1 – Al-Faatiha – الفاتحة 00:00 1:1 – Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.1:2 – Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;1:3 – Mai rahama, Mai jin ƙai;1:4 – Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.1:5 – Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.1:6 – Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.1:7 – Hanyar waɗanda Ka yi wa ni’ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.