AREWA 24 TAMUCE
Faduwar Dalibai A Jarrabawar JAMB
Sau dayawa harda wasu acikin Malamai na ta fadar cewa Kallon Shirye_Shiryen Film Series. Sune Silar Faduwar Dalibanda Sukayi JAMB A bana 2021.
Daga Alqalamin ✍️Ismail Hussaini Alpholwy
@MatanasanMarutanBauchi
Sabanin Ra’ayi danganeda Fahimtata dakuma Wadansu damuka tattauna akan batun awani ganawar damukayi ta Online da ‘Yan uwana marubuta.
A iya fahimtarmu bakawai Kallon series bane yakayarda Mutane a jarrabawar bana ba. Duk da Cewa yana daya daga cikin abubuwa uku acikinsu. Sune Kallan film, Yawan Sauraron kida, dakuma Wasannin Wayar hannu (Games)
Wadanda dukka wadannan abubuwa suna Faruwane ta cikin wayoyin hannuwan mu. Yadda zakasamu Mace ko na miji yana da Game Apps Sama da Goma Sha ga kuma Film Series Suma Sama da Ashirin Ga kuma wakoki na Hippop dama Jazz Music dana Hausa dama na Turanci dana Kudanci Hardana Videos na Fitsara da Lalata Tarbiyya.
To taya yaro zai dau littafi yayi karatu, bacin ga irin wadannan Shirmen da lalacewan acikin wayarsa. Dasu zai kwana kuma yatashi kuma ba akoyar dashi Tsoron Allah ba.
Laifin iyayene dasuke sakaci da Wayoyin Yaransu dakuma Yaran dasuka taso Basu bibiyar kafafen Alkhairi acikin wayoyin dakuma Social Media.
Dolene Mu kame daga barin abinda Zai Cutar mana da imaninmu dama Kuruciyarmu gaba daya.
Burin Turawan yamma akoda Yaushe Shine Muzama Malalata Mukasa komai Sai sun mana.
In iyayenmu basu ankaraddamu ba wataran Za’a iya wayar gari bazamu iyayin komaiba, Sai abinda Turawa Sukaso suyi damu, domin anriga da makara komai ayanzu nasu ake kwaikwayo. Anmanta da Cewa akwai Tsarin Rayuwa Islamiyya dakuma Christianity. Duk abinda Yahudu Sukazo dashi Shine Ake bi.
Idan da wasu iyayen Zasu duba Profile na Socil Media na Yaranau Musamman Facebook da Twitter dakuma Istagram da Tictok Wallahil Azim sai sun farfasa Wayoyin Yaransu. Yin hakan kuma abanza ne. Don zai je ga na Abokansa.
Mafita garemu Shine Adasawa Yara Tsoron Allah Acikin Zuqatansu kawai tahanyar Nasihohi da Addu’ar Shiriya domin Tafiya tayi Nisa. baza’a taba iya Hanasu rike wayoyi Dukansu inma babu ahannun wancan akwai ahannan wancan kuma Munsan Cewa ba’a Rowan Wuta. in aikin Shedancine kana Zaune za Akawomaka, kuma ba aganin Tsadarsa domin Akan iya Sayan plartform domin Series Film Amma daukar Nauyin Tafseer kuwa Sai cikin Azumi.
Domin Allah iyaye Akoyar da ‘ya’ya Tsoron Allah, Allah yakawo mana mafita Arayuwa.