NEMAN AURE AMUSULUNCI
Dasunan Allah mai rahama maijinkai Haqiqa ANeman Aure yanada matukar amfani musan dokoki da ka idoji da hakkokin ta. AMUSULUNCI Dan kankanin Bincikena da kuma baiwar Da Allah yayi mani zanyi rubutu bisa abinda nake karantawa dakuma wadanda nake gani.


A Zamantakewarmu tayau da kullum. Neman aure. Muhimmin abune GA mutane musani kuma mukiyayesu. Zangina zantukana ne akan wannan muhimmin hadisi, ruwayar Bukhari da Muslim. Manzon Allah (s.a.w) yace “Ana Auren mace don abubuwa guda biyar 1:-kyawunta 2:-nasabar danginta 3:-addininta 4:-dukiyarta 5:-kyawu halinta Sai kuma yace kazabi ma abociyar addini zata zamomana. Yalwar hanu Abin ake cewa yalwar hanu shine zata zamo bata cutaddakai kuma bazata bari acucekaba. Dan uwa mai karatu kaga neman. Mace mai addinima nada matukar fa’ida, Idan kana Neman mace mai addini Zaka San halayenta kamar haka Haku, Kunya, Kaskantaddakai, tsoron Allah, Amana, Juriya, Kirki, mutunci da karamci. Wannan shine halayen mace mai addini, atakaice. Qa’idojin Neman Aure AMUSULUNCI :- Yazamto wacce zaka Neman tana da kamun kai. :- Yazamto tana kana sonta tana sonka son da babu tilastawa. :- Yazamto wacce kakeso tanada hankali da nutsuwa. :- Yazamto mai. Kyawun hali mai addini da tarbiyya. :- Ta zama wacce takeda nutsuwa da kamala da kyau. Ahaqiqanin gaskiya Wannan sune matakan Allah ubangiji ya daukaka musulunci da musulmi. da alkalamin Ismail Hussaini adam IHSAN Assalafy Alpholtawy Matakan Bayar da Tarbiyya Akwai matakai ko hanyoyi da ake bi wajen bayar da tarbiyya da suka haɗa da nuni, lura, umarni da kuma hani. Nuni: Abin da ake nufi da nuni a nan shi ne aikata aiki a aikace, wanda daga nan shi wanda ake tarbiyantarwa zai gani ya koya. Tirƙashi, masu iya magana sun ce; “Idan mutum ya ce zai baka riga, to duba ta jikinsa”. Wannan magana ta zo daidai da faɗin Larabawa cewa; “Maras abu baya bayar da shi”. Saboda haka dole ne mai bayar da tarbiyya ya zama mai tarbiyya. Wannan hanya ta bayar da tarbiyya ita ce mafi tasiri da kuma muhimmanci wajen bayar da tarbiyya. Saboda haka dole ne masu bayar da tarbiyya; iyaye, malaman makaranta da sauran jama’a suma su zama masu tarbiyya. Misali, dole iyaye su zama masu tsafta a aikace, kafin su dasa halin tsafta a zukatan ‘ya’yansu. Idan yaro ya tashi ya ga iyayensa suna share gida tsaf-tsaf, basa barin kwanon abinci da dauɗa, basa jefar da sutura ko’ina a ciki da wajen ɗaki, to a haka shi ma zai girma mai kula da tsafta. Kuma zai tashi shi tsafta ya sani bai san ƙazanta ba. Saboda haka da zarar ya fara zuwa makaranta malaman makaranta ba za su wahala da shi ba. Umarni da Hani (Kwaɓa): Umarni shi ne a riƙa gaya wa yaro yi kaza. Misali, idan yaro ya tsoma hannun hagu cikin kwanon abinci, ko ya riƙe abinci da hannun hagu zai kai bakinsa, sai a gaya masa cewa, wannan ba shi ne hannun cin abinci ba, ga na cin abinci nan. Da haka zai gane hannun dama dana hagu. Shi kuwa hani shi ne kore abu. A wannan gaɓar kuma yana nufin kare ko dakatar da yaro daga aikata aikin da ba mai kyau ba. A cikin wannan misalin dana kawo a sama, akwai gaurayen hani da kuma umarni. Yaro ya tsoma hannun hagu domin cin abinci, sai aka hana shi; wato aka dakatar da shi daga cigaba da amfani da hannun hagu. Sannan aka gaya masa; wato aka umarce shi da amfani da hannun dama. Lura/Kula: Lura ko kula, suna ɗaukar ma’anar saka ido a kan kai-komo na yaro; wato zirga-zirgar yara. Wannan hanya ta lura, cikamakonta shi ne kwaɓa. A nan, iyaye za su saka ido sosai game da zirga-zirgar ‘ya’yansu, duk lokacin da suka ga wata baƙuwar halayya maras kyau, sai su yi maza-maza su ɗauki matakin da ya dace tun kafin ta zama jiki. Da zarar yaro ya fara fita wajen gida domin zuwa makaranta; wato daga shekaru uku zuwa sama, to fa dole iyaye su riƙa lura da shi sosai, saboda yanzu kuma ya je ya gwamutsa da sauran yara daga gidaje barkatai. Saboda haka idan iyaye basu saka lura ba, to tarbiyyar ‘ya’yansu sai ta koma barkata TARBIYYA _Tarbiyya aba ce mai wahala, sai an dage an tashi tsayin daka sannan za’a dasa ta, ya ku Iyaye abu na farko daya kamata ku cusa a zuƙatan yaran ku, ko zuciyar yarinyar ku, ko kuma zuciyar ɗan ku Shine *TSORON ALLAH* domin samun nagartacciyar rayuwa a tare dasu da kuma tarbiyya mai kyau._ _Daga lokacin da yaro ya fara wayo, ya fara magana, yasan abincin da zai sanya a bakin sa, ko kuma abin sha to daga wannan lokacin ya kamata ku fara cusa masa jin tsoron Allah a zuciyar sa sannan su San Wane ne Manzon Allah S.W.A, Menene Matsayin sa a Wajen Al’ummar Duniya baki ɗaya da Wajen Allah.._ _ku cusawa yaran ku jin tsoron Allah ta hanyar sanar dasu ubangiji, abinda yayi umarnin a aikata da kuma abinda yayi hani a kai.kamin ku jefa yaran ku a makarantar boko ku fara tura su ta islamiya, malamai magada Annabawa nayin nasu kuma kuna yin naku to insha’Allahu tarbiyar yaran ku zata zamo mai sauƙi a wurin ku a lokacin da suka balaga suka gama mallakar hankalin kan su._ _Sa’annan ku cusawa yaran ku son ilimi na addini dana zamani Kasancewar ilimi Shine Ginshiƙin Rayuwa, hakkin kune iyaye ku bawa ƴaƴan ku ilimi wanda zai amfanar da su duniya da lahira, ba ƴaƴan ku kawai ba hatta ku iyaye yana da kyau ku samarwa kan ku ilimi. Shi ilimi haske ne mai haskaka rayuwar ɗan adam ta kowanne fanni ba kawai don neman aikin abin duniya ba..wanda mafi akasarin iyaye yanzu sun fi gina ilimin ƴaƴan su akan neman aikin abin duniya duk da cewar hakan ba laifi bane amma ya kamata mu nazartu muyi duba sose akan hakan, muyi faɗi tashi mu jajirce mu cije don ganin mun inganta rayuwar ƴaƴa da ilimi na addini domin da shine za’a tafi lahira saɓanin na duniya da inda muka same shi anan zamu bar shi._ _Sose muke tafka kuskure a rayuwar yanzu, an cusawa yara musamman mata son abin duniya, ku farka iyaye musamman iyaye mata, kin cusawa ɗiyar ki son abin duniya, kin cika rayuwar ƴar ki da burin abin duniya, kin ƙawata idanuwan ta da hangen abin cikin duniya an manta da mutuwa na tafe a kowanne lokaci. fatan ki, burin ki, mafarkin ki, jin daɗin ki, kwanciyar hankalin ki, tayi-tayi ta gama Secondary School ta Shiga Jami’a tayi degree tayi Masters Domin ta tara Muku Dukiya kuyi kuɗi duniya tasan da ɗiyar ku ko ɗan ku, ku huce takaicin duniya, hakan yana da kyau kuma ba laifi bane sai dai ta gefe guda a kwai illa, akwai matsala._ _Duk saboda wannan burin kun hana ƴar’ku aure, baku sashi a cikin lissafin da zai inganta rayuwar ƴar’ku, terming ɗin ku da terget naku shine kawai wancan duk saboda kada burdget naki ke uwa ya rushe (ga wasu iyayen). Shin idan anyi auren nan ba’a karatunne?, shin idan anyi auren nan ba’a aikinne?, shin idan tayi auren nan zai hanata dukkan muradin ki da kike son ya cika?. Kin Hanata yin Aure, ƴaƴayen mu ba duwatsu ba, b marasa lafiya, sha’awa na Damin ta, Samari kullum kawo mata hari suke, koda yaushe tana tare da su a makaran ta ko a waje, yau da gobe sai Allah ba fata ake ba, Allah ya tsare mu ya tsare mana ƴaƴayen mu._ _Mu riƙa kai zuciya nesa a kan yaran mu, duka da hantara da zagi da mummunar kalma basu zasu gyara yaro ba face ƙara lalata shi, ku dinga yawan yi masu adu’a a koda yaushe, kar ku faɗi kalma mara daɗi a kansu a lokacin da suka ɓata maku rai, don Allah iyaye mu iya bakin mu akan yaran mu, kar mu manta matsayin bakin mu akan su, fata na gari da adu’a ta gari a kansu shine dai-dai.._ _ku koyar da yaran ku da sabar masu yin sallah akan lokaci, ku koyar dasu adu’oin neman tsari da kariya kamar yanda ma’aiki ya koyar damu, ku zama masu lura da irin fina-finan da suke kallo domin kuwa shima kallo na ɓata tarbiyar yaro ya rusa duk ginin da kayi a baya, ku sabar masu da sauraran wa’azi kamar yanda ya kamata bakin ku ya saba wajen yi masu wa’azi._ _Haka Zalika ku kasance abin koyi ga yaren ku, kuyi ƙoƙarin aikata abu mai kyau tayanda zasu gani su ɗauka daga gare ku.. Ku zama masu zama da yaran ku kuna shiga cikin su domin jin matsalolin su, sannan ku zama masu sanya ido a duk abubuwan da yaran ku ke gudanarwa na yau da kullum tun kama daga kan ƙawaye, lura da irin abokan da yaro ke mu’amala dasu yana da kyau matuƙa da gaske, kuma hanya ce ta kiyaye yaron ki daga faɗawa ga miyagun abokai, idan har kun sanya ma yaro ido akan abokan tarayyar sa lalle tabbas zai ji tsoron zama da ɓata gari, zai yi duk yanda zai yi yaga yayi ƙoƙarin nisan ta da banzan abokai, fatan mu Allah ya kare mana zuri’a ya kuma shiryar dasu._ _mu guji kuma mu kiyaye bama ƙananun yaran mu da suka tasa wayar hannu, wannan waya da muke ganin ta haƙiƙanin gaskiya ba ƙaramar musiba bace, haɗari ce babba ga rayuwar ƴaƴa wallahi, don haka mu kiyaye basu waya musamman ta android a lokacin da suke da ƙarancin shekaru…. Ku zama masu sanya ido a kan shige da ficen ƴaƴan ku musamman ke uwa da kike zaune cikin gida koda yaushe, ba kowanne wuri ya kamata ku bar yaran ku suke zuwa ba, kuma ba’a koda yaushe ya kamata kuke barin su fita ba, duk da cewar rayuwar yanzu ta sauya yaran mu sunfi mu wayo da dabara… Idan dama ma da hali duk sanda ƴarki mace ta buƙaci zuwa wani wuri kiyi mata jagora, sannan ki hani yaran ki tarayya da ƙawaye barkatai._ _yake uwa ki zama mai sa’ido sosai da sosai akan ɗiyar ki mace wajen duban irin littafan hausa dana turan ci da take karantawa, ki tsoratar da ƴar’ki kiyi mata barazana da karanta littafin daya kauce hanyar kunya da tarbiyya, haka zalika idan ƴarki ta taso da sha’awar rubuta littafi shima ki tsoratar da ita ki mata baraza na ta yanda zata ji tsoro ta kuma kiyaye rubuta abinda ba shi da kyau, ki tunatar da ita cewa lalle ubangiji zai tsaida ita akan abinda ta rubuta, ki zama mai bincikar wayar ta akai-akai, ki zama ƴar jarida ga yaran ki, kisa musu ido akan duk abinda zasu samu, bi ma’ana dukkan abinda kika gani a hannun su ki sasu gaba ki titsiye su don jin daga ina suka samo shi?, taya suka same shi?, koda yaro zai ce maki ga wurin daya samu kuyi ƙoƙarin bin diddigin inda ya same su ɗin… Karku sabarwa yaron ku da riƙe kuɗi domin kuɗi na ɗaya daga cikin abinda ke rusa tarbiyar yaro._ _yake uwa ta gari, ki sanya ido akan fitar ƴarki daga gida wajen sanya sutura, ki tuna musulunci ki tuna faɗin Allah maɗaukakin sarki a cikin littafin sa mai tsarki mai girma, ki tilastata ki sabar mata da suturce jikin ta a yayin da zata fita… Idan mai sanya hijab ce ki sanya ido wurin ganin kayan data sanya aciki da kuma abinda ke ƙunshe cikin jakar hannun ta, domin wasu ƴaƴan namu kan yaudare mu da fuska biyu.. Ki hani yarinyar ki da amsar kuɗin hannun samari, ki kuma hani yaran ki da saurin miƙa hannu, ki hani yaran ki da kwaɗayi da son abin duniya._ _ya ku iyaye na gari, daga lokacin da kuka fahimci ƴaƴan ku na buƙatar aure, lalle kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, hakan shi zai hana yaɗuwar ɓarnar dake faruwa a doron ƙasar mu, ba komi ke jefe ƴaƴan mu cikin baƙincikin rayuwa ba sai wajen tauye masu hakki da muke, musamman ƴaƴa mata, don Allah iyaye da zarar kun fuskanci ƴaƴan ku na son aure kuyi masu domin shine mafita kuma shine kariyar su daga faɗawa mummunar halaka, kuma shine yayewar damuwar da za’a shiga a gaba._ _Daga ƙarshe karmu manta zamu cimma kyakykyawan burin mu ne akan tarbiyantar da yaran mu wajen yawan tunsar dasu faɗin Allah da Ma’aikin Allah._ _Ya Allah kasa mu dace, Allah kuma ya bamu ikon sauke hakkin ƴaƴan mu da Allah ya ɗora mana domin Ƴaƴa Amana ce Allah ya bamu._ Daga *® MATSALAR FYADE GA “YA” YA MATA…. KALUBANE GA IYAYE…… idan kacire yara kanana wayanda basusan fari da baqi ba wallahi sauran yan matan wasu lefinsu ne Dana iyayensu saboda gurbatar tarbiyya. Akwai Hadith na manzon Allah (saw) annabi yake cewa …. Sayaqulu fi akirizzamani nisa’un kasiyatun ariyatun. Sai annabi yace il anu hunna fa inna hunna mal ulatu, subhanallah sai yasake cewa wallahi lajidanna rihal janna, alhalin wa inna rihaha la yujadu min masiratun kaza wa kaza. To gaba daya inka duba babban matsalar wannan zamanin yanzu shine wayewa tayi yawa haka kawai yarinya takai mace iya mace Amma saita bata wasanta. a farkon fari duk bikin daza ayi saitayi anko karasa a gidan ubanwa take samo kudin Kuma dinki me daukar hankali, kaga yarinya kullum bakinta abude washa da haqora farare tass tana sheqa dariya me daukar hankali, tana tafiya tana bada style kala kala, ko makaranta zataje saita qwalqwale jiki tayi wankan siga ana tafiya tsaraici yana fita kuma wallahi iyayen suna kallo su aganinsu lokacin wance fah yayi abarta kawai taci duniyar ta ai ansan dai tunda tanada kyau Dole a aureta. To wallahi muddin diyarka ko diyarki tana irin wannan tsiyar karma gayu su afka mata kayi kumfar baki tayi suka mayar tunda dayawanku aurenma in anzo sai kuce tafara level 100 saita kammala tukunna kokuma kuce mutum yaje saiya yi gini ku bakwason haya, kokuma kuce adaidaita yake ja bazai iyaba, ko ace waye babanka daga kace malam halliru me kwado da linzami za a durama ashar akoreka. kai wallahi wa tama kidan jogo zatabi takai kanta ayi mata shi Amma daga baya sai iyayen su juya kaset din suce ai fyade ne. Dabara taragewa iyaye kuyiwa yayanku tarbiya kuyimusu aure da wuri in ansamu fitacce kunga dai auren annabi (saw) da nana Aisha Kuma ahanasu kwadayi Adena Dora musu tallah. Allah yakaremu da zuriyarmu daga dukkan sharri amin amin.
You must be logged in to post a comment.