UWA TA GARI

UWA TAGARI SA’AR YA’YA.

“Wallahi dukkanin wani jin daɗin da kake dashi a wannan duniyar matuƙar aka ce baka mori uwa ba, baka yi sa’ar samun uwa tagari ba, to haƙiƙa jin daɗinka ragagge ne”

“Dukkanin uwar da zata yawaita addu’ar alkhairi ga ƴa’ƴanta, zata kame bakinta daga zagi da aibanta su da kuma tsinuwa a garesu, to haƙiƙa wannan itace uwa tagari ga ƴa’ƴanta kuma mai bawa al’umma kariya ce, domin idan ta tsine musu ba iya ita kaɗai zasu dama ba, hatta jama’ar waje suma sai sun addabe su, sabida ita tsinuwar uwa akan ƴa’ƴanta haƙiƙa ba ƙaramar illa bace, sannan kuma idan tayi musu addu’ar alkhairi suka zama na ƙwarai to lallai ba iya ita kaɗai zata mora ba, hatta ma jama’ar waje sai sun amfana dasu, sabida haka ki zamto uwa tagari ga ƴa’ƴanki”

“Lallai uwa tagari bata la’antar ƴa’ƴanta, kana kuma bata la’antar na wasu, domin dukkanin uwar da zatayi riƙo da ɗabi’ar la’antar ƴa’ƴan wasu, to haƙiƙa wataran itama za’a la’anci nata, koda kuwa ba’a la’anci natan ba, to watarana da kanta zata la’ance su tunda bakinta ya saba da la’antar na wasu, amma idan ta zamto tagari mai yawan addu’a ga ƴa’ƴanta, to haƙiƙa inshaa Allahu sai Allah ya basu kariya a duk inda suke saidai idan jarabawar Allah ta sauka a garesu gameda wani ibtila’in rayuwar”