Tarbiyya a Ƙasar Hausa
Gabatarwa
Kalmar tarbiyya, ararriyar kalma ce daga Larabci ( ﺍﻟﺘﺮﺑﻴﺔ aka Hausantar da ita. Kalma ce magamaiya, wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta renon jikin yaro; hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa, tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a, a al’ummance da kuma ɗaiɗaiku.
Ƙololin buƙatar tarbiyya ita ce gina cikakken mutum mai amfanar da kansa da kuna waninsa.
Bisa la’akari da wannan faffaɗar ma’ana da wannan kalma take da ita, rubutun zai taƙaitu ne wajen yin magana a kan abin da ya shafi ruhi da kuma cuɗanya. Zai yi magana bakin gwargwado a kan ma’anar tarbiyya, manufarta, amfaninta, masu bayar da ita, jerin wasu kyawawan halaye da kuma yadda Bahaushe yake bayar da tasa tarbiyyar, da sauransu bakin gwargwadon iyawa.
Ma’anar Tarbiyya
Saboda zamowar kalmar tarbiyya mai tushe a Larabci, zan kawo ma’anarta a Larabce da cewa, “Ita ce ayyukan ɗaukakowar halittu, wato ƙarawa mutum mutumtaka domin ya samu kaiwa cikakkiyar daraja matabacciya a jiki da aiki da ruhi da kuma cuɗanya”, Abu Hamza (2013). Daga wannan ma’ana za mu iya fahimtar cewa, tarbiyya reno ce. Saboda dukkan abubuwan nan da aka ambata suna ƙunshe cikin reno. Shi kuwa reno ana yin sa ne mataki-mataki. Sai dai ya fi zafi a tsakanin ranar farko ta haihuwa zuwa shekara uku. A wannan tsakanin komai yi wa mutum ake yi. Ɗawainiyoyin suna fara raguwa ne bayan an yaye mutum wato daga watanni 15 na haihuwa zuwa shekaru
2. Daga wannan mataki yawancin yara sukan fara yi wa kawukansu wasu abubuwan kamar ci da sha da sauran ƙananan abubuwan rayuwa.
Daga wannan mataki na yaye kuma, sai a shiga kiwonsa, da ma’ana ta lura da zirga-zirgarsa ƙut-da-ƙut har zuwa kamar shekaru 5 ko 6, idan zai kai kansa mahallaka ko dai a ce da shi bari, ko kuma a je a ɗauke shi ko a janye shi da sauransu.
Idan ya haura shida kuma, to ya fara kai wa matakin da zai fara cuɗanya da wajen gida, sai kuma ya shiga makaranta. A makarantar ma renonsa ake yi, saboda a koyar da shi ne alaƙoƙin da suka shafi rayuwarsa ta duniya da kuma ta lahira, iya tsawon karatunsa da ma rayuwar baki ɗaya.
Saboda haka idan muka koma kan waccar ma’ana ta tarbiyya muka ciro kalmomin cewa, ayyuka ne da ke ɗaukaka halitta, za mu gan su cikin wannan ɗan taƙaitaccen bayani game da reno da na yi.
Ana kuma iya cewa, tarbiyya ita ce horas da yaro kyawawan halaye domin ya zama mutum nagari. Ko kuma a ce, hanya ce ta nuna wa yaro yadda zai tashi da kyawawan halaye ababen yabo a cikin jama’a.
Manufar Tarbiyya
Babbar manufar tarbiyya ita ce samar da mutum mai kyawawan halaye ababen yabo domin ya zama mai amfanar da kansa da kuma waninsa.
Amfanin Tarbiyya
Amfanin tarbiyya ba zai ƙidayu ba, amfaninta na ƙarshe; wato maƙurar amfanin nata shi ne mutum ya samu kansa a gidan Aljana a lahira, a nan duniya kuma ya zama son kowa, ƙin wanda bai samu ba.
Waɗannan gajiyoyi da za a ci; duniya da lahira, su ne maƙura, sai kuma wasu ɗaiɗaikun abubuwa da zan lissafo kamar haka:
Tsarkake Halaye: Tarbiyya tana tsarkake halayen mutum ya zama mai kyawawan halaye.
Sauƙin Rayuwa: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya rayu, rayuwa mai sauƙi. Saboda zamowarsa mai wadatar zuci.
Farin Ciki: Mutum mai cikakkiyar tarbiyya akan same shi cikin annashuwa a mafiya yawan lokutansa. Saboda koda wani abu can gefe ya ɓata masa rai, to yasan idan ya zo yin hulɗa da wani wanda abin bai shafe shi ba, sai ya danne wancan ɗacin a ransa shi kaɗai.
Girma da Ɗaukaka: Kyakkyawar tarbiyya tana ɗaukaka darajar mutum a idon mutane a nan duniya, haka nan ma a wajen Ubangiji Mai Girma da Buwaya.
Kwarjini: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya zama mai kwarjini.
Matakan Bayar da Tarbiyya
Akwai matakai ko hanyoyi da ake bi wajen bayar da tarbiyya da suka haɗa da nuni, lura, umarni da kuma hani.
Nuni: Abin da ake nufi da nuni a nan shi ne aikata aiki a aikace, wanda daga nan shi wanda ake tarbiyantarwa zai gani ya koya. Tirƙashi, masu iya magana sun ce; “Idan mutum ya ce zai baka riga, to duba ta jikinsa”. Wannan magana ta zo daidai da faɗin Larabawa cewa; “Maras abu baya bayar da shi”. Saboda haka dole ne mai bayar da tarbiyya ya zama mai tarbiyya.
Wannan hanya ta bayar da tarbiyya ita ce mafi tasiri da kuma muhimmanci wajen bayar da tarbiyya. Saboda haka dole ne masu bayar da tarbiyya; iyaye, malaman makaranta da sauran jama’a suma su zama masu tarbiyya. Misali, dole iyaye su zama masu tsafta a aikace, kafin su dasa halin tsafta a zukatan ‘ya’yansu. Idan yaro ya tashi ya ga iyayensa suna share gida tsaf-tsaf, basa barin kwanon abinci da dauɗa, basa jefar da sutura ko’ina a ciki da wajen ɗaki, to a haka shi ma zai girma mai kula da tsafta. Kuma zai tashi shi tsafta ya sani bai san ƙazanta ba. Saboda haka da zarar ya fara zuwa makaranta malaman makaranta ba za su wahala da shi ba.
Umarni da Hani (Kwaɓa): Umarni shi ne a riƙa gaya wa yaro yi kaza. Misali, idan yaro ya tsoma hannun hagu cikin kwanon abinci, ko ya riƙe abinci da hannun hagu zai kai bakinsa, sai a gaya masa cewa, wannan ba shi ne hannun cin abinci ba, ga na cin abinci nan. Da haka zai gane hannun dama dana hagu.
Shi kuwa hani shi ne kore abu. A wannan gaɓar kuma yana nufin kare ko dakatar da yaro daga aikata aikin da ba mai kyau ba. A cikin wannan misalin dana kawo a sama, akwai gaurayen hani da kuma umarni. Yaro ya tsoma hannun hagu domin cin abinci, sai aka hana shi; wato aka dakatar da shi daga cigaba da amfani da hannun hagu. Sannan aka gaya masa; wato aka umarce shi da amfani da hannun dama.
Lura/Kula: Lura ko kula, suna ɗaukar ma’anar saka ido a kan kai-komo na yaro; wato zirga-zirgar yara. Wannan hanya ta lura, cikamakonta shi ne kwaɓa. A nan, iyaye za su saka ido sosai game da zirga-zirgar ‘ya’yansu, duk lokacin da suka ga wata baƙuwar halayya maras kyau, sai su yi maza-maza su ɗauki matakin da ya dace tun kafin ta zama jiki.
Da zarar yaro ya fara fita wajen gida domin zuwa makaranta; wato daga shekaru uku zuwa sama, to fa dole iyaye su riƙa lura da shi sosai, saboda yanzu kuma ya je ya gwamutsa da sauran yara daga gidaje barkatai. Saboda haka idan iyaye basu saka lura ba, to tarbiyyar ‘ya’yansu sai ta koma barkatai.
TARBIYYA
_Tarbiyya aba ce mai wahala, sai an dage an tashi tsayin daka sannan za’a dasa ta, ya ku Iyaye abu na farko daya kamata ku cusa a zuƙatan yaran ku, ko zuciyar yarinyar ku, ko kuma zuciyar ɗan ku Shine *TSORON ALLAH* domin samun nagartacciyar rayuwa a tare dasu da kuma tarbiyya mai kyau._
_Daga lokacin da yaro ya fara wayo, ya fara magana, yasan abincin da zai sanya a bakin sa, ko kuma abin sha to daga wannan lokacin ya kamata ku fara cusa masa jin tsoron Allah a zuciyar sa sannan su San Wane ne Manzon Allah S.W.A, Menene Matsayin sa a Wajen Al’ummar Duniya baki ɗaya da Wajen Allah.._
_ku cusawa yaran ku jin tsoron Allah ta hanyar sanar dasu ubangiji, abinda yayi umarnin a aikata da kuma abinda yayi hani a kai.kamin ku jefa yaran ku a makarantar boko ku fara tura su ta islamiya, malamai magada Annabawa nayin nasu kuma kuna yin naku to insha’Allahu tarbiyar yaran ku zata zamo mai sauƙi a wurin ku a lokacin da suka balaga suka gama mallakar hankalin kan su._
_Sa’annan ku cusawa yaran ku son ilimi na addini dana zamani Kasancewar ilimi Shine Ginshiƙin Rayuwa, hakkin kune iyaye ku bawa ƴaƴan ku ilimi wanda zai amfanar da su duniya da lahira, ba ƴaƴan ku kawai ba hatta ku iyaye yana da kyau ku samarwa kan ku ilimi. Shi ilimi haske ne mai haskaka rayuwar ɗan adam ta kowanne fanni ba kawai don neman aikin abin duniya ba..wanda mafi akasarin iyaye yanzu sun fi gina ilimin ƴaƴan su akan neman aikin abin duniya duk da cewar hakan ba laifi bane amma ya kamata mu nazartu muyi duba sose akan hakan, muyi faɗi tashi mu jajirce mu cije don ganin mun inganta rayuwar ƴaƴa da ilimi na addini domin da shine za’a tafi lahira saɓanin na duniya da inda muka same shi anan zamu bar shi._
_Sose muke tafka kuskure a rayuwar yanzu, an cusawa yara musamman mata son abin duniya, ku farka iyaye musamman iyaye mata, kin cusawa ɗiyar ki son abin duniya, kin cika rayuwar ƴar ki da burin abin duniya, kin ƙawata idanuwan ta da hangen abin cikin duniya an manta da mutuwa na tafe a kowanne lokaci. fatan ki, burin ki, mafarkin ki, jin daɗin ki, kwanciyar hankalin ki, tayi-tayi ta gama Secondary School ta Shiga Jami’a tayi degree tayi Masters Domin ta tara Muku Dukiya kuyi kuɗi duniya tasan da ɗiyar ku ko ɗan ku, ku huce takaicin duniya, hakan yana da kyau kuma ba laifi bane sai dai ta gefe guda a kwai illa, akwai matsala._
_Duk saboda wannan burin kun hana ƴar’ku aure, baku sashi a cikin lissafin da zai inganta rayuwar ƴar’ku, terming ɗin ku da terget naku shine kawai wancan duk saboda kada burdget naki ke uwa ya rushe (ga wasu iyayen). Shin idan anyi auren nan ba’a karatunne?, shin idan anyi auren nan ba’a aikinne?, shin idan tayi auren nan zai hanata dukkan muradin ki da kike son ya cika?. Kin Hanata yin Aure, ƴaƴayen mu ba duwatsu ba, b marasa lafiya, sha’awa na Damin ta, Samari kullum kawo mata hari suke, koda yaushe tana tare da su a makaran ta ko a waje, yau da gobe sai Allah ba fata ake ba, Allah ya tsare mu ya tsare mana ƴaƴayen mu._
_Mu riƙa kai zuciya nesa a kan yaran mu, duka da hantara da zagi da mummunar kalma basu zasu gyara yaro ba face ƙara lalata shi, ku dinga yawan yi masu adu’a a koda yaushe, kar ku faɗi kalma mara daɗi a kansu a lokacin da suka ɓata maku rai, don Allah iyaye mu iya bakin mu akan yaran mu, kar mu manta matsayin bakin mu akan su, fata na gari da adu’a ta gari a kansu shine dai-dai.._
_ku koyar da yaran ku da sabar masu yin sallah akan lokaci, ku koyar dasu adu’oin neman tsari da kariya kamar yanda ma’aiki ya koyar damu, ku zama masu lura da irin fina-finan da suke kallo domin kuwa shima kallo na ɓata tarbiyar yaro ya rusa duk ginin da kayi a baya, ku sabar masu da sauraran wa’azi kamar yanda ya kamata bakin ku ya saba wajen yi masu wa’azi._
_Haka Zalika ku kasance abin koyi ga yaren ku, kuyi ƙoƙarin aikata abu mai kyau tayanda zasu gani su ɗauka daga gare ku.. Ku zama masu zama da yaran ku kuna shiga cikin su domin jin matsalolin su, sannan ku zama masu sanya ido a duk abubuwan da yaran ku ke gudanarwa na yau da kullum tun kama daga kan ƙawaye, lura da irin abokan da yaro ke mu’amala dasu yana da kyau matuƙa da gaske, kuma hanya ce ta kiyaye yaron ki daga faɗawa ga miyagun abokai, idan har kun sanya ma yaro ido akan abokan tarayyar sa lalle tabbas zai ji tsoron zama da ɓata gari, zai yi duk yanda zai yi yaga yayi ƙoƙarin nisan ta da banzan abokai, fatan mu Allah ya kare mana zuri’a ya kuma shiryar dasu._
_mu guji kuma mu kiyaye bama ƙananun yaran mu da suka tasa wayar hannu, wannan waya da muke ganin ta haƙiƙanin gaskiya ba ƙaramar musiba bace, haɗari ce babba ga rayuwar ƴaƴa wallahi, don haka mu kiyaye basu waya musamman ta android a lokacin da suke da ƙarancin shekaru…. Ku zama masu sanya ido a kan shige da ficen ƴaƴan ku musamman ke uwa da kike zaune cikin gida koda yaushe, ba kowanne wuri ya kamata ku bar yaran ku suke zuwa ba, kuma ba’a koda yaushe ya kamata kuke barin su fita ba, duk da cewar rayuwar yanzu ta sauya yaran mu sunfi mu wayo da dabara… Idan dama ma da hali duk sanda ƴarki mace ta buƙaci zuwa wani wuri kiyi mata jagora, sannan ki hani yaran ki tarayya da ƙawaye barkatai._
_yake uwa ki zama mai sa’ido sosai da sosai akan ɗiyar ki mace wajen duban irin littafan hausa dana turan ci da take karantawa, ki tsoratar da ƴar’ki kiyi mata barazana da karanta littafin daya kauce hanyar kunya da tarbiyya, haka zalika idan ƴarki ta taso da sha’awar rubuta littafi shima ki tsoratar da ita ki mata baraza na ta yanda zata ji tsoro ta kuma kiyaye rubuta abinda ba shi da kyau, ki tunatar da ita cewa lalle ubangiji zai tsaida ita akan abinda ta rubuta, ki zama mai bincikar wayar ta akai-akai, ki zama ƴar jarida ga yaran ki, kisa musu ido akan duk abinda zasu samu, bi ma’ana dukkan abinda kika gani a hannun su ki sasu gaba ki titsiye su don jin daga ina suka samo shi?, taya suka same shi?, koda yaro zai ce maki ga wurin daya samu kuyi ƙoƙarin bin diddigin inda ya same su ɗin… Karku sabarwa yaron ku da riƙe kuɗi domin kuɗi na ɗaya daga cikin abinda ke rusa tarbiyar yaro._
_yake uwa ta gari, ki sanya ido akan fitar ƴarki daga gida wajen sanya sutura, ki tuna musulunci ki tuna faɗin Allah maɗaukakin sarki a cikin littafin sa mai tsarki mai girma, ki tilastata ki sabar mata da suturce jikin ta a yayin da zata fita… Idan mai sanya hijab ce ki sanya ido wurin ganin kayan data sanya aciki da kuma abinda ke ƙunshe cikin jakar hannun ta, domin wasu ƴaƴan namu kan yaudare mu da fuska biyu.. Ki hani yarinyar ki da amsar kuɗin hannun samari, ki kuma hani yaran ki da saurin miƙa hannu, ki hani yaran ki da kwaɗayi da son abin duniya._
_ya ku iyaye na gari, daga lokacin da kuka fahimci ƴaƴan ku na buƙatar aure, lalle kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, kuyi gaggawar yi masu, hakan shi zai hana yaɗuwar ɓarnar dake faruwa a doron ƙasar mu, ba komi ke jefe ƴaƴan mu cikin baƙincikin rayuwa ba sai wajen tauye masu hakki da muke, musamman ƴaƴa mata, don Allah iyaye da zarar kun fuskanci ƴaƴan ku na son aure kuyi masu domin shine mafita kuma shine kariyar su daga faɗawa mummunar halaka, kuma shine yayewar damuwar da za’a shiga a gaba._
_Daga ƙarshe karmu manta zamu cimma kyakykyawan burin mu ne akan tarbiyantar da yaran mu wajen yawan tunsar dasu faɗin Allah da Ma’aikin Allah._
_Ya Allah kasa mu dace, Allah kuma ya bamu ikon sauke hakkin ƴaƴan mu da Allah ya ɗora mana domin Ƴaƴa Amana ce Allah ya bamu._
Daga *
MATAKAN TARBIYYA
Daga. Alqalamin Ismail Smart
Dasunan ALLAH Mai RAHAMA Mai JINKAI.
Haqiqa tarbiyya dolece a addinin mu na musulunci musan man ma na iyalanka/ki
Domin ALLAH MADAUKAKI yana cewa:
﷽
ﯾﺎ ﺃﯾﻬﺎﺍﻟﺬﯾﻦ ﺁﻣﻨﻮ ﻗﻮ ﺃﻧﻔﺴﮑﻢ ﻭﺃﻫﻠﯿﮑﻢ ﻧﺎﺭﺍ ﻭﻗﻮﺩﻫﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻭﺍﻟﺤﺠﺎﺭﺓ
Awannan aya ALLAH yayi umarni ga Muminai dasu Kare kansu da iyalansu daga wata wutta Wanda yakasance makamashinta mutane ne dakuma duwatsu.
ALLAH UBANGIJI katsaremu amin ya RABBI. Awannan ‘Bangaren Nakeson nayi rubutu domin yan uwa musulmai su anfana.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI ya dafamin
MATAKIN FARKO
(Neman Aure zuwa da yakai 5yrs)
Dole Akan kowa Idan yazo neman aure
Yanemi Mai addini Da hali nagari Da kakkyawar zuciya. Ba kawai kyawun fuskaba ko wani martaba ko nasabar Abokin zama ba. Kuma yazamto anyi auren tanasonsa yana sonta.
Domin hakanne Zaisa suji dadin zamantakewarsu ta Aure Kuma hakan Zaisa yayansu sutaso dason junansu Da Bin doka ko umarnin Da akayi masu. Domin kada yazamto uwa tace fari uba yace Bahakaneba Baki yake. Bayan haka
Yazama dole asakawa yaro kakkyawar suna alokacin dayake jinjiri. Yazama dole ka karantar Da matanka tsarin tarbiyyar addinin musulunci ko kasa akarantar da ita Awannan sahar kokuma MA kafin wannnan lokacin. Ma’ana kafin ta sami d’a (yara).
Domin kaso saba’in Cikin Dari (70%) Na Tarbiyyar cikin Gida maqasudinsa na uwace. Yazama dole takasance Mai Lura da Meke gudana me sukeso me yakamata suyi ko so Bari duk wadannan uwace takeda hakkin koyar da yaranta.
Dakuma koyardasu Ibaadaat Kamar Sallah Azumi Dakuma koyamusu karatun Alqur’ani da tilawarsa dama haddarsa. Har sukai 10yrs Kafin daga bisani Sai Aturasu Islamiya. Sucigaba da karatu daneman ilimin addini. Hakan zaisa sutaso da ganin girman iyayansu. Dama duk wanda yagirmesu tayadda basai ance ga malam waneba kafin sudaina abinda sukeyi.
MATAKI NA BIYU
(Daga 5yrs zuwa 15 to 18yrs)
Dolene akan iyaye su San abokanan yayansu, Susan Kuma menene alaqarsu dasu Domin duk kyawun tarbiyyar dakasamu agida abokai sukan wargazashi, matsawar dakayi abota da marasa tarbiyya koda baka zama tamkarsu ba. Zaka rudu da wani hali acikin munanan halayyarsu.
Yazama dole iyaye su bawa yayansu tarbiyyar addini da wayewar rayuwa tahanyar sanaddasu yadda zasuyi addini da hikimomin tsara rayuwa bisa kykkyawar tsari. Kamar koyamusu dabarun kare kai da addu’o’in neman tsari da kariya. Da sanardasu tarihohi Wanda zasu sami hikima da, wa’azozi acikinsa. Domin abinciken masana kwakwalwar dan adam sun yarda akan cewa kwakwalwar dan adam takan bude da adana bayanai alokacin da mutum yake dan shekaru takwas (8) zuwa Sha biyar (15) koda haddane mutum yafi nutsuwa dashi awannan lokacin Inhar kaga yaro ya natsu awannan lokacin to tabbas ana kyautata zaton shiryayye ne. Inkuma ya kangare kuwa yanada wuyar shiryuwa Yakamata iyaye sudunga zama da yaransu suna zantawa dasu domin suji damuwoyi da bukatunsu, Harsu san tahanyar da zasu bullo musu gurin bada shawara ko kore musu matsalarsu tarayuwa.
MATAKI NA UKU NAKARSHE
(Daga 15/18yrs. zuwa auraddasu)
Yakamata iyaye su lura da yayansu su san menene wane/wacce tafi/yafi kwarewa akai saisu dage gurin nema masu mafita ta hanyar basu tallafi ko jari domin samun damar gudanar da harkokin rayuwarsa cikin sauki batare da yana zauneba saidai kullum abashi.
Domin hakan yana kashe zuciyar mutum yazanto baya iya kafuwa da kansa balle ma har yagina wasu. Saidai kullum a bani_bani sai kuma bin abokai da yawace yawacen banza da hofi, da bin bangar siyasa, wadda daga karshe ke jawo mutum yakoma ta’asa da ‘barna acikin al’uma kokuma ma yakama shaye_shaye da bin mugaye mutane. Duk adalilin rashin aikin yi. ALLAH ya tsaremu da zuri’armu baki daya.
Rashin aikinyi na daya daga cikin abubuwa mafi girma wanda suke lalata tarbiyya arayuwar mutane.
Allah ka bawa iyayen mu hakurin zama damu kasauke musu hanyar dazasu tarbiyyantar damu tarbiyya ta Addinin musulunci, ALLAH kajikan maifina kahaskaka qabrinsa.
“Ribar dake Cikin Auren Mace Ma’abociyar Addini …”
Kamar Yadda Ya tabbata A Hadithn Annabi ﷺ Da Yake Cewa Ana Auren Mace Saboda Abubuwa Hudu;
Kyawunta,
Nasabar ta,
Dukiyar ta
Sai Addinin ta…
Sai Shugaba AlayHiS Salaam Yace; Ku Auri Ma’abociyar Addini, Sai Hannun Ku (Zuri’ah) Yayi Albarka…
(1) Riba ta Farko Na Auren Mace Mai Addini Shine Kasancewar Ita Annabi ﷺ Yaiwa Mumini Za’bi…
(2) Tarbiyar ‘Ya’yan Ka Zata Inganta Saboda Dacewa Da Mace Mai Addini Wajen Karantar Dasu da Kuma Tarbiyantar Dasu…
(3) Godiya Daga Abinda Ka Bata Duk Ƙanƙantar Sa, Zata Nuna Farin Ciki da Wannan Kyautar taka A Bayyane Saboda tasan Wanda Baya Godewa Allah Bazai Godewa Mutane ba…
(4) Zata Kasancewa Mai tinatar dakai Lamarin Allah da Manzan Sa ﷺ tare Kwantar Maka da Hankali A Duk Halin da Ka Shiga Na Kuncin Rayuwa da Matsi…
(5) Zata Dinga Takaita Buƙatarta Gwargwadon Samun ka, Kuma Bazata Dinga Ɗora Maka Nauyin Abinda tasan Bazaka Iya Ba…
(6) Zata Kula Dakai tare da Nuna Maka Soyayya dan Allah Badan Abinda Kake dashi Ba Ko Makamancin Haka…
(7) Zata Zama Duniyar Farin Cikin Ka Saboda Ta Kasance ta Gari A Wajen Ka, Mai Kyautata Maka da Saka Farin Ciki A Rayuwar Ka Dan Kyautata Aljannar ta dake Ƙarƙashin Ka…
Shugaban Halitta ﷺ Yana Cewa; Duniya Mai Daɗi Ce Mafi Alkhairin Daɗin Duniya Shine Allah Ya Baka Mace
ta gari…

ماشاءاللہ
LikeLike