DARASI, NASIHA MUHIMMIYA ZUWA GA SAMARIN DAKE ZUWA FIRA BADA NIYYAR AURE BA (2095)
.
Wani Daga Cikin Masu Hikima Yace Bayaso Ya Fara Soyayya da Ya”Mace Idan Har Bashi Da Shirin Yin Aure !
.
Aka Tambayeshi Meyasa ?
Yace Saboda Bayaso Zuciyarsa Ta Narke Zuwa Ga Wacce Yake So Daga Bisani Kuma Su Rabu
.
Saboda Zuciyarsa Zata Iya Haifar Da Tabon Da Ba Zai Taba Mantawa Dashi Ba a Sanadin Rabuwarsu
.
Shiyasa Idan Ba Dagaske Kake Zuwa Fira Wurin Ya”Mace Ba Kada Ka Batawa Kanka Lokaci Ka Bata Mata Lokaci Kayi Haquri Ka Janye Shine Kwanciyar Hankalinka
.
Domin Duk Abin Da Zaka Fada Mata Da Sunan Soyayya Wallahi Qarya Kake Don Ba Aurenta Zakai Ba Kuma Yaudara Ta Shiga Ciki Ta Fuskar Qarerayi Don Ka Burgeta
.
Wadda Hakan Kuma Bai Kamata Ba Hatta Shari’a Bata Amince Da Irin Wannan Soyayyar Ba Don Kuwa Qarya Ta Shiga Ciki ta Fuskar Yaudara Wadda Annabi Yayi Mana Kashedi Akan Qarya
.
Annabi Sallallahu Alaihi Wa’ala Ahalihi Wasallam Yayi Mana Gar Gadi Akan Qarya Yace (Iyya Kum Wal Kazib Fa’innal Kaziba Ya Hadi Ilal Fujur Wa Innal Fujur Ya Hadi Ilan Nari)
.
Annabi Yace Na Haneku Da Yin Qarya Domin Tana Mai Da Mutum Fajiri Shi Kuwa Fajirci Yana Kai Dan Adam Wuta, Saboda Haka Wadda Yake Zuwa Wurin Ya”Mace Da Sifar Soyayya Kuma a Ransa Ba Aurenta Zaiyyi Ba tofa Ya Shiga Sahun Maqaryata Ta Fuskar Yaudara
.
Don Kuwa Duk Abin Da Zai Fada Mata Game Da Soyayyarsa Gareta Qarya Yake Ba Dagaske Yake Ba Saboda Ribar Soyayya Ga Masoya Shine Ta Kaisu Zuwa Ga Mallakar Juna Matsayin Mata Da Miji
.