Rabo ba# Aminci Ya Tabbata a Gareni Ranar da Aka Haifeni da Ranar da Zan Mutu da Kuma Ranar da Za’a Tasheni Rayayye# Wannan Shine Isah ‘Dan Maryam, Zance Né Na Gaskiya Wanda Suke Musu”* (Maryam: 30-34). Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك* WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE ➖➖➖➖➖➖➖➖➖ FITOWA TA BIYU _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_ _*KWADAITARWAR MANZON ALLAH (ﷺ) GAME DA BIYAYYA GA IYAYE*_ _Hakika *Manzon Allah(ﷺ)* Ya Kwadaitar da Wannan Al’ummah Lada da Kuma Falalar Biyayya da Iyaye Hatta Iyayen da Musulmai ba, Sannan Kuma Ya tsoratar game da Sa6a Musu, Kamar Yanda Zamu Gani a Hadisai Masu Zuwa:_ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩٍ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﺳﺄﻟﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﻠﺖ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﺃﻱ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺃﻓﻀﻞ؟ ﻗﺎﻝ : )) ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻰ ﻣﻴﻘﺎﺗﻬﺎ (( ،ﻗﻠﺖ : ﺛﻢ ﺃﻱ؟ ﻗﺎﻝ : )) ﺛﻢ ﺑﺮُّ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦِ (( ،ﻗﻠﺖ : ﺛﻢ ﺃﻱ؟ ﻗﺎﻝ : )) ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ (( ؛ ( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺣﺪﻳﺚ ٥٢٧ / ﻣﺴﻠﻢ ﺣﺪﻳﺚ ٨٥)}* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Mas’ud (ra)* Yace: Na Tambayi *Manzon Allah (ﷺ)* Nace: Ya Annabin Allah, Wane Aiki ne Yafi Falala? Sai Yace: *“Sallah Akan Lokacinta”.* Sai Nace Sannan Me? Sai Yace: *“Sannan Biyayya ga Iyaye”*. Sannan Nace Sai Mene? Sai Yace: *“Jihadi don ‘Daukaka Kalmar Allah”*. (Bukhari:257, Muslim:85)._ _Ya Dan Uwa Ka Duba Girman Jihadi don Daukaka Kalmar Allah, Wanda Duk Wanda Ya Mutu a Halin Jihadi Bashi da Sakamakon da ya Gaza Shiga Aljannah, Sannan Ko Hisabi Baza’ayi Musu ba Saboda Falalar Abinda Suka Mutu Akai. Tare da Haka *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Gabatar da Biyayya gareshi._ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ : ﺟﺎﺀ ﺭﺟﻞ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺎﺳﺘﺄﺫﻧﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ،ﻓﻘﺎﻝ : )) ﺃﺣﻲٌّ ﻭﺍﻟﺪﺍﻙ؟ (( ، ﻗﺎﻝ : ﻧﻌﻢ،ﻗﺎﻝ : )) ﻓﻔﻴﻬﻤﺎ ﻓﺠﺎﻫِﺪْ (( ؛ ( ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺣﺪﻳﺚ ٣٠٠٤ / ﻣﺴﻠﻢ ﺣﺪﻳﺚ ٢٥٤٩)}.* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Amru (ra)* Yace: Wani Mutum Yaje Wurin *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Neman Ayi Masa Izinin Fita Jihadi, sai *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Shin Iyayenka Suna Raye?”* Sai Mutumin Yace Eh. Sai *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Kaje Kayi Jihadinka a Wurinsu”.* (Bukhari: 3004, Muslim: 2549)._ _*Imam Ibn Hajar Al-Asqalany (rh)* Yayi Karin Bayani Game da Wannan Hadisin Inda Yake Cewa: “Jihadi Yana Haramta Matukar Iyaye Basu Amince da Fitar ba, Amma da Sharadin Iyayen su Zamo Musulmai. Domin Yi Musu Biyayya Farillah ce ta Ainihi (Wajibi), Fita Jihadi Kuma Farillah ce ta Kifaya (Mustahabbi)”. *(Fathul Bary: V-6, p163)*_ *{ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ، ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : )) ﻻ ﻳَﺠﺰﻱ ﻭﻟﺪٌ ﻭﺍﻟﺪًﺍ ﺇﻻ ﺃﻥ ﻳﺠﺪَﻩ ﻣﻤﻠﻮﻛًﺎ ﻓﻴﺸﺘﺮﻳَﻪ ﻓﻴُﻌﺘﻘَﻪ (( ؛ ( ﻣﺴﻠﻢ – ﺣﺪﻳﺚ ١٥١٠)}* _An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“’Da Bazai Iya Sakawa Mahaifinsa ba Sai fa Idan Ya Samu Mahaifin ne a Matsayin Bawa, Sai Ya Siyeshi Sannan Ya ‘Yantashi”*. (Muslim: 1510)._ *{ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪٍ ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ : ﺃﻥ ﺭﺟﻠًﺎ ﻫﺎﺟﺮ ﺇﻟﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣِﻦ ﺍﻟﻴﻤﻦ، ﻓﻘﺎﻝ : )) ﻫﻞ ﻟﻚ ﺃﺣﺪ ﺑﺎﻟﻴَﻤﻦ؟ (( ، ﻗﺎﻝ : ﺃﺑﻮﺍﻱ،ﻗﺎﻝ : )) ﺃَﺫِﻧﺎ ﻟﻚ؟ (( ، ﻗﺎﻝ : ﻻ،ﻗﺎﻝ : )) ﺍﺭﺟِﻊْ ﺇﻟﻴﻬﻤﺎ ﻓﺎﺳﺘﺄﺫﻧﻬﻤﺎ، ﻓﺈﻥ ﺃﺫﻧﺎ ﻟﻚ ﻓﺠﺎﻫِﺪْ، ﻭﺇﻻ ﻓﺒَﺮَّﻫﻤﺎ (( ؛ ( ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ) ( ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ ﺣﺪﻳﺚ ٢٢٠٧)}.* _An Kar6o Daga *Abi-Sa’eedil Khudry (ra)*, Lallai Wani Mutum Yayi Hijirah Daga Yaman Zuwa Wurin *Manzon Allah(ﷺ)* Sai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace Dashi: *“Shin Kanada Wani a Yaman?”*. Sai Mutumin Yace: Eh Inada Iyaye na. Sai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *“Shin Su Sukayi Maka Izini?”* Sai Yace: A’a. Sai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace Dashi: *“Ka Koma Zuwa Garesu Ka Nemi Izininsu, Idan Sukayi Maka Izini Sai Kazo Kayi Jihadi. Idan Kuma Sukaqi Amincewa, to Kayi Musu Biyayya”*. (Abi-Daud: 2207)._ _An Kar6o Daga *Jabir bn Abdullah (ra)* Lallai Wani Mutum Yace: Ya *Manzon Allah (ﷺ)* Lallai Inada Dukiya da Yaro, Kuma Mahaifiya Yanason Ya Kwace Dukiyata. Sai *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Kai da Dukiyarka Ai Na Mahaifinka ne”.* (Ibn-Majah:1855)._ _*Imamud ‘Dahãwy (rh)* Yana Cewa: “Wani 6angare Na Malamai Suna Cewa: “Duk Abinda Yaro Zai Samu Nashi ne Shi Kadai Banda Mahaifinsa. Zancen da *Manzon Allah (ﷺ)* Yayi ba Yana Nuna Cewa Duk Abinda Yaro ya Mallaka Mallakin Ubansa Bane. Abinda Yake Nufi Shine Baya Kamata Ga Yaro Ya Sa6awa Mahaifinsa Saboda Wani Abu, Wajibine Yayi Masa Biyayya Gwargwadon Iko”. (Sharhu Ma’anil Ãthar Lid ‘Dahãwy: Vol. 4, P. 169)._ _Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_ *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك* WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE ➖➖➖➖➖➖➖➖➖ FITOWA TA UKU _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_ _*ZANTUKAN MAGABATA NA KWARAI*_ _*GAME DA BIYAYYA GA IYAYE*_ _Idan Bamu Manta ba, a Rubutu Mu Daya Gabata Mun Fara Kawo Maganganun Magabata Na Kwarai Game da Yiwa Iyaye Biyayya. A Yau Idan Allah Ya Yarda Zamu Cigaba daga Inda Muka tsaya._ *{ﻗﺎﻝ ﻟﻘﻤﺎﻥ ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ ﻻﺑﻨﻪ : ﻳﺎ ﺑﻨﻲ، ﻣَﻦ ﺃﺭﺿﻰ ﻭﺍﻟﺪﻳﻪ ﻓﻘﺪ ﺃﺭﺿﻰ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦَ، ﻭﻣﻦ ﺃﺳﺨَﻄﻬﻤﺎ ﻓﻘﺪ ﺃﺳﺨَﻂ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦَ؛ ( ﺑﺮ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ – ﻷﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﺍﻟﻄﺮﻃﻮﺷﻲ ﺹ – ٣٧)}* _*Luqman* Yana Cewa ‘Dansa: *“Yakai ‘Dãna! Duk Wanda Ya Yardar da Mahaifansa, Hakika Ya Yardar da Me Rahama. Kuma Duk Wanda Ya Fusatasu, Hakika Ya Fusata Me Rahama”*. (Birrul Walidain Na Abi-Bakar ‘Dardushy: P. 8)._ _Hakika Wannan Zance Na Luqman Yayi Daidai da Zancen *Annabi* Da Yake Cewa: *“Yardan Allah Yana Cikin Yardan Iyaye, Kuma Fushin Ubangiji Yana Cikin Fushin Mahaifa”*. Saboda Haka Idan Kana Bukatar Ubangiji Ya Yarda Dakai, to ka Kyautatawa Mahaifansa Har Su Yarda Dakai. Idan Kuma Kafi Bukatar Fushin Ubangiji da Uqubarsa, to Ka Cigaba da Wulakantasu Lallai Ubangijin Shi Kuma Yana nan a Madaka._ *{ﻗﺎﻝ ﻟﻘﻤﺎﻥ ﻻﺑﻨﻪ : ﻳﺎ ﺑﻨﻲ، ﺇﻥ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦِ ﺑﺎﺏٌ ﻣﻦ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﺇﻥ ﺭﺿﻴَﺎ ﻋﻨﻚ ﻣﻀﻴﺖَ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﻭﺇﻥ ﺳﺨِﻄﺎ ﺣُﺠِﺒﺖ؛ ( ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ٨٠)}* _Har Wayau *Luqman* Yana Fadawa ‘Dansa Cewa: *“Lallai Mahaifa Kofa ne Daga Cikin Kofofin Aljannah, Idan Suka Yarda Dakai Zaka Zarce Aljannah. Idan Kuma Sukayi Fushi Dakai, Za’a Shamakanceka Daga Shiga Aljannah”*. (Kitabul Birr Was Sila Na *Ibn Jauzy* p. 80)._ *{ﺭﻭﻯ ﻋﺒﺪﺍﻟﺮﺯﺍﻕ ﻋﻦ ﻃﺎﻭﺱ ﺑﻦ ﻛﻴﺴﺎﻥ ﻗﺎﻝ : ﻣِﻦ ﺍﻟﺴﻨَّﺔ ﺃﻥ ﻳﻮﻗَّﺮَ ﺃﺭﺑﻌﺔ : ﺍﻟﻌﺎﻟﻢ، ﻭﺫﻭ ﺍﻟﺸَّﻴﺒﺔ، ﻭﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ، ﻭﺍﻟﻮﺍﻟﺪ، ﻗﺎﻝ : ﻭﻳﻘﺎﻝ : ﺇﻥ ﻣِﻦ ﺍﻟﺠﻔﺎﺀ ﺃﻥ ﻳﺪﻋﻮَ ﺍﻟﺮﺟﻞُ ﻭﺍﻟﺪَﻩ ﺑﺎﺳﻤِﻪ؛ ( ﻣﺼﻨﻒ ﻋﺒﺪﺍﻟﺮﺯﺍﻕ – ﺝ – ١١ – ﺭقم ٢٠١٣٣)}* _*Abdulrazak* Ya Ruwaito Daga *’Dawus bn Kaisãn* Yace: *“Yana Daga Cikin Sunnah a Girmama Mutane Hudu: Malami, da Mutum Me Furfura, da Shugaba da Kuma Mahaifi”*. Ya Kasance Yana Cewa: “Yana Daga Cikin Jafa’i Mutum Ya Kira Mahaifinsa da Sunansa”. (Musannaf Abdulrazaq: Vol. 11 No. 20133)._ *{ﻟﻤﺎ ﻣﺎﺗﺖ ﺃﻡ ﺇﻳﺎﺱ ﺑﻦ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺑﻜﻰ، ﻗﻴﻞ ﻟﻪ : ﻣﺎ ﻳﺒﻜﻴﻚ؟ ﻗﺎﻝ : ﻛﺎﻥ ﻟﻲ ﺑﺎﺑﺎﻥِ ﻣﻔﺘﻮﺣﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﻭﻏُﻠِّﻖ ﺃﺣﺪُﻫﻤﺎ؛ ( ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ – ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ٧٢)}* _A Yayin da Mahaifiya *Iyyas bn Mu’awiya* Ta Rasu Yayita yin Kuka. Sai Akace Dashi Menene Yake Sakaka Kuka? Sai Yace: *“Na Kasance Inada Kofofi Guda Biyu Budaddu Zuwa ga Aljannah, A Yau An Kulle Guda ‘Daya”.* (Kitabul Birri Was Silah Na *Ibn Jauzy*: P. 72)._ *{ﻗﺎﻝ ﻣﻜﺤﻮﻝ ﺍﻟﺸﺎﻣﻲ : ﺑﺮُّ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ ﻛﻔَّﺎﺭﺓٌ ﻟﻠﻜﺒﺎﺋﺮ؛ ( ﺷﺮﺡ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻟﻠﺒﻐﻮﻱ ﺝ – ١٣ ﺹ – ١٣)}* _*Makhul Ash-Shamy* Yana Cewa: *“Biyayya ga Iyaye Yana Kankare Manyan Zunubai”*. (Sharhu Sunnah Na Bagawy: Vol. 13, p. 13)._ *{ﻗﺎﻝ ﺳﻔﻴﺎﻥ ﺑﻦ ﻋﻴﻴﻨﺔ : ﻣَﻦ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕِ ﺍﻟﺨﻤﺲَ ﻓﻘﺪ ﺷﻜﺮ ﻟﻠﻪ، ﻭﻣﻦ ﺩﻋﺎ ﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻪ ﻋﻘﺒﻬﺎ ﻓﻘﺪ ﺷﻜﺮ ﻟﻬﻤﺎ؛ ( ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ – ﻻﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﺍﻟﻌﺴﻘﻼﻧﻲ – ﺝ – ٢ – ﺹ – ١٠)}* _*Sufyãn bn Uyaina* Yana Cewa: *“Duk Wanda ya Sallaci Sallolli Biyar, Hakika Ya Godewa Allah. Wanda Duk Yayiwa Iyayensa Addu’a Bayan Sallolin, Hakika Ya Godewa Iyayensa”*. (Fathul Bary: Vol. 2, P. 10)._ *{ﻗﺎﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﺤﻴﺮﻳﺰٍ : ﻣَﻦ ﻣﺸﻰ ﺑﻴﻦ ﻳﺪَﻱْ ﺃﺑﻴﻪ ﻓﻘﺪ ﻋﻘَّﻪ، ﺇﻻ ﺃﻥ ﻳﻤﺸﻲ ﻓﻴﻤﻴﻂ ﻟﻪ ﺍﻷﺫﻯ ﻋﻦ ﻃﺮﻳﻘﻪ، ﻭﻣﻦ ﺩﻋﺎ ﺃﺑﺎﻩ ﺑﺎﺳﻤﻪ ﺃﻭ ﺑﻜﻨﻴﺘﻪ ﻓﻘﺪ ﻋﻘَّﻪ، ﺇﻻ ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻝ : ﻳﺎ ﺃﺑﺖِ؛ ( ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ – ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ١١٧)}* _*Muhammad bn Muhairiz* Yace: *“Duk Wanda Yake Tafiya a Gaban Mahaifinsa, Hakika Ya Sa6a Masa; Sai fa Idan Ya Shiga Gaban Nasa ne Domin Kauda Abinda Zai Cutar Dashi ne. Kuma Duk WanKumYa Kira Mahaifinsa da Sunansa ko da Alkunyarsa Hakika Ya Sa6a Masa, Sai Dai Idan Zaice Ya Mahaifina”.* (Al-Birri Was Silah Na *Ibn Jauzy*: 117)._ *{ﻗﺎﻝ ﻣﺠﺎﻫﺪُ ﺑﻦ ﺟﺒﺮٍ : ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻟﻠﻮﻟﺪ ﺃﻥ ﻳﺪﻓﻊ ﻳﺪَ ﻭﺍﻟﺪﻩ ﻋﻨﻪ ﺇﺫﺍ ﺿﺮﺑﻪ، ﻗﺎﻝ : ﻭﻣَﻦ ﺷﺪ ﺍﻟﻨﻈﺮ ﺇﻟﻰ ﻭﺍﻟﺪﻳﻪ ﻓﻠﻢ ﻳَﺒَﺮَّﻫﻤﺎ، ﻭﻣَﻦ ﺃﺩﺧﻞ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺣﺰﻧًﺎ ﻓﻘﺪ ﻋَﻘَّﻬﻤﺎ؛ ( ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ – ﻻﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ – ﺹ – ١١٧)}* _*Mujãhid bn Jubrin* Yana Cewa: *“Baya Dacewa ga Yaro Ya Ture Hannuna Mahaifinsa a Lokacin da Yake Dukansa. Wanda Duk Ya tsananta Kallo ga Mahaifinsa, be Girmamashi ba. Duk Wanda Ya Sanyasu Damuwa, Hakika Ya Sa6a Musu”*. (Albirru Was Silah Na *Ibn Jauzy*: 117)._ _Dan Uwa Ka Duba Kaga Yanda Magabata Suke Girmama Sha’anin Mahaifa, Yanda Suke Ganin Sa6a Musu da Fusatasu Tamkar Yankan Tikitin Jahannama ne._ _Yanzu Ya Rage Gareni Dakai Mu Duba Alaqar Dake tsakanin mu da Mahaifan Mu, Shin Akwai Kyakkywan Alaqa tsakanin Mu Dasu? Idan Akwai Sai Mu dage Wajen Kara Kyautata Musu. Idan Kuma Babu Kyakkyawar Alaqa a tsakaninmu, Sai Mu Koma Mu Roqesu Gafara Kafin Lokaci Ya Qure Domin Samun tsira Anan Duniya Da Gobe Qiyama._ _*Allah Ka Sakawa Iyayenmu da Alkhairi, Wadanda Suka Rasu Kuma Ka Gafarta Musu Kasa Aljannah Ce Makomarsu*_ _Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_ *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك* WAJIBCIN BIYAYYA GA IYAYE FITOWA TA HUDU _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_ _*ADDU’AR IYAYE NAGARI KARBABBA CE*_ _Lallai Yana Daga Cikin Girmamawa da Ubangiji Yayiwa Iyaye Nagari Shine Amsar Addu’arsu Nagari da ma Wanda ba Nagari ba ga ‘Ya’yansu, Musamman a Lokacin da Girma Yazo Musu. Wannan Kuma Abu ne da Yake Aukuwa Akan Idanun mu a Wannan Rayuwar Tamu ta Duniya. Hakika *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Fadakar Damu Akan Haka a Cikin Hadisai Masu Yawa, ga Kadan Daga Cikinsu:_ *{ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ، ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ”ﺛﻼﺙُ ﺩﻋﻮﺍﺕٍ ﻣﺴﺘﺠﺎﺑﺎﺕ : ﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻤﻈﻠﻮﻡ، ﻭﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻤﺴﺎﻓﺮ، ﻭﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ ﻋﻠﻰ ﻭﻟﺪﻩ“. (صحيح في أدب الهفرد:٤٨٨)}* _An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)*, Daga *Annabi (ﷺ)* Yace: *“Addu’ar Guda Uku Kar6a66u ne: Addu’ar Wanda Aka Zalunta; da Addu’ar Matafiyi; da Kuma Addu’ar Mahaifi Akan ‘Dansa”.* Hadisi ne Ingantacce (Sahih Adabul Mufrad: 488)._ _*Hasanul Basary* Yana Cewa: “Addu’ar Mahaifa Tana Tabbatar da Dukiyar Yaro. Sannan Addu’ar Mahaifa Tana Sadar da Dukiya Yaro”. (Al-Birru Was-Sila Na *Ibn Jauzy*: 120- 123)._ _*YARDAN IYAYE NAGARI TANA DAGA YARDAR ALLAH*_ _Wajibi ne Mu Sani Cewa Lallai Akwai Dangantaka tsakanin Yardan Ubangiji da Kuma Amincewar Mahaifa. Saboda Hakane Ya Zam Wajibi Akan ‘Ya’ya da Su Kwadaitu Wajen Neman Yardan Mahaifansu ta Hanyar Yi Musu Biyayya a Cikin Abinda Be Sa6awa Mahalicci ba, Domin Samun Yardan Allah Anan Duniya da Gobe Kiyama. Hakika Annabin Mu Ya Shiryar Damu Haka a da Dama Daga Cikin Haidisansa:_ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮٍﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ، ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ”ﺭﺿﺎ ﺍﻟﺮﺏِّ ﻓﻲ ﺭﺿﺎ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ، ﻭﺳﺨَﻂ ﺍﻟﺮﺏِّ ﻓﻲ ﺳﺨﻂ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ“. (ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ) ( ﺻﺤﻴﺢ الترمذي:١٥٤٩)}* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Amru bn Ass (ra)*, Daga *Annabi (ﷺ)* Yace: *“Yardar Ubangiji Tana Cikin Yardan Mahaifa, Kuma Fushin Ubangiji Yana Cikin Fushin Mahaifa”*. Hadisi ne Ingantacce (Sahih Tirmizi: 1549)._ _Wannan Hadisi Dalili ne Akan Falalar Kyautatawa Mahaifa da Kuma Wajibcin Yin Hakan. Domin Aikata Hakan Shine Sababin Samin Yardan Ubangiji. Sannan Har Wayau Hadisin Yana Razanarwa Akan Sa6awa Mahaifa da Kuma Haramcin Sa6a Musu. Domin Sa6a Musun Yana Sabbabawa Mutum Haduwa da Fushin Ubangiji._ *{ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﻗﺎﻝ : ”ﻛﺎﻧﺖ ﺗﺤﺘﻲ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻭﻛﻨﺖ ﺃﺣﺒﻬﺎ، ﻭﻛﺎﻥ ﻋﻤﺮ ﻳﻜﺮﻫﻬﺎ، ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻲ : ﻃﻠِّﻘْﻬﺎ، ﻓﺄﺑﻴﺖُ، ﻓﺄﺗﻰ ﻋﻤﺮُ ﺍﻟﻨﺒﻲَّ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺬﻛﺮ ﺫﻟﻚ ﻟﻪ، ﻓﻘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻃﻠِّﻘْﻬﺎ“. (ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ )( ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﻟﻸﻟﺒﺎﻧﻲ ﺣﺪﻳﺚ: ٤٢٨٤)}* _An Kar6o Daga *Abdullahi bn Umar bn Khaddab (ra)* Yace: *“Na Kasance Inada Mata Kuma Ina Matukar Sonta, Umar Kuma Ya Kasance Baya Sonta, Sai Yace Dani: “Na Saketa, Sai Naqi Sakinta. Sai Umar Yaje Wurin Manzon Allah (ﷺ) Ya Ambata Masa Abinda Ke Faruwa, Sai Annabi Yace Ya Saketa”*. (Abi-Daud: 4284)._ _*Fa’idah Mai Muhimmanci:* _Yakamata Iyaye Su Fahimci Cewa Wanda Ya Nemi ‘Dansa da ya Saki Matarsa *Umar bn Khaddab* ne. Ba Kowane Uba Bane Yake da Ikon Aiwatar da Abinda *Umar* Ya Nemi ‘Dansa dayi ba. Musamman Ma Idan Aka Samu Sa6ani tsakanin Mahaifin Yaro da Matar Yaron Akan Abin Duniya, Mahaifin Yaro Kamata Yayi Ya Duba Mas’alar ta Hanyar Adalci, Idan Har Matarc da Gaskiya, Wajibi ne a Tabbatar Mata da Gaskiyarta Uban Kuma Yayi Hakuri Kada Yace Zai Tursasa ‘Dansa Akan Ya Saki Matarsa. Amma Idan Laifinta Ya Sa6awa Ubangiji ne Kamar Batayin Sallah, Ko Magulmaciya ce, Kuma Anyi Mata Nasiha Taqiji, Wannan Uban Miji Yanada Iko Akan Ya Umurci ‘Dansa da ya Saki Matarsa Kamar Yanda *Umar* Yayi. Kuma Wajibi ne ‘Dan Nasa Yayi Masa Biyayya._ _Wani Mutum Ya Tambayi *Imam Ahmad bn Hambal* Cewa: Lallai Mahaifinsa Ya Umurceshi da ya Saki Matarsa, Sai *Imam Ahmad* Yace: *“Kada Ka Sake ta”*. Sai Mutumin Yace: Shin ba *Umar* Ya Umurci ‘Dansa *Abdullahi* da ya Saki Matarsa ba? Sai *Imam Ahmad* Yace: *“Ka Bari Har Sai Mahaifinka Ya Zamo Kwatankwacin Umar”*. (Al-Adabush Shar’iyya)._ _An Tambayi *Imam Ibn Taimiyya (rh)* Game da Mutumin da Mahaifiyarsa ta Umurcesa da ya Saki Matarsa. Sai. *Ibn Taimiyya* Yace: *“Baya Halatta a Gareshi da Ya Saki Matarsa, Sai dai Wajibi ne Yayi Mata Biyayya, Amma Sakin Matarsa Baya Cikin Yi Mata Biyayya”*. (Adabush Shar’i: 447)._ *{ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺪﺭﺩﺍﺀ : ﺃﻥ ﺭﺟﻠًﺎ ﺃﺗﺎﻩ ﻓﻘﺎﻝ : ﺇﻥ ﻟﻲ ﺍﻣﺮﺃﺓً، ﻭﺇﻥ ﺃﻣﻲ ﺗﺄﻣﺮﻧﻲ ﺑﻄﻼﻗﻬﺎ،ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﺪﺭﺩﺍﺀ : ﺳﻤﻌﺖُ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ : ”ﺍﻟﻮﺍﻟﺪُ ﺃﻭﺳﻂُ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻨﺔ, ﻓﺈﻥ ﺷﺌﺖَ ﻓﺄﺿِﻊْ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺒﺎﺏ، ﺃﻭ ﺍﺣﻔَﻈْﻪ“. ( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ: ١٥٤٨}* _An Kar6o Daga *Abi-Darda’i (ra)* Lallai Wani Mutum Yazo Masa Sai Yace: Lallai Inada Mata, Kuma Mahaifiyata ta Umurceni Dana Saketa. Sai *Abi-Darda’i* Yace: Dashi: Naji *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa: *“Mahaifa Sune Mafi Alkhairin Kofofin Aljannah. Idan Kaso Ka Tozarta Wannan Kofar, Ko Kuma Ka Kiyayeta”*. (Tirmizi: 1548)._ _Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_ *سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك* IDAN KUNASO MUCI GABA SAI KUYI MANA MAGANA TA EMAIL