NASIHA 12345

MABUƊAN RAYUWAR ZUCIYARKA.

“Zuciyar mutum wani lokacin takan yi rauni ta dalilin saɓon Allah da kuma barin aikata kyawawan aiyuka, wani lokacin kuma takan ƙarfafu ta dalilin aikata kyawawa da kuma kamewa daga munana”

Akwai ababe da dama waɗanda idan ka dimauci yinsu a rayuwarka, to tabbas inshaa Allahu zuciyarka kullum zata kasance cikin tabbatacciyar rayuwa kuma mai inganci da samun ƙarfi wajen bautar Allah da yaƙini dashi, misalin su sune kamar haka:-

🔹Tadabburin alƙur’ani mai girma.

🔹Yawan tsayuwar sallar cikin dare.

🔹Barin yin zalunci ga wasu.

🔹Barin yawan aiyukan zunubi.

🔹Da kuma taimakon bayin Allah.